Other

'nunar fari

Ma'ana

Kalmar nan "'nunar fari" tana nufin wani kaso ne na nunar fari na hatsi da kayan lambu da ake girba a kowanne lokacin girbi.

  • Isra'ilawa kan bada waɗannan nunar fari ga Allah a matsayin baiko na hadaya.
  • Hakanan ana amfani da wanan kalma a cikin Littafi mai Tsarki in an ambaci ɗan fari a matsayin ana amfani da ita sabo da wanan ɗan fari na iyalin to shi ne mai amfani da sunan iyalin.
  • Sabo da Yesu ya tashi daga matattu ana kiransa "nunar fari" na masu bi, amma kuma wata rana zai dawo a raye.
  • Masu bi cikin Kristi suma ana kiran su "nunar fari" na dukkan halitta, wanan na nuna wata dama ta musamman da kuma matsayi na waɗanda Yesu ya fansa su zama mutanensa.

Shawarwarin Fassara:

  • A cikin amfani da wanan kalma cikin sauƙi ita ce "kaso na farko" (na hatsi)" ko "kaso na farko."
  • In mai yiwuwa nemoron kalmar nan cikin salon magana a nuna mabambantan ma'anoni a ayoyi da bam da ban. Wanan ma zai nuna fahimtuwa tsakanin kalma ta zahiri da kuma amfani da salon magana.

(Hakanan duba: ɗan fari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 31:4-5
  • 2 Tassalonikawa 02:13
  • Fitowa 23:16-17
  • Yakubu 01:18
  • Irmiya 02:03
  • Zabura 105:36

'yanci, halin 'yanci, 'yantarwa, ikon kai, na kyauta, mutumum mai 'yanci, yardar kai, dama

Ma'ana

Kalmar nan "'yanci" ko "'yancin kai" tana nufin hali na rashin kasancewa a ƙangin bauta, ko duk wani abu da kan tauye 'yanci. wata kalma da ake mora a memakon "'yanci" ita ce "dama."

  • Batun nan na nufin a "'yantar da mutum" wato a samar da wata hanya da wani mutum ba zai ƙara zama a ƙangin bauta ba.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, waɗannan kalmomin akan fi yawan moron su ta salon magana domin a nuna yadda mai bi ya kuɓuta daga ikon zunubi.
  • Samun "dama" ko "'yanci" zai iya nufin zama da 'yanci na yin rayuwa ƙarƙashin ikon Ruhu mai Tsarki.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "'yanci" za'a iya fassara ta da kalmar da ke nuna ikon yin rayuwar 'yanci, wato rashin zama cikin "ƙangin bauta" ko "takura"
  • Kalmar "'yanci" ko "dama" za'a iya fassara ta da yanayi na kasancewa da "ikon kai ba tare da wata takura ba.".
  • Kalmar nan "'yantarwa" za'a iya fassara ta da aba mutum damar zama da 'yanci ko a "'yanto mutum daga bauta."
  • Mutumin da aka "'yantar" an sake shi kenan" ko kuma an "fitar da shi" daga ƙangin bauta.

(Hakanan duba: hani, bautarwa, bawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 04:26
  • Galatiyawa 05:1
  • Ishaya 61:1
  • Lebitikus 25:10
  • Romawa 06:18

'yantarwa

Ma'ana

Ma'anar "'yantarwa" shi ne furtawa a fili cewa wannan mutum bashi da laifi game da taka shari'a ko halin da bai dace ba wanda ake ƙarar sa akai.

  • Ana amfani da kalmar nan a Littafi Mai Tsarki wajen yin magana akan gafarta wa masu zunubi.
  • Yawancin lokaci ana magana ne akan rashin gaskiyar 'yantar da mugayen mutane da masu tawaye gãba da Allah.
  • A yin fasara za mu iya cewa, "furta rashin aibu" ko "shari'a bata same shi da laifi ba."

(Hakanan duba: gafartawa, laifi, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 25:1-2
  • Fitowa 21:28
  • Fitowa 23:07
  • Ishaya 05:23
  • Ayuba 10:12-14

'yar'uwa, 'yan'uwa mata

Ma'ana

'Yar'uwa talika ce mace wadda a ƙalla suka haɗa ɗaya daga cikin iyaye da wani. A na ce mata 'yar'uwa ga wannan mutumin ko shi ya zama ɗan'uwan ta.

  • A Sabon Alƙawari, "'yar'uwa" anyi amfani da ita sosai idan ana magana kan mace wadda ta kasance mai bi cikin Yesu Almasihu.
  • Wasu lokutan faɗar "'yan'uwa maza da mata" akan yi amfani da ita ga dukkan masu bada gaskiya cikin Almasihu, dukkan maza da mata.
  • A Littafin Tsohon Alƙawari Waƙar Suleman, " 'yar'uwa" ana nufin mace masoyiya ko abokiyar aure.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya fi kyau a fassara wannan kalmar da kalma mafi sauƙi da ake amfani da ita a yaren da nufin 'yar'uwa ta jini, sai dai idan kuma wannan ɗin zai bada ma'ana marar kyau.
  • Wasu hanyoyin domin fassara wannan zai iya haɗawa da "'yar'uwa cikin Almasihu" ko "'yar'uwa cikin ruhaniya" ko " matan da suka gaskata da Yesu" ko "'yan'uwa mata masu bada gaskiya."
  • Idan zai yiwu zai fi kyau ayi amfani da kalmar iyali.
  • Idan yaren na da kalmar mace a kalmar "mai bi", zai zama hanya mafi kyau domin fassara wannan.
  • Idan ana nufin matar da ake ƙauna, za a iya fassara wannan ta wurin amfani da kalmar mace ga "abar ƙauna" ko " masoyiya."

(Hakanan duba: ɗan'uwa cikin Almasihu, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:16-17
  • Maimaitawar Shari'a 27:22
  • Filimon 01: 02
  • Romawa 16:01

a bada aiki, an sanya

Ma'ana

Wannan kalma "a bada aiki" ko "an sa" manufar shi ne zaɓen wani domin ya aikata wata hidima musamman.

  • Annabi Sama'ila ya yi annabci cewa Sarki Saul zai "sa" samarin Isra'ila su yi bauta cikin sojoji.
  • Musa ya "ba" kowanne ɗaya daga cikin kabilar Isra'ila yankin ƙasar Kan'ana domin su zauna a cikinta.
  • A ƙarƙashin shari'ar Tsohon Alƙawari, wasu kabilun Isra'ila an sanya su su zama firistoci, masu zane, mawaƙa da magina.
  • Ya danganta ga nassin "sa wa" za a iya fassara shi a ce "bada" ko "zaɓa" ko "a zaɓa domin aikin."
  • Wannan kalma "an sanya" zai iya zama "zaɓaɓɓe" ko "an sa shi aiki."

(Hakanan duba: zaɓa, Sama'ila, Saul (Tsohon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:48
  • Daniyel 12:13
  • Irmiya 43:11
  • Yoshuwa 18:02
  • Littafin Lissafi 04:27-28
  • Zabura 078:55

a bada rahoto, rahontanai, an bada rahoto,

Ma'ana

Kalmar "rahoto" na manufar a faɗi wa mutane game da wani abin da ya faru, yawancin lokuta ana bada bayanin abin da ya faru. Rahoto abin da ake faɗi ne ana kuma iya rubutawa.

  • "Rahoto" na iya zama "faɗi" ko "yi bayani" ko "faɗi a dalla-dalla."
  • Faɗin nan "kada ka faɗi wa kowa wannan rahoto" ana iya cewa "kada ka yi magana da wani game da wannan" ko "kada ka gaya wa kowa game da wannan."
  • Haka kuma, ana fassara "rahoto" kamar "yin bayani" ko "bada labari" ko "bada kasafi," dukka ya danganta da yadda yanayin zancen yake.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 05:22-23
  • Yahaya 12:38
  • Luka 05:15
  • Luka 08:34
  • Matiyu 28:15

a rubuce yake

Ma'ana

Faɗar "kamar yadda a rubuce" ko "abin da aka rubuta" sun bayyana a wurare dayawa cikin Sabon Alƙawari kuma suna nufin umarnai da anabcen da aka rubuta cikin Litattafan Ibraniyanci.

  • Wani lokaci "kamar yadda aka rubuta" na bayyana abin da aka rubuta cikin Shari'ar Musa.
  • Wani lokacin kuma kalmar an ɗauko ne daga abin da wani cikin annabawa ya faɗi a Tsohon Alƙawari.
  • Ana iya fassara ta "kamar yadda aka rubuta cikin Shari'ar Musa" ko "kamar yadda annabawa suka rubuta tun dã" ko "abin da ya faɗi cikin shari'un Allah wanda Musa ya rubuta tun dã."
  • Wani kwatancin kuma shi ne a ajiye "a rubuce yake" a rubutun taƙaitaccen bayani abin da wannan ke nufi.

(Hakanan duba: doka, shari'a annabi, maganar Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 05:13-15
  • Ayyukan Manzanni 13:29
  • Fitowa 32:15-16
  • Yahaya 21:25
  • Luka 03:4
  • Markus 09:12
  • Matiyu 04:06
  • Wahayin Yahaya 01:03

a sama, can cikin samaniya

Ma'ana

Wannan furci "a sama" da "can cikin samaniya" maganganu ne dake nuffin "sama."

  • Wata ma'anar "can cikin samaniya" shi ne "mafificin ban girma."
  • Za a iya yin amfani da furcin a sauƙaƙe, haka, "cikin ƙolƙolin itace" ma'ana, "cikin itace mafi tsayi."
  • Wannan magana "a sama" ma'anarta can cikin sararin sama, kamar yadda sheƙar tsuntsu take can sama. A wannan yanayi za a iya fassarawa haka, "can sama cikin sarari" ko "a cikin dogon itace.
  • Kalmar nan "sama" zai iya zama wuri mai tudu ko mahimmancin mutum ko abu.
  • Wannan furci "daga can sama" za a iya fassra shi haka "daga sama."

(Hakanan duba: sama, girmamawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Makoki 01:13
  • Zabura 069:29

abin sha mai ƙarfi, abubuwan sha masu ƙarfi

Ma'ana

Wannan kalma "abin sha mai ƙarfi" na nufin abubuwan shan da aka gauraya suka zama giya a cikin su.

  • Giya akan yi tane daga kodai hatsi ko 'ya'yan itace da suke kaiwa ga harzaƙuwa.
  • Irin wannan "abin sha mai ƙarfin" sun haɗa da ruwan inabi, bammi, giya, da tuffar sida. A Littafi Mai Tsarki, ruwan inabi aka fi ambata a kowanne abin sha.
  • Firistoci da kowanne mutum da ya yi wata rantsuwa ta masamman kamar ta "ranzuwar Banaziri ko Naziranci" ba a basu izinin shan gaurayayyun abubuwan sha ba.
  • Wannan kalmar akan iya fassara ta da "gaurayayyen abin sha" ko "ruwan giya."

(Hakanan duba: inabi, Banaziri, rantsuwa, giya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ishaya 05:11-12
  • Lebitikus 10:09
  • Luka 01:14-15
  • Littafin Lissafi 06:03

Aike, Aiko, aikawa, aika waje, aikawa waje

Ma'ana

A "aike" shi ne sa wani ko wani abu ya je wani wuri. A "aika waje" na nufin wani ya ce da wani ya je aike ko wata manufa.

  • A koyaushe mutum wanda aka "aika" ansa shi ne ya yi wani aiki na masamman.
  • Magana kamar " aika ruwa" ko "aika annoba" na nufin "la'anta ta zo". Wannan irin maganar anfi amfani da ita akan Yahweh ne yake sa wannan ya auku.
  • Kalmar " aike" akan yi amfani da ita wurin magana kamar " aika magana" ko A "aika sako," wanda yake nufin ba wani sako ya gayawa wani.
  • A "aika" wani da "wani" abu na nufin "abã" da wannan abin ga wani ya "bã" wani, akan aika wannan da nisa domin wani ya karɓa
  • Yesu lokuta da dama ya yi amfani da wannan maganar " wanda ya aiko ni" yana nufin Yahweh Uba wanda ya, "aiko" shi duniya don ceton mutane. Wannan ma a fassara shi kamar wanda ya bada kai.

(Hakanan duba: zaɓa, fansa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:33-34
  • Ayyukan Manzanni 08:14-17
  • Yahaya 20:21-23
  • Matiyu 09:37-38
  • Matiyu 10:05
  • Matiyu 10:40
  • Matiyu 21:1-3

aiki, aikace-aikace, aikin ƙarfi, ma'aikaci, ma'aikata, aiki tuƙuru

Ma'ana

Kalmar aikin ƙarfi na nufin kowanne irin aiki tuƙuru.

  • Gabaɗaya dai aiki na ma'anar kowanne irin aiki dake buƙatar ƙarfi. Ana yawan cewa aikin nada wuya.
  • Ma'aikaci shi ne kowanne taliki dake kowanne irin aiki.
  • A turance, ana amfani da kalmar "aikin ƙarfi" kuma da nufin naƙuda. Amma a Hausa babu haka. Kalmar ciwon haihuwa naƙuda ake cewa. Wasu harsunan suna iya kasancewa da kalmomi daban daga wannan.
  • Hanyoyin fassara "aikin ƙarfi" zasu iya haɗawa da "aiki" ko "aiki tuƙuru" ko "aiki mai wuya" ko "ayi aiki tuƙuru."

(Hakanan duba: tuƙuru, zafin naƙuda)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 02:09
  • 1 Tasalonikawa 03:05
  • Galatiyawa 04:10-11
  • Yakubu 05:04
  • Yahaya 04:38
  • Luka 10:02
  • Matiyu 10:10

aiki, cikin naƙuda, ciwon naƙuda, zafin haihuwa, zafin haihuwar ɗa

Ma'ana

Macen dake "cikin naƙuda" tana fuskantar zafin dake kaiwa ga haihuwar ɗanta. Ana kiran waɗannan "ciwon naƙuda."

  • A cikin wasiƙarsa zuwa ga Galatiyawa, manzo Bulus ya yi amfani da wannan kalma a cikin misalai yana bayyana tsananin gwagwarmayarsa wurin taimakon 'yan'uwansa masubi zu ci gaba da zama kamar Almasihu.
  • Ana kuma amfani da misalin zafin naƙuda a Littafi Mai Tsarki a nuna yadda bala'o'i zasu zo a kwanakin ƙarshe suna kuma yawaita da tsanani akai-akai.

(Hakanan duba: naƙuda, kawakin ƙarshe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 04:19-20
  • Galatiyawa 04:19
  • Ishaya 13:08
  • Irmiya 13:21
  • Zabura 048:06
  • Romawa 08:22

akasiya

Ma'ana

Wannan kalma "akasiya" sunan wani ƙaramin itace ne ko a ce itace ne da yake toho a ƙasar Kan'ana tun zamanin dã; har wa yau suna nan da yawa a yankin.

  • Shi itacen akasiya kalarsa na lemu ne kuma ƙasa-ƙasa yake yana da tauri da jurewa, wannan yasa shi yana da amfani wajen kayayyakin gini.
  • Wannan itace ruɓa bata cinsa domin yana da tauri baya aje ruwa a jikinsa, yana kuma da baiwar kariya dake hana ƙwari lalata shi.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, an yi amfani da akasiya domin gina rumfar sujada da kuma akwatin alƙawari.

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, rumfar sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 10:3-4
  • Fitowa 25:3-7
  • Fitowa 38:6-7
  • Ishaya 41:19-20

akuya, awakai, fatar akuya, bunsurun azaze, 'yan awakai

Ma'ana

Akuya wata 'yar madai-daiciyar dabba ce da ke da ƙafafu huɗu wadda ta yi kama da tunkiya, kuma akan yi kiwon ta ne sabo da namanta da kuma madara. sabuwar haihuwar akuya ita ake kira "'yar akuya."

  • Kamar tumakai, awakai dabbobi ne masu muhimmanci domin miƙa hadaya, musamman a idin ƙetarewa.
  • Ko da yake awakai da tumakai suna da kamanci sosai, a waɗanan hanyoyin ne suka bambanta:
  • Awakai gashinsu sumul yake; tumaki kuma a yamutse nasu yake.
  • Wutsiyar akuya a tsaye take amma ta tunkiya lilo take ƙasa.
  • Har kulum tumakai kan so su tsaya tare da makiyayi, amma awakai sukan fi son zaman kansu kuma sukan yi yawo nesa da makiyayinsu.
  • A kwanakin Littafi Mai Tsarki, awakai su ne kan samar da madara a Isra'ila.
  • Ana amfani da fatar awakai domin yin rumfa da kuma yin jakkunan riƙe ruwan inabi.
  • A cikin Tsoho da kuma Sabon Alƙawari akan alamta awakai da mutane mara sa adalci, wataƙila sabo da yadda suke guduwa daga wurin mai kiwon su.
  • Isra'ilawa ma kan mori awakai su nuna alamar ɗaukan zunubi. Lokacin da aka yi hadaya da akuya, firist zai ɗora hannuwansa bisa akuyar akaoro na biyu wanan akuyar mai rai sai ya kora ta jeji a matsayin alamar cewa wanan akuaya na ɗauke da zunuban mutane.

(Hakanan duba: garke, hadaya, tumakai, adalci, ruwan inabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 12:3-4
  • Farawa 30:32
  • Farawa 32:10
  • Farawa 37:31
  • Lebitikus 03:12-14
  • Matiyu 25:33

al'ada, al'adu

Ma'ana

Kalmar "al'ada" na nufin wani abinda aka saba yi ko aikatawa na dogon lokaci wanda kuma ake barwa mutane na tsararraki masu zuwa.

  • Yawanci a cikin Littafi Mai Tsarki kalmar "al'adu" na nufin koyarwa da ayyukan sabo wanda mutane ke yi, ba shari'un Allah ba. Faɗar "al'adar mutane" ko "al'adar 'yan'adam" ya bayyana ta.
  • Faɗar kamar haka "al'adun dattawa" ko "al'adun ubanni" yana nufin ainihin al'adun Yahudanci da ayyukan da shugabannin Yahudanci suka ƙarawa sharu'un Allah waɗanda Allah yaba Isra'ilawa ta wurin Musa. Kodayake waɗannan ƙarin al'adu basu zo daga Allah ba, mutane sun zaci cewa dole suyi biyayya dasu domin su zama adalai.
  • Manzo Bulus ya yi amfani da kalmar "al'ada" ta hanya daban domin ya nuna koyarwa game da ayyukan Kiristoci da suka zo daga Allah da cewar shi da sauran manzanni sun koyar wa sabobbin masu bada gaskiya.
  • A zamanin yanzu, akwai al'adun Kiristoci da yawa da ba a koyar ba a cikin Littafi Mai Tsarki, a maimako sakamakon al'adun da aka karɓa ne a tarihi kuma ake aikatawa. Waɗannan al'adu a koyaushe a kwatantasu da hasken abin da Allah ya koya mana a cikin Littafi Mai Tsarki.

(Hakanan duba: manzo, gaskatawa, Kiristoci, kakanni, tsararraki, Bayahude, shari'a, Musa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tasalonikawa 03:6-9
  • Kolosiyawa 02:08
  • Galatiyawa 01:13-14
  • Markus 07:02
  • Matiyu 15:03

al'adu, koyarwa, imani iri-iri, ka'idoji, ilimi

Ma'ana

Kalmar nan "al'adu" ma'anarta mai sauƙi ita ce "koyarwa." Har kullum tana magana ne akan koyarwar addini.

  • Bisa ga koyarwar krista, al'adu na nufin dukkan wata koyarwa game da Allah Uba, Ɗa da ruhu mai tsarki- haɗe da halaiyarsa, nagartarsa, da kuma duk abin da ya yi.
  • Hakanan tana nufin dukkan wani abu da Allah ya koyawa krista game da yaddaza su yi zaman tsarki da ke ba shi ɗaukaka.
  • Kalmar nan "al,ada" a waɗansu lokutan ana amfani da ita don a ambaci koyarwar ƙarya ta addinan duniya waɗanda mutane suka ƙago. Wurin ya baiyana kalmar a fili.
  • Haka nan kalmar za'a iya fassara ta da cewa "koyarwa ce."

(Hakanan duba: koyi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 01:03
  • 2 Timoti 03:16-17
  • Markus 07:6-7
  • Matiyu 15:7-9

al'ƙalai, mahukunta

Ma'ana

Alƙali wani zaɓaɓɓen mutum ne wanda yake mahukunci game da shari'a.

  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, al'ƙalai sukan sasanta jayayya tsakanin mutane.
  • Ya danganta ga nassi, hanyoyin fassara wannan magana za su haɗa da "alƙali mai mulki" ko "wanda hukuma ta zaɓa" ko "shugaban birni."

(Hakanan duba: alƙali, shari'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 16:20
  • Ayyukan Manzanni 16:35
  • Daniyel 03:1-2
  • Luka 12:58

al'ul

Ma'ana

Wannan kalma "al'ul" wani babban itacen fir ne mai launi ja-ƙasa ƙasa. Kamar sauran itatuwan fir, yana da ƙaho da ganyaye masu tsini kamar allura.

  • Tsohon Alƙawari yawancin lokaci yakan yi magana akan itacen al'ul game da Lebanon, inda suka tsira da yawa.
  • An yi amfani da katakan al'ul domin gina haikali a Urshalima.
  • An kuma yi amfani da su domin hadayu da tsarkake baye-baye.

(Hakanan duba: itacen fir, tsantsa, hadaya, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 14:1-2
  • 1 Sarakuna 07:1-2
  • Ishaya 02:13
  • Zakariya 11:02

al'umma, al'ummai

Ma'ana

Al'umma babbar ƙungiyar mutane ce da suke da wasu sharuɗɗan mulki. Yawancin lokaci mutanen da suka zama al'umma sun fito ne daga zuriya ɗaya da kuma yare ɗaya.

  • Yawancin lokaci "al'umma" na da tsarin al'adunta da kuma iyakar ƙasarta.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki "al'umma" zata iya zama ƙasa (kamar Masar ko Itiyofiya), amma dai yawancin lokaci ana nufin ƙungiyar mutane ne, tunbane in ana ambatonsu da yawa. Da mahimmanci a duba nassi.
  • Al'ummai a cikin Littafi Mai Tsarki sun haɗa da waɗannan: Isra'ilawa, Filistiyawa, Asiriyawa, Babiloniyawa, Kan'aniyawa, Romawa, Girik, da dai sauransu.
  • Wani lokaci kalmar nan "al'umma" ana amfani da ita a kwatanta zuriyar wasu ƙungiyar mutane, kamar lokacin da Allah ya gaya wa Rebeka cewa 'ya'ya maza da zata haifa "al'umma biyu" ce da za su yi faɗa da junansu. Za a iya fassara wannan haka "za su kafa al'umma biyu" ko "kakannin ƙungiyar mutane biyu."
  • Wannan kalma da aka fassarata zuwa "al'ummai" wani lokaci ana amfani da ita a kira "waɗanda ba yahudawa ba" ko "mutanen da ba sa bauta wa Yahweh". Yawancin lokaci yadda aka yi ammfani da ita a nassi yakan fid da ma'anar a sarari.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, wannan kalma "al'umma" za a iya fassara ta haka "ƙungiyar mutane" ko "mutane" ko "ƙasa."
  • Idan yaren na da wata kalma domin "al'umma" da ya sha bamban da waɗannan to, sai suyi amfani da ita duk lokacin da ta sake maimaita kanta a cikin Littafi Mai Tsarki indai ya shiga nassi dai-dai kuma ba matsala.

Wannan kalma da ta nuna yawa "al'ummai" za a iya fassara ta a ce "ƙungiyar mutane."

(Hakanan duba: Asiriya, Babila, Kan'ana, Al'ummai, Girik, ƙungiyar mutane, Filistiyawa, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Taski:

  • 1 Tarihi 14:15-17
  • 2 Tarihi 15:06
  • 2 Sarakuna 17:11-12
  • Ayyukan Manzanni 02:05
  • Ayyukan Manzanni 13:19
  • Ayyukan Manzanni 17:26
  • Ayyukan Manzanni 26:04
  • Daniyel 03:04
  • Farawa 10:2-5
  • Farawa 27:29
  • Farawa 35:11
  • Farawa 49:10
  • Luke 07:05
  • Markus 13:7-8
  • Matiyu 21:43
  • Romawa 04:16-17

alade, aladu, gursuni, aladen jeji

Ma'ana

Alade wani dabba ne mai ƙafa huɗu, yana da kofato ana kuma kiwonsa domin nama. Ana kiran namansa "naman alade" Wani suna kuma da aka san shi da ita shi ne "gursuni."

  • Allah ya cewa Isra'ilawa kada su ci naman alade su kuma ɗauke shi marar tsarki. Har yau Yahudawa sun ɗauki aladu marasa tsarki kuma basa cin namansu.
  • Ana kiwon aladu a gonaki domin a sayar wa mutane naman.
  • Akwai wani irin alade da ba a kiwonsa a gona amma yana zama a jeji ne ana kiransa "aladen jeji." Aladun jeji suna da ƙahonni dabbobi ne masu hatsari da kuma ban razana.
  • Wani lokaci ana kiran manyan aladu "hogs" da Turanci.

(Hakanan duba: tsabta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 02:22
  • Markus 05:13
  • Matiyu 07:6
  • Matiyu 08:32

alkama

Ma'ana

Alkama wani irin hatsi ne da mutane ke shukawa domin abinci. A duk lokacin da Littafi ya ambaci "hatsi" ko "iri," yawancin lokuta ana manufar alkama ne ko ƙwayar iri.

  • Ƙwayar irin alkama ko hatsi na tsirowa ne a bisa kan dashen.
  • Bayan an girbe alkamar, ana rarrabe hatsin daga zangarniyar ta wurin sussukewa. Kan dashen alkamar ana kiransa da suna "haki" kuma ana zuba su a ƙasa domin dabbobi su kwanta bisa.
  • Bayan sussuka, ƙaiƙayin dake zagaye da irin ana rarrabe su daga hatsin ta wuri sheƙewa a kuma zubar da shi.
  • Mutane na niƙa tsabar alkama zuwa gãri, su kuma yi amfani da ita wurin yin gurasa.

(Hakanan duba: bali, ƙaiƙayi, hatsi, iri, sussuka, shiƙa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 27:36-38
  • Fitowa 34:21-22
  • Yahaya 12:24
  • Luka 03:17
  • Matiyu 03:12
  • Matiyu 13:26

alƙali, alƙalai

Ma'ana

Alƙali wani taliki ne wanda ke ɗaukar matakin menene dai-dai ko laifi sa'ad da mutane suka sami saɓani a tsakaninsu, musamman a al'amuran da suka shafi shari'a.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, yawanci ana kiran Allah Mai shari'a ko Mai hukunci domin shine Alƙali cikakke wanda ke ɗaukar mataki na ƙarshe game da abin da ke dai-dai ko laifi.
  • Bayan da mutanen Isra'ila suka shiga ƙasar Kan'ana kafin kuma su fara yin sarakunan da suka yi mulkinsu, Allah na zaɓar shugabanni da ake kira "alƙalai" su bida su a lokuttan tsanani. Yawanci waɗannan alƙalai hafsoshin sojoji ne waɗanda suka ceto Isra'ila ta wurin kayar da maƙiyansu.
  • Kalmar "alƙali" ana iya kiransa kuma "mai ɗaukar mataki" ko "shugaba" ko "mai kuɓutarwa" ko "gwamna," ya danganta ga nassin.

(Hakanan duba: gwamna, alƙali, shari'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:08
  • Ayyukan Manzanni 07:27
  • Luka 11:19
  • Luka 12:14
  • Luka 18:1-2
  • Matiyu 05:25
  • Rut 01:01

alwashi, rantsuwa, rantsewa da

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki rantsuwa alƙawari ne za a yi wani abu. Mutumin dake yin rantsuwar ana buƙatar ya cika wannan alƙawarin. Rantsuwa tana buƙatar a zama da aminci, da kuma gaskiya.

  • A majalisar shari'a, ma'shaidi yawancin lokaci yakan yi rantsuwa da alƙawari cewa dukkan abin da zai faɗi gaskiya ne kuma haka yake.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki wannan magana "rantsuwa" furta rantsuwa ake yi.
  • Wannan magana "rantsewa da" ma'anarta yin amfani ne da sunan wani abu ko sunan wani mutum domin ya zama tushen iko da aka kafa rantsuwar a kai.
  • Wani lokaci waɗannan maganganu ana amfani da su a gauraye, misali "rantsewa da rantsuwa."
  • Ibrahim da Abimelek sun rantse da rantsuwa lokacin da suka yi alƙawari ga juna game da amfani da wata rijiya.
  • Ibrahim ya cewa bawansa ya rantse zai samo wa Ishaku mata daga cikin 'yan'uwansa.
  • Allah ma ya yi rantsuwa da ya yi wa mutanensa alƙawarai.
  • A zamanin yau ma'anar wannan kalma "rantsuwa" shi ne "magana marar dacewa." Wannan ba ma'anarta ba ce a cikin Littafi Mai Tsarki.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta bisa ga nassi, "rantsuwa" za a iya fassarata a ce "jingina" ko "alƙawari."
  • Yin rantsuwa za a iya fassarawa haka "ɗaukar alƙawari" ko "jingina" ko mutum ya amince zai yi wani abu."
  • Wasu hanyoyin fassara "na rantse da sunana" shi ne "yin amfani da sunana domin tabbatar da alƙawarin."
  • "Rantsewa da sama da ƙasa" za a iya fassarawa zuwa "yin alƙawari ne cewa za a yi wani abu, ana kuma sanar da sama da ƙasa su tabbatar."
  • A tabbata fassarar "rantsuwa ko "wa'adi" bai da manufar zagi. Babu wannan ma'anar a cikin Littafi Mai Tsarki.

(Hakanan duba: Abimelek, alƙawari, wa'adi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 21:23
  • Farawa 24:03
  • Farawa 31:51-53
  • Farawa 47:31
  • Luka 01:73
  • Markus 06:26
  • Matiyu 05:36
  • Matiyu 14:6-7
  • Matiyu 26:72

amarya, amare, na amarya

Ma'ana

Amarya itace ta mace cikin bikin aure wadda ake aura wa miji, wato ango.

  • Wannan kalma "amarya" an misalta masu bada gaskiya ga Yesu da ita, wato ikilisiya.
  • Yesu shi ne misalin "ango" domin ikilisiya.

(Hakanan duba: ango, ikilisiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 22:16
  • Ishaya 62:5
  • Yowel 02:16

ambaliya

Ma'ana

Kalmar "ambaliya" a taƙaice tana nufin wani babban ruwa mai tsabagen yawa daya lulluɓe ƙasa bakiɗaya.

  • Wannan kalma kuma ana amfani da ita a cikin salon magana ko misali da nufin wani abu mai tsabagen yawa, musamman wani abin da ya faru nan da nan.
  • A zamanin Nuhu, mutane sun zama miyagu sosai har yasa Allah ya afko da ambaliyar ruwa ya rufe dukkan sararin duniya, har ya rufe ƙololuwar tsaunuka. Dukkan wanda baya tare da Nuhu cikin jirgi ya nutse. Dukkan sauran ambaliyoyi suna rufe taƙaitattun wurare ne.
  • Wannan kalma kuma na iya zama aikatau, kamar a "an rufe ƙasar da ambaliyar ruwan kogi."

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara ma'anar "ambaliya" a sarari zasu haɗa da "malalar ambaliyar ruwa" ko "babban ruwa."
  • A kwatantawar misali "kamar ambaliya" zai iya ajiye ainihin kalmar, ko ana iya amfani da misanyar kalma da zata nuna wani abin da ke nuna malalowar ambaliya a cikin sa, kamar kogi.

Ayoyin Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 11:10
  • Farawa 07:6-7
  • Luka 06: 46-48
  • Matiyu 07:24-27
  • Matiyu 24:37-39

amfani, riba, ana amfana, marar amfani

Ma'ana

Sau da yawa, wannan magana "riba" na nufin samun wani abu mai kyau ta wurin yin waɗansu ayyuka.

Wani abu nada "amfani" ga wani idan ya kawo masu abubuwa masu kyau ko idan ya taimake su kawo abubuwa masu kyau ga wasu mutane.

  • Amma masamman, wannan magana "riba" na magana ne akan kuɗin da ake samun ƙaruwa ta wurin cinikaiya. Kasuwanci yana da "riba" idan ya ribato kuɗi fiye da abin da aka kashe.
  • Ayyuka nada amfani idan sun kawo kyawawan abubuwa ga mutane.
  • 2 Timoti 3:16 ya ce dukkan Nassi yana da "amfani" wajen tsawatarwa da koyarwa da tarbiyar da mutane cikin aikin adalci. Wannan ya nuna cewa koyarwar Littafi Mai Tsarki na da taimako da kuma amfani domin koya wa mutane suyi rayuwa bisa ga nufin Allah.

Wannan magana "babu wata riba" na nufin wani abu ya zama ba amfani.

  • Ma'anar wannan shi ne rashin amfanin komai ko a kasa taimakon wani ya ci ribar wani abu.
  • Dukkan abin da ba zai zama da riba ba bai kamata a yi shi ba domin ba ya bada amfani.
  • Za a iya fassara shi haka, "ba amfani" ko "wofi" ko "ba zai amfana ba" ko "ƙasƙantaccen abu" ko "ba zai cika buri ba" ko "ba zai kawo riba ba."

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, wannan magana "riba"' za a iya fassara shi haka "sakamako" ko "taimako" ko "riba."
  • Wannan magana "ribato" za a iya fassara shi haka, "amfani" ko "mai kawo ƙaruwa" ko "zai taimaka."
  • Idan "an amfana" daga wani abu za a iya fassarawa haka "an ribato daga" ko "an ci ribar kuɗi daga" ko an sami taimako daga."
  • A sha'anin kasuwanci, wannan magana "riba" za a iya fassara ta da kalma ko furci mai ma'ana haka "ribar kuɗi da aka samu" ko "kuɗi mai tarin yawa" ko "ragowar kuɗi."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayuba 15:03
  • Littafin Misalai 10:16
  • Irmiya 02:08
  • Ezekiyel 18:12-13
  • Yahaya 06:63
  • Markus 08:36
  • Matiyu 16:26
  • 2 Bitrus 02:1-3

amincewa, tabbaci, tabbatacce, tabbatarwa

Ma'ana

Wannan kalma "amincewa" yana nufin tabbatarwa cewa wani abu gaskiya ne ko kuma haƙƙaƙewar cewa zai faru.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma "bege" yawancin lokaci ana nufin jira ne da sa zuciya domin wani abin da lallai zai faru. UBL yawancin lokaci takan fasara wannan haka "amincewa" ko "amincewa da lokacin gaba" musamman sa'ad da ana nufin tabbatar da karɓar abin da Allah ya alƙawarta wa masu bada gaskiya

ga Yesu.

  • Yawancin lokaci wannan kalma "amincewa" ana magana ne musamman akan cewa hakika masu bada gaskiya ga Yesu wata rana za su kasance tare da Allah a sama har abada.
  • Wannan furci " mu amince wa Allah" ma'anarta shi ne mu sa zuciya sosai za mu samu ko mu ɗanɗana abin da Allah ya alƙawarta.
  • "Zama da amincewa" tana da wannan ma'ana, wato gaskatawa da alƙawaran Allah ana aikatawa da tabbacin cewa Allah zai yi abin da ya ce zai yi. Wannan kalma kuma tana iya zama da ma'ana haka, gabagaɗi da kuma ƙarfin hali.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "amincewa" za a iya fassara ta haka, "tabbaci" ko "tabbatarwa sosai."
  • Wannan furci "ka yi ƙarfin hali" za a iya fassara shi zuwa, "dogara" ko "ka tabbatar akan abu" ko "ka sani ba shakka."
  • Wannan kalma "hakinka" zai iya zama da ma'ana haka "gabagaɗi" ko "tare da sakankancewa."
  • Bisa ga yadda za a yi amfani da kalmar a rubutu, ga yadda za a iya fassara "amincewa" za a ce, "tabbatarwa sosai" ko "sa zuciya" ko "hakikancewa."

(Hakanan duba: gaskatawa, gaskatawa, gabagaɗi, aminci, bege, dogara)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:


amini

Ma'ana

Wannan kalma "amini" ana nufin mutumin da yake tafiya da wani mutum ko wanda yake hulɗa da wani, kamar a cikin abokantaka ko aure.

  • Aminai sukan ɗanɗana halin rayyuwa tare, su ci tare, su tallafi juna su kuma ƙarfafa juna.
  • Ya danganta ga yadda za a yi amfani da shi cikin nassi, wannan kalma za a iya fasara ta da wata kalma ko furci da ma'ana haka, "aboki" ko "abokin tafiya" ko "mai tallafawa da ake tafiya tare."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 37:16
  • Ibraniyawa 01:09
  • Littafin Misalai 02:17
  • Zabura 038:11-12

ango, anguna

Ma'ana

A cikin bikin aure, ango shi ne namiji wanda zai auri amarya.

  • A al'adar Yahudawa a lokacin Littafi Mai Tsarki, ango shi ne uban biki shi wanda ya zo ya karɓi amaryar.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, sau da yawa ana ce da Yesu "ango" wanda wata rana zai zo domin "amaryarsa," wato ikilisiya.
  • Yesu ya misalta almajiransa da abokan ango waɗanda suke biki sa'ad da ango yana tare da su, amma za suyi baƙinciki sa'ad da ya tafi.

(Hakanan duba : amarya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ishaya 62:5
  • Yowel 02:15-16
  • Yahaya 03:30
  • Luka 05:35
  • Markus 02:19
  • Markus 02:20
  • Matiyu 09:15

annabin ƙarya, annabawan ƙarya

Ma'ana

Annabin ƙarya mutum ne da ke yiƙirarin cewa soƙonsa daga Allah ne.

  • Ba kasafai anabcin annabawan ƙarya ke cika ba. Wanan ya nuna cewa ba gaskiya bane anabcin nasu.
  • Annabawan ƙarya kan koyar da saƙonni da ke hannun riga da abin da littafi mai tsarki ya faɗa.
  • Kalmar nan za'a iya fassara ta da "mutumin da ke ƙaryar cewa shi ɗan saƙo ne na Allah" ko wani dake ƙaryar cewa yana faɗin maganar Allah ne."
  • Sabon Alƙawari yana koyar da cewa a ƙarshen zamani za'a sami annabawan ƙarya da yawa waɗanda za su yi ƙoƙari su ruɗi mutane da tunanin cewa su daga Allah suke.

(Hakanan duba: cika, annabi, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 04:1-3
  • 2 Bitrus 02:1
  • Ayyukan Manzanni 13:6-8
  • Luka 06:26
  • Matiyu 07:16
  • Matiyu 24:23-25

annoba, annobai

Ma'ana

Annobai wasu abubuwa ne masu faruwa da suke kawo wahala ko mutuwa ga mutane da yawa. Yawancin lokaci annoba cuta ce mai bazuwa nan da nan ta kuma sa mutane da yawa su mutu kafin a iya tsaida ita.

  • Annobai da yawa suna da dalilan aukuwa, amma wasu Allah ne yake aikowa domin hukunta mutane sabili da zunubi.
  • A zamanin Musa, Allah ya aiko annobai goma gãba da Masar domin a tilastawa Fir'auna ya saki Isra'ila su bar Masar. Waɗannan annobai sun haɗa da, ruwa ya koma ya zama jini, cututtukan fata, amfanin gonakai ƙwari suka lalatar, da ƙanƙara, aka kwana uku duhu baƙi ƙirin, da mutuwar 'ya'yan fari maza.
  • Za a iya fassara wannan haka "bala'i mai bazuwa" ko "cuta mai yaɗuwa" zai dai danganta ga yadda yake a nassi.

(Hakanan: ƙanƙara, Isra'ila, Musa, Fir'auna)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 24:13-14
  • Fitowa 09:14
  • Farawa 12:17-20
  • Luka 21:11
  • Wahayin Yahaya 09:18

annuri, masu annuri, yin annuri, aikin annuri

Ma'ana

Kalmar nan "annuri" tana nufin kasancewa da murna sabo da nasara ko kuma wata albarka ta musamman.

  • Yin "annuri" ya haɗa da jin nishaɗi kan wani abu na mamaki, mutum zai zama da annuri akan dukkan ayuka masu nagarta na Allah.
  • Wanan nishaɗi na iya sa mutum ya zama da taƙama sabo da wanan murnar da yake yi game da wanan nasarar ko kuma wadatar.
  • Wanan kalmar "annuri za'a iya fassara ta da "bikin murna" ko yin wani babban taro na murna."
  • Ya danganta ga wurin, kalmar nan annuri za'a iya fassara ta da "yabo cikin murna" ko "yin biki tare da yabon kai" ko "tunƙaho."

(Hakanan duba: fahariya, murna, farin ciki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 02:1
  • Ishaya 13:3
  • Ayuba 06: 10
  • Zabura 068:1-3
  • Zafaniya 02:15

asiri, asirai, asirtattun al'amuran gaskiya, ɓoyayyun al'amuran gaskiya

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan "asiri" na nufin wani abu da ba a sani ba ko kuma mai wuyar ganewa da Allah ke bayyanawa.

  • Sabon Alƙawari ya ce bisharar Almasihu asiri ne da ba a san shi ba a zamanan da suka wuce.
  • ‌Ɗaya daga cikin abubuwan da aka ambata asiri ne shi ne ɗayantakar Yahudawa da Al'ummai cikin Almasihu.
  • Za a iya fassara wannan ya zama "asiri" ko ɓoyayyun ayyuka ko "wani abin da ba a sani ba.

(Hakanan duba: Almasihu, Al'ummai, labari mai daɗi, Yahudawa, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Kolosiyawa 04:2-4
  • Afisawa 06: 19-2
  • Luka 08:9-10
  • Markus 04:10-12
  • Matiyu 13:11

azaba, azabta, azabtarwa, masu azabtarwa

Ma'ana

Kalmar "azaba" na nufin tsanantacciyar wahala. A azabtar da wani na nufin a sa wannan taliki ya sha wuya ta hanyar tsananin mugunta.

  • Wasu lokuta kalmar "azaba" na nufin jin zafi da wahala a zahiri. A misali, littafin Wahayin Yahaya ya bayyana irin azaba a zahiri da masu sujada ga "bisan" zasu sha a zamanin ƙarshe.
  • Shan wuya kuma na iya ɗaukar kamanni a zafi a ruhaniya da lamiri, kamar yadda Ayuba ya fuskanta.
  • Manzo Yahaya ya rubuta a Littafin Wahayin Yahaya cewa mutanen da basu bada gaskiya ga Yesu ba a matsayin mai ceton su zasu fuskanci azaba ta har abada a cikin ƙoramar wuta.
  • Wannan kalma za a iya fassarawa haka "tsanantacciyar wahala" ko "sanya wani ya sha wuya mai girma" ko "tsananin zafi." Wasu masu fassarar za su iya ƙara "a zahiri" ko "a ruhaniya" domin a fayyace ma'anar.

(Hakanan duba: bisan, har abada, Ayuba, Mai ceto, ruhu, wahala, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 02:08
  • Irmiya 30:20-22
  • Littafin Makoki 01:11-12
  • Luka 08:28-29
  • Wahayin Yahaya 11:10

azumi, yin azumi, ci gaba da azumi, azumi fa yawa

Ma'ana

Kalmar nan "yin azumi" tana nufin a dena cin abinci na tsawon wani lokaci, kamar na tsawon yini ko fiye. A waɗansu lokutan akan haɗa da shan ruwa.

  • Azumi kan temaki mutane su mai da hankali ga Allah su kuma yi addu'a ba tare da samun wani cikas ba game da shirin abinci da kuma cin abincin.
  • Yesu ya fallashi shugabannin addinin Yahudawa, sabo da yin azumi da dalilai na kuskure, sukan yi azumi domin sauran mutane suga suna azumi domin su yi tunanin cewa su adalai ne.
  • A waɗansu lokutan mutane kan yi azumi sabo da suna cikin baƙin ciki sosai, ko kuma damuwa game da wani abu.
  • Kalmar yin azumi za'a iuya fassara ta da "ƙauracewa cin abinci" ko kuma ƙin cin abinci."
  • Kalmar "azumi" za'a iya fassara ta da "lokaci na rashin cin abinci" ko "lokaci na "ƙauracewa abinci."

(Hakanan duba: shugabannin Yahudawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 21:8-10
  • 2 Tarihi 20:03
  • Ayyukan Manzanni 13:1-3
  • Yona 03:4-5
  • Luka 05:34
  • Markus 02:19
  • Matiyu 06:18
  • Matiyu 09:15

azurfa

Ma'ana

Azurfa wani ƙarfe ne mai ƙyalƙyali da daraja da ake amfani da shi ayi kuɗi, kayan ado, akwatina da abubuwan ado.

  • Akwatina da yawa da akan yi su tare da azurfa kofuna da butoci, da sauran abubuwan da ake amfani da su wurin girki, abinci, ko hidima.
  • Azurfa da zinariya anyi amfani da su wurin gina bagadin haikali. Haikalin dake Yerusalem yana da akwatunan da akayi su da azurfa.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, shekel abuna mai nauyi, kuma sayansa yana kan farashi na waɗansu shekel na azurfa. A cikin Sabon Alƙawari akwai kuɗin azurfa da akan auna da shekel.
  • 'Yan'uwan Yosef sun sayar dashi ya zama bawa akan shekel ashirin na azurfa.
  • Yahuda ya karɓi shekel talatin na azurfa ya bashe da Yesu.

(Hakanan duba: rumfar sujada, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 18:9-11
  • 1 Sama'ila 02:36
  • 2 Sarakuna 25:13-15
  • Ayyukan Manzanni 03:06
  • Matiyu 26:15

ba dai-dai ba, ya zalunci, zãlunce, kuskuren, azzãlumi, yi ba dai-dai ba, a musguna, an musguna, cuci, zafi, rauni, mai kawo rauni

Ma'ana

Yi wa wani "ba dai-dai ba" na nufin ka yiwa wannan mutum rashin adalci da rashin gaskiya.

  • Kalmar "musguna" na nufin aikatawa ba dai-dai ba ko cikin garaje ga wannan mutum, a haddasawa wani rashin ji daɗi a zahiri da cikin lamiri.
  • Kalmar "cuci" na bayyana yiwa wani rauni. Yawancin lokutai ana amfani da ita a nuna jin "rauni na jiki."
  • Ya danganta da nassin, waɗannan kalmomi za a iya fassarasu a matsayin "ayi wa wani ba dai-dai ba" ko "a nuna rashin adalci" ko "a cutar da wani" ko "a nuna masa cutarwa" ko "rauni."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:26
  • Fitowa 22:21
  • Farawa 16:05
  • Luka 06:28
  • Matiyu 20:13-14
  • Zabura 071:13

ba'alumme, al'ummai

Ma'ana

A lokacin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma ana amfani da ita a fassara mutanen dake bautar gumaku maimakon Yahweh.

  • Duk abubuwa game da mutanen nan, kamar su bagadan da suke sujada, al'adunsu na addini, da irin bangaskiyarsu, ana kiransu "al'ummanci."
  • Ayyukan sujadar Al'ummai ga abin da suka gaskata ya haɗa da bautar gumaku da hallitu.
  • Wasu addinan al'ummai sun haɗa har da fasikanci da yanka mutane a cikin sujadarsu.

(Hakanan duba: bagadi, gumaka, hadaya, sujada, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 10:20-22
  • 1 Korintiyawa 12:1-3
  • 2 Sarakuna 17:14-15
  • 2 Sarakuna 21:4-6

bacci, ayi bacci, anyi bacci, yin bacci, mai bacci, rashin bacci, jin bacci

Ma'ana

Waɗannan kalmomi za su samar da ma'anoni da yawa da suka danganci mutuwa.

  • Yin "barci" ko "kasancewa "cikin bacci" kan zama misalin ma'anar "mutuwa."
  • Batun "jin bacci" na nufin fara bacci, ko, misalin mutuwa.
  • A "yi bacci da ubannin wani" na nufin a mutu kamar yadda kakanni suka yi, ko a mutu kamar kakanni.

Shawarwarin Fassara:

  • A "ji bacci" akan fassara shi da " nan da nan aji bacci" ko "a fara bacci" ko " a mutu," ya danganta da ma'anarsa.
  • Lura: yana da mahimmanci ayi amfani da misalin maganar dake cikin wannan in da mai sauraro bai fahimci ma'anar ba. Misali, da Yesu ya ce da almajiransa La'azaru "bacci" yake yi sun ɗauka da gaske baccin yake yi. A wannan wurin, ba zai bada ma'ana ba idan aka fassara shi da "ya mutu."
  • Waɗansu yarurrukan na iya samun banbanci ga mutuwa ko macewa da za a iya amfani da ita a maganar "bacci" da "yin bacci" ba zai bada ma'ana ba.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 18:27-29
  • 1 Tasalonikawa 04:14
  • Ayyukan Manzanni 07:60
  • Daniyel 12:02
  • Zabura 044:23
  • Romawa 13:11

bagadin turare, turaren bagadi

Ma'ana

Bagadin turare wani sassaƙa ne daga itace wanda firist zai ƙona turare a matsayin baiko ga Allah. Ana kuma kiransa bagadin zinariya.

  • Bagadin turare an yi shi ne da katako, samansa da gefunansa an dalaye su da zinariya. Tsawonsa kimamin rabin mita ne, faɗinsa ma rabin mita ne, zurfinsa mita guda ne.
  • Da farko an ajiye shi a cikin rumfar sujada. Sa'an nan aka ajiye shi cikin haikali.
  • Kowacce safiya da kuma yammaci firist zai ƙona turare akai.
  • Za a iya fasara shi haka "bagadi domin ƙona turare" ko, "bagadin zinariya" ko, "wurin ƙona turare" ko, "teburin turare."

(Hakanan duba: turaren ƙonawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 01:11-13

baiko na hatsi, baye-baye na hatsi

Ma'ana

Baiko na hatsi kyauta ce garin alkama ko sha'ir da akan ba Allah, a mafi yawan lokuta bayan baiko na ƙonawa.

  • Hatsin da za'a yi amfani da shi domin baiko na hatsi dole ya zama an niƙa shi da laushi sosai. Waɗansu lokutan akan dafa shi kafin a miƙa shi, amma a waɗansu lokutan akan bar shi a hakanan ba tare da an dafa ba.
  • A kan ƙara mai da gishiri garin alkamar, amma ba tare da yisti ba ko zuma.
  • Wani kaso na baiko na hatsi akan ƙone wani kason kuma firistoci ne ke ci.

(Hakanan duba: baiko na ƙonawa, baiko na laifi, hadaya, baiko na zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 23:27-29
  • Fitowa 29:41-42
  • Littafin Alƙalai 13:19
  • Lebitikus 02:2

baiko na laifi, baye-baye na laifi

Ma'ana

Baiko na laifi baiko ne ko kuma hadaya da Allah ya buƙaci Ba'isra'ile ya yi idan ya yi wani laifi cikin tsautsayi kamar rashin nuna ladabi ga Allah ko ɓata mallakar wani.

  • Wanan baikon ya haɗa da hadayar dabbobi da biyan hakin yin zunubi da zinariya da azurfa, ko kuɗi
  • Bugu da ƙari, mutumin da ya yi laifin shi ne ke da haƙin biyan duk wata ɓarnar da aka yi.

(Hakanan duba: baiko na ƙonawa, baiko na hatsi, hadaya, baiko na zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 06:3
  • 2 Sarakuna 12:16
  • Lebitikus 05:5-6
  • Littafin Lissafi 06:12

baiko na sha

Ma'ana

Baiko na sha hadaya ce ga Allah wadda ta ƙunshi zuba ruwan inabi akan bagadi. Akan fi yawan miƙa ta ne tare da baiko na ƙonawa da baiko na hatsi.

  • Bulus ya nuna ransa a matsayin kamar baikon sha da ake zubawa. Wanan ya nuna cewa ya sadaukar da rayuwarsa dukka ga bautar Allah da kuma baiyanawa mutane labarin Yesu, duk da yake ya san cewa zai sha tsanani watakila ma a kashe shi sabo da hakan.
  • Mutuwar Yesu akan gicciye ita ce ainahin hadaya ta sha, kamar yadda aka zubar da jininsa akan gicciye sabo da zunubanmu.

Shawarwarin Fassara:

  • Wata hanya kuma ta fassara wanan ita ce "baiko na sabon 'ya'yan inabi"
  • Da bulus ya ce ana tsiyaye shi kamar baiko na ruwan inabi" za' iya fassarta shi da na sadaukar da kaina ne ɗungun domin koyar da saƙon Allah ga mutane, kamar dai yadda ake tsiyaye baiko na sha baki ɗaya akan bagadi."

(Hakanan duba: baio na ƙonawa, baiko na hatsi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 25:29
  • Ezekiyel 45:16-17
  • Farawa 35:14
  • Irmiya 07:16-18
  • Littafin Lissafi 05:15

baiko na yardar rai, baye-baye na yardar rai

Ma'ana

Baiko na yardar rai wata irin hadaya ce ga Allah wadda Shari'ar Musa bata bukata ba. Zaɓi ne na mutum ya bada wanan baiko.

  • Idan wanan baikon yardar ran ta dabba ce za'a miƙa hadaya to in dabbar tana da ɗan wani lahani ba damuwa,yun da yake zaɓin mutum ne kuma bayarwa ce ta yardar rai.
  • Isra'ilawa suka ci hadayar dabbobi a matsayin wani sashe na bikin idi.
  • A lokacin bayar da baikon yardar rai shi ne a lokacin da Isra'ilawa ke murna wanan ya nuna girbi ya yi kyau domin mutane na da wadataccen abinci.
  • Littafin Ezra ya baiyana ire-iren baiko na yardar rai da aka kawo domin sake gina haikali. Waɗanan baye baye sun haɗa da zinariya da azurfa, kuɗi, da daruna da sauran kayayyakin da aka yi da zinariya da azurfa.

(Hakanan duba: baiko na ƙonawa, Ezra, idi, baiko na hatsi, baiko domin laifofi, shari'a, baiko domin zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 29:6
  • 2 Tarihi 35:7-9
  • Maimaitawar Shari'a 12:17
  • Fitowa 36:2-4
  • Lebitikus 7:15-16

baiko na zumunci, baye-baye na zumunci

Ma'ana

A cikin Tsohon Alkawari "baiko na zumunci"wata irin hadaya ce da akan bayar sabo da dalilai daban da ban, kamar yi wa Allah godiya ko kuma cika wa'adi.

  • Wanan baikon na bukatar hadayar dabba da zata iya zama mace ko namiji. Wanan ta bambanta da baiko na ƙonawa, da ke bukatar dabba namiji.
  • Bayan an bayar da kaso na hadayar Allah, sai shi mutumin da ya kawo hadayar zumunci ya raba naman tare da firistoci da sauran Isra'ilawa.
  • Akwai abinci da ke tattare da wanan baikon wanda ya haɗa da gurasa marar yisti.
  • A waɗansu lokuta ana kiran ta "baiko na salama."

(Hakanan duba: baikon ƙonawa, cikawa, baiko na hatsi, baiko na laifi, baiko na salama, firist, hadaya, gurasa marar yisti, wa'adi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 21:25-27
  • 2 Tarihi 29:35
  • Fitowa 24:5-6
  • Lebitikus 03:3-5
  • Littafin Lissafi 06:13-15

baikon hatsi, baye-bayen hatsi, baye-bayen gari

Ma'ana

"Baikon gari" ko "baikon hatsi" hadaya ne ga Allah na tsaba ko waina da aka yi da garin hatsi.

  • Wannan magana "abinci" ana nufin hatsi da aka niƙa ya zama gari.
  • Akan kwaɓa garin da ruwa ko mai domin ayi bugaggiyar waina. Wani lokaci ana baɗa mai akan wainar.
  • Irin wannan baiko yawancin lokaci ana miƙa shi da baiko na ƙonawa.

(Hakanan duba: baiko na ƙonawa, hatsi, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 44:30-31
  • Yowel 02:14

baikon ƙonawa, baye-bayen, baiko na wuta

Ma'ana

Wannan "baikon ƙonawa" wata irin hadaya ce ga Allah da ake ƙonawa ƙurmus da wuta akan bagadi. Ana miƙa shi domin ayi kaffara domin zunuban mutane. Ana kiransa kuma "baiko na wuta."

  • Dabbobin da ake amfani da su domin wannan baiko yawancin lokaci tumaki ne ko awaki amma bijimai da tsuntsaye ma ana yi da su.
  • Akan ƙona duk dabbar a wannan baikon sai ko dai fatar. akan ba firist fatar.
  • Allah ya umarci mutanen Yahudawa su miƙa baye-baye na ƙonawa sau biyu a rana.

(Hakanan duba: bagadi, kaffara, maraƙi, firist, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 40:5-7
  • Farawa 08:20
  • Farawa 22:1-3
  • Lebitikus 03:05
  • Markus 12:33

baikon salama, baye-baye na salama

Ma'ana

"Baikon salama" ɗaya ne daga cikin hadayun baye-bayen da Allah ya umarci Isra'ilawa suyi. Wani lokaci ana ce da shi "baiko domin godiya" ko "baiko na zumunta."

  • Wannan baiko ya ƙunshi yin hadayar dabbar da bata da lahani, akan yayyafa jinin dabbar akan bagadi, a kuma ƙona kitsen, da kuma sauran gaɓoɓin dabbar dabam.
  • ‌Ƙari bisa wannan hadayar akwai baikon waina marar gami da mai gami, wanda za a ɗibiya bisa baikon ƙonawa a ƙona.
  • Da firist da mai miƙa hadayar an yardar masu su ci daga cikin abincin da aka miƙa.
  • Wannan baiko ya kwatanta zumuncin Allah da mutanensa.

(Hakanan duba: baikon ƙonawa, zumunta, baiko na zumunta, baikon na hatsi, firist, hadaya, gurasa marar gami)

Wuraren da ake samunsa a cikin Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila13:8-10
  • Ezekiyel 45:16-17
  • Yoshuwa 08:30-32
  • Lebitikus 09:3-5
  • Littafin Misalai 07:13-15

baikon zunubi, baye-baye na zunubi

Ma'ana

"Baikon zunubi" na daga cikin hadayu da Yahweh ya umarci Isra'ila su yi.

  • Wannan baikon ya haɗa da hadayar maraƙi, a ƙona jininsa da kitsensa a kan bagadi, a kuma ɗauki sauran jikin dabbar a ƙone ta a wajen sansanin Isra'ilawa.
  • Dukkan ƙone wannan dabbar na nuna yadda Yahweh ya je da tsarki da kuma yadda zunubi yake da razanarwa.
  • Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa idan ana so a tsarkaka daga zunubi, dole a zub da jini don ya biya tamanin zunubin da akayi.
  • Hadaya da dabba bazai kawo gafarar zunubi ta har abada ba.
  • Mutuwar Yesu akan gicciye ta biya hukuncin zunubi, na dukkan lokaci. Shi ne cikakken baikon zunubi.

(Hakanan duba: bagadi, saniya, gafara, hadaya, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 29:20-21
  • Fitowa 29:35-37
  • Ezekiyel 44:25-27
  • Lebitikus 05: 11
  • Littafin Lissafi 07:15-17

baka da kibiya, bakoki da kibau, baka

Ma'ana

Wannan wani irin makami da ya kunshi harbi da kibau daga baka mai igiya. A lokacin Littafi Mai Tsarki akan yi amfani da shi wajen yaƙar abokan gãba da kuma kisan dabbobi don abinci.

  • Akan yi baka da itace, ƙashi, ƙarfe, ko wasu abubuwa masu tauri, kamar ƙahon barewa. Yana da siffar tankwarewa ana kuma jan sa da ƙarfi da igiyar zare ko igiyar inabi.
  • Kibiya aba ce mai jikin kara da kai mai tsini a ɗaya karshen karan. A zamanin dã ana yin kibiya da kayayyaki daban-daban kamar su itace, ƙashi, dutse, ko ƙarfe.
  • Mafarauta da mayaƙa sune suka fi amfani da bakoki da kibau.
  • Wannan kalma "kibiya" wani lokaci ana amfani da ita a yi misali a cikin Littafi Mai Tsarki zai iya zama hari daga maƙiya ko hukuncin Allah.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 21:16
  • Habakuk 03:9-10
  • Ayuba 29:20-22
  • Littafin Makoki 02:04
  • Zabura 058:6-8

Bakarariya, bushewa

Ma'ana

Idan wata "bakarariya" ce ana nufin bata haihuwa kuma bata 'ya'ya.

  • ‌Ƙasar da take bakarariya bata iya fitar da tsire-tsire.
  • Matar dake bakarariya itace wadda bata iya ɗaukar ciki ko ta haifi yaro.

Shawarwarin Fassara:

  • Sa'ad da aka fassara ƙasa da kalmar nan "bakarariya" za a iya fassara ta da ta zama "marar taki" ko "marar 'ya'ya" ko "marar shuki."
  • Idan ana faɗi game da bakarariyar mace, za a iya yin fassara haka "marar ɗa" ko "bata iya haihuwar 'ya'ya" ko "bata iya ɗaukar cikin yaro."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 02:5
  • Galatiyawa 04:27
  • Farawa 11:30
  • Ayuba 03:07

baƙon haure, baƙin haure, bare, na ƙasar waje, baƙo daga ƙasar waje, bãƙi 'yan ƙasar waje

Ma'ana

Kalmar nan "baƙo ɗan ƙasar waje" tana nufin wani mutum da ke zama a ƙasar da ba tasa ba.Wani sunan da ake kiran sa da shi shi ne "baƙon haure."

  • A cikin Tsohon Alƙawari, wanan kalmar ana moron tadomin ambaton duk wani mutum da ya zo daga wani jinsin mutane na daban ya zo ya zauna a cikin waɗanda ba jinsa ba.
  • Hakanan baƙo ɗan ƙasar waje mutum ne wanda harshensa da al'adarsa sun bambanta da na wani yanki.
  • Misali, lokacin da Na'omi da iyalinta suka je Mowab, sun zama bãƙi a can. Bayan Na'omi da Rut sun koma Isra'ila sai Rut ta zama "baƙuwa" domin ita ba asalin 'yar Isra'ila ba ce.
  • Manzo Bulus ya faɗawa Afisawa cewa kafin su san Kristi, su "bãƙi ne" ga alƙawarin Allah.
  • A waɗansu lokuta "bãƙo" akan fasarta shi da "zayayye," amma wanan ba wai yana magana akan baƙuwar fuska bane kawai.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 02:17
  • Ayyukan Manzanni 07:29-30
  • Maimaitawar Shari'a 01:15-16
  • Farawa 15:12-13
  • Farawa 17:27
  • Luka 17:18
  • Matiyu 17:24-25

bali

Ma'ana

Wannan kalma "bali" sunan wata tsaba ce da ake amfani da ita wajen yin waina.

  • Shi tsiron bali yana da kara mai tsawo da kai a bisansa inda ƙwayoyin suke fita ko girma.
  • Bali ya fi yi da kyau a yanayi mai ɗumi saboda haka ake girbinsa a farkon damina.
  • Sa'ad da aka casa bali, za a raba tsabar da ake ci da ƙaiƙayinta marar amfani.
  • Tsabar bali kanta za a niƙata ta zama gari, sa'annan a kwaɓa ta da ruwa ko mai a yi waina.
  • idan ba a san bali ba, za a iya fasara shi haka "hatsin da ake kira bali" ko "hatsin bali."

(Hakanan duba: hatsi, sussuka, alkama)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 11:12-14
  • Ayuba 31:40
  • Littafin Alƙalai 07:14
  • Littafin Lissafi 05:15
  • Wahayin Yahaya 06:06

banmamaki, abin banmamaki

Ma'ana

Wannan kalma "ban mamaki" yana nuna mamaki na girmamawa da ya zo daga ganin wani gagarumin abu, da iko, da kuma ƙasaita.

  • Wannan kalma "ban mamaki" yana nuna wani mutum ko wani abu dake kawo ɗoki mai razanarwa.
  • Wahayin ɗaukakar Allah wanda annabi Ezekiyel ya gani yana da "ban mamaki" ko "mai kawo mamaki."
  • Ga yadda mutum ke nuna mamaki idan ya ga zatin Allah: tsoro, sunkuyar da kai ko durƙusawa ƙasa, a rufe fuska, da kuma rawar jiki.

(Hakanan duba: tsoro, ɗaukaka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 17:21
  • Farawa 28:16-17
  • Ibraniyawa 12:28
  • Zabura 022:23
  • Zabura 147:4-5

banza, na banza, wofi, fanko, marar amfani, marar ma'ana

Ma'ana

Kalmar "banza" na bayyana wani abin dake marar amfani ko wanda bashi da manufa. Abubuwan banza fanko ne da kuma rashin daraja.

  • Kalmar "na banza" na bayyana abin dake mai rashin amfani ko fanko. Tana iya nufin girman rai ko fãɗin rai.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, wasu allolin ana kwatanta su da abin banza da baza su iya kuɓutarwa ko su yi ceto ba. Abin wofi suke basu kuma da wani amfani ko manufa.
  • Idan aka yi wani abu "a banza" wannan na nufin babu wani sakamako mai kyau daga cikinsa. Wannan al'amari bai biya buƙata da komai ba.
  • A "gaskata a banza" na nufin gaskatawa ga abin da ba gaskiya ba kuma yana kawo sa ran da babu bege.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, kalmar "banza" za a iya fassarawa haka "wofi" ko "marar amfani" ko "marar bege" ko "marar daraja" ko "marar ma'ana."
  • Wannan faɗar "a banza" za a iya fassarawa haka "marar sakamako" ko "babu sakamako" ko "domin babu dalili" ko "babu manufa."
  • Kalmar "banza" za a iya fassarawa haka "girman kai" ko "babu wani abin daraja" ko "rashin bege."

(Hakanan duba: allolin ƙarya, isasshe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 15:1-2
  • 1 Sama'ila 25:21-22
  • 2 Bitrus 02:18
  • Ishaya 45:19
  • Irmiya 02:29-31
  • Matiyu 15:09

basira, lafazi, tattali

Ma'ana

Wannan magana "basira" yana fassara mutumin dake tunani mai zurfi game da ayyukansa sa'an nan ya ɗauki mataki mai hikima.

  • Yawancin lokaci "basira" na nufin iya yanke shari'a ne game da abubuwan dake buƙatar aikatawa, kamar sarrafa kuɗi ko dukiya.
  • Koda shi ke "basira" da "hikima" sun zo kusan ɗaya a ma'ana, yawancin lokaci "hikima" ta haɗa kowanne ɓangare kuma tafi nunawa akan abubuwan addini tsarin rayuwa.
  • Ya danganta ga nassi, za a kuma iya fassara "basira" haka "gwani" ko "hankali" ko "hikima."

(Hakanan duba: wayau, ruhu, hikima)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Misalai 08:4-5
  • Littafin Misalai 12:23-24
  • Littafin Misalai 27:12

bauta, 'yan bauta, bautattu

Ma'ana

Kalmar nan "bauta" tana nufin a tilastawa wani ya zauna a wani wuri nesa da ƙasarsa ko gidansa.

  • A kan tura mutane bauta domin horo ko dalilai na siyasa.
  • Mutanen da a ka mallake su a kan kwashe su zuwa ƙasar da ta mallake su domin su yi musu aiki.
  • "'Yan bautar Babila" ('yan bauta) wani lokaci ne a cikin tarihin Littafi mai Tsarki a lokacin da a ka kwashe Yahudawa zuwa bauta Babila,an tilasta musu su zauna a Babila wadda ya kai shekaru saba'in.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan za'a iya fassara ta da "kora can" ko a hana mutum zama."
  • Kalmar nan "bauta" za'a iya fassara ta da "korawa na wani lokaci" ko "lokacin da aka hana wa mutum "'yanci na kewayawa"
  • Hanyoyin Fassara "'yan bauta" sun haɗa da "mutane da aka kwashe zuwa bauta", ko "mutanen da suka je bauta babila."

(Hakanan duba: Babila, Yahuda)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 24:14
  • Daniyel 02:25-56
  • Ezekiyel 01:1-3
  • Ishaya 20:4
  • Irmiya 29:1-3

bautacce, bautatu, wanda aka bautar, kamamme, ƙangin bauta, kamammu, haɗawa

Ma'ana

A "bautar" da wani na nufin a tilastawa mutum ya bauta wa ubangijinsa ko shugabanci na ƙasa. A bautar wanan na ƙara nuna cewa a kasance ƙarƙashin biyarwar wani.

  • Mutumin da ke cikn bauta tilas ne ya bauta wa waɗansu ba tare da an biya shi ba kuma ba shi da 'yancin yin abin da yake so'
  • Hakan nan bautarwa na nufin a ƙwace'yancin mutum.
  • Wata ma'ana kuma ta "ƙangin bauta" ita ce a mayar da mutum "bawa".
  • A cikin salon magana, mutane sun kasance ƙarƙashin ƙangin "bautar zunub" har sai da Yesu ya zo ya'yantar da mu daga ikon zunubi.
  • Sa'ad da mutum ya karɓi sabon rai a cikin Almasihu, ya dena zama bawan zunubi, amma ya zama bawa ga aikin adalci.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "bautarwa" a'a iya fassara ta da cewa a sa mutum ya rasa 'yanci" ko kuma ya "bautawa wasu" ko asa wani a ƙarƙashin waɗansu."
  • Ƙaulin nan a "bautar ga wasu" ko asa sa wani a ƙanginbauta" ko kuma a "bautar da wani ta hanyar tilastawa."

(Hakanan duba:'yanci, adalci, bawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 04:3
  • Galatiyawa 04:24-25
  • Farawa 15:13
  • Irmiya 30:8-9

bawa, bayi, bauta, yin bauta, abokan bauta, bauta, yin hidima, hidimomi, hidimar ganin ido

Ma'ana

Kalmar "bara" na nufin "bawa" tana kuma nufin mutumin da yake yi wa wani mutum aiki, ko da son shi ko kuma da tilastawa. waɗannan irin abubuwan da suka kewaye wannan kalma sune suka bada cikakkiyar ma'anar ko mutumin bara ne ko bawa. kalmar " bawa" na nufin yin abu don taimakawa wasu mutane. Zai iya kuma zama "yin sujada". A cikin Littafi Mai Tsarki akwai karancin banbanci tsakanin bara da bawa kamar yadda muke da su a yau. Barori da bayi dukka na da matuƙar amfani a gidan iyayen gidansu kuma da yawa a kan ɗauke su kamar iyalan gidan. Yawancin lokuta bara kan zabi ya zama bara na har abada ga ubangidansa.

  • Bawa wani irin bara ne da kan zama mallakar mutumin da yake yi masa aiki. Mutumin da ya sawo bawan yana kiransa "na sa" ko "ubangida". wadan iyayen gidan sukan zauna da bayinsu cikin ƙunci, amma waɗansu sukan zauna da su cikin lumana, a matsayin bayin da suma suna ɗaya daga cikin iyalin gidan.
  • A zamanin dă mutane kanyi niyya da kansu su zama bayin mutumin da yake binsu kuɗi domin su iya biyan wannan bashin ga mutumin.
  • A nassin mutumin da yake yiwa bãƙi hidima kuma wannan na nufin " damuwa da" ko " bada abinci ga" ko " samar da abinci ga". lokacin da Yesu ya faɗi wa almajiransa su "ba" da kifin ga mutane, za a iya fassara wannan da. " rarrabawa" ko " badawa" ko "bayarwa".
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, Kalmar "Ni bawanka ne" anyi amfani da ita a matsayin alamar girmamawa da hidima ga mutumin da yake sama da kai kamar sarki. Ba ana nufin mai maganar shi ainihin bawa ba ne.
  • Kalmar "bauta" za a iyi fassara ta da "yin hidima ga" ko "yin aiki ga" ko "kula da" ko " biyayya" ya danganta da nassin.
  • A Tsohon Alƙawari, annabawan Yahweh da sauran mutane da suke bautar Yahweh ana kiransu "bayinsa".
  • A "bautawa Yahweh"ana iya fassara shi da " yin bauta da biyayya ga Yahweh" ko "yin aikin da Yahweh ya Umarta."
  • A Sabon Alƙawari, mutanen da suka yi biyayya ga Yahweh ta wurin bada gaskiya ga Almasihu an kira su " bayinsa".
  • A "samar da abinci" na nufin kawo abinci ga mutane waɗanda suka zauna a tebura, ko bakiɗaya domin a raba abinci."
  • Mutane waɗanda suke koyar da waɗansu game da Yahweh na cewa suna bautawa Yahweh da waɗanda suke koyarwa.
  • Manzo Bulus ya rubuta wa kiristoci na Korintiya game da yadda suka "bautawa" tsohon alƙawari. Wannan na nufin biyayya da shari'un Musa. Yanzu suna "bauta" a sabon alƙawari. Wato domin Yesu ya bada kansa bisa gicciye, masu gaskatawa da Yesu sun sami dama ta wurin Ruhu Mai Tsarki su gamshi Yahweh su kuma yi zaman tsarki.
  • Bulus ya yi magana kan ayyukansu game da "hidimarsu" ga tsohon ko sabon alƙawari. Wannan za a iya fassara shi da " bautawa" ko " biyayya" ko "miƙa kai ga".
  • Kiristoci suma an kira su da "bayin adalci," wanda misãli ne da ya danganta sa kai ga biyayya ga Yahweh da kuma miƙa kai irin ta bara ga ubangidansa.

(Hakanan duba: miƙa kai, bautarwa, iyali, ubangida, biyayya, adalci, alƙawari, shari'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:29-31
  • Ayyukan Manzanni 10:7-8
  • Kolosiyawa 01:7-8
  • Kolosiyawa 03:22-25
  • Farawa 21:10-11
  • Luka 12:47-48
  • Markus 09:33:35
  • Matiyu 10:24-25
  • Matiyu 13:27-28
  • 2 Timoti 02:3-5
  • Ayyukan Manzanni 06:2-4
  • Farawa 25:23
  • Luka 12:37-38
  • Luka 22:26-27
  • Markus 08: 7-10
  • Matiyu 04:10-11
  • Matiyu 06: 24

biki, bukukuwa, yin biki

Ma'ana

Kalmar nan "biki" tana nufin wani al'amari ne da ƙungiyar mutane ke gudanarwa tare da cin abinci mai yawa tare, sau da dama akan yi shi ne domin nuna farin ciki kan wani abu. A aikace kalmar nan "biki" tana nufin a ci abinci mai yawa ko kuma halartar wurin cin abinci tare.

  • A sau da yawa akwai akwai ire-iren abinci na musamman da akan shirya sabo da wani biki.
  • Bukukuwan addini da Allah ya umarta ga Yahudawa su yi sun haɗa da yin taro tare. Sabo da wanan dalilin yasa ake kiran tattaruwar "bukukuwa"

A cikin Littafi Mai Tsarki, sarakuna da sauran mawadata da mutane masu iko kan shirya biki domin nishaɗantar da iyalansu da kuma abokansu.

  • A cikin labarin ɓattacen ɗa, uban ya yi biki na musamman sabo da dawowar ɗansa.
  • A waɗansu lokutan biki kan ɗaoki tsawon kwanaki.
  • Kalmar nan "ayi biki" za'a iya fassara ta da a ci ayi nishaɗi ko kuma yin murna ta wurin "cin abinci na musamman, ko kuma da yawa."
  • Ya danganta ga wurin, "biki" za'a iya fassara shi "yin murna tare haɗe da cin abinci mai yawa" ko kuma "taron liyafa."

(Hakanan duba: biki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 02:12-14
  • Farawa 26:30
  • Farawa 29:22
  • Farawa 40:20
  • Yahuza 01:12-13
  • Luka 02:43
  • Matiyu 22:1

binbini, tunani

Ma'ana

Wannan magana "binbini" ɗaukar lokaci ne ayi tunani akan wani abu a hankali da zurfi kuma.

  • Wannan furci yawancin lokaci ana amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki game da tunani da Allah da koyarwarsa.
  • Zabura 1 ta ce mutumin dake binbini akan shari'ar Ubangiji "dare da rana" zai zama da babbar albarka.

Shawarwarin Fassara:

  • Za a iya fassara "binbini akai" a ce "yin tunani a hankali da zurfi" kuma ko "a duba da tunani" ko "yin tunani yawancin lokaci."
  • Wannan furci "binbini" za a iya fassara shi haka "tunani mai zurfi." Wannan furci "binbinin zuciyata" za a iya fassara ta haka "abin da nake tunani ƙwarai a kai" ko "abin da nake tunani da yawa akansa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 24:63
  • Yoshuwa 01:8-9
  • Zabura 01:1-2
  • Zabura 119:15

birni mai tsarki, birane masu tsarki

Ma'ana

A cikin littafi mai tsarki "birni mai tsarki" na nufin Yerusalem.

  • Wanan kalmar ana amfani da ita domin ambaton tsohon birnin Yerusalem hakanan kuma da sabuwar Yerusalem inda Allah ke zama yake kuma mulki a cikin mutanensa.
  • Wannan kalma za a fassara ta ta wurin haɗa kalmomin "birni" da "tsarki" da kamar yadda sauran fassarori suka mora.

(Hakana duba: sama, tsarki, Yerusalem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Matiyu 04:5-6
  • Matiyu 27:51-53
  • Wahayin Yahaya 21:1-2
  • Wahayin Yahaya 21:9-10
  • Wahayin Yahaya 22:18-19

bisa ga doka, a shar'ance, bisa ga shari'a, rashin doka

Ma'ana

Kalmar "bisa ga doka" na nufin abin da aka yadda ayi bisa ga shari'a ko abin da aka buƙata. Akasin wannan shi ne "rashin doka," wanda a taƙaice yake nufin "rashin shari'a."

  • A cikin Littafi Mai tsarki, wani abu "bisa ga doka" ne idan abin da shari'ar Allah mai tsarki ta yadda da shi ne, ko bisa ga shari'ar Musa da sauran dokokin Yahudawa. A bin da yake na "rashin doka" shi ne wanda "ba a yadda da shi ba" bisa ga shari'a.
  • Ayi wani abu "bisa ga doka" na nufin ayi shi "da kyau" ko "ta hanya mai kyau."
  • Abubuwa da yawa da shari'ar Yahudawa ta nuna su a matsayin marar doka ko rashin shari'a ko abubuwan da basu yadda da shari'ar Allah ba game da ƙaunar mutane.
  • Ya danganta da nassin, hanyoyin fassara "bisa ga doka" zasu haɗa da "bada dama" ko "bisa ga shari'ar Allah" ko "bin shari'unmu" ko "dai-dai" ko "dacewa."
  • Furcin "bisa ga shari'a ne?" ana iya fassarawa a matsayin "shari'armu ta yadda da haka?" ko "wannan wani abin da shari'armu ta bada dama ne?"

Kalmar "rashin shari'a" ko "rashin doka" ana amfani da su a bayyana ayyukan da aka yi na karya doka.

  • A cikin Sabon alƙawari, kalmar "rashin doka" ba ana amfani da ita kawai bane a bayyana karya shari'ar Allah, amma kuma yawanci na ma'anar karya shari'un Yahudawa da mutune suka kafa.
  • Cikin shekaru Yahudawa sunyi ƙari akan shari'un da Allah ya basu. Shugabannin Yahudawa zasu kira wani abu "rashin shari'a" idan bai yi dai-dai da shari'un da mutane suka kafa ba.
  • Sa'ad da Yesu da almajiransa suke zagar hatsi a ranar Asabaci, Farisiyawa sunyi zargin su da yin "abin da bai halarta ba" domin yana karya dokar Yahudawa na barin yin aiki a wannan ranar.
  • Sa'ad da Bitrus yace cin abinci marar tsabta "ba bisa ga shari'a ba ne" a gare shi, yana nufin cewa idan yaci waɗannan abinci zai karya shari'un da Allah yaba Isra'ilawa game da kada su ci wasu ire-iren abinci.

Kalmar "marar doka" na bayyana mutum wanda baya biyayya da dokoki. Sa'ad da wata ƙasa ko ƙungiyar mutane na cikin halin "rashin doka," akawi bazuwar rashin biyayya, tawaye, da ayyukan fasikanci.

  • Taliki marar doka na cike da rashin biyayyya kuma baya biyayya da shari'un Allah.
  • Manzo Bulus ya rubuta cewa a kwanakin ƙarshe za a yi "mutumin rashin shari'a," ko "marar doka," wanda shaiɗan zai zuga shi ya aikata miyagun abubuwa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "rashin doka" a fassara ta da yin amfani da kalmar ko bayani dake nuna "babu doka" ko "karya doka."
  • Wasu hanyoyin fassara "rashin doka" zasu iya zama "ba a bada dama ba" ko "ba bisa ga dokar Allah ba" ko "bai yadda da shari'unmu ba."
  • Furci "gãba da shari'a" ma'ana ɗaya ce da "rashin doka."
  • Kalmar "marar doka" ana iya fassarawa a matsayin "ta'addanci" ko "rashin biyayya" ko "kaucewa shari'a."
  • Kalmar "rashin shari'a" ana iya fassarawa a matsayin "rashin biyayya da wata shari'a" ko "ta'addanci (gãba da shari'un Allah)."
  • Furcin "mutumin rashin shari'a" ana iya fassarawa a matsayin "mutumin da baya biyayya da kowacce irin doka" ko "mutumin da ya yi tawaye gãba da shari'un Allah."
  • Yana da muhimmanci ayi amfani da "shari'a" a wannan kalmar, idan mai yiwuwa ne.
  • Ayi la'akari da cewa "rashin doka" yana da wata ma'ana daban da wannan kalmar.

(Hakanan duba: shari'a, Musa, Asabaci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Matiyu 07:21-23
  • Matiyu 12:02
  • Matiyu 12:10
  • Markus 03:04
  • Luka 06:02
  • Ayyukan manzanni 02:23
  • Ayyukan manzanni 10:28
  • Ayyukan manzanni 02:03
  • Titus 02:14
  • 1 Yahaya 03:4-6

bĩsa, bĩsashe

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, sunan nan "bĩsa" yawancin lokaci ana nufin "dabba" ne.

  • bĩsan jeji wani irin dabba ne dake zaune a sake a kurmi ko a jeji da mutane basu taɓa horonsa ba.
  • Bĩsan gida shi yana zaune da mutane ana kuma ajiye shi domin abinci ko aiki, kamar huɗar gonaki. Yawancin lokaci ana amfani da kalman nan "bĩsashe" domin irin waɗannan dabbobi.
  • Tsohon Alƙawari a littafin Daniyel da Sabon Alƙawari a littafin Wahayin Yahaya sun bayyana wahayai dake da bĩsashe da suka kwatanta mugayen ikoki da mulkoki masu gãba da Allah.
  • Waɗansu bĩsashen an rubuta su da fasali mai ban tsoro, kamar su kawuna dayawa da ƙahonni barkatai. Yawancin lokaci suna da ƙarfi da iko, ana nuna kamar suna a matsayin ƙasashe, al'ummai ko mulkokin siyasa.
  • Hanyoyin da za a fasara wannan za a haɗa da su, "hallitu" ko "hallitaccen abu" ko "dabba" ko "dabbar jeji," ya danganta bisa ga nassin.

(Hakanan duba: hukuma, Daniyel, dabbobi, ƙasa, iko, bayyana, Belzebul)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 15:32
  • 1 Sama'ila 17:44
  • 2 Tarihi 25:18
  • Irmiya 16:1-4
  • Lebitikos 07:21
  • Zabura 049:12-13

biyayya

Ma'ana

Wannan kalma "biyayya" ma'anar ta yin abin da aka umarta. Wannan furci "mai biyayya" ma'anarta mutumin da yake yin biyayya. "Biyayya" dabi'a ce da mai biyayya yake da ita. Wani lokaci umarnin na kada a yi wani abu ne, misali "kada ka yi sata."

  • Yawancin lokaci wannan kalma "biyayya" ana amfani da ita game da biyayya da umarnai ko dokokin wani mutum mai iko.
  • Misali, mutane suna biyayya da dokokin shugabannin ƙasa, mulki, ko wasu ƙungiyoyi da suka tsara.
  • 'Ya'ya suna yiwa iyayensu biyayya, bayi suna yiwa iyayengidansu biyayya, mutane suna yiwa Allah biyayya, 'yan ƙasa suna yin biyayya da dokokin ƙasar su.
  • Sa'ad da wani cikin hukuma ya dokaci mutane kada su yi wani abu, sukan yi biyayya ta wurin ƙin yin abin nan.
  • Wasu hanyoyin fassara biyayya za su haɗa da kalman nan ko maganganun masu ma'ana haka "yi abin da aka umarta" ko "bi doka" ko "yi abin da Allah ya ce a yi."
  • Wannan kalma "biyayya" za a iya fassara ta haka "yin abin da aka umarta" ko "bin dokoki" ko "yin abin da Allah ya umarta."

(Hakanan duba: ɗan ƙasa, umarni, rashin biyayya, mulki, shari'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 05:32
  • Ayyukan Manzanni 06:7
  • Farawa 28:6-7
  • Yakubu 01:25
  • Yakubu 02:10
  • Luka 06:47
  • Matiyu 07:26
  • Matiyu 19:20-22
  • Matiyu 28:20

bizne, an bizne, biznewa, jana'iza

Ma'ana

Wannan kalma "bizne" yawancin lokaci ana nufin sa gawa ne a rami ko wasu wuraren biznewa. Wannan furci "jana'iza" aiki ne na bizne wani abu ko kuma za a iya amfani da shi a faɗi wani wurin bizne abu.

  • Yawancin lokaci mutane sukan bizne gawa ta wurin saka shi can cikin rami a ƙasa sa'annan a rufe da ƙura.
  • Wani lokaci akan sa gawa a wani abu kamar akwati kamar makara kafin a bizne shi.
  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, akan bizne matattun mutane a cikin kogo ko makamancin wuri haka. Bayan da Yesu ya mutu, aka lulluɓe gawarsa a cikin likkafani aka sa a kabarin dutse da aka datse da babban dutse.
  • Wannan kalma "wurin biznewa" ko "ɗakin biznewa" ko "turakar biznewa" ko "kogon bizne wa" dukka ana nufin inda ake sa gawa a rufe.
  • Akwai wasu abubuwa da za a iya bizne su, misali kamar yadda Akan ya bizne azurfa da wasu abubuwa da ya sãta daga Yeriko.
  • Wannan furci "ya ɓoye fuskarsa" yawancin lokaci ana nufin "ya rufe fuskarsa da hannunsa."
  • Wani lokaci wannan kalmar "ɓoyewa" ma'anarta "biznewa" kamar yadda Akan ya ɓoye abubuwa a ƙasa da ya sãto daga Yeriko. Wannan ya nuna cewa ya bizne ne a cikin ƙasa.

(Hakanan duba: Yeriko, kabari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 09:9-10
  • Farawa 35:4-5
  • Irmiya 25:33
  • Luka 16:22
  • Matiyu 27:07
  • Zabura 079:1-3

budurwa, budurwai, budurci

Ma'ana

Budurwa mace ce wadda bãta taɓa saduwa da namiji a jima'i ba.

  • Annabi Ishaya yace budurwa ce zata haifi Almasihu.
  • Maryamu budurwa ce sa'ad da ta haifi Yesu. Ba shi da uba a mutuntaka.
  • Wasu yarurrukan na iya samun wata kalmar dake iya bayyana budurwa.

(Hakanan duba: Almasihu, Ishaya, Yesu, Maryamu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 24:15-16
  • Luka 01:27
  • Luka 01:35
  • Matiyu 01:23
  • Matiyu 25:02

ɓarawo, ɓarayi, fashi, fahe-fashe, anyi fashi, ɗanfashi, 'yanfashi, yin fashi, 'yanta'adda, tawaye

Ma'ana

Kalmar "ɓarawo" na ma'anar wani wanda ke satar kuɗi da kadarori daga wasu mutane. Jam'in "ɓarawo" shi ne "ɓarayi." Kalmar "ɗanfashi" yawanci na nufin ɓarawo wanda kuma ke amfani da makamai a zahiri ko ya tsoratar da mutanen da yake yiwa satar.

  • Yesu ya faɗi misali game da mutumin Samariya wanda ya lura da Bayahude wanda 'yanfashi suka kaiwa farmaki. 'Yanfashin sunyi wa Bayahuden duka suka yi masa rauni kafin suka sace kuɗaɗensa da tufafi.
  • Dukkan ɓarayi da 'yanfashi sukan zo farat ɗaya suyi sata, sa'ad da mutane basu zato. Yawanci suna amfani da rufewar duhu su ɓoye abin da suke yi.
  • A tunanin misali, Sabon Alƙawari ya kwatanta Shaiɗan a matsayin ɓarawo wanda ke zuwa ya yi sata, ya kashe, kuma ya hallakar. Wannan na nufin shirin Shaiɗan shi ne ya yi ƙoƙarin ya hana mutanen Allah yi masa biyayya. Idan ya yi nasara da yin haka Shaiɗan zai riƙa sacewa daga gare su abubuwa kyawawa da Allah ya shirya domin su.
  • Yesu ya yi bayanin farat ɗayan dawowarsa kamar farat ɗayan zuwan ɓarawo ya yi sata daga wurin mutane. Kamar yadda ɓarawo ke zuwa sa'ad da mutane basu zata ba, haka Yesu zai dawo a sa'ad da mutane basu zata ba.

(Hakanan duba: albarka, ta'addanci, gicciyewa, duhu, mai hallakarwa, iko, Samariya, Shaiɗan)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 03:10
  • Luka 12:33
  • Markus 14:48
  • Littafin Misalai 06:30
  • Wahayin Yahaya 03:03

ɓarna, abin da aka ɓarnatar, ɓarnatawa, aikin ɓarnatarwa, ayukan ɓarna

Ma'ana

Kalmar nan ɓarna ko ɓarnatarwa tana ma'anar a ɓarnatar da mallakar wani, ko kuma a mayar da ƙasa kufai, ko a hallakar da ita, wanan ya haɗa da karkashe da kuma kame mutanen ƙasar.

  • Wanan na ma'anar mummunar ɓarnatarwa.
  • Alal misali,birnin saduma an "ɓarnatar" da shi ta wurin hukuncin Allah, sabo da zunubin mutanen ƙasar
  • Kalmar nan ɓarnatarwa zata iya nuna abin takaici da ƙuncin da ya biyo bayan hukuncin hallakawa.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan ɓarna za'a iya fassara ta da "hallakarwa ɗungun" ko kuma "a mai da wuri ya zama kufai ɗungun."
  • Ya danganta dai da abin da wurin ke nufi, amma dai barnatarwa na nufin "ayi kaca-kaca da wuri baki ɗaya" ko kuma ya jawo "mummunan takaici" ko "masifa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 08:24-25
  • Irmiya 04:13
  • Lissafi 21:30
  • Zafaniya 01:13

ɓarna, ɓarnatarwa, lalacewa, ƙare sarai, zaman banza, ƙango, yasasshiyar ƙasa, yasassun ƙasashe, zama marar ƙarfi

Ma'ana

A ɓarnatar da abu na nufin a yar da abin kamar abin banza ko kuma a yi amfani da shi ta rashin hikima. Abin dake "lallatacce" ko "ƙango" na manufar ƙasa ko birnin da aka lalatar har abin dake iya zama cikinta.

  • Kalmar "ɓarnatarwa" na bayyana abin dake ciwo har ga zama kufai. Mutumin dake lalacewa yakan rame dukka saboda cutarsa ko domin rashin abinci.
  • A "lalatar" da birni ko ƙasa na nufin a hallakar da shi.
  • Wata kalmar ta "yasasshiyar ƙasa" na iya zama "hamada" ko "jeji." Amma yasasshiyar ƙasa na iya zama kuma dama mutane na zama nan kuma ƙasar dã tana da itatuwa da dashe-dashe dake bãda amfanin abinci.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 06:06
  • Lebitikus 26:39
  • Matiyu 26:08
  • Wahayin Yahaya 18:15-17
  • Zakariya 07:13-14

ɓatanci, ɓata suna, masu ɓata suna, yin ɓatanci,

Ma'ana

Ɓatanci ya haɗa da faɗin abubuwa marasa kyau (da ba a rubuce ba) game da wani mutum. A faɗi waɗannan abubuwa ba a (rubuta su ba) game da wani mutum ana ɓata sunansa ne. wanda yake faɗar irin wannan abubuwan shi mai ɓatanci ne.

  • ‌Ɓatanci na iya zama rahoto na gaskiya ya kan kuma iya zama ƙarya, yakan sa mutane su dinga yiwa wanda aka ɓata ɗin kallon banza.
  • A yi "ɓatanci" akan iya fassara shi da "yin magana saɓanin wani" ko "yaɗa mugun labari" ko "yin sũka."
  • Mai yin ɓatanci ana kiransa "mai bada labari" ko "mai baza labari."

(Hakanan duba: saɓo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 04:13
  • 1 Timoti 03:11
  • 2 Korintiyawa 06:8-10
  • Markus 07:20-23

ɓatawa, kufai, ɓãtacce

Ma'ana

A "ɓata" wani abu na nufin a lalatar, a hallakar, ko a sa abu shi zama abu marar amfani. kalmar "kufai" na nufin sauran ƙurar da ta rage bayan an hallakar da wani abu.

  • Annabi Zefaniya ya yi magana game da ranar fushin Allah kamar "ranar kufai" da za a shar'anta a kuma hukunta duniya.
  • Littafin Misalai ya ce lalatarwa da hallakarwa na jiran marasa Allah.
  • kalmar "lallatarwa" ko a "washe" ko a "maida wofi" ko a "karya."
  • Kalmar "ɓatawa" ko "ɓatacce" za a iya fassarawa haka "kufai" ko "rushe gine-gine" ko "lalatar da birni" ko "birkitarwa" ko "fashewa" ko "hallakarwa" ya danganta da nassin.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 12:7-8
  • 2 Sarakuna 19:25-26
  • Ayyukan Manzanni 15:16
  • Ishaya 23:13-14

ɓaure, ɓauraye

Ma'ana

Ɓaure wani ɗan itaciya ne mai taushi da kuma zaƙi da akan samu daga itatuwa. Idan ya nuna yakan zama da kaloli da yawa, haɗe da ruwan ƙasa, rawaya, tsanwa-tsanwa.

  • Itacen ɓaure kanyi tsawon mita shida yana kuma da manyan ganyaye da ke bada inuwa mai ƙayatarwa. 'ya'yan sun kai a ƙalla mita 3-5 a tsawo
  • Adamu da Hawwa'u sun yi amfani da ganyen itacen ɓaure domin su suturta kansu bayan da suka yi zunubi.
  • Akan iya a ci ɗanyun 'ya'yan ɓaure ko kuma,ayi kauɗa ko a adanasu a yayyanka a matse su a cikin wainar da za'a ci nan gaba.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, ɓaure na da muhimmanci domin samar da abinci da kuma kuɗin shiga.
  • Kasancewar itatuwan ɓaure masu 'ya'ya an nuna shi a cikin Littafi Mai Tsarki akan alamu ne na wadatuwa.
  • A lokuta da yawa Yesu ya yi amfani da itacen ɓaure domin nuni da kuma koyar da almajiransa gaskiyar al'amura na ruhu.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Habakuk 03:17
  • Yakubu 03:12
  • Luka 13:7
  • Markus 11:14
  • Matiyu 07:17
  • Matiyu 21:18

ɓice, ɓicewa, gagara ɓicewa

Ma'ana

Wannan magana "ɓicewa" ma'anarta shi ne a ɓice ko a tsaida wani abu da yake neman a biya burinsa.

  • Wannan magana anfi amfani da ita wajen kashe ƙishin ruwa da hanyar da za a tsaida ƙishi tawurin shan wani abu.
  • Ana kuma amfani da ita wajen kashe wuta.
  • Bulus ya yi amfani da wannan kalma "ɓicewa" a cikin misali sa'ad da ya koyar da masu bada gaskiya "kada su ɓice Ruhu Mai Tsarki." Ma'ana kada a hana mutane ba Ruhu Mai Tsarki dama ya fito da 'ya'yansa da baiwarsa a cikinsu. Ɓice Ruhu Mai Tsarki shi ne hana Ruhu Mai Tsarki 'yancin bayyana ikonsa a sarari da aikinsa cikin mutane.

(Hakanan duba: 'ya'ya, kyauta, Ruhu Mai Tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki.

  • 1 Tasalonikawa 05:19
  • Ezekiyel 20:47
  • Ishaya 01:31
  • Irmiya 21:12

cancanta, cin jarabawa, rashin cancanta, faɗuwa jarabawa

Ma'ana

Wannan magana "cin jarabawa" ana nufin samun 'yancin karɓar tagomashi ko samun karɓuwa cewa wani yana da wata baiwar iyawa.

  • Mutumin da ya "ci jarabawa" domin wani aiki na musamman dole yana da baiwa da koyarwar da zai yi wannan aiki.
  • A cikin wasiƙarsa zuwa ga iklisiyar Kolosiya, manzo Bulus ya rubuta cewa Allah yaba masu bada gaskiya "yardar ci" su sami rabo a cikin mulkinsa na haske. Manufar wannan shi ne Allah ya basu dukkan abin da suke buƙata suyi rayuwa irin tasa.
  • Mai bada gaskiya ba zai yi aiki domin ya sami 'yancin zama mai rabo a mulkin Allah ba. Ya ci jarabawa domin Allah ya fanshe shi ta wurin jinin Yesu.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, "cancanta" za a iya fassarawa haka "shiryayye" ko "mai hattara" ko "samun iyawa."
  • Idan an sa mutum ya "ci jarabawa" za a iya fassarawa haka "an shirya shi" ko "an ba shi iyawa" ko "an ƙarfafa masa gwiwa."

(Hakanan duba: Kolosse, allantaka, mulki, haske, Bulus, fansa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 01:3-5

cikakke, mai cikasawa, cikasa, kammala

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma "cikakke" ma'anarsa girma ko ƙosawa a cikin rayuwar Kirista. Idan an cikasa ko kammala wani abu wato anyi ta aiki akan wannan abin har sai da ya zama dai-dai yadda yakamata babu wani abin aibatawa.

  • Zama cikakke da kammalalle na nufin Kirista wanda yake yin biyayya, ba marar zunubi ba.
  • Wannan kalma "cikakke" na da ma'anar "kammalalle" ko "guda ɗungum."
  • A Sabon Alƙawari cikin Littafin Yakubu an ce naciya a cikin gwaje-gwaje yakan kawo cikawa da ƙosawa ga mai bada gaskiya.
  • Idan Kiristoci suna binciken Littafi Mai Tsarki suna kuma biyayya dashi zasu fi zama cikakku da ƙosassu a cikin ruhaniya domin zasu ƙara zama kamar Kiristi a cikin halinsu.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana za a iya fassarata haka, "marar aibu" ko "babu kuskure" ko "marar cikas" ko "babu laifi" ko "ba shi da wani laifi."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 12:02
  • Yakubu 03:02
  • Matiyu 05:46-48
  • Zabura 019:7-8

cin amana, maci amana, mai yashewa

Ma'ana

Wannan kalma "cin amana" shi ne yin wani abin ruɗi don a cuci wani mutum. "Maci amana" shi ne mutumin da ya saida abokinsa dake dogara gare shi.

  • Yahuda "maci amana" ne domin ya gaya wa shugabannin Yahudawa yadda za su kama Yesu.
  • Cin amanar da Yahuda ya yi mugun abu ne musamman domin shi manzo ne na Yesu wanda ya karɓi musanyar kuɗi don ya faɗa wa shugabannin Yahudawa wata magana game da Yesu wadda za ta kai Yesu ga mutuwar rashin adalci.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, kalmar nan "cin amana" za a iya fassarata ta zama "yin ruɗi don a cuci wani" ko "a bayar ga maƙiyi" ko "yiwa wani maƙirci."
  • Wannan kalma "cin amana" za a iya fasrata haka "mutum wanda ya ci amana" ko "mai fuska biyu" ko "mai bashewa."

(Hakanan duba: Yahuda Iskariyoti, shugabannin Yahudawa, manzo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:52
  • Yahaya 06:64
  • Yahaya 13:22
  • Matiyu 10:04
  • Matiyu 26:22

cin hanci, toshi

Ma'ana

"Cin hanci" shi ne bada wani abu mai daraja, misalin kuɗi, domin ka rinjayi wannan mutumin ya yi wani abin rashin gaskiya.

  • Sojojin da suka yi tsaron kabarin Yesu daba kowa a ciki an basu cin hanci kuɗi domin suyi karya game da abin da ya faru.
  • Wani lokaci akan ba ma'aikatan hukuma cin hanci domin su ƙyale laifi ko su jefa kuri'a yadda ake so.
  • Littafi Mai Tsarki ya hana bayarwa da karɓar cin hanci.
  • Kalmar nan "cin hancii" za a iya fasara shi haka "biyan rashin gaskiya" ko" biya don ayi ƙarya" ko "lada domin karya dokoki."
  • Za a iya fassara "bada cin hanci" da kalma ko furci mai ma'ana haka, "biya domin a rinjayi wani" ko "biya domin a yi alfarma marar gaskiya" ko " a biya don a sami alheri.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 08:1-3
  • Littafin Mai Wa'azi 07:7
  • Ishaya 01:23
  • Mika 03:9-11
  • Littafin Misalai 15:27-28

dabbobi

Ma'ana

Wannan kalma "dabbobi" na nufin naman da ake kiwo a gida domin abinci da wasu ayyuka kuma. Wasu dabbobin ana horar da su domin aiki.

  • Ire-iren dabbobin sun haɗa da tumaki, shanu, awaki, dawakai, da jakuna.
  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, ana gwada arzikin mutum da yawan dabbobin da yake da su.
  • Ana amfani da dabbobi don su bada abubuwa kamar ulu, madara, mai, kayan gida, da tufafi.
  • Wannan kalma za a iya fasarata haka "dabbobin gida."

(Hakanan duba: saniya, sã, jaki, akuya, doki, tukiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 03:15-17
  • Farawa 30:29
  • Yoshuwa 01:14-15
  • Nehemiya 09:36-37
  • Littafin Lissafi 03:41

dabo, sihiri, ɗan dabo, 'yan dabo, masu magana da ruhohi, masu sha'ani da kurwai

Ma'ana

Wannan kalmar "dabo" ma'anarta sha'ani ne na amfani da ikon ruhohi da ba daga Allah ba. "ɗan dabo ko boka" mutum ne dake yin dabo ko bokanci.

  • A Masar, sa'ad da Allah ya yi abubuwan al'ajibi ta hannun Musa, bokayen Fir'auna na Masar suka iya yin wasu abubuwa, amma ikonsu ba daga Allah bane.
  • Yawancin lokaci bokanci jifa ce don ruɗar da hankali ko maimaita wasu maganganu domin wani abu mai ban mamaki ya faru.
  • Allah ya umarci mutanensa kada su aikata waɗannan sha'ani na bokanci ko duba.
  • Mai sihiri shima kamar boka yake, yawancin lokaci yana amfani da dabo ko bokanci ya cuci wasu.

(Hakanan duba: duba, Masar, Fir'auna, iko, sihiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 41:08
  • Farawa 41:22-24
  • Farawa 44:3-5
  • Farawa 44:15

damisa, damisoshi

Ma'ana

Damisa wata dabba ce babba, mai kama da mage, dabbar daji ce mai kalar ruwan ƙasa da ɗigo-ɗigon baƙi.

  • Damisa wata irin dabba ce dake kama wasu dabbobi ta kuma cinye su.
  • A cikin Littafi Mai tsarki, ana kwatanta bala'in farat ɗaya a matsayin damisa, wadda ke afkawa farautarta farat ɗaya.
  • Annabi Daniyel da manzo Yahaya sunyi zance game da ruyoyi inda suka ga wani bisa mai kama da damisa.

(Hakanan duba: bisa, Daniyel, farauta, wahayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 07:06
  • Hosiya 13:07
  • Wahayin Yahaya 13:1-2
  • Waƙar Suleman 04:8

dangantaka da, yin soyayya, kwanta da, kwana da, kwanciya da

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, waɗannan kalmomin an jaddadasu da suke nuna yin jima'i.

  • Maganar "kwana da" wani yana nuna yin jima'i da wannan mutumin. idan ya wuce shi ne "kwanta da."
  • A littafin tsohon alƙawari "waƙar suleman", an yi amfani da kalmar " yin soyayya" don fassara kalmar "ƙauna", wanda a nassin ake maganar yin jima'i. Wannan na da dangantaka da maganar "soyayya da wani".

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu yarurrukan na iya amfani da maganganu daban-daban ga wannan magana a matakai daban-daban, ya danganta ko waɗanda abin ya shafa ma'aurata ne ko kuma suna da wata dangantaka. Yana da mahimmanci a tabbatar da cewa fassarar wannan magana tana da ma'ana mai kyau a kowanne mataki.
  • Ya danganta ga fannin, maganganu kamar waɗannan akan iya amfani da su a fassara "kwana da": "kwanciya da" ko "yin soyayya" ko "kusanci da".
  • Waɗansu hanyoyin yin fassarar kuma "samun dangantaka da " kan haɗa da "samun dangantakar yin jima'i da" ko "samun dangantakar aure da".
  • Kalmar " yin soyayya" akan iya fassara ta da "ƙaunar" ko "kusanci". ko kuma akwai wata magana da take ta ainahi da kan fassara wannan a cikin yaren da ake aiki da shi.
  • Yana da mahimmanci a duba abin da aka mora wajen fassara wannan abin su zama amintattu ga jama'ar da za su yi amfani da wannan fassarar Littafi Mai Tsarki.

(Hakanan duba: aikin lalata)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:1-2
  • 1 Sama'ila 01:19
  • Maimaitawar Shari'a 21:13
  • Farawa 19:05
  • Matiyu 01:25

dangi, dangogi, dangartaka, ɗan'uwa, 'yan'uwa

Ma'ana

Kalmar "dangi" na nufin 'yan'uwan wani taliki na jini, da ake la'akari da su a matsayin ƙungiya. kalmar "ɗan'uwa" ana nufin dangi namiji.

  • "Dangi" na nufin ɗan'uwan mutum na kurkusa, kamar su iyaye da ƙanne da yayye, ko yana iya haɗawa ma da dangi na nesa, kamar su innoni, su bãbã, su kawu, ko 'ya'yan su inna da bãbã da su kawu da abokan wasa dukka.
  • A tsohuwar Isra'ila, idan mutum ya mutu, ana buƙatar ɗan'uwansa na kusa ya auri gwauruwar, ya yi tattalin dukiyarsa, ya kuma taimaka sunan iyalin ya ci gaba. Wannan ɗan'uwa ana kiransa "ɗan'uwan fansa."
  • Wannan kalma "dangi" ana iya fassara ta a matsayin, "ɗan'uwa ko iyali."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Romawa 16:9-11
  • Rut 02:20
  • Rut 03:09

dankari, dankarai

Ma'ana

Kalmar "dankari" na nufin ƙasan ƙofar ɗaki ko sashen gini dake gab da cikin ƙofa.

  • Wasu lokuta dankari wani katako ne ko dutse dole sai an tsallake shi kafin a shiga cikin ɗaki ko gini.
  • Da ƙofa duk da buɗewar rumfa suna iya kasancewa da dankari.
  • Wannan kalma ayi amfani da ita a yi fassara a yaren wurin dake nuna wurin da ake takawa ko tsallakewa idan za a shiga gida.
  • Idan babu wata irin kalma haka, "dankari" ana iya fassarawa haka, "bakin ƙofa" ko "buɗewa" ko "hanyar shiga," ya danganta da nassin.

(Hakanan duba: ƙofa, rumfa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 09:17-19
  • Ezekiyel 09:03
  • Ishaya 06:04
  • Littafin Misalai 17:19

danƙa wa, a yi abu, alkawari

Ma'ana

Wannan kalma "danƙa" ko "uziri" ana cewa an ɗauki matakiyi ko alƙawarin ayi wani abu.

  • Mutumin da yayi alƙawari ya yi wani abu akan ce "ya bada kai" yayi abin.
  • A "danƙa" aiki shi ne a bada yin wannan aikin ga wani mutum. Misali, a cikin 2 Korantiyawa Bulus ya ce Allah ya "danƙa" (ko ya "ba mu") aikin taimakon mutane su sulhuntu ga Allah.
  • Waɗannan kalmomi "danƙa kai" da "yarda" yawancin lokaci ana nufin yin wani abin da ba dai dai ba kamar "ya danƙa kansa ga yin zunubi" ko "yin zina" ko "yin kisan kai."
  • Wannan furci "an ba shi aiki" za a iya fasara shi zuwa "an danƙa masa aiki" ko "an ba shi amanar aiki" ko " an rataya aikin a wuyansa."
  • Wannan kalma "abin da aka yi alƙawarin za a yi" za a iya fassara shi haka "aikin da aka bayar" ko "alƙawarin da aka yi."

(Hakanan duba: zina, aminci, alƙawari, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 28:07
  • 1 Bitrus 02:21-23
  • Irmiya 02:12-13
  • Matiyu 13:41
  • Zabura 058:02

daraja, tamani, tsada, maikyau

Ma'ana

Wannan kalma "daraja" na bayyanawa akan mutane ko abubuwa da aka ɗauke su da tamani.

  • Wannan magana "duwatsu masu daraja" ko "kayan ado masu daraja" ana nufin duwatsu da suke da launuka ko wasu zane dake sa a gansu da kyau ko amfani.
  • Ga misalin duwatsu masu daraja: lu'u lu'u rubbobi da tukoki.
  • Zinariya da azurfa ana kiransu "duwatsu masu daraja."
  • Yahweh ya ce mutanensa suna da "daraja" a idonsa (Ishaya 43:4)
  • Bitrus ya rubuta cewa ruhu mai tawali'u da natsuwa abu ne mai daraja a idanun Allah (1 Bitrus 3:4).
  • Za a iya fassara wannan haka "mai tsada" ko "masoyi" ko "ana ji da shi" ko "mai tsada sosai."

(Hakanan duba: zinariya, azurfa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 01:01
  • Ayyukan Manzanni 20:22-24
  • Daniyel 11: 38-39
  • Littafin Makoki 01:7
  • Luka 07:2-5
  • Zabura 036:08

datse

Ma'ana

Wannan kalma "datse" ma'anarta a ware ko raba wani da wasu mutane, a yashe da wani ko a fitar da wani can gefe daga ƙungiya. Zai kuma iya zama kisa daga mahukunci sabili da zunubi.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, rashin biyayya ga umarnan Allah yakan sa a datse mutum, ko a raba shi da mutanen Allah da kuma fuskarsa.
  • Allah kuma ya ce zai "datse" ko ya hallakar da al'umman da ba Isra'ilawa ba domin basu yi masa sujada ba ko su yi masa biyayya kuma maƙiyan Isra'ila ne.
  • Wannan furci "datse" an yi amfani da ita lokacin da Allah ya sa kogi ya dena gangarowa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "datsewa" za a iya fassarata haka "a kore shi" ko "a sallame shi" ko "a raba shi da" ko "a kashe" ko "a hallaka."
  • Ya danganta ga yadda aka yi amfani da shi, za a iya fassara wannan magana "a datse" ta zama "a lalatar" ko "a sallame shi" ko "a rabu da" ko "a lalatar."
  • Idan ana magana game da gangarowar ruwaye da aks datse, za a iya fassara shi haka "aka tsaida su" ko "aka sa su dena gangarowa" ko "aka raba su."
  • Ma'anar yanka wani abu da wuƙa zai banbamta da yadda aka yi amfani da wannan kalma "datsewa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 17:14
  • Littafin Alƙalai 21:06
  • Littafin Misalai 23:18

dattijo, dattawa, tsoho

Ma'ana

Dattawa sune waɗanda suka manyanta a ruhaniya waɗanda aka danƙawa sha'anin gudanar ayukan Ikkilisiya da kuma ayuka na ruhaniya a cikin mutanen Allah.

  • Kalmar nan "dattijo" ta samo asali ne ganin cewa tun farko an san dattawa a matsayin mutane masu yawan shekaru, waɗanda sabo da shekarunsu da abubuwan da suka fuskanta suka zama da hikima.
  • A cikin Tsohon Alƙawari dattawa sun temaka wajen shugabantar Isra'ilawa akan tabbatar da adalci a cikin mutane da kuma shari'ar Musa.
  • A cikin Sabon Alƙawari, dattawan Yahudawa sun ci gaba da zama dattawa a cikin mutanensu, su ne kuma masu yi wa mutane shari'a.
  • A farkon Ikkilisiyar Krista, dattawa su ne ke gudanar da al'amura na ruhaniya a taron masubi.
  • Dattawa a waɗannan Ikkilisiyu sun haɗa da matasa waɗanda suka manyanta akan al'amura na ruhaniya.
  • Za'a iya fassara kalmar a matsayin "dattawan mutane" ko mutanen da suka girma a ruhaniya da ke shugabantar ikilisiya."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 11:1-3
  • 1 Timoti 03:1-3
  • 1 Timoti 04:14
  • Ayyukan Manzanni 05:19-21
  • Ayyukan Manzanni 14:23
  • Markus 11:28
  • Matiyu 21:23-24

doki, dawaki, dokin yaƙi, dawakan yaki, bayan doki

Ma'ana

Doki wata babbar dabba ce mai ƙafa huɗu wadda a cikin Littafi mai Tsarki ake moron ta domin aikin gona da kuma ɗaukan mutane.

  • Waɗansu dawakan ana morarsu su gungura karusai, waɗansu kuma na ɗaukan mutane.
  • Akan fi morar dawakai da linzami takunkumi a kansu sabo da a iya sarrafa su.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki an ɗauke su akan babubuwa ne masu daraja da kuma dukiya, mafi yawa akan amfaninsu a fagen yaƙi. Misali, wani sashe na dukiyar Sarki Suleman mai girma ita ce dubban dawakansa da karusansa da yake da su.
  • Dabbobi da ke kama da doki sune jaki da alfadari.

(Hakanan duba: karusa, jaki, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 18:04
  • 2 Sarakuna 02:11
  • Fitowa 14:23-25
  • Ezekiyel 23:5-7
  • Zakariya 06:08

Dokoki Goma

Ma'ana

"Dokoki Goma" dokoki ne da Allah ya ba Musa a Tsaunin Sinai yayin da Isra'ilawa suke zaune a jeji akan hanyarsu ta zuwa ƙasar Kan'ana. Allah ya rubuta waɗannan dokoki a bisa allunan dutse guda biyu.

  • Allah yaba Isra'ilawa dokoki da yawa da zasu yi biyayya, amma dokoki goma dokoki ne saboda su taimaki Isra'ilawa su ƙaunaci su kuma yi sujada ga Allah su kuma ƙaunaci sauran mutane.
  • Waɗannan dokoki suna cikin fannin alƙawarin Allah da mutanensa. Ta wurin biyayya da abinda Allah ya dokace su suyi, mutanen Isra'ila zasu nuna suna ƙaunar Allah kuma su nasa ne.
  • Allunan dutsen tare da dokokin da aka rubuta a kansu an ajiye su cikin Akwatin Alƙawari, wanda ke wuri mafi tsarki na rumfar sujada daga bisani kuma, a haikali.

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, doka, jeji, shari'a, biyayya, Sinai, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 04:13-14
  • Maimaitawar Shari'a 10:3-4
  • Fitowa 34:27-28
  • Luka 18:18-21

duba, mai duba, mai gani ɗan tsubu

Ma'ana

Kalmar nan "duba" da "tsubu" tana nufin wani aiki ne na ƙoƙarin samun sadarwa daga ruhohi ta wata hanya mai mai irin wani iko. Mutumin da ke yin haka a wani lokaci akan kira shi "mai duba" ko "ɗan tsubu."

  • A cikin Tsohon Alkawari Allah ya unarci Isra'ilawa da kada us yi duba ko tsubu.
  • Allah ya bar mutanensa su nemi sadarwa daga wurinsa ta wurin waɗansu duwatsu na Urim da Tumin waɗanda aka keɓe domin amfanin babban firist sabo da wanan dalili. Amma bai bar mutanensa su nemi sadarwa ta wurin temakon ruhohi ba.
  • 'Yan tsubu na arna na amfani da dabaru kala-kala domin ƙoƙarin samun sadarwa daga ruhohi na duniya. A waɗansu lokutan sukan yi ƙonƙonto ta wurin waɗansu sassan mushen dabbobi, ko kuma wurga ƙasusuwan matattun dabbobi a ƙasa, domin neman yadda za su yi fassara a matsayin sadarwa daga alloli na ƙarya
  • A cikin sabon Alkawari, Yesu da manzanni suma sun ƙi aikin duba da tsubu, da maitanci, da sihiri. Duk waɗannan sun ƙunshi yin amfani da ikon miyagun ruhohi, kuma Allah ya hana wanan.

(Hakanan duba: manzo, allan ƙarya, sihiri, bokanci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 06:1-2
  • Ayyukan Manzanni 16:16
  • Ezekiyel 12:24-25
  • Farawa 44:05
  • Irmiya 27:9-11

Duhu

Ma'ana

Kalmar nan "duhu" tana nufin rashin kasancewar haske. Akwai kuma waɗansu ƙarin bayanai game da yadda aka baiyana kalmar nan duhu:

  • A cikin salon magana, "duhu" na nufin "rashin tsarki" ko "makanta ta ruhu."
  • Hakanan tana da nasaba da duk wani abu da ya shafi zunubi da gulɓatar halaiya.
  • Furcin nan "Mulkin duhu" yana nufin duk wani abu da na mugunta ko kuma wanda sheɗan ya jagoranta.
  • Hakanan ana duban kalmarnan duhu akan wata magana ce a fakaice da nufin mutuwa.
  • Mutanen da ba su san Allah ba ana cewa da su "Ma surayuwa a cikin duhu," wanan na nufinba su fahimci ayukan adalci na zahiri ba.
  • Allah haske ne (aikin adalci) duhu kuma (aikin mugunta) duhu kuma ba zai yi nasara da wannan hasken ba.
  • Wurin horo na waɗanda suka ƙi Allah a wasu lokuta ana kiransa da "wuri mai matsananci duhu."

Shawarwarin Fassara:

  • Ya fi kyau ayi fassarar kalmar kamar yadda aka mare ta a cikin juyin littafin wadda ke nufin rashi kasancewar haske. Hakanan zai iya zama duhu na ɗakin da ba haske ko kuma lokacin dare.
  • Cikin salon magana, ana moron kalmar domin a nuna yadda haske ya bambanta da duhu, a matsayin hanya ta baiyana aikin mugunta da yaudara waɗanda suka bambanta da halin nagari da gaskiya.
  • Ya danganta da yadda ayar ta baiyana, ƙarin hanyoyi na yin fassara za su iya zama kamar, "duhu na dare" (wanda shi ne akasin haske na rana") ko kuma "kasa ganin komai, kamar haske" ko "aikin mugunta, ko wuri mai duhu".

(Hakanan duba: mazambaci, mallaka, daula, haske, fansa, mai adalci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 01: 06
  • 1 Yahaya 02: 08
  • 1 Tasolinikawa 05: 05
  • 2 Samai'la 22 : 12
  • Kolosiyawa 01:13
  • Ishaya 05: 30
  • Irmiya 13:16
  • Yoshuwa 24:7
  • Matiyu 08: 12

duniya, duniyanci, na duniya

Ma'ana

Kalmar nan "duniya" tananufin muhalli inda mutane ke rayuwa a ciki da dai sauran waɗansu hallitu.

  • "Duniya har ila yau zata iya zama ƙasa ko ƙurar da ta rufe duniya.
  • Wanan kalmar wani salon magana ne da aka mora domin a nuna mutanen da ke zama a duniya.
  • Furcin nan "bari duniya ta yi murna" da kuma zai shari'anta duniya misalai ne na salon magana a kan wanan maganar.
  • Kalmar nan na duniya tana magana ne akan abu na fili, waɗanda har kullum suka bambanta da na ruhaniya.

Shawarwarin Fassara:

  • Wanankalmar za'a iya fassara ta da irin kalmar tsohon harshe ko makusantanharsuna ke mora wadda ke nuna wanan duniyar da muke zama a ciki.
  • Ya danganta ga abin da ke wurin "duniya' za'a iya fassara ta da Wanan sarqrin da me rayuwa a cikinta, ko kuma "ƙura" a lokacin da aka yi amfani da irin wanan salon maganar za'a iya nuna "mutane da ke rayuwa a duniya" ko kowanne abu da ke a duniya.
  • Yadda zaka iya fassrasa shi ne abu na zahiri ko "abubuwan da mu ke gani a wanan duniya" ko "abubuwan da ake gani."

(Hakanan duba: ruhu, duniya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 1:38-40
  • 2 Tarihi 02:11-12
  • Daniyel 04:35
  • Luka 12:51
  • Matiyu 06:10
  • Matiyu 11:25
  • Zakariya 06:5

dusar ƙanƙara, anyi ƙanƙara, ana ƙanƙara

Ma'ana

Kalmar "ƙanƙara" na nufin farin daskararren ruwa falle-falle da yake saukowa daga hadari a wuraren da yanayin iskarsu yake da sanyi.

  • Ƙanƙara kan faɗo a wuraren da masu bisa a Isra'ila, amma baya daɗewa a ƙasa yake narkewa. Kan tsaunuka na samun ƙanƙara da ke daɗewa. Misali ɗaya na wurin da aka ambata a Littafi MaiTsarki da yake da ƙanƙara shi ne Tsaunin Lebanon.
  • Abin da yake da matuƙar haske yana da kalar da akan danganta ta da ƙanƙara. Misali, a Littafin Wahayin Yahaya tufafi da gashin Yesu an kwatanta su da "fari kamar ƙanƙara."
  • Farin ƙanƙara yana nuna tsarki da tsabta. Misali, maganar " zunubanmu za suyi fari kamar ƙanƙara" na nufin Yahweh zai wanke dukkan mutanensa daga zunubansu.
  • Waɗansu yarurrukan na iya nufin ƙanƙara da "daskararren ruwa" ko "falle-fallen ƙanƙara" ko "falle-falle daskararre."
  • "Ruwan ƙanƙara" na nufin ruwan da ya fito daga narkakkiyar ƙanƙara.

(Hakanan duba: Lebanon, tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 04:06
  • Ayuba 37:4-6
  • Matiyu 28: 03
  • Zabura 147:16
  • Wahayin Yahaya 01:14

ɗamara, zuriya,

Ma'ana

Wannan kalma "ɗamara" na nufin sashen jikin nan na dabba ko mutum da yake tsakanin ƙasusuwan haƙarƙari da ƙasusuwan kwankwaso, anfi saninsa da mãra.

  • Wannan furci "tattara ɗamara" manufar shi ne a shirya a yi aiki tuƙuru. Wannan ya zo daga al'adar tattara riga daga ƙasarta a cusa ta cikin igiyar ɗamara domin a samu a yi tafiya cikin sawaba.
  • Wannan kalma "ɗamara" yawancin lokaci ana amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki wannan sashin baya na dabba da ake hadaya da shi
  • A cikin Littafi Mai Tsarki ana amfani da "ɗamara" da manufar 'ya'yan golayen namiji inda zuriyarsa ke fiitowa.
  • Wannan furci "zai fito daga mararka" za a iya fassarawa haka "zai zama tsatsonka"' ko "za a haifeshi daga irinka" ko 'Allah zai sa ya fito daga gare ka.
  • Sa'ad da ana magana akan wani sashen jiki, za a iya fassara shi haka "mãra" ko "kwankwaso" ko "ɗamara," ya danganta ga nassi.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:13
  • 2 Tarihi 06:09
  • Maimaitawar Shari'a 33:11
  • Farawa 37:34
  • Ayuba 15:27

ɗan inabi, ya'yan inabi, garkar 'ya'yan inabi

Ma'ana

Ɗan inabi wani ɗan ƙarami, kwallon ɗan itace ne, mai kofe mai taushi kuma yakan fita ne a jikin inabi. A kan yi amfani da ruwansa domin yin ruwan inabi.

  • 'Ya'yan inabi suna nan kala-kala, kamar kore-kore, mai ruwan tsanwa, ko ja
  • Yadda itacen inabi yake yakan kai kamar mita uku a girma.
  • Mutane kan dasa inabi a cikin lambu wanda ake kira garka. Kuma sukan zama wata babbar garka ce ta inabi.
  • 'Ya'yan inabi abinci ne mai matuƙar muhimmanci a kwanaki Littafi Mai Tsarki kuma zama da garka ta inabi wanan na nuna alamar wadata.
  • Domin hana 'ya'yan inabi lalacewa, mutane kan fi yawan shanya su. Busassun 'ya'yan inabi ana kiran su "kauɗar inabi" kuma ana moron su domin ayi wainar kauɗar inabi.
  • Yesu ya faɗi misali game da garkar 'ya'yan inabi domin ya koyar da almajiransa game da mulkin Allah.

(Hakanan duba: inabi, garkar inabi, ruwan inabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 23:24
  • Hosiya 09:10
  • Ayuba 15:33
  • Luka 06:43-44
  • Matiyu 07:15-17
  • Matiyu 21:33

ɗan ƙasa

Ma'ana

‌Ɗan ƙasa mutum ne wanda yake zaune musamman cikin birni, ƙasa, ko mulki. Ana nufin mutum musamman wanda sananne ga hukuma cewa mazaunin wurin ne.

  • Ya danganta bisa ga yadda yake cikin rubutu, za a iya fassarawa haka "mazaunin wuri" ko "mazauni sananne."
  • ‌Ɗan ƙasa zai iya zama a yankin da take cikin gundumar wata babbar mulki da sarki yake mulki akai. Ga misali, Bulus ɗan ƙasar mulkin Roma ne, wadda ta ƙunshi larduna da yawa kuma dabam dabam; Bulus ya zauna cikin ɗaya daga cikin waɗannan lardunan.
  • Haka ma a misalce, masu gaskatawa da Yesu ana kiransu "'yan ƙasar" sama domin za su zauna a can watarana. Kamar ɗan ƙasar ƙasa, Kristoci 'yan mulkin Allah ne.

(Hakanan duba: masarauta, Bulus, lardi, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 21:39-40
  • Ishaya 03:03
  • Luka 15:15
  • Luka 19:14

ɗauka

Ma'ana

Wannan kalma "ɗauka" ma'anar ta shi ne "a ɗaga wani abu sama." Akwai wasu salon amfani da ita.

  • Sa'ad da ana magana akan mace da ta ɗauki ciki , ma'anar ita ce, "tana da juna biyu."
  • "Ɗaukar nawaiya" ma'anar shi ne "samun matsaloli cikin abubuwa." Waɗannan abubuwa masu wuya za su iya zama na jiki ko tashin hankali.
  • Wasu furci da dama a Littafi Mai Tsarki kamar "haifar 'ya'ya" na da ma'ana haka "bada 'ya'ya" ko "yana da 'ya'ya."
  • Wannan furci "bada shaida" ma'anarta "a furta abu" ko "ka faɗi abin da ka gani ko ka aiwatar."
  • Wannan furci cewa "ɗa ba zai ɗauki zunubin mahaifinsa ba" fassarar ita ce "ba za a kama ɗa da laifi ba" ko "ba za a hukunta ɗa domin zunuban mahaifinsa ba.
  • Yawancin lokaci wannan kalma za a iya fassara ta haka "a ɗauka" ko "a kama domin" ko "a fitar" ko "a samu" ko "a jure," ya danganta dai ga nassin.

(Hakanan duba: nauyi, Elisha, jurewa, ɗiyan, laifi, rahoto, tunkiya, ƙarfi, shaida,shaida)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Makoki 03:27

ɗauka sama, ɗauka sama da, cinma wani

Ma'ana

Wannan furci "ɗauka sama" yawancin lokaci ana ambaton yadda Allah ke ɗaukar mutum zuwa sama farat ɗaya, ta hanyar ban mamaki.

  • Wannan furci "tarar da" ana nufin cinma wani mutum bayan zafin gudu domin a tarar da shi. Wata kalma mai ma'ana haka ita ce "tarar da."
  • Manzo Bulus yayi magana yadda aka "ɗauke shi" zuwa sama ta uku. Za a iya fasara wannan haka "ɗauka sama."
  • Bulus ya ce sa'ad da Yesu zai komo, za a "ɗauke Kristoci sama" gaba ɗaya mu sadu da shi a sararin sama.
  • Wannan furcin "zunubaina sun kamo ni" za a iya ba shi ma'ana haka "ina karɓar sakamakon zunubaina" ko "domin zunubaina nake shan wahala" ko "zunubaina suna sani cikin wahala."

(Hakanan duba: al'ajibi, shan kai, wahala, matsala)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 12:1-2
  • Ayyukan Manzanni 08:39-40

ɗaura, ɗamararre, rufaffe, ɗaurarre, maɗauri, ɗaure cikin maɗauri, ɗaurarre cikin maɗauri, ɗaura ɗammara, zamge ƙugu ta gefe

Ma'ana

Kalmar nan "ɗaura" tana nufin a ɗaura wani abu a kewaye da wani abu, takan fi nuna amfani da igiya ko maɗauri a ɗaure a ƙugu domin hana sutura faɗuwa ko kwaɓewa.

  • Kalmar Littafi Mai Tsarki game da, "ku yi ɗammara" tana magana ne akan cewa mutum ya tare haɓar suturarsa domin ya ji daɗin tafiya mafi yawan lokuta a lokacin aiki.
  • Wanan kalmar za'a iya fassara ta a matsayin "yin shiri domin yin aiki" ko kuma yin shiri domin yin wani abu mai wuya.
  • Batun nan "ku yi ɗammara" za'a iya fassara shi cikin salon magana a harshen da ake fassara ya bada ma'ana iri ɗaya wato "ku shirya kanku domin yin aiki" ko "ku yi shirin aiki."
  • Kalmar nan "ku yi ɗammara da" za a iya fassara ta da "ku kewaye kanku" ko "kurufe kanku da."

(Hakanan duba: ɗamara)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:13
  • Ayuba 38:3

ɗian itace, 'ya'yan itace, marar 'ya'ya

Ma'ana

Kalmar nan "ɗan itace" tana nufin waɗansu irin itatuwa da za'a yi ci. Abu mai "'ya'ya" yana da 'ya'ya da sosai. Kalmar nan akan more ta cikin salon magana a cikin Littafi Mai Tsarki.

  • A lokuta da yawa Littafi Mai Tsarki kan ambacin 'ya'ya ya yi magana akan ayukan mutum. Kamar dai 'ya'yan itace ke nuna yadda itacen yake, haka nan kalmomin mutum da aikinsa ke nuna yadda yake da kuma irin halinsa.
  • Mutum kan iya bada 'ya'ya na ruhaniya masu kyau ko munana 'ya'ya na da ma'ana mai kyau da ke nuna bada 'ya'ya masu kyau.
  • Haka nan akan mori bada 'ya'ya a yi salon magana ta nuna "bunƙasa" kusan kullum wanan na nufin samun 'ya'ya da yawa da kuma zuriya, da kuma issashen abinci da sauran dukiya.
  • A batu na bai ɗaya "'ya'ya na" na nufin duk wani abu da ya zo ko kuma wani abu ya samar da shi. Misali, "'ya'ya na hikima" suna magana ne akan abubuwa masu kyau da ke samuwa ta wurin zama mai hikima.
  • Kalmar na "'ya'ya na ƙasa" tana magana akan duk wani abu da ƙasa ke bayarwa domin mutane su ci. Wanan ya haɗa ba wai 'ya'yan itace kawai ba, amma sun haɗa da ganyaye, da tsaba, da mabunƙusa.
  • Wanan salon magana "'ya'ya na Ruhu" na halayen kirki da Ruhu ke bayarwa a cikin rayuwar mutanen da ke yi masa biyayya.
  • Kalmar nan "'ya'ya na mahaifa" tana nufin "abin da mahaifa ke samar" - wato 'ya'ya.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya fi kyau a fassara kalmar nan ta wurin amfani da kalmar "'ya'ya" wadda ake mora domin yin fassara da ake moro akan kalmar 'ya'yan itace. A cikin harsuna ya fi kyau a mori kalmar jam'i, "'ya'ya" na itace muddin ya wuce guda ɗaya.
  • Ya danganta ga abin da ke wurin, kalmar bada "'ya'ya" za'a iya fassara ta da bada 'ya'ya masu yawa na ruhaniya, "zama da 'ya'ya da yawa" ko "wadata."
  • Kalmar nan "albarkar ƙasa" za'a iya fassara ta da "abincin da ƙasa ke bayarwa" ko "irin abin da ƙasa ke bayarwa a yankin."
  • A lokacin da Allah ya hallici sojoji da mutane, ya umarce su su zama da bada "'ya'ya da kuma ruɓanɓanya" wanda ke nufin cewa a zama da "'ya'ya 'ya'ya" da kuma zuriya ko "zama da 'ya'ya da yawa."
  • Kalmar nan "albarkar mahaifa" za'a iya fassara ta za'a iya fassara ta da cewa "abin da mahaifa ke bayarwa" ko "'ya'ya da mata ke haifa" ko kuma "'ya'ya." Lokacin da Elizabet ta ce da Maryamu, "mai albarkane ɗan da ke cikin mahaifarki," abin da take nufi shi ne "mai albarka ne ɗan za ki haifa". Harshen da za'a yi zai iya amfani da irin wanan kalma.
  • Kalmar nan "'ya'yan inabi," za'a iya fassara ta da '"ya'yan itace."
  • Ya danganta ga wurin, kalmar zata iya zama bada "'ya'ya sosai" ko "ta zama da 'ya"ya sosai", zai zama da "'ya'ya sosai," ko "wadatuwa sosai."
  • Manzo Bulus ya baiyana "aiki mai 'ya'ya" za'a iya fassara ta da "aiki wanda zai bada sakamako mai nagarta," ko "yin aikin da zai kawo mutane da yawa ga bada gaskiya cikin Yesu Kristi."
  • "Albarkar Ruhu" za'a iya fassara ta da "aikin da Ruhu mai Tsarki ke yi"

ko kuma "magana ko aikin da ke nuna cewa Ruhu mai Tsarki na aiki a cikin wani mutum."

(Hakanan duba: zuriya, tsabar hatsi, 'ya'yan inabi, Ruhu mai Tsarki, inabi, mahaifa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 05:23
  • Farawa 01:11
  • Luka 08:15
  • Matiyu 03:8
  • Matiyu 07:17

fãda, fãdodi

Ma'ana

Wannan kalma "fãda" ana nufin gini ne ko gida inda sarki ke zama, da shi da iyalinsa da barorinsa.

  • Babban firist shima yana zaune a fãda mai ɗakuna da yawa, kamar yadda aka faɗi a Sabon Alƙawari.
  • Fadodi wurare ne da aka darjanta, da gine-gine masu ado, da kayan ɗaki masu kyau.
  • Gine-gine da kayayyakin fãda an yi su ne da duwatsu ko katakai, yawancin lokaci ana dalaye su da abubuwa masu tsada kamar su zinariya, katakai, da haurin giwa.
  • Mutane da yawa kuma sun zauna a fãda suka yi aiki a harabarta wadda ta ƙunshi ɗakuna da yawa da shirayu.

(Hakanan duba: harabu, babban firist, sarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 28:7-8
  • 2 Sama'ila 11:2-3
  • Daniyel 05:5-6
  • Matiyu 26:3-5
  • Zabura 045:08

faɗakarwa, faɗake-faɗake, faɗake

Ma'ana

Faɗakarwa wani abu ne da yake bada kashedi ga mutane game da wani abin da zai iya cutar su. "A kasance a faɗake" shi ne a zama da damuwa da tsoro game da wani abin dake da hatsari ko neman abkuwa.

  • Sarki Yehoshafat ya sami faɗakarwa lokacin da ya ji cewa Mowabawa suna shirin kawo wa masarautar Yahuda hari.
  • Yesu ya gaya wa almajiransa kada hankalinsu ya tashi sa'ad da suka ji bala'i na faruwa a ƙarshen kwanaki.
  • Wannan furci "sanar da faɗakarwa" ana nufi bada kashedi. A zamanin dã, mutum na iya bada faɗakarwa ta wurin yin ƙãra da wani abu.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan za a "faɗakar da wani" shi ne "za a sa shi ya damu" ko "a dami wani."
  • Zama "a faɗake" za a iya juya shi ya zama "a damu" ko "a tsorata" ko "a damu ainun"
  • Furci haka "bada faɗakarwa" za a iya fassara shi ya zama "faɗaka ga jama'a ko "a yi shelar hatsari na zuwa" ko "a busa ƙaho domin a faɗakar cewa hatsari na zuwa."

(Hakanan duba: Yehoshafat, Mowab)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 11:44-45
  • Irmiya 04:19-20
  • Littafin Lissafi 10:9

fahariya

Ma'ana

Wannan kalma "fahariya' fassararta shi ne girman kai, a fili kuma ƙiriƙiri.

  • Mutum mai fahariya zai ɗaukaka kansa.
  • Yin fahariya yana ƙunshe da tunanin cewa wasu mutane basu da muhimmanci ko kuma basu da baiwa kamar kai kanka.
  • Mutanen da basa ɗaukaka Allah kuma suna tawaye gãba da shi masu girman kai ne domin ba sa shaidar yadda girman Allah yake.

(Hakanan duba: a sanda abu, taƙama, fahariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 04:18
  • 2 Bitrus 02:18
  • Ezekiyel 16:49
  • Littafin Misalai 16:05
  • Zabura 056:1-2

fahariya, girman kai,

Ma'ana

Wannan magana "girman kai" ana nufin mutumin da a tunaninsa shi wani babba ne, kuma masamman yana tunanin yafi sauran mutane.

  • Mutum mai girman kai yawancin lokaci ba yakan amsa laifinsa ba. Ba shi da tawali'u.
  • Girman kai yakan kai ga rashin biyayya ga Allah a hanyoyi da yawa.
  • Wannan magana "girman kai" za a iya amfani da ita ta hanyar dake dai-dai, misali, "fahariya da" wani abin da wani mutum ya yi ko "fahariya da 'ya'yansa. Wannan furci "yin taƙama da aikinka" ana nufin "ka sami murna cikin aikinka domin kana yin sa da kyau.
  • Mutum zai iya taƙama da abin da ya yi ba tare da girman kai ba. Wasu yarurruka suna da maganganu daban domin "'girman kai" mai ma'ana biyu.
  • Wannan magana "girman kai" kullum bashi da kyau, yana da ma'anar "mai gamtsin baki" ko "mai hila" ko "ɗaukaka kansa."

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "girman kai" za a iya fassarata haka, "fahariya" ko "ɗaga kai" ko mai ganin kansa wani abu."
  • A wasu nassosin, za a iya fassara "girman kai" haka, "murna" ko "gamsuwa" ko "jin daɗi."
  • "Yin fahariya da" za a iya fassara shi haka, "farinciki da" ko "gamsuwa da" ko "murna game da (cikawar abu)."
  • Wannan furci "ka yi taƙama cikin aikinka" za a iya fassara shi haka, "ka sami gamsuwarka cikin aikin da kake yi da kyau."
  • Wannan furci "ka yi fahariya da Yahweh" za a iya fassara shi haka, "ka ji daɗi akan dukkan abubuwan al'ajibi da Yahweh ya yi" ko "yi farinciki akan yadda Yahweh yake."

(Hakanan duba: taurin kai, tawali'u, murna)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 03:6-7
  • 2 Korintiyawa 01:12
  • Galatiyawa 06:3-5
  • Ishaya 13:19
  • Luka 01:51

fahimta, fahimci, gane, fahimtar, tunani

Ma'ana

Kalmar "fahimta" na manufar a ji ko karɓar bayani a san me yake nufi.

  • Kalmar "fahimci" na iya nufin "ilimi" ko "hikima" ko ganewa yadda za a iya yin wani abu.
  • A fahimci wani na nufin a san yadda wannan mutum ke ji.
  • Sa'ad da yake tafiya kan hanya zuwa Imawus, Yesu ya sa almajiran suka fahimci ma'anar nassin game da Almasihu.
  • Ya danganta da nassin, kalmar "fahimta" ana iya fassararta haka "sani" ko "yarda" ko "sasancewa" ko "a san menene ma'anar wani abu."
  • Yawanci kalmar "fahimta" ana iya fassara ta da cewa "ilimi" ko "hikima" ko "zurfi."

(Hakanan duba: bangaskiya, sani, mai hikima)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayuba 34:16-17
  • Luka 02:47
  • Luka 08:10
  • Matiyu 13:14
  • Littafin Misalai 03:05

fankama, alfarma

Ma'ana

Kalmar nan "fankama" tana nufin mutum ya zama da girman kai, mutum mai fankama yana tunanin kansa a matsayin babban mutum ne.

  • A sau da yawa wanan kalmar na magana ne akan mutum mai girman kai wanda ya dulmiya cikn yin zunubi ga Allah.
  • Har kullum mutum mai fankama yakan yi taƙama (tunƙaho) da kansa.
  • Mutum mai fankama wawa ne, ba mai hikima ba.
  • Wanan kalmar har ila yau za'a iya fassara ta da "girman kai" ko "daƙiƙanci" ko "ɗaukaka kai"
  • Salon maganar nan "idanu masu alfarmar banza" za'a iya fassara ta da "hanyar dube ta fahariya" ko "duban waɗansu ba 'a bakin komai ba" ko "mutum mai girman kai wanda ke yi wa waɗansu duban reni."

(Hakanan duba: taƙama, girman kai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 03:1-4
  • Ishaya 02:17
  • Misalai 16:18
  • Misalai 21:24
  • Zabura 131:1

fara, fari

Ma'ana

Wannan kalma "fãri" na nufin wasu manyan ƙwari ne masu tashi cikin cincirindonsu su yi ɓarnar cinye dukkan ganyaye da suka tarar.

  • Fãrin nan manya ne, dogaye da fukafukai, kafafunsu na baya suna basu gwanintar tsalle mai nisa.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, an yi kwatanci da cincirindon fãri a matsayin hoton mummunar lalatarwa da zai abko wa Isra'ila saboda rashin biyayyarsu.
  • Allah ya aiko da fãri suka zama ɗaya daga cikin annobai goma da ya aiko gãba da Masarawa.
  • Sabon Alƙawari ya ce ƙwaƙƙwaran abincin Yahaya mai yin baftisma fãri ne sa'ad da yake zaune a jeji.

(Hakanan duba: bawa, Masar, Isra'ila, Yahaya (mai Baftisma))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 06:28
  • Maimaitawar Shari'a 28:38-39
  • Fitowa 10:3-4
  • Markus 01:06
  • Littafin Misalai 30:27-28

farilla, farillai

Ma'ana

Farilla rubutu ne na masamman na shari'a da aka tanada don ta bada jagora ga yadda jama'a zasu zauna.

  • Kalmar "farilla" ma'anarsa kusan ɗaya da "sharuɗɗai" da "doka" da "shari'a". Duk waɗannan kalmomi sun ƙunshi umarnai da buƙatun da Allah ya ba mutanensa ko masu mulki suke ba jama'ansu.
  • Sarki Dauda ya ce ya zaunar da kansa cikin farillan Yahweh.
  • Kalmar "farilla" za a iya fasarta ta da "doka ta masamman" ko "umarni na masamman."

(Hakanan duba: umarni, doka, shari'a, sharaɗi, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 11:11-13
  • Maimaitawar Shari'a 06:20-23
  • Ezekiyel 33:15
  • Littafin Lissafi 19:02

farilla, farillai, ka'idodi, baye-baye, ayyuka, dokoki, shariɗɗu, al'adu

Ma'ana

Ka'idodi shariɗɗu ne dake shugabantar da mutane a kan tafarkin da zasu bi. Wannan kalma ma'anarta ta yi kusan ɗaya da "naɗawa."

  • Wasu lokatai farillai al'adu ne da suka zama tsayayyu domin an saba yin su shekara da shekaru.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, ka'idodi ayyuka ne da Allah ya umarta a yi. Wani lokaci yakan ce a yisu har abada,
  • Wannan magana "ka'ida" za a iya fassara ta zuwa "dokar mutane" ko "ayyuka" ko "shari'a" ya danganta ga nassi.

(Duba kuma: umarni, doka, shari'a, naɗawa, farilla)

Wuraren da za ake samunsa a cikin Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 04:13-14
  • Fitowa 27:20-22
  • Lebitikus 08:31-33
  • Malakai 03:6-7

farinciki, cike da farinciki, jin daɗi

Ma'ana

Farinciki wani yanayi ne na jin daɗi a rai ko gamsuwa mai zurfi dake zuwa daga Allah. Wannan kalma "cike da farinciki" tana maganar wani taliki mai jin daɗi sosai kuma cike da murna mai zurfi.

  • Wani taliki na jin farinciki sa'ad da yake cikin yanayi mai zurfi na cewa abin da yake fuskanta mai kyau ne sosai.
  • Allah shine mai bayar da farinciki na gaskiya ga mutane.
  • Samun farinciki baya dogara ga al'amura masu gamsarwa. Allah na iya ba mutane farinciki ko sa'ad da mawuyatan abubuwa ke faruwa a rayuwarsu.
  • Wasu lokuta ana kwatanta wasu wurare a matsayin cike da farinciki, kamar su gidaje ko birane. Wannan na ma'anar cewa mutanen dake ciki suna cike da farinciki.

Kalmar "farinciki" na ma'anar cike da farinciki da murna.

  • Wannan kalma yawanci na ma'anar zama cikin yanayin murna sosai game da abubuwa masu kyau da Allah yayi.
  • Ana iya fassara ta a matsayin "yin murna sosai" ko "jin daɗi sosai."
  • Sa'ad da Maryamu tace "raina na farinciki cikin Allah Maicetona," tana nufin "Allah Maicetona ya sani murna sosai" ko "Ina jin farinciki sosai saboda abin da Allah Maicetona yayi mani."

Shawarwarin Fassarawa:

  • Kalmar "farinciki" ana iya fassara ta a matsayin "murna" ko "jin daɗi" ko "babbar murna."
  • Faɗin, "yi farinciki" ana iya fassara ta a matsayin "farinciki" ko "yin murna sosai" ko ana iya fassara ta a matsayin "yin farinciki sosai cikin nagartar Allah."
  • Talikin dake cike da farinciki ana iya kwatanta shi a matsayin "mai murna sosai" ko "jin daɗi" ko "murna mai zurfi."
  • Faɗin kamar haka "a yi sowa ta farinciki" ana iya fassara ta a matsayin "a yi sowa ta hanyar da za a nuna murna sosai."
  • "Birni cike da farinciki" ko "gida cike da farinciki" ana iya fassara ta a matsayin "birnin da mutane cike da farinciki ke zama" ko "gida cike da mutane masu farinciki."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Nehemiya 08:10
  • Zabura 048:02
  • Ishaya 56:6-7
  • Irmiya 15:15-16
  • Matiyu 02:9-10
  • Luka 15:07
  • Luka 19:37-38
  • Yahaya 03:29
  • Ayyukan Manzanni 16:32-34
  • Romawa 05:1-2
  • Romawa 15:30-32
  • Galatiyawa 05:23
  • Filibiyawa 04:10-13
  • 1 Tasalonikawa 01:6-7
  • 1 Tasalonikawa 05:16
  • Filimon 01:4-7
  • Yakubu 01:02
  • 3 Yahaya 01:1-4

fasihi, mai saurin fahimta,

Ma'ana

Kalmar "fasihi" na nuna mutum wanda yake da hikima da wayau, musamman a wurin aikata abubuwan zahiri.

  • Yawancin lokaci "fasihi" yana da ma'ana da rabi bata da kyau tunda akan danganta shi da sonkai.
  • Fasihin mutum ya cika mai da hankali kan taimakon kansa, ba waɗansu ba.
  • waɗansu hanyoyin fassara wannan ka iya haɗawa da "wayo" ko "dabara" ko " mai fasaha" ko "mai hikima", ya danganta da inda kalmar ta fito.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:


fassara, yin fassara, fassartacce, aikin fassara sunan fassara, sunayen fassarori, mai yin fassara

Ma'ana

Kalmomin nan yin "fassara" da "suna fassara" na nufin fahimta da kuma baiyana ma'anar wani abu da ba afahimce shi ba sosai.

  • A sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki waɗannan kalmomin an more su ta hanyar fassarar mafarki da wahayi iri-iri.
  • A lokacin da sarkin Babila ya sami waɗansu mafarkai masu rikirkitarwa, Allah ya taimaki Daniyel ya fassara da kuma baiyana ma'anarsu.
  • Yin "fassarar mafarki" yin bayani ne da kumabada ma'anar ta mafarkin.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, a waɗansu lokutan Allah na amfani da mafaki ya baiyana wa mutanensa abin da zai faru a nan gaba. Sabo da haka fassarar waɗannan mafarkai ana yin anabcin su.
  • Kalmar nan "yin fassara" zata iya zama fitar da waɗansu ma'anoni ne na waɗansu abubuwa, kamar yadda yanayi zai kasance bisa ga yadda zafi ko sanyi zai zama ko yadda iska zata zama.
  • Hanyoyin "fassara waɗannan kalmomi" zasu haɗa da, "fito da ma'anar" ko "bayanin kan" yadda wani "al'amari yake."
  • Kalmar nan "fasartawa" zata iya zama "faiyacewa" ko "ma'ana."

(Hakanan duba: Babila, Daniyel, mafarki, annabi, wahayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 12:10
  • Daniyel 04:4-5
  • Farawa 40:4-5
  • Littafin Alƙalai 07:15-16
  • Luka 12:56

fir, fira-firai

Ma'ana

Fir wata irin itaciya ce da kullum tana nan kore shar a cikin dukkan shekara kuma tana da ƙwanso da yake da iri.

  • Itaciyar fir ana kiranta "korayen" bishiyoyi.
  • A kwanakin dã ana amfani da itacen fir domin yin kayayyakin ƙiɗa, da kuma yin waɗansu abubuwa, kamar kayayyakin gine-gine, kwami, gidaje, da haikali.
  • Waɗansu misalai na itatuwan fir da aka ambato a cikin Littafi Mai Tsarki su ne fain, sidar,sifires da yunifar.

(Hakanan duba: sidar, sifires)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 27:4-5
  • Ishaya 37:24-25
  • Ishaya 41:19-20
  • Ishaya 44:14
  • Ishaya 60:12-13
  • Zabura 104:16-18

firgita, firgitarwa, firgice, ta'addanci, tsorata, tsoratarwa, faɗuwar gaba, rawar jiki

Ma'ana

Kalmar "firgita" wani yanayi ne na matuƙar jin tsoro. A "firgita" wani na ma'ana asa wani taliki ya tsorata ƙwarai.

  • "Firgita" shi ne wani abu ko wani kawo babban tsoro da fargaba. Misalin firgita zai iya zama kai farmaki ga rundunar mayaƙan maƙiyi ko annoba ko cuta dake bazuwa, suna kashe mutane da yawa.
  • Waɗannan firgitarwar ana kwatantasu da "firgicewa." Wannan kalmar za a iya fassarawa haka, "abin sa tsoro" ko "abin haifar da tsoro."
  • Hukuncin Allah wata rana zai kawo firgitarwa ga mutane marasa tuba waɗanda suka yi watsi da alherinsa.
  • "Firgitarwar Yahweh" za a iya fassarawa haka "bayyanuwar Yahweh mai firgitarwa" ko "hukuncin Yahweh mai fargaba" ko "sa'ad da Yahweh yasa babban tsoro."
  • Hanyoyin fassara "fargaba" zasu haɗa da "matuƙar tsoro" ko "fargaba mai zurfi."

(Hakanan duba: magabci, tsoro, hukunci, annoba, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 02:25
  • Fitowa 14:10
  • Luka 21:09
  • Markus 06:48-50

fitarwa, korewa, jefarwa, wurgarwa

Ma'ana

  • "Fitarwa" ko "korewa" duk suna nufin a tilasta wa mutum ko wani abu ya tafi daga inda yake.
  • Wannan kalma "fitarwa" ma'anarsu ɗaya da a "jefar." Ma'anar jefa taru shi ne a saki taru cikin ruwa.
  • A cikin misali, "jefarwa" ko "fitarwa" wani zai iya ba su manufar ƙin wani mutum ko kuma korarsa.

Shawarwarin Fasara:

  • Ya danganta ga nassin, ga wasu hanyoyin da za a iya fassarawa, "a fitar da ƙarfi" ko "a kora shi" ko "a rabu da."
  • Wannan furci "idan za a fitar da al'jannu" za a iya fassara shi haka "a sa al'jannun su fita" ko "a kori mugun ruhun waje" ko "a kori al'jannun" ko "a umarci al'jan ɗin ya fita."

(Hakanan duba: aljani, mai aljani, tuli)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:17-19
  • Markus 03:13-16
  • Markus 09:29
  • Matiyu 07:21-23
  • Matiyu 09:32-34
  • Matiyu 12:24
  • Matiyu 17:19-21

fitila, fitilu

Ma'ana

Kalmar "fitila" a taƙaice ana nufin abin da ke bada haske. Fitilun da aka yi amfani dasu a zamanin Littafi Mai tsarki fitilu ne dake amfani da mai. Irin fitilar da aka yi amfani da ita a zamanin Littafi Mai tsarki wani ƙaramin kasko ne dake da mazurarar mai haɗe da shi, wanda ke bada haske idan aka ƙona.

  • Ita dai fitilar mai dãma kasko ne da ake cikawa da man zaitun, sai a saka zaren lagwani cikin man domin a ƙona.
  • Game da wasu fitilun, tukunyar ko butar na da siffar tulu ne, wanda ake yi wa ƙarshen wata 'yar kafa domin ta iya riƙe zaren lagwanin.
  • Ana iya riƙe fitilar mai ko a ɗauke ta a ɗora a mazauni domin hasken ta ya cika ɗakin ko gidan.
  • A cikin nassi, ana amfani da fitilu a hanyoyin misalai da yawa a matsayin alamar haske da rai.

(Hakanan duba: mazaunin fitila, rai, haske)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 11:36
  • Fitowa 25:3-7
  • Luka 08:16-18
  • Matiyu 05:15
  • Matiyu 06:22
  • Matiyu 25:03

furci, furtawa, furtacce, wanda ake furtawa, aikin furtawa, abubuwan da aka furta, shela, shelantarwa, wanda aka yi shela, wanda aka sa aka sani, ambato, ambatacce, wanda ake ambato, wanda aka faiyacce

Ma'ana

Kalmar furci na ma'anar "furtawa" wato a ambaci abu cikin tsari a furta wa mutane da kuma jaddada wani abu.

  • "Furci ba wai magana ba ce kawai" ba kuma furta muhimmancin abin da ake furtawa bane kawai, amma jan hankali ne ga wandda ke yin furcin.
  • Misali, a cikin Tsohon Alƙawari saƙo daga Allah yakan zo ne ta wurin "furcin Yahweh" ko kuma "wannan shi ne furcin Yahweh." Wannan batun na jaddada cewa Yahweh ne da kansa yake faɗin wannan. Duk da cewa saƙon ya zo daga Yahweh yana nuna mahimmancin saƙon.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin "furci" za a iya fassara shi da cewa "shela ce" ko "yin shela a cikin bainar mutane" ko "saƙo mai ƙarfi" ko "jan hankalin ƙasa."
  • Kalmar nan "Furci" za'a iya fassara ta a matsayin "bada bayani" ko "shelantawa."
  • Kalmar nan "wannan furcin Yahweh ne" za'a iya fassara ta da cewa "wannan shine abin da Yahweh ya faɗi."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 16:24
  • 1 Korintiyawa 15:31-32
  • 1 Sama'ila 24:17-18
  • Amos 02:16
  • Ezekiyel 05:11-12
  • Matiyu 07:21-23

fushi, yin fushi, haushi

Ma'ana

"Yin fushi" ko a ce "ina da fushi" ana nufin rashin gamsuwa, cakuna da tashin hankali game da wani abu ko gãba da wani.

  • Sa'ad da mutane suka yi fushi, yawancin lokaci zunubi ne da son kai, amma wani lokaci fushi ne mai adalci domin an yi shi ne gãba da rashin adalci da ya auku.
  • Fushin Allah (ana kiransa "hasala") yana nuna zafin rashin jin daɗinsa game da zunubi.
  • Wannan furci "cakuna don ayi fushi" yana nufin "tayar da ɓacin rai."

(Hakanan duba: hasala)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Afisawa 04:26
  • Fitowa 32:11
  • Ishaya 57:16-17
  • Yahaya 06:52-53
  • Markus 10:14
  • Matiyu 26:08
  • Zabura 018:08

fuska, fuskoki, fuskanta,fuskanci, na fuskanta, fuskanci ƙasa

Ma'ana

Kalmar nan fuska tana nufin sahshen gaba kan mutum. Wanan kalma tana da salon magana mai ma'ana da yawa.

  • Ƙaulin nan "fuskaka" a sau da yawa salon magana ne na cewa "kai" kamar dai kalmar nan "fuskata" wadda take nufin "ni."
  • A ma'ana ta fili, a fuskanci wani ko wani abiu na nufin a dubi inda wanan mutum ko wanan abin yake.
  • A "fuskanci juna" na nufin a kalli juna kai tsaye."
  • "Fuska da fuska" na nufin mutane biyu na kallon juna a zahirance, a kusa kusa.
  • Da Yesu ya "fuskanci Yerusalem," wanan na nufin yana da ƙudiri na tafiya Yerusalem.
  • A "juya wa wani fuska" ko mutane ko birni wanan na nufin aƙi goyon baya ko kuma aƙi wanan mutumin baki ɗaya.
  • Kalmar nan "fuskar ƙasa" tana nufin illahirin duniya kuma kusan kullum ana moron ta ne don a baiyana dukkan duniya. Misali, "yunwa da ta rufe fuskar duniya" wanan na nufin bazuwar yunwa ne ko'ina a duniya wadda ta shafi dukkan mutanen da ke rayuwa a duniya.
  • Salon maganar nan "kada ka ɓoye mini fuskarka" na nufin "kada ka ƙi mutanenka" ko "kada ka yashe da mjutanenka"ko "kada ka dena lura da mutanenka."

Shawarwarin Fassara:

  • Idan mai yiwuwa ne, ya fi kyau amori kalmar da tayi daidai da kalmar a harshen da ake so ayi wa fassara.
  • Kalmar nan "fuska" za'a iya fassara ta da "juyowa"ko ko a "fuskanci wurin kai tsaye" ko a "duba fuskar abin."
  • Ƙaulin nan "fuska da fuska" za'a iya fassara shi da "duba na ƙut" ko na "ido da ido" ko "kallon tsabar ido."
  • Ya danganta da abin da ke wurin, ko a "gaban idonsa" za'a iya fassara shi da a "gabansa" ko "yana wurin"
  • Ƙaulin nan "ya juya fuskarsa wurin," za'a iya fassara shi da "ya doshi wurin" ko kuma "ya tunkari wurin."
  • Ƙaulin nan "ya ɓoye fuskarsa" za'a iya fassara shi da ya juya baya daga wurin," ko "ya dena taimako" ko "kariya" ko kuma ya "ƙi."
  • Ya juya fuskarsa "gãba" da birnin ko "mutanen, za'a iya fassara wanan da " ko "fushi" da kuma "hallakarwa" ko "ƙin karɓa" ko ɗaukan mataki na "ƙiyayya" da kuma saukar da hukunci a kai."
  • Ƙaulin nan "ka faɗa musu a fuskokinsu" za'a iya fassara shi da "ka faɗa musu kai tsaye" ko "ka faɗa musu a gabansu" ko "ka faɗa musu kai da kanka,"
  • Ƙaulin nan "a fuskar ƙasa" za'a iya fassara shi da "ko'ina cikin ƙasar"ko "a cikin dukkan ƙasar" ko "ga mazaunan dukkan ƙasar."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 05:04
  • Farawa 33:19

fyaɗi, sussukewa, sussukarwa, sussuka

Ma'ana

Kalmar "fyaɗi" ko "sussuka" na nufin fanni na farko na raba alkama da hatsi daga sauran zangarniyar.

  • Sussukar alkama na raba hatsin daga harawar da zangarniyar. Daga baya sai a "sheƙe" hatsin domin a ware hatsin gabaɗaya daga dukkannkayan da ba a so, sai a bar fannin hatsin da za a iya ci.
  • A lokutan Littafi Mai Tsarki, "masussuka" wani babban dutse ne mai fãɗi ko wani wuri da ake kwashe juji, wanda ke bada wuri mai ƙarfi, da sarari miƙaƙƙe wanda zai iya murje zangarkun hatsin ya fitar da hatsin.
  • Wasu lokuta ana amfani da "keken sussuka" ko "gargaren sussuka" a murje hatsi a kuma raba su daga harawar da zangarniyar.
  • Ana kuma amfani da "injin sussuka" ko "fai-fan sussuka" a ware hatsi. Ana yi masu haƙoran katako ko ƙarfe a ƙarshen su.

(Hakanan duba: harawa, hatsi, shiƙa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 03:1-3
  • 2 Sarakuna 13:07
  • 2 Sama'ila 24:16
  • Daniyel 02:35
  • Luka 03:17
  • Matiyu 03:12
  • Rut 03:1-2

gabagaɗi, ƙarfin hali, nacewa

Ma'ana

Dukkan waɗannan kalmomi suna nufin ƙarfin zuciya da jigon faɗar gaskiya da yin abin dake dai-dai koda shike yana da wuya da hatsari kuma.

  • Mutum mai "gabagaɗi" baya jin tsoron yin abu da faɗar abin da ke nagari da kuma abin dake dai-dai, kamar su kare mutane da ake wulaƙantasu. Za a iya fassara wannan ya zama "ƙarfin hali" ko "marar tsoro."
  • A cikin Sabon Alƙawari, almajirai suka ci gaba da yin wa'azi "gabagaɗi" game da Almasihu a wuraren tattaruwar jama'a, koda shike akwai hatsarin jefawa a kurkuku ko kisa. Za a iya fassara wannan haka "da ƙarfin hali" ko "tare da ƙarfin hali" ko "nacewa."
  • Irin "gabagaɗin" almajirai na farko cikin yaɗa labari mai daɗi na mutuwar fansa akan gicciye da Almasihu ya yi, ya sa bishara ta yaɗu a dukkan Isra'ila da maƙwabtan ƙasashe har ya iyakar duniya. Za a kuma iya fassara "gabagaɗi" haka "ƙarfin hali da gabagaɗi."

(Hakanan duba: gabagaɗi, labari mai daɗi, fansa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:28
  • 1 Tasalonikawa 02:1-2
  • 2 Korintiyawa 03:12-13
  • Ayyukan Manzanni 04:13

gaɓa, gaɓoɓi, gaɓar jiki

Ma'ana

Wannan kalma "gaɓa" ana nufin ɓangare guda na sassan jiki ko ƙugiya mai yawa.

  • Sabon Alƙawari ya fayyace Kiristoci "gaɓoɓin" jikin Kristi ne. Masu bada gaskiya ga Almasihu suna cikin ƙungiyar da take da gaɓoɓi da yawa.
  • Yesu Kristi shi ne "kan" jiki, kowannen mu kuma gaɓar jikin ne. Ruhu mai Tsarki yana ba kowanne gaɓan jiki baiwa ta musamman domin taimakon jiki gabaɗaya ya yi aiki da kyau.
  • Kowanne mutum guda dake aiki cikin ƙungiyoyi kamar su Majalisar Yahudawa da ta Farisawa ana kiransu "gaɓoɓin" waɗannan ƙungiyoyin."

(Hakanan duba: jiki, Farisawa, majalisa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 06:15
  • 1 Korantiyawa 12:14-17
  • Littafin ‌Lissafi 16:02
  • Romawa 12: 05

gami, yisti, tsimi, mai gami, marar gami

Ma'ana

"Gami" kalma ce da ake morarta wurin bayyana wani abu dake sa ƙullin fulawa ya faɗaɗa ya kuma tashi. "Yisti" wani irin gami ne na musamman.

  • A wasu fassarorin turanci, kalmar gami ana fassara ta a matsayin "yisti" wanda kayan gami ne na zamani wanda ke cika curin ƙullin filawa da kunfan iska, wanda ke sanya ƙullin ya faɗaɗa kafin a gasa shi. Ana markaɗe yistin cikin curin ƙullin filawar domin ya bazu ya game dukkan curin ƙullin.
  • Zamanin Tsohon Alƙawari, yadda ake yin gamin ko abin sa kumburi shi ne ana ajiye ƙullin da aka cura na ɗan lokaci kaɗan. Ana ajiye kaɗan daga cikin ƙullin da aka yi amfani da su a baya domin yin amfani da su cikin wani ƙullin da za ayi a gaba.
  • Lokacin da Isra'ilawa suka kuɓuta daga Masar, basu sami lokacin da har zasu jira ƙullin ya tashi ba, saboda haka sai suka yi gurasa marar gami da zasu yi guzuri a kan hanya. Domin tunasshewa kan wannan, Yahudawa kowacce shekara suna yin Bikin ƙetarewa ta wurin cin gurasa marar gami.
  • Kalmar "gami" ko "yisti" ana moriyarta ne a bayyana cikin Littafi Mai Tsarki yadda zunubi ke bazuwa ko'ina cikin dukkan rayuwar mutum ko kuma yadda zunubi ke rinjayar wasu mutane.
  • Yana iya zama kuma koyarwar ƙarya wadda ke bazuwa ga mutane dayawa har ya rinjayesu.
  • Kalmar "gami" ana kuma yin amfani da ita a bayyana yadda mulkin Allah ke bazuwa bisa mutane daga mutum ɗaya zuwa ga wani.

Shawarwarin Fassara:

  • Za a iya fassara wannan a matsayin "gami" ko "abin da ke sanya curin ƙulli ya tashi" ko "abin sanya faɗaɗa." Kalmar "tashi" za a iya bayyana ta a matsayin "faɗaɗa" ko "ya yi girma" ko "ya kumbura."
  • Idan aka yi amfani da kayan gami na gargajiya domin asa curin ƙullin yin gurasa ya tashi, za a iya amfani da wannan kalmar. Idan yaren yana da sanannar kalmar da aka fi amfani da ita, wadda ke ma'anar, "gami," zai fi kyau ayi amfani da kalmar.

(Hakanan duba: Masar, Ƙetarewa, gurasa marar gami)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 12:08
  • Galatiyawa 05:9-10
  • Luka 12:1
  • Luka 13:21
  • Matiyu 13:33
  • Matiyu 16:08

garaya mai ƙoƙo, gara, garayu

Ma'ana

garaya da garayu wasu ababen waƙane masu tsarkiyu da Isra'ilawa suka yi amfani da su su yiwa Allah sujada.

  • Ita garaya tayi kama da ɗan ƙaramin molo, tana da tsarkiyoyi da suka bi ta kan fuskarta.
  • Garaya mai ƙoƙo tana kama da gita ta zamani, da wani ɗan akwatin katako da dogon wuya da tsarkiya ta bi kai.
  • Idan za a kaɗa garaya, za a danne wasu igiyoyi da yatsun hannu guda sa'an nan a kaɗa igiyoyin da yatsun ɗaya hannun.
  • Da garaya da molo ana kaɗa su ta wurin ja da danna tsarkiyoyinsu.
  • Yawan tsarkiyoyin sun bambanta, amma Tsohon Alƙawari musamman ya yi magana a kan kayan kiɗi masu tsarkiyoyi goma.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 10:11-12
  • 1 Sama'ila 10:5-6
  • 2 Tarihi 05:11-12

gargaɗi, kashedi

Ma'ana

Kalmar nan "gargaɗi" bada kashedi ne ko bada shawara ga wani.

  • Yawancin lokaci ma'anar "gargaɗi" bada shawara ne ga wani kada ya yi wani abu.
  • A jikin Almasihu, ana koya wa masu bi su gargaɗi juna domin a guje wa zunubi kuma mu yi zaman tsarki.
  • A maimakon "gargaɗi" zamu iya juya shi ya zama "ƙarfafawa domin kada a yi zunubi" ko "faɗakar da wani kada ya yi zunbi."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Nehemiya 09:32-34

garkuna, garke, yin garke, garka, garkar dabbobi

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki "garke" na nufin wataƙungiya ta tumakin ko awaki da "garka" kuma na nufin rundunar shanu ko ta aladu.

  • Harsuna da bam daban na da mabambantan hanyoyi na ba garkunan dabbobi suna ko kuma tsuntsaye.
  • A misali, a Ingilishi shima yana moron ƙungiyar dabbobi domin ambaton garken dabbobi.
  • A ayoyin da aka ambaci "garkuna da kumarunduna" domin yin ƙari da "tumaki" misalin idan harshen ba shi da wani suna domin ambaton dabbobi iri-iri.

(Hakanan duba: akuya, sa, alade, tunkiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 10:28-29
  • 2 Tarihi 17:11
  • Maimaitawar Shari'a 14:22-23
  • Luka 02:8-9
  • Matiyu 08:30
  • Matiyu 26:31

garma, garemani, masu huɗa, mai huɗa, ƙasar da ba a yi mata huɗa ba

Ma'ana

"Garma" wani kayan gona ne da ake amfani da shi domin pasa ƙasa saboda a shirya ta domin shuka

  • Garemani suna da fila-filai masu tsini masu shiga ƙasa. yawancin lokaci suna da mariƙi da manomi ke amfani da su ya bida garmar.
  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, shanu biyu ke jan garma ko wasu dabbobi.
  • Yawancin garemani an yi su ne da ice mai tauri, sai ko 'yan fila-filan masu tsini da aka yi su da ƙarfe, kamar su tagulla ko baƙin ƙarfe.

(Hakanan duba: tagulla, bijimi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 08:10-12
  • Maimaitawar Shari'a 21:04
  • Luka 09:07
  • Luka 17:07
  • Zabura 141:5-7

gatari, gatura

Ma'ana

Gatari ƙotace mai ruwan ƙarfe ana amfani da ita domin sara ko sare itatuwa.

  • Yawancin lokaci gatari yana da dogon makami na itace da ƙatuwar wuƙar ƙarfe ƙarshenta.
  • Idan a al'adarku kuna da wani abu haka mai kama da gatari, sai a yi amfani da shi a fassara "gatari."
  • Ga wasu hanyoyin fassara "gatari" za a ce, "abin yanka itace" ko "katako mai wuƙa" ko katako mai dogan mariƙi domi sara."
  • A cikin wani sha'ani a Tsohon Alƙawari, ruwan gatari ya faɗa cikin rafi, saboda haka yana da kyau idan abin da ake fassararsa yana da ruwan ƙarfe da zai iya faɗuwa daga makamin itacensa.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 06:7-8
  • 2 Sarakuna 06:05
  • Littafin Alƙalai 09:48-49
  • Luka 03:9
  • Matiyu 03:10
  • Zabura 035:03

gida, gidaje, saman gidaje,samman gidaje, ɗakin ajiya, ɗakunan ajiya, masu tsaron gidaje

Ma'ana

Kalmar nan "gida"akan more ta cikin salon magana a cikin Littafi mai Tsarki ba.

  • Waɗansu lokutan tana nufin "dukkan abin da ke cikin gida" wato tana magana akan mutanen da ke zama a cikin gidan.
  • Sau dayawa "gida" na nufin zuriyar mutum ko sauran dangi. Misali, kalmar nan "gidan Dauda" na nufin dukkan zuriyar sarki Dauda.
  • Kalmar nan "gidan Allah" da "gidan Yahweh" tana nufin haikali ko bukka. Waɗannan kalmomi za su iy nufin inda Allah ke zama.
  • A cikin Ibraniyawa 3, "gidan Allah" an more shi a matsayin wani manuni domin a ambaci mutanen Allah ko kai tsaye a ambaci duk wani abu dake da nasaba da Allah.
  • Kalmar nan "gidan Isra'ila" zata iya nufin dukkan al'ummar Isra'ila.

Shawarwarin Fassara

  • Ya danganta ga wurin, za'a iya fassara "gida" da "dukkan iyali" ko "mutane" ko "iyali" ko "haikali" ko wurin zama."
  • Kalmar nan "gidan Dauda" za'a iya fassara ta da "kabilar Dauda" ko "iyalin Dauda" ko "zuriyar Dauda," duk wani abu da ke da nasaba da wannan za'a iya yin fassararsa kamar haka.
  • Hanyoyi da yawa da za'a iya fassara "gidan Isra'ila" sun haɗa da "mutanen Isra'ila" ko " zuriyar Isra'ila" zuriyar Isra'ilawa,"
  • Kalmar nan "gidan Yahweh" za'a iya fassara ta da "haikalin Yahweh" ko "wurin da ake bautawa Yahweh" ko "wuri inda Yahweh ke saduwa da mutanen sa" ko wurin da Yahweh ke zama."
  • "Gidan Allah" za'a iya fassara ta ta irin wannan hanya.

(Hakanan duba: Dauda, zuriya, gidan Allah, dukkan iyali, mulkin Isra'ila, bukka, haikali, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:42
  • Ayyukan Manzanni 07:49
  • Farawa 39:04
  • Farawa 41:40
  • Luka 08:39
  • Matiyu 10:06
  • Matiyu 15:24

gigita, gigitacce, na na gigitarwa, mai gigitarwa, aikin gigitarwa, abin da ke gigitarwa, abin da ke kawo gigitarwa, abubuwan abubuwan gigitarwa

Ma'ana

Kalmar nan "gigita" tana nufin wani zuzzurfan jin tsoro ne na wata masifa duk wanda ke cikin irin wanan hali sai ace "ya gigice."

  • Gigita akan jita ne kuma ta wuce ainahin tsoro na ɗan wani abu.
  • Hakika duk lokacin da wani ya gigice ya shiga yanayin ɗimauta.

(Hakanan duba: tsoro, gigita)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 28:37
  • Ezekiyel 23:33
  • Irmiya 02:12-13
  • Ayuba 21:4-6
  • Zabura 055:05

ginsi, ginsosi,

Ma'ana

Kalmar "jinsi" ko "jinsosi" suna nufin ƙungiyoyi ko rukunonin abubuwa waɗanda keda dangantaka da juna a ɗabi'arsu.

  • A cikin Littafi Mai tsarki, ana amfani da wannan kalma musamman wajen bambantawa tsakanin ire-iren itatuwa da na dabbobi waɗanda Allah ya yi da ya halicci duniya.
  • Yawanci akwai bambanci iri-iri a cikin kawanne "jinsi." Misali, dawakai, alfadarai, da jakuna dukkan su 'yan "jinsi" iri ɗaya ne, amma rukuni daban-daban.
  • Babban abin da ya bambanta kowanne "jinsi" a matsayin ƙungiya daban shi ne 'yan waɗannan ƙungiya suna haihuwar irin "jinsinsu." 'Yan ƙungiyar rukuni daban basu iya yin haka da juna.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara wannan kalma na iya haɗawa da "iri" ko "aji" ko "ƙungiya" ko "ƙungiyar itatuwa da dabba" ko "rukuni."

Wuraren da ake samunsu a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 01:21
  • Farawa 01:24
  • Markus 09:29
  • Matiyu 13:47

giraya, girayu, mai giraya, masu giraya

Ma'ana

Giraya wani kayan kiɗa ne, da ke da sanda tsaye da ɗan wani komo wanda ke ɗaure da tsarkiyoyi ko lilo.

  • A kwanakin Littafi Mai Tsarki ana moron itacen fir domin yin girayu da sauran waɗansu kayayyakin kiɗa.
  • A mafi yawan lokuta akan riƙe girayu ne a hanu ana kaɗa su a lokacin tafiya.
  • A wurare da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki, girayu an baiyana girayu a matsayin kayan kiɗa da ake mora a yabi Allah da kuma yi masa sujada.
  • Dauda ya rubuta zabura da yawa waɗanda aka tsara su ta samfarin giraya.
  • Hakanan ya kaɗa wa Sarki Saul domin kwantar da mugun ruhun da ke damun sarki.

(Hakanan duba: Dauda, fir, zabura, Saul (Tsohon Al‌ƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 15:16-18
  • Amos 05:23-24
  • Daniyel 03:5
  • Zabura 33:1-3
  • Wahayin Yahaya 05:8

girbi, girbe-girbe, girbewa, mai girbi, magirba,

Ma'ana

Kalmar "girbi" na manufar girbi na hatsi. Magirbi shi ke girbin hatsin.

  • Magirba na girbin hatsi da hannunsu, suna tuge dashen ko su yanka su da abin yanka.
  • Kalmar girbi ana amfani da ita ne a bayyana yadda ake shelar bisharar Yesu domin kawo mutane ga iyalin Allah.
  • Ana kuma nuna yadda mutum ke samun ladar ayyukansa na cewa "mutum ya girbi abin da ya shuka."
  • Wasu hanyar fassarar na nufin a yi girbi da kuma magirbi.

(Duba kuma: bishara, girbi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 06:9-10
  • Matiyu 06:25-26
  • Matiyu 13:30
  • Matiyu 13:36-39
  • Matiyu 25:24

girmamawa, bada girma, girmama

Ma'ana

Kalmar "girmamawa" na manufar yanayi na zurfin, bangirma ga wani ko wani abu. Girmama wani ko wani abu kana nuna girman wannan mutum ko abu.

  • Wannan yanayin na nunawa ne ta ayyukan mutum ta girmama wanda ake girmamawa.
  • Tsoron Ubangiji na can cikin girmamawar da mutum ke nunawa ta aikin biyayyarsa ga dokokin Allah.
  • Ana iya fassara kalmar a ce "tsoro da bangirma" ko "girmamawa da gaske."

(Hakanan duba: tsoro, bangirma, biyayya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:15-17
  • Ibraniyawa 11:7
  • Ishaya 44:17
  • Zabura 005:7-8

gofa

Ma'ana

Wannan kalma "gofa" wani irin itacen fir ne da yake da yawa a yankin da mutane ke zaune a lokacin Littafi Mai Tsarki, musamman ƙasashen dake gaɓas da Tekun Baharmaliya.

  • Sifrus da Lebanon wurare ne biyu da Litttafi Mai Tsarki ya ambace su musamman suna da itatuwan gofa da yawa.
  • Katakan da Nuhu ya gina jirgi mai yiwuwa na gofuna ne.
  • Saboda itacen gofa yana da kauri ga iya daɗewa, mutanen dã sun yi amfani da su domin gina kwale kwale da kuma wasu gine gine.

(Hakanan duba: akwati, Sifuros, itacen fir, Lebanon)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 11:19-21
  • Farawa 06:14
  • Hosiya 14:08
  • Ishaya 44:14
  • Ishaya 60:13
  • Zakariya 11:02

gonar inabi, gonakin inabi

Ma'ana

Gonar inabi babban wuri ne inda aka renon kuringar inabi kuma ake yin noman inabi.

  • Gonar inabi ana zagaye ta da shinge domin ta kãre amfanin gonar daga ɓarayi da kuma dabbobi.
  • Allah ya kwatanta Isra'la kamar kuringar inabin da bata bãda 'ya'ya masu kyau ba.
  • Ana iya fassara kuringar inabi a matsayin "lambun gonar inabi" ko "dashen inabi."

(Hakanan duba: inabi, Isra'ila, itacen inabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 09:20-21
  • Luka 13:06
  • Luka 20:15
  • Matiyu 20:02
  • Matiyu 21:40-41
  • Matiyu 21:40-41

gudu, tsere, gudu, mai tsere, masu tsere, yin tsere, fusata, cikin hanzari, rugawa da sauri, kwararowa, watsarwa, tarwatsarwa, zubowa, tsallakewa, haurawa, tafiya da sauri

Ma'ana

A yi "gudu" na manufar "tafiya cikin sauri da ƙafafu," fiye da yadda za a iya yi idan ana tafiya.

Wannan kalmar ana amfani da ita ne a yi bayani kamar a ce: A "yi tsere ta yadda za a sami nasara"- ma'ana yin nufin Allah da naciya kamar yadda ake yi kamar ana gasar cin nasara a wasanni. Yin "tsere a cikin hanyar umarninka" - na manufar cewa ka yi murna da hanzarta yin biyayya da dokokin Allah. "Bin wasu alloli" na manufar naciya da yin sujada ga wasu alloli. "Na gudu zuwa gare ka domin ka ɓoye ni" na manufar juyawa ga Allah cikin sauri domin neman mafaka a lokacin da kake fuskantar matsaloli. Ruwa da wasu abubuwa masu gudu kamar hawaye, jini, zufa, da kuma kogi ana iya cewa suna "kwararowa." Ana kuma iya cewa suna "zubowa." Iyakar wani ƙasa ko yanki ana iya cewa ya "tafi har" zuwa ga kogi ko iyakar wata ƙasar. Wato wannan ƙasar na "daura" da kogi ko wata ƙasa. Kogi da kwararrafai na iya "bushewa," ma'ana babu sauran ruwa cikinsu kuma. Ana iya cewa "sun bushe" ko "sun zama busassu." Kwananakin bukukuwa na ɗaukar lokutansu," ma'ana "sun wuce" ko "sun ƙãre" ko "sun tsaya."

(Hakanan duba: allolin ƙarya, jimiri, mafaka, juyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 06:18
  • Galatiyawa 02:02
  • Galatiyawa 05:07
  • Filibiyawa 02:16
  • Littafin Misalai 01:16

gulɓatattun shedu, rahoton ƙarya, shedar ƙarya, mashedi na ƙarya, masu shedar ƙarya

Ma'ana

Kalmar nan "mashedi na ƙarya" da "gulɓataccen mashedi" tana nufin mutumin wanda ke faɗar abin da na gaskiya ba game da wani ko kan wani al'amari, har kullum akan tsara hakan ne musamman a kotu.

  • "Shedar ƙarya" ko "rahoton ƙarya" wanan tsintsigarin ƙarya ce da aka faɗa.
  • A bada "shedar ƙarya" wanan na nufin ayi ƙarya ko kuma a bada rahoton ƙarya game da wani al'amari.
  • Littafi mai tsarki ya bada misalai da yawa na yadda ake yin hayar shedun ƙarya su yi wa wani ƙarya domin a hukunta mutumin ko kuma a kashe shi.

Shawarwarin Fassara:

  • A bada "shedar ƙarya" ko "shedu na ƙarya" za'a iya fassara shi da yin wani "furci na ƙarya" ko kuma bada "rahoton ƙarya game da wani" ko yiwa wani ƙarya.
  • Idan ana maganar "shedar ƙarya" game da mutum, za'a iya fassara ta da "mutumin da ya faɗi "ƙarya" ko kuma ya yi "shedar ƙarya" ko kuma mutumin da ya faɗi "abubuwan da ba gaskiya ba."

(Hakanan duba: sheda, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 19:19
  • Fitowa 20:16
  • Matiyu 15:18-20
  • Matiyu 19:18-19
  • Littafin Misalai 14:5-6
  • Zabura 027:11-12

gulma, yin gulma, magulmaci, mai magana mara kangagado

Ma'ana

Kalmar nan "gulma" tana nufin yin maganar abin da ya shafi rayuwar wani, sau da yawa ta hanyar da bata dace ba, ko ta hanyar ɓatanci, kuma sau da dama abin da ake faɗar ba'a tabbatar da gaskiyarsa ba.

  • Littafi Mai Tsarki ya ce baza labaranda basu dace ba game da wani bai kamata ba, gulma da tsegumi na ɗaya daga cikin waɗanan misalan irin wanan maganar marar dacewa.
  • Gulma tana da cutarwa ga wanda aka yi gulma a kansa, domin takan shafi dangantakar mutumin da sauran mutane.

(Hakanan duba: tsegumi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 05:13
  • 2 Korintiyawa 12:20
  • Lebitikus 19:15-16
  • Littafin Misalai 16:28
  • Romawa 01:29-31

gurasa

Ma'ana

Gurasa abinci ne da ake yinsa daga gari cuɗe da ruwa da mai sai ayi ƙullu. Wannan ƙullun za a yanyanka a cuccura su sa'annan a gasa.

  • Sa'ad da kalmar nan "curi" tana ita kaɗai, ana nufin "curin gurasa" ne.
  • Akan yi ƙullun gurasa yawancin lokaci da wani abin da yake sa shi ya kumbura, kamar gamin yisti.
  • Za a iya yin gurasa ba tare da gamin yisti ba saboda haka ba zai tashi ba. A cikin Littafi Mai Tsarki ana ce da wannan "gurasa marar gami" ana amfani da shi domin abincin idin ƙetarewa na Yahudawa.
  • Da shike gurasa shi ne babban abinci na mutane da yawa a lokacin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma ana amfani da ita cikin Littafi Mai Tsarki a kamanta dukkan abinci.
  • Wannan kalma "gurasar da aka miƙa ga Allah" yana magana akan curin gurasan nan goma shabiyu da aka sa akan tebur na zinariya a rumfar taruwa ko haikali wadda hadaya ne ga Allah. Waɗannan gurasa kabilun Isra'ila ne goma shabiyu kuma don firist ne kaɗai zai ci. Za a iya fassara wannan haka "gurasar da ta nuna Allah yana zaune tsakiyar su."
  • Wannan misalin kalmar, "gurasa daga sama" ana faɗin wannan farin abinci na musamman da ake kira "manna" wanda Allah ya tanada domin Isra'ilawa lokacin da suke ta yawo a hamada.
  • Yesu kuma ya kira kansa "gurasar da ta zo daga sama" da kuma "gurasar rai."
  • Lokacin da Yesu da almajiransa suke cin abincin Idin ‌Ƙetarewa tare kafin mutuwarsa, ya kwatanta gurasa marar gami na ‌Ƙ‌etarewa da jikinsa da za a ƙuje a kuma kashe akan gicciye.
  • Sau da yawa wannan kalma "gurasa" za a iya fassarata ace "abinci."

(Hakanan duba: Ƙetarewa, rumfar sujada, haikali, gurasa marar gami, yisti)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:46
  • Ayyukan Manzanni 27:35
  • Fitowa 16:15
  • Luka 09:13
  • Markus 06:38
  • Matiyu 04:04
  • Matiyu 11:18

gwaji, gwaje-gwaje, tabbatarwa

Ma'ana

Kalmar "gwaji" na nufin wani yanayi ne inda wani abu ko wani taliki ke shan "gwaji" ko jarabawa.

  • Gwaji zai iya zama sauraren ƙara domina tabbatar da ko wani taliki marar laifi ne ko mai laifin abin da ake tuhuma.
  • Kalmar "gwaji" zai kuma iya zama mawuyacin yanayi da wasu talikai ke fuskanta sakamakon gwajin bangaskiyarsu da Allah ke yi. Wata kalmar wannan ita ce "a jaraba" ko "jarabawa" wani irin gwaji ne
  • Mutane da yawa a Littafi Mai Tsarki sun fuskanci jarabawa domin a ga ko zasu ci gaba da gaskatawa da biyayya da Allah. Sun sha gwaje-gwaje waɗanda suka haɗa da duka, sanyawa kurkuku, ko kashesu ma saboda bangaskiyarsu.

(Hakanan duba: gwadawa, jarabawa, marar laifi, mai laifi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 04:34
  • Ezekiyel 21:12-13
  • Littafin Makoki 03:58-61
  • Littafin Misalai 25:7-8

gyale, gyalulluka, lulluɓewa, kware lulluɓi

Ma'ana

Kalmar "gyale" na bayyana wata sutura marar kauri da ake amfani da ita domin rufe kai, a rufe kai ko fuska domin kada a ganta.

  • Musa ya rufe fuskarsa da gyale bayan da ya zauna a gaban Yahweh, domin walƙiyar fuskarsa shi ɓoyu ga mutanen.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, mataye suna rufe kansu da gyale, lokatai da dama kuma har da fuskarsu, idan suna cikin mutane ko inda mazaje suke.
  • Kalmar aiki "gyale" na nufin a rufe wani abu da gyale.
  • A wasu fassarorin, kalmar "gyale" ana morarsu a kira labule mai kauri da ya rufe mashigin wuri mafi tsarki. Amma "labule" yafi dai-dai a yi amfani da shi a wannan nassin, domin yana da kauri, yadi mai kauri.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "gyale" za a iya fassarawa haka "suturar lulluɓewa marar kauri" ko "suturar lulluɓewa" ko "abin lulluɓe kai."
  • Wasu al'adun, za ya iya kasancewa suna da kalmar gyale domin mata. Zai zama da muhimmanci a sami wata kalmar daban idan za a yi amfani da ita game da Musa.

(Hakanan duba: Musa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 03:12-13
  • 2 Korintiyawa 03:16
  • Ezekiyel 13:18
  • Ishaya 47:1-2
  • Waƙar Suleman 04:3

hadaya, hadayu, hadayar, yin hadaya, baiko, baye-baye

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Mai Tsarki, kalmomin nan "hadaya" da "baiko" na nuna kyautai na musamman da ake bayar wa ga Allah domin yi masa sujada. Haka mutane na miƙa hadayu ga allolin ƙarya.

  • kalmar "baiko" na nufin kowanne abu da aka miƙa ko bayar. Kalmar "hadaya" kuma na nufin duk wani abin da aka bayar wanda ke daga farashi mai yawa ga wanda ke bayarwa.
  • Baye-baye ga Allah abubuwa ne na musamman da ya buƙaci Isra'ilawa su bayar domin su nuna hidimarsu da biyayyarsu gare shi.
  • Sunayen ire-iren baye-baye, kamar su "baye-baye na ƙonawa" da "baiko na salama," na bayyana irin baikon da ake bayarwa.
  • Hadayar Yesu ne kaɗai, cikakkiya na Allah, ‌Ɗa marar laifi, na iya tsarkake mutane daga zunubansu hadayu na dabbobi basu iya yi ba.
  • Faɗin nan "ku miƙa kanku hadaya rayayya" na nufin, "yin rayuwarka cikin cikakkiyar biyayya ga Allah, kuna sadaukar da komai domin ku bauta masa."

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "baiko" za a iya fassarawa haka "kyauta ga Allah" ko "wani abin da aka ba Allah" ko "wani abu mai daraja da aka miƙa ga Allah."
  • Ya danganta da nassin, kalmar "hadaya" ita ma za a iya fassarawa "wani abu mai daraja da aka bayar cikin sujada" ko "wata dabba ta musamman da aka kashe aka miƙa wa Allah."
  • Aikata "hadaya" za a iya fassarawa haka "a bayar da wani abu mai muhimmanci" ko a "kashe dabba a kuma bayar ga Allah."
  • Wata hanyar fassara "ku miƙa kanku a matsayin hadaya mai rai" zata iya zama "yayin da kuke rayuwa, ku miƙa kanku ga Allah ɗungum kamar dabbar da aka miƙa a bisa bagadi."

(Hakanan duba: bagadi, baiko na ƙonawa, baiko na sha, alloli na ƙarya, baiko na zumunta, baiko na yardar rai, baiko na salama, firist, baiko na zunubi, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:06
  • Ayyukan Manzanni 07:42
  • Ayyukan Manzanni 21:25
  • Farawa 04:3-5
  • Yakubu 02:21-24
  • Markus 01:43-44
  • Markus 14:12
  • Matiyu 05:23

haifuwar faiko

Ma'ana

Kalmar nan haihuwar farko tana nufin tsatson mutane ko dabbobi ne waɗanda aka fara haifa.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, "haihuwar farko" tana nufin ɗa namiji da aka fara haifa.
  • A kwanakin Littafi Mai Tsarki, ɗan fari akan bashi babban matsayi a cikin iyali sau biyu bisa iyali akan sha'anin gãdo.
  • A lokuta da yawa ɗan fari na dabbobi ne akan miƙa hadaya ga Allah.
  • A ana iya amfani da wanan batun akan ambace shi ta hanyar salon magana. Misali banin Isra'ila ana kiran su 'yan fari na Allah sabo da Allah ya ba su wata dama ta musamman fiye da sauran al'umma.
  • Yesu ɗan Allah ana kiransa ɗan fari na Allah sabo da iko mai muhimmanci fiye da kowa.

Shawarwarin Fassara:

  • In anga "haihuwar farko" ta faru ita kaɗai a wuri, za'a iya fassara ta da namiji ɗan fari" ko "ɗan fari," tun tuni abin da ake mora kenan.
  • Waɗansu hanyoyi da za'a fassara wanan kalmar za su haɗa da "ɗan fari namiji da aka fara haifa, ko ɗa namiji na farko a cikin iyali" ko " ko ɗa na farko."
  • Sa'ad da aka mori wanan ta salon magana ana alaƙanta ta da Yesu, za'a iya fassara wanan kalma a nuna "ɗa da ke da iko akan komai."
  • Lura: A tabbatar cewa fassarar wanan kalma akan Yesu bai nuna cewa an halicce shi ba ne.

(Hakanan duba: gãdo, hadaya, ɗa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Kolosiyawa 01:15
  • Farawa 04:3-5
  • Farawa 29:26-27
  • Farawa 43:33
  • Luka 02:6-7
  • Wahayin Yahaya 01:5

haƙuri, yin abu da haƙuri, rashin haƙuri

Ma'ana

Wannan magana "haƙuri" ma'anarta jurewa cikin matsaloli masu wuya. Yawancin lokaci haƙuri na tare da jira.

  • Lokacin da mutane suke haƙuri da wani mutum, ana nufin suna nuna ƙauna ne ga mutumin kuma suna yafe dukkan laifofin da mutumin ya aikata.
  • Littafi Mai Tsarki ya koya wa 'ya'yan Allah suyi haƙuri sa'ad da suke fuskantar matsaloli kuma suke haƙurce wa junansu.
  • Saboda jinƙansa, Allah yana da haƙuri zuwa ga mutane, koda shi ke masu zunubi ne waɗanda sun cancanci hukunci.

(Hakanan duba: jimiri, gafartawa, naciya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 03:20
  • 2 Bitrus 03:8-9
  • Ibraniyawa 06:11-12
  • Matiyu 18:28-29
  • Zabura 037:7
  • Wahayin Yahaya 02:02

hallaka

Ma'ana

Wannan kalma "hallaka" tana da ma'ana haka yin amfani da abu dukka. Akwai wasu fasarar a misalce.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma "hallaka" yawancin lokaci ana nufin lalatar da abubuwa ko mutane.
  • Akan ce wuta takan hallaka abubuwa, ma'ana tana lalata su tawurin cinye su.
  • An kwatanta Allah da "wuta mai cinyewa," wannan fasarar fushinsa ne akan zunubi. Fushinsa yakan jawo hukunci mai tsanani ga masu zunubi da basu tuba ba.
  • Idan an lashe abinci ana nufin an cinye ko a shanye shi kakaf.
  • Wannan furci "hallaka ƙasa" za a iya fassara ta haka, "lalata ƙasar."

Shawarwarin Fassara:

  • Idan an ce hallaka ƙasa ko mutane, wannan kalma za a iya fassara ta ta zama "lalatarwa."
  • Idan ance wuta, ta "hallaka" za a iya fasara shi a ce "ƙonewa ƙurmus."
  • Kurmi mai cin wuta da Musa ya gani "ba a cinye shi ba" za a iya juya shi ya zama "bai ƙone ƙurmus ba" ko "bai ƙone dukka ba.
  • Idan za a yi magana akan cin abu, za a iya fassara "hallaka" ya zama "ci" ko "lankwame."
  • Idan ƙarfin wani ya "hallaka" ma'ana ƙarfinsa "ya ƙare" ko "ya tafi."
  • Wannan furci, "Allah wuta ne mai hallakarwa" za a iya fassara shi haka, "Allah kamar wuta ne mai ƙona abubuwa ƙurmus" ko "Allah yana fushi gãba da zunubi kuma zai hallaka masu zunubi kamar wuta."

(Hakanan duba: lanƙwame, hasala)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 18:38-40
  • Maimaitawar Shari'a 07:16
  • Irmiya 03:23-25
  • Ayuba 07:09
  • Littafin Lissafi 11:1-3

hallaka, na hallakarwa, hallakakke, mai hallakarwa, masu hallakarwa, hallakarwa, rusawa, cutarwa

Ma'ana

A hallaka wani abu wannan na nufin a kawo ƙarshen abu baki ɗaya, har ya kai ga abin ya ƙare baki ɗaya.

  • Kalmar nan mai hallakarwa tana nufin, "mutum wanda ke hallakarwa"
  • Ana fin amfani da wannan kalma a cikin Tsohon Alƙawari domin a nuna duk wani da ke hallaka mutane, misali sojoji mahara.
  • Lokacin da Allah ya aika mala'ika domin ya kashe dukkan 'ya'yan fari a masar, an kira wannan mala'ika da kalmar "mai hallakar da 'ya'yan fari maza."
  • A cikin littafin W/Yahaya game da kwanakin ƙarshe, Sheɗan ko kuma waɗansu mugayen ruhohi ana kiran sa "mai hallakarwa" Shi ne "mai kasherwa" domin manufgarsa ita ce ya hallakar, ya kuma rushe duk wani abu da Allah ya hallita.

(Hakanan duba: mala'ika, Masar, 'ya'yan fari, bikin ƙetarewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 12:23
  • Ibraniyawa 11:28
  • Irmiya 06:26
  • Littafin Alƙalai 16:24

hallakawa, kashe, yanka, kisa, kisan kai, kashewa, kisa, kashe-kashe

Ma'ana

A "hallaka" mutum ko dabba na nufin a kashe shi. yawancin yakan zama kisa ta hanya mai wahala ko ta'addanci, idan mutum ya kashe dabba ya hallakata.

  • Idan ana magana kan dabba ko mutane da yawa, kalmar "yankawa" ita aka fi amfani da ita.
  • Yayyankawa shima ana kiransa "yankawa."
  • Faɗar "hallakarwa" za a iya fassara ta da "hallaka mutane" ko "mutanen da aka kashe."

(Hakanan duba: yankawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 28:23
  • Ishaya 26:21

hallita, hallitu, ma'hallici

Ma'ana

Wannan kalma "hallita" ma'anarta shi ne ayi wani abu, ko a sa wani abu ya zamo. Dukkan abin da aka hallita ana kiransu "hallitu." Akan ce da Allah "Ma'hallici" domin shi ne ya sa kome a dukkan faɗin sammai suka kasance.

  • Lokacin da ake amfani da wannan kalma game da Allah daya hallici duniya, ana nufin bai yi ta da kome ba.
  • Sa'ad da mutane suka "hallici" wani abu, sun yi shi ne da wani abin da ya rigaya ya kasance.
  • Wani lokaci ana amfani da kalmar nan "hallita" a misalta wani abin da ba shi ganuwa, kamar a ce hallita salama ko hallita sabuwar zuciya a cikin wani mutum.
  • Wannan kalma "hallitu" ya ambato tun farkon duniya ne lokacin da Allah ya hallici dukkan kome. Za a iya amfani da shi a faɗi dukkan kome da Allah ya hallita. Wani lokaci kalmar nan "hallitu" yana magana ne musamman game da mutanen duniya.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu yaruruka za su buƙaci kai tsaye su ce Allah ya hallici duniya "ba daga wani abu ba" domin su tabbabatar sun fid da ma'anar.
  • Wannan furci, "tun daga hallitar duniya" ma'anar ta, "tun lokacin da Allah ya hallici duniya."
  • Wata furci mai kama da waccan ita ce, "a farkon hallitu" za a iya fasasra ta haka "lokacin da Allah ya hallici duniya a farkon lokaci" ko "lokacin da aka hallici duniya da farko."
  • Yin wa'azin labari mai daɗi "ga dukkan hallitu" na nufin a yi wa'azin labari mai daɗi "ga dukkan mutane a ko'ina a doron duniya."
  • Wannan furci "bari dukkan hallitu su yi farin ciki" ma'anar ta, "bari dukkan abin da Allah ya hallita su yi farin ciki."
  • Ya danganta yadda za a yi amfani da shi cikin nassi, "hallita" za a iya fassara ta haka, "a yi" ko "sa abu ya zamo" ko "yin wani abu ba daga kome ba."
  • Wannan kalma "Ma'hallici" za a iya fassara shi haka, "Wannan da yayi abu dukka" ko "Allah, da yayi duniya dukka."
  • Furci kamar haka "Ma'hallicinka" za a iya fassara shi haka "Allahn da ya hallice ka."

(Hakanan duba: Allah, labari mai daɗi, duniya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 11:9-10
  • 1 Bitrus 04:17-19
  • Kolosiyawa 01:15
  • Galatiyawa 06:15
  • Farawa 01:01
  • Farawa 14:19-20

hallitu

Ma'ana

Wannan kalma "hallitu" ana nufin dukkan masu rai da Allah ya hallita, 'yan adam da dabbobi.

  • Annabi Ezekiyel yayi bayyani akan wasu "rayayyun hallitu" a wahayinsa ta ɗaukakar Allah. Bai fahimce su ba, saboda haka ya basu wannan suna.
  • Yi lura da wannan kalma "hallitu yana da ma'ana dabam tun da shi ke ya haɗa da dukkan abin da Allah ya hallita, da masu rai da abubuwan da basu da rai (kamar su ƙasa, ruwa, da taurari). Wannan kalma "hallita" ya haɗa da abubuwa masu rai ne kaɗai.

(Hakanan duba: halicci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 04:10-12
  • Ezekiyel 01:09
  • Yoshuwa 10:28
  • Lebitikus 11:46-47
  • Wahayin Yahaya 19:04

hamada, jeji, daji, hamadoji

Ma'ana

Hamada, ko jeji, wuri ne bussashe, kuma saimo inda 'yan itatuwa kima ne kawai ke tsira su yi girma a wurin.

  • Ƙasar hamada wuri ne da ba a yin ruwa yake kuma da 'yan tsirai kaɗan da 'yan dabbobi kima.
  • Sabo da yanayi mai zafi na wurin mutane kima ne ke iya zama a wurin to shima ana kiransa "busarshiyar hamada"
  • Hamada na da ma'anar zama a tantagaryar dajin da ba ruwa inda ba kowa
  • Wannan kalmar za iya fassara ta a matsayin "yasasshen wuri" ko "wurin da ba kowa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 13:16-18
  • Ayyukan Manzanni 21:38
  • Fitowa 04:27-28
  • Farawa 37:21-22
  • Yahaya 03:14
  • Luka 01:80
  • Luka 09:12-14
  • Markus 01:03
  • Matiyu 04:01
  • Matiyu 11:08

hamayya, kai ƙara, roƙo, roƙe-roƙe

Ma'ana

Wannan magana "roƙo" tambaya ce wadda ake son wani mutum ya amsata da gaggawa. Roƙo neman abu ne da gaggawa a wurin wani.

  • Yawancin lokaci idan ana "roƙo" mutumin dake roƙon yana jin nauyin buƙatarsa kuma yana ji lallai yana buƙatar taimako.
  • Mutane zasu yi roƙo ko suyi gaggawar ƙara ga Allah domin jinƙai ko su tambaye shi ya basu wani abu, ko domin kansu ko wasu.
  • Wasu hanyoyin fassara wannan zai haɗa da waɗannan "roƙo" ko "tambaya" ko tambaya da gaggawa."
  • Wannan magana "roƙo" za a iya fassarawa haka "roƙo da gaggawa" ko "matsawa."
  • A tabbata an bayyana shi a fili cikin nassi saboda kada wanna maganar ta zama kamar ana roƙon kuɗi.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 08:3-5
  • Littafin Alƙalai 06:31
  • Luka 04:39
  • Littafin Misalai 18:17

hankali, tunarwa, tunawa, abin tunashewa, ra'ayi ɗaya

Ma'ana

Wannan kalma "hankali" na nufin wannan fannin mutum dake tunani yana kuma yin zaɓi.

  • Hankalin kowanne mutum shi ne jimilar tunaninsa da hikimarsa.
  • "Samun hankali irin na Almasihu" shi ne mutum ya riƙa tunani da aiki irin da wanda Almasihu zai yi. Wato za a yi biyayya ga Allah Uba, a yi biyayya da koyarwar Almasihu, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
  • "Sauya ra'ayi" shi ne wani ya yi zaɓi daban ko ya bada ra'ayi daban da wanda ya bayar da farko.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "hankali" za a iya fassarawa haka "tunani" ko "la'akari" ko "zato" ko "fahimta."
  • Wannan magana "tuna da" za a iya fassara ta haka "tuna" ko "ka yi lura da wannan" ko "ka tabbata ka san wannan."
  • Wannan furci "zuciya, rai, da tunani za a iya fassara su haka "abin da ake ji a jiki, abin da ka gaskata, da abin da kake tunani a kai."
  • Wannan magana "ya canza tunaninsa ya tafi" za a iya fassarawa haka "ya zaɓi ra'ayi daban ya tafi" ko "duk da haka ya zaɓa" ko "ya sauya ra'ayinsa ya tafi."
  • Wannan magana raba hankali" za a iya fassara shi a ce "shakka" ko "ruwan ido" ko "yana da ruɗaɗɗen tunani."

(Hakanan duba: gaskatawa, zuciya, rai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 10:27
  • Markus 06:51-52
  • Matiyu 21:29
  • Matiyu 22:37
  • Yakubu 04:08

hanu, hannuwa, miƙawa, riƙewa, ta hanun, ɗora hanu, ɗora hanunsa bisa, hanun dama, hanuwan dama, daga hanun

Ma'ana

Akwai salon magana da yawa game da "hanu" a cikin Littafi Mai Tsarki:

  • A "danƙa" wani abu ga wani na nufin asa wani abu a cikin hanuwan wanan mutumin.
  • Kalmar nan "danƙa" ana yawan moron ta domin baiyana ikon Allah da kuma aikinsa, misali inda Allah ya ce "Ashe ba hanuna ne ya halilci duka waɗannan abubuwa ba?"
  • Ƙauli kamar "miƙa aiki" ko a "danƙa shi a hanuwan" na nufin asa wani ya kasance a ƙarƙashin sarrafawar wani da bam.
  • Waɗansusalon maganar da ake mora sun haɗa da:
  • "Ɗora hanu kan wani" na nufin a "cutar"
  • A "ceta daga hanun" na nufin a hana wani cutar da wani.
  • Mataki na kasancewa a "hanun dama" na nufin a "bangon dama na", ko "zuwa hanun" ko "zuwa hanun dama"
  • Batun nan "ta wurin hanun wani" na nufin "ta" ko "ta hanyar" abin da wanan mutum ya yi. Misali, "ta hanun Ubangiji" na nufin cewa Ubangiji ne ya bar wani abu ya faru.
  • Ɗora hannuwa a kan wani akan fi yin sa ne idan ana furta wa wani albarka.
  • Kalmar nan "ɗora hannuwa" tana nufin ɗora hanu akan mutum domin a keɓe wanan mutumin domin hidimar Ubangiji ko kuma yin addu'a domin warkewa.
  • Da Bulus yace "rubutun hanuna ne," yana nufin cewa wanan sashe na wasiƙa shi ne da kansa ya rubuta, a memakon ya ce da wani ya rubuta.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗanan batutuwa da sauran waɗansu salo na magana za'a iya fassara su ta amfani dawaɗansu ire-iren salon magana da ke da ma'ana iri ɗaya. ga ɗaya ma'anar kuma za'a iya fassara ta ta wurin moron fassara ta kai tsaye da ke cikin harshen (duba mislin da ke sama).
  • Batun nan "ka bashi fatun nan masu rubutu" za'a iya fassara shi da "ka sa fatun nan masu rubutu a hanunsa." Ba wai an bashi ya riƙe shi ba ne ya zama nasa, amma dai ya more shi na ɗan wani lokaci.
  • Idan aka ce "hanu" yana nufin mutum misali a cikin "hanun Allah ne na yi wanan" za'a fassara shi da cewa "Allah ne ya yi wanan."
  • Kalmomi kamar "miƙa su ga hanunuwan maƙiyansu ya yi dai-dai d877ya "sallama su ga hanun maƙiyansu," za' iya fassara shi da cewa "a bar makiyansu su yi nasara da su" ko a sa maƙiyansu mamaye su" ko a ba maƙiyansu iko a kansu."
  • A "mutu ta hanun" za'a fassara shi da "su ne waɗanda za su kashe shi."
  • Batun nan "a hanun dama na" za'a iya fassara shi da "a gefen dama na."
  • A batun Yesu da ke "zaune a hanun dama na Allah" idan wanan bai bada ma'ana ba a harshen da ke nuna wani babban matsayi da iko dai-dai, to za'a iya amfani da kalmomin da suka yi dai-dai da wanan. Ko a mori ɗan gajeren bayanin da ke da wanan ma'ana ta "a hanun dama na Allah, a madadin matsayi mafi girmamawa."

(Hakanan duba: magafci, albarka, kamammu, girmamawa, iko)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:25
  • Ayyukan Manzanni 08:17
  • Ayyukan Manzanni 11:21
  • Farawa 09:5
  • Farawa14:20
  • Yahaya 03:35
  • Markus 07:32
  • Matiyu 06:3 .

haraji, harajai, sa haraji, mai biyan haraji, mai karɓar haraji, masu karɓar haraji

Ma'ana

Kalmar "haraji" da "harajai" na nufin kuɗi ko kayayyaki da mutane ke biya ga gwamnatin da take mulkarsu. "Mai karɓar haraji" ma'aikacin gwamnati ne wanda aikinsa shi ne karɓar kuɗin da jama'a ya kamata su biya ga gwamnati a matsayin haraji.

  • Yawan kuɗin da ake biya a haraji ya danganta da darajar abin ko farashin abin da mutum ke da shi.
  • A lokacin Yesu da manzanni, gwamnati Roma ta buƙaci haraji daga dukkan mazaunan Roma, harda Yahudawan.
  • Idan ba a biya haraji ba gwamnati kan ɗauki mataki kan wannan mutumin domin su karɓi abin da ake binsa.
  • Yosef da Maryamu sunyi tafiya zuwa Betlehem domin a ƙidaya su a ƙidayar da ake yi domin a sawa duk mazaunan daular Roma haraji.
  • Kalmar "haraji" akan fassara ta da, "buƙatar biya" ko "kuɗin gwamnati" ko "kuɗin haikali," ya danganta da nassin.
  • "Biyan haraji" akan fassara shi da, "biyan kuɗi ga gwamnati" ko "karɓar kuɗi domin gwamnati" ko "biyan abin da aka buƙata." "Karɓar haraji" akan fassara shi da "karɓar kuɗi domin gwamnati."
  • "Mai karɓar haraji" mutum ne mai yiwa gwmnati aiki ya karɓi kuɗin da ya kamata mutane su biya.
  • Mutanen da suka karɓarwa Roma haraji sukan biɗi kuɗi mai yawa daga mutane fiye da abin da gwamnati ta buƙata. Masu karɓar harajin sai su ajiye wani kuɗin domin kansu.
  • Saboda masu karɓar harajin sun cutar da mutane sai Yahudawa suka ɗauke su masu zunubi fiye da kowa.
  • Yahudawa sun ɗauki Yahudawa masu karɓar haraji macutan jama'arsu domin suna yiwa gwamnatin Roma aiki wanda ke tsanantawa mutanen Yahuda.
  • Kalmar "masu Karɓar haraji" kalma ce mai sauƙi a Sabon Alƙawari, dake nuna yawan yadda Yahudawa suka rena masu karɓar haraji.

(Hakanan duba: Bayahude, Roma, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 20:21-22
  • Markus 02:13-14
  • Matiyu 09:7-9
  • Littafin Lissafi 31:28-29
  • Romawa 13:6-7
  • Luka 03: 12-13
  • Luka 05:27-28
  • Matiyu 05: 46-48
  • Matiyu 09:10-11
  • Matiyu 11:18-19
  • Matiyu 17:26-27
  • Matiyu 18:17

harajin ƙasashe, adashe, tãra

Ma'ana

Kalmar "harajin ƙasashe" na nufin kyauta daga wani mai mulki zuwa wani mai mulkin, saboda dalilin neman kariya da kyakkyawan zumunci a tsakanin ƙasashensu.

  • Harajin ƙasashe zai iya zama wani biyan kuɗaɗe da wani mai mulki ko gwamnati ke buƙata daga mutanen, kamar biyan kuɗaɗen kan iyakoki shiga wurare ko haraji.
  • A lokutan Littafi Mai Tsarki, sarakuna da masu mulki dake tafiye-tafiye wasu lokuta suna biyan harajin ƙasashe ga sarkin lardin da suke wucewa a cikin tafiyarsu domin su tabbatar cewa zasu sami kariya da kiyayewa.
  • Yawanci harajin ƙasashe na haɗawa da wasu abubuwan baya ga kuɗaɗe, kamar su abinci, kayan ƙanshi da yaji, suturu masu tsada, da ƙarafuna masu tsada kamar su zinariya.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, "harajin ƙasashe" za a iya fassarawa haka "kyautattakin hukuma" ko "haraji na musamman" ko "biyan da ake buƙata."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 18:1-2
  • 2 Tarihi 09:22-24
  • 2 Sarakuna 17:03
  • Luka 23:02

harshe, harsuna, yare

Ma'ana

Akwai misalai da yawa dake da ma'anonin "harshe" a cikin Littafi Mai Tsarki.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, ma'anar misalin da aka fi sani domin wannan kalmar "yare" ko "furci."
  • Wasu lokuta, "harshe" zai iya nufin yaren mutane da wasu ƙungiyar mutane suke magana da shi.
  • Wasu lokutan kuma ana nufin yaren ruhaniya da Ruhu Mai Tsarki ke bayarwa ga masu gaskatawa da Almasihu a matsayin "ɗaya daga cikin baye-bayen Ruhu."
  • A faɗar "harsunan" wuta ana nufin "tuƙuƙin" wuta.
  • A faɗar "harshena ya yi farinciki," kalmar "harshe" yana nufin mutum ɗungum.
  • A faɗar "harshen ƙarya" yana nufin muryar wani taliki ko furci.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, kalmar "harshe" za a iya fassarawa da "yare" ko "yaren ruhaniya." Idan ba a tantance wanda ake nufi ba, zai fi kyau a fassara haka "yare."
  • Sa'ad da ake nufin wuta, wannan kalma za a fassara haka, "tuƙuƙi."
  • A faɗar "harshena ya yi farinciki" za a iya fassarawa haka "Nayi farinciki na yabi Allah" ko "Ina yabon Allah da farinciki."
  • A faɗar, "harshen dake ƙarya" za a iya fassarawa haka "talikin dake ƙarya" ko "mutanen dake ƙarya."
  • A faɗar kamar haka "da harsunansu" za a iya fassarawa haka "da abin da suka ce" ko "da maganganunsu."

(Hakanan duba: baiwa, Ruhu Mai Tsarki, murna farinciki, yabi, farinciki, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 12:10
  • 1 Yahaya 03:18
  • 2 Sama'ila 23:02
  • Ayyukan Manzanni 02:26
  • Ezekiyel 36:03
  • Filibiyawa 02:11

hasala, huci, husata

Ma'ana

Hasala jin haushi ne na fitar hankali da ba za a iya tsai da shi ba. Sa'ad da mutum ya yi fushin fitar hankali, ma'ana wannan mutumin na bayyana haushinsa ta hanyar dake cutarwa.

  • Hasalar fitar hankali na faruwa ne sa'ad da tunanin sanin yakamata ya kuɓuce wa mutum har da bai iya riƙe kansa da yanayinsa ba.
  • kalmar "huci" na iya zama hurawa da ƙarfi, ana iya kwatanta shi da haukan ruwan teku mai "hauka."
  • Idan "al'ummai suka yi huci "a nan ne kuma mutane marasa tsoron Allah ke yi masa rashin biyayya da tayarwa.
  • A "cika da hasala" na nufin a yi ɗaukewa gabaɗaya da baƙinciki.

(Hakanan duba: fuushi, kãme kai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:25
  • Daniyel 03:13
  • Luka 04:28
  • Littafin Lissafi 25:11
  • Littafin Misalai 19:03

haske, haskoki, haskakawa, walƙiya, rana, hasken rana, asuba, fahimtarwa, ganarwa

Ma'ana

Akwai misalai da yawa da ake amfani dasu a matsayin "haske" a Litttafi Mai Tsarki. Yawancin lokaci ana amfani da shi a kwatanta adalci, tsarki, da gaskiya.

  • Yesu ya ce, "Ni ne hasken duniya" domin ya ganar ya kawo sakon Allah na gaskiya ga duniya ya kuma kuɓuto mutane daga duhun zunubansu.
  • An umarci Kristoci su yi "tafiya cikin haske," ma'ana yakamata su yi rayyuwa yadda Allah yake so su kuma guje wa mugunta.
  • Manzo Yahaya ya ce "Allah haske ne" a cikinsa kuma babu duhu ko kaɗan.
  • Haske da duhu suna hannun riga da juna. Duhu shi ne rashin haske gabaɗaya.
  • Yesu ya ce "shi ne hasken duniya" ma biyansa su haskaka kamar haske a cikin duniya ta wurin yin rayuwa wadda ta nuna yadda girman Allah yake sosai.
  • "Tafiya cikin haske" yana a madadin faranta wa Allah rai ne, muna yin abin da yake da kyau nagari kuma. Tafiya a cikin duhu yana a madadin rayuwa cikin tawaye gãba da Allah, ana yin mugayen abubuwa.

Shawarwarin Fassara:

  • Sa'ad da ake fassara, yana da kyau a riƙe ma'anar "haske" da duhu" a sauƙaƙe har ma lokacin da ake yin amfani da su a misali.
  • Mai yiwuwa zai zama dole a faɗi inda akwai kamanni a nassi. Misali, "yin tafiya kamar 'ya'yan haske" za a kuma fassara shi haka "zama da buɗaɗɗiyar rayuwar adalci, kamar wani mutum mai tafiya cikin hasken rana kau.
  • A tabbatar fassarar "haske" bai nuna wani abu da yake bada haske ba, kamar fitila. Fassarar wannan kalma yakamata ya nuna ana magana ne akan hasken kansa.

(Hakanan duba: duhu, tsarki, adalci, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 01:07
  • 1 Yahaya 02:08
  • 2 Korintiyawa 04:06
  • 2 Korintiyawa 04:06
  • Ayyukan Manzanni 26:18
  • Ishaya 02:05
  • Yahaya 01:05
  • Matiyu 05:16
  • Matiyu 06:23
  • Nehemiya 09:12-13
  • Wahayin Yahaya 18:23-24

hasumiyar tsaro, hasumiyoyin tsaro, hasumiya

Ma'ana

Kalmar "hasumiyar tsaro" gini ne mai tsayin gaske inda matsara ke kula da birni ko da wani bala'i na zuwa. Waɗannan hasumiyoyin akan yi su da duwatsu.

  • Masu gidaje wani lokacin su na gina hasumiyoyin tsaro domin tsaron gonakinsu kada a yi masu sata.
  • Hasumiyoyin sun haɗa har da inda matsaran ko kuma iyalansu ke zama, domin su yi tsaron amfanin gonarsu dare da rana.
  • Hasumiyoyin tsaro na birane ana gina su da tsayi sama da ganuwar birnin domin matsara su iya gani ko makiya na gabato birnin domin kai masa farmaki.
  • Kalmar "hasumiyar tsaro" ana amfani a matsayin alamar kariya daga maƙiya.

(Hakanan duba: magabci, tsaro)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 27:25-27
  • Ezekiyel 26:3-4
  • Markus 12:1-3
  • Matiyu 21:33-34
  • Zabura 062:02

hatimi, hatimai, hatimtacce, hatimcewa, marar hatimi

Ma'ana

Hatimce abu na nufin a ajiye abu a rufe da wani abin da zai zama da wuya a buɗe ba tare da an karya hatimin ba.

  • Yawancin lokuta hatimi ana sa masa alama na ãdo domin a nuna sãƙon na wane ne.
  • Kãkin zuma ko ƙaro ana amfani da shi domin hatimce wasiƙu ko wasu takardu masu muhimmanci da suke buƙatar tsaro sosai. Lokacin da kãkin zuman ko ƙaron ya bushe ya kuma yi ƙarfi, wasiƙar ba za a iya buɗe ta ba sai an karya hatimin. Shi wanda ya karɓi saƙon zai ga hatimin da ba a ɓalle ba sai ya kuma sasance da cewa ba a buɗe shi ba.
  • An sanya hatimi a bisa dutsen dake kabarin Yesu domin a hana ko wane mutum daga matsar da dutsen.
  • Manzo Bulus ya ambaci Ruhu Mai Tsarki a matsayin "hatimi" domin nuna cewa cetonmu tabbatacce ne.

(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, kabari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 02:03
  • Ishaya 29:11
  • Yahaya 06:27
  • Matiyu 27:66
  • Wahayin Yahaya 05:02

hatsi, tsabar hatsi, filayen hatsi

Ma'ana

Kalmar nan "hatsi" abin da take nufi a kullum shi ne iri amfanin gona kamar alkama, sha'ir, dawa, gero, ko shinkafa. Hakanan zai iya zama duk wani abu mai tsaba.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, tsabar da aka fi ambato ita ce alkama da sha'ir
  • Zangarniyar hatsi wani sashe ne na amfani da ke fitar da tsaba.
  • A yi la'akari da cewa a Tsohuwar fassarar Littafi Mai Tsarki duk wata kalma hatsi na nufin hatsi ne kai tsaye. A sabuwar fassarar turanci shima "hatsi" na nufin tsabar wani irin hatsi ne.

(Hakanan duba: zangarniya, alkama)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 42:3
  • Farawa 42:26-28
  • Farawa 43:1-2
  • Luka 06:2
  • Markus 02:24
  • Matiyu 13:7-9
  • Rut 01:22

hayayyafa, riɓaɓɓanya, ƙaruwa

Ma'ana

Wannan magana "riɓanɓanya" ma'anarta a ƙaru sosai a yi yawa. Zai iya zama a sa wani abu ya ƙara yawa, kamar na sa ciwo ya ƙara zafi.

  • Allah ya cewa dabbobi da mutane su "hayayyafa" su cika duniya. Wannan umarni ne cewa a haihu da yawa bisa ga iri.
  • Yesu ya sa gurasa da kifi su ƙaru domin ya ciyar da mutane 5000. Yawan abincin ya yi ta ƙaruwa har ma aka sami abincin ya yi yawa fiye da mutanen da aka ciyar.
  • Ya danganta ga nassi, wannan magana za a iya fassara ta haka "ƙaruwa" ko "a sa abu ya ƙaru" ko "ya ƙaru da yawa a ƙididdiga" ko "ƙaruwa a lamba" ko "ƙaruwa ba iyaka."
  • Wannan furci "yawaita naƙudarki" za a iya fassarawa haka "naƙudarki zai yi zafi ainu" ko " za a sa ki ji ciwo sosai."
  • "‌Ƙara ninka dawakai" na nufin "an dinga haɗamar sayan dawakai ba iyaka."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 08:01
  • Farawa 09:07
  • Farawa 22:17
  • Hosiya 04:6-7

holoƙon curin moɗa, gora, kwanon zube

Ma'ana

Holoƙon itace, ko curin ƙarfe, ko curin yumɓu da ake amfani da shi domin yin zuben zinariya, azurfa, ko wani ƙarfe da za a narkar da shi, sa'annan a zuba shi cikin wannan holoƙon mazubi domin zuben ya ɗauki kamanninsa idan ya daskare.

  • Ana amfani da moɗar zube ayi duwatsu masu daraja, kwanoni, tasoshin cin abinci, da sauransu.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki akan faɗi abu game da moɗayen zube lokacin da ake magana akan zuben siffofi da ake gumaku da su.
  • Akan gasa karfe har sai ya ɗauki zafin da zai narke domin a zuba moɗa mai siffar da ake so.
  • Zuben abu shi ne a siffanta abu ta wurin zuba narkakken karfe a moɗa mai surar abin da ake so ya zama bayan ya daskare.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana za a iya fassarata haka, "siffa" ko "kama" ko "yin wani abu."
  • Wannan kalma "siffanta" za a iya fassarawa haka "siffa" ko "sura"
  • Wannan "moɗa" za a iya fassarawa da ma'ana haka "kwano mai siffa" ko "akushi da aka sassaƙa."

(Hakanan duba: gunki, zinariya, gunki, azurfa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 32:04

horo, hukunta, hukunci

Ma'ana

Wannan magana "hukunta" ma'anar ta shi ne a sa wani ya wahala da abu marar daɗi saboda ya yi abin da ba dai-dai ba. Wannan magana "hukunci" na nufin horo marar daɗi da aka bayar saboda wannan mugun aiki.

  • Yawancin lokaci ana bada hukunci da nufin a ƙarfafa mutum ya bar yin zunubi.
  • Allah ya hukunta Isra'ilawa lokacin da suka yi masa rashin biyayya, musamman lokacin da suka yiwa gumaku sujada. Saboda zunubansu, Allah ya bar maƙiyansu su kai masu hari su kuma cafke su.
  • Allah mai adalci ne adali kuma, saboda haka dole ya hukunta zunubi. Kowanne mutum ya yiwa Allah zunubi ya kuma cancanci hukunci.
  • An hukunta Yesu domin dukkan muguntar da kowanne mutum ya taɓa aikatawa. Ya karɓi hukuncin kowanne mutum a kansa koda shi ke shi bai aikata wani laifi ba bai kuma cancanci wannan hukuncin ba.
  • Wannan furcin "kuɓuta daga hukunci" da " a tafi ba hukunci" ma'anar sa shi ne a yanke shari'a ba za a hukunta mutane domin laifinsu ba. Yawancin lokaci Allah yana barin zunubi ya tafi ba hukunci sa'ad da yana jiran mutane su tuba.

(Hakanan duba: adalci, tuba, adalci, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 04:18
  • 2 Tasalonikawa 01:09
  • Ayyukan Manzanni 04:21
  • Ayyukan Manzanni 07:59-60
  • Farawa 04:15
  • Luka 23:16
  • Matiyu 25:46

Hukuman Yahudanci, shugaban Yahudanci

Ma'ana

Taken "shugaban Yahudanci" ko "hukuma na Yahudanci" na nufin shugabannin addini kamar su firistoci da malaman shari'un Allah. Suna kuma da ikon aiwatar da hukunce-hukunce game da wasu al'amuran da ba na addini ba.

  • Shugabannin Yahudanci sun haɗa da babban firist, manyan firistoci, da marubuta (malaman shari'u).
  • Ƙungiyoyi biyu mafi muhimmanci na shugabannin Yahudanci sune Farisiyawa da Sadukiyawa.
  • Shugabannin Yahudawa saba'in ne suke taruwa a Majalisar Yahudanci a cikin Yerusalem domin su aiwatar da hukunce-hukunce game da al'amuran shari'a.
  • Yawancin shugabannin Yahudanci suna da fahariya da tunanin cewa su masu adalci ne. Suka yi kishin Yesu suka kuma nemi su cutar da shi. Suna nuna cewa sun san Allah amma basu yi masa biyayya.
  • Yawancin lokaci furta kalmar "Yahudawa" na nufin shugabannin Yahudanci, musamman a cikin rukunin in da suke jin haushin Yesu kuma suna neman suyi masa dabara ko su cutar da shi.
  • Waɗannan tãke ana iya fassara su a matsayin "masu mulkin Yahudawa" ko "waɗanda ke mulki bisa mutanen Yahudawa" ko "shugabannin addinin Yahudanci."

(Hakanan duba: Bayahude, manyan firistoci, majalisa, babban firist, Farisi, firist, Sadusi, marubuci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 16:22-23
  • Yahaya 02:19
  • Yahaya 05: 10-11
  • Yahaya 05: 16
  • Luka 19:47-48

hukuncin Allah ya isa

Ma'ana

Kalmar nan "hukuncin Allah ya isa hukunci ne wanda in an yi babu damar ɗaukaka ƙara ko tsira.

  • A lokacin da aka ɗauki Isra'ila zuwa bautar talala, annabi Ezikiyel ya ce, hukuncin Allah ya isa ya saukar musu."
  • Ya danganta ga abin da ke wurin, za'a iya fassara ta a matsayin "masifa" ko "hukunci" ko "rashin bege."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 07:5-7
  • Ezekiyel 30:09
  • Ishaya: 06:5
  • Zabura 092:6-7

hutawa, sauran, an huta, hutawa, rashin hutu, rashin kwanciyar hankali

Ma'ana

Kalmar "hutawa" na ma'anar ka bar aiki domin ka sami lokaci don hutu ko sabunta karfi. kalmar "sauran" na nuna ragowar wani abu. "Hutu" tsayawa ne daga yin aiki.

  • Ana iya cewa wani abu na "kwance" bisa kan wani gun, wannan na manufar yana "tsaye" ko "zama" nan.
  • Jirgin ruwan da ya "zo ya zauna" wani wurin ya "tsaya" ko "tsaya" ko "sauka" nan.
  • Yayin da wani ko dabba ya huta, suna zama ko kwance domin su sami wartsakewar kansu.
  • Allah ya umarce Isra'ilawa da su huta a rana ta bakwai na mako. Wannan ranar hutu an kira ta da suna Asabaci."
  • A kwantar da wani abu bisa kan wani abin na nufin a "ajiye" ko "ɗora" shi nan.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, a "hutar da (kai)" za a iya fassarawa haka "a bar aiki" ko ya "wartsake kansa" ko a "daina ɗaukar kaya."
  • A "hutarda ko ɗora" kaya ko wani abu za a iya fassarawa haka "wuri" ko "ɗora" ko "jera" wannan kaya ko wani abu.
  • Sa'ad da Yesu ya ce, "Zan baku hutawa," za a iya fassara wannan haka "Zan sa ku daina ɗaukar kayanku" ko "Zan sa ku zauna cikin salama" ko "Zan ikonta ku da ku huta ku kuma dogara gare ni."
  • Allah ya ce, "ba za su shiga hutuna ba," ana iya fassara wannan magana haka "baza su amfana da albarkar hutuna ba" ko "ba za su amfana da farinciki da salama dake zuwa daga dogara gare ni ba."
  • Kalmar "sauran" za a iya fassarawa haka "waɗanda suka rage" ko "dukkan sauran mutanen" ko "dukkan abubuwan da suka rage."

(Hakanan duba: ringi, Asabaci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 06:41
  • Farawa 02:03
  • Irmiya 06:16-19
  • Matiyu 11:29
  • Wahayin Yahaya 14:11

idi, idodi

Ma'ana

A bai ɗaya idi wani taro ne da mutane ko al'uma ke yi.

  • Kalmar nan "idi" a cikin Tsohon Alƙawari ma'anarta ita ce wani "keɓaɓɓen lokaci"
  • Idodin da Yahudawa ke yi ana yin su ne bisa keɓaɓɓun lokuta ko yanayoyin da Allah ya umarce su su yi.
  • A waɗansu fassarori na turanci, akan mori kalmar "biki" a memakon "idi" sabo da bikin ya haɗa da cin abinci mai yawa tare.
  • Akwai idodi da yawa da Yahudawa ke yin bikinsu a kowacce shekara:
  • Idin Ƙetarewa
  • Idin nunar 'ya'yan hatsi na farko
  • Idin Makonni (Fentakost)
  • Idin Kakaki
  • Idin Kafara
  • idin Bukkoki
  • Dalilan yin waɗannan idodin shi ne domin a godewa Allah da kuma tunawa da ayukansa na al'ajabi da ya yi domin kariya da kuɓutarwa da kuma tanadin da ya yiwa mutanensa.

(Hakanan duba: biki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 23:31
  • 2 Tarihi 08:13
  • Fitowa 05:01
  • Yahaya 04:45
  • Luka 22:01

iko, ƙasaita, ƙarfafa, jarumi, manyan ayyuka

Ma'ana

Wannan magana "iko" manufarta shi ne samun ƙasaitaccen ƙarfi.

  • Yawancin lokaci wannan kalma "iko" wata magana ce maimakon "ƙarfi." Sa'ad da ake magana akan Allah ma'anar zai zama "ƙarfi."
  • Wannan furci "jarumawan mutane" yawancin lokaci ana nufin mutane masu ƙarfin hali masu nasara a yaƙi. Amintattun ƙungiyar Dauda waɗanda suka taimake shi suka kare shi ana ce dasu "jarumawan mutane."
  • Allah ma, ana ce da shi "mai ikon nan."
  • Wannan furci "ayyukan iko" yawancin lokaci ana nufin abubuwan ban mamaki da Allah yake yi musamman al'ajibai.
  • Wannan magana tana kusan ɗaya da "mai iko dukka," wanda yawancin lokaci ana amfani da ita a bayyana Allah, ma'ana, yana da dukkan iko.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, wannan magana "iko" za a iya fassara ta haka "ƙarfi" ko "abin mamaki" ko "mai ƙarfi."
  • Wannan furci "ikonsa" za a iya fassarawa haka "ƙarfinsa" ko "ikonsa."
  • A cikin Ayyukan Manzanni an ambaci Musa da cewa shi "mutum ne mai iko cikin maganarsa da ayyukansa." Za a iya fassara wannan haka "Musa ya faɗi maganganu masu iko daga Allah ya kuma yi al'ajibai." ko "Musa ya faɗi maganar Allah da iko ya kuma yi abubuwan ban mamaki da yawa."
  • Zai danganta ga nassi, za a iya fassara "manyan ayyuka" haka "abubuwan ban mamaki da Allah ke yi" ko "al'ajibi" ko "Allah yana yin abubuwa da iko."
  • Wannan magana "iko" za a iya fassarawa haka kuma, "iko" ko "ƙarfi mai girma."
  • Kada a ruɗe a gama wannan magana da wata kalma ta turanci mai ma'anar watakila, misali, "mai yiwuwa za a yi ruwa."

(Hakanan duba: Mai Iko Dukka, al'ajibi, iko, ƙarfi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:22
  • Farawa 06:4
  • Markus 09:38-39
  • Matiyu 11:23

inuwa, inuwoyi, rufewa rufe, Inuwa

Ma'ana

Kalmar "inuwa" Na nufin duhun da wani abu ke samarwa ta wurin kare hasken. Yana kuma da alamar ma'anoni da yawa.

  • "Inuwar mutuwa" na nufin cewa mutuwa nanan ko kusa, kamar yadda inuwar ta nuna kasancewar abin.
  • Lokuta da dama a cikin Littafi Mai Tsarki, an kwatanta rayuwar mutum da inuwa, wadda ba ta daɗewa ba ta da komai kuma.
  • Wasu lokutan kuma anyi amfani da "inuwa" a matsayin "duhu"
  • Littafi Mai Tsarki ya yi magana kan ɓuya ko karewa cikin inuwar fikafikan Yahweh ko hannuwansa. wannan shi ne hoton samun kariya da ɓuya daga haɗari. Waɗansu hanyoyin fassara "inuwa" ta wurin amfani da hanya mafi sauƙi wanda aka mora wajen nuna inuwa ta ainihi.

(Hakanan duba: duhu, haske)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 20:09
  • Farawa 19:08
  • Ishaya 30:02
  • Irmiya 06:04
  • Zabura 017:08

iri, maniyi

Ma'ana

Iri sashe ne na dashe da ake shukawa a cikin ƙasa domin ya bãda 'ya'ya dashe kamarsa. Yana kuma da wasu ma'ana na misalai da yawa.

  • Kalmar "iri" ana moriyarsa ne ta wurin misali ana kamanta shi da ƙananan sinadarai a cikin mutum dake haɗuwa da wasu sinadaran a cikin mace su sa jariri ya yi girma a cikin ta. Gun-gun waɗannan sinadarai su ake kira maniyi.
  • Dangantaka da wannan, "iri" ana kuma amfƒani da shi da nufin 'ya'yan mutum ko zuriyarsa.
  • Yawanci wannan kalma na da ma'anar jimla, da nufin irin hatsi fiye da ɗaya ko zuriya fiye da ɗaya.
  • A cikin misalin manomi na shuka iri, Yesu ya kwatanta irinsa a matsayin maganar Allah, wadda ake shukawa a zukatan mutane domin a haifar da ɗiyan ruhaniya mai kyau.
  • Manzo Bulus ya yi amfani da wannan kalma "iri" yana manufa da maganar Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Game da ainihin iri, zai fi kyau a fassara kalmar "iri" yadda ake amfani da shi a harshen a matsayin abin da manomi ke shukawa a gona.
  • A kuma yi amfani da ainihin ma'anar kalmar a nassosin da aka yi amfani da ita a matsayin maganar Allah.
  • Game da yadda aka yi amfani da kalmar a misali mai manufar mutanen da suke daga layin iyali ɗaya, zai fi nuna wa a sarari idan aka yi amfani da kalmar "zuriya" a maimakon iri. Wasu yarurrukan suna iya suna da kalma dake ma'anar "'ya'ya ko jikoki."
  • Game da "iri" na mutum ko mace, sai a nemi hanyar da yaren ke faɗar wannan ta hanya da ba za a kunyatar da mutane ba.

(Hakanan duba: zuriya, 'ya'ya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 18:32
  • Farawa 01:11
  • Irmiya 02:21
  • Matiyu 13:08

itacen dabino, itatuwan dabino

Ma'ana

"Itacen dabino"wani irin dogon ice ne da dogayen rassa masu taushin lanƙwasa, kuma suna sama karshen itacen a baje ta kowanne gefe.

  • Itacen dabino a cikin Littafi mai Tsarki wani itace ne dake bada 'ya'yan da ake kira "dabino." siffar ganyayensa kamar na gashin kaza ne.
  • Itacen dabino yana girma ne inda yanayi yake da zafi, da kuma damshi. Ganyayensa sukan kasance kore shar dukkan shekara.
  • Da Yesu zai shiga Urshalima bisa jaki, mutane suka shimfiɗa rassan dabino a ƙasa a gabansa.
  • Rassan dabino na nuna salama da biki saboda nasara.

(Hakanan duba: jaki, Yerusalem, salama)

Wuraren da ake samunsa a LIttafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 06:29-30
  • Ezekiyel 40:14-16
  • Yahaya 12:12-12
  • Littafin ‌Lissafi 33:09

itacen inabi, itatuwan inabi

Ma'ana

Kalmar "itacen inabi" na bayyana wani dashe ne dake bi ta ƙasa ko ta haurawa wasu itatuwa ko wasu gine-gine. Kalmar "itacen inabi" cikin Littafi Mai Tsarki ana morarta ne kawai a bayyana itatuwan inabi masu bãda 'ya'ya yawancin lokutai kuwa ana nufin kuringun inabi ne.

  • A Littafi Mai Tsarki, kalmar "itacen inabi" na kusan kowanne lokaci na manufar "kuringar inabi."
  • Rassan kuringar inabin na harɗe da asalin tushen wanda ke basu ruwa da wasu sinadarai domin su yi girma.
  • Yesu ya kira kansa " itacen inabi" mutanensa kuma "rassa." A wannan nassin, kalmar "itacen inabi" za a iya fassarawa haka "reshen kuringar inabi" ko "reshen dashen inabi."

(Hakanan duba: inabi, gonar inabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 40:09
  • Farawa 49:11
  • Yahaya 15:01
  • Luka 22:18
  • Markus 12:03
  • Matiyu 21:35-37

Iwa, Iwoyi

Ma'ana

Kalmar "iwa" wani dashe ne mai tsawon reshe dake girma cikin ruwa, ana samun ta ne a bakin kogi ko tafki.

  • Iwoyin cikin Kogin Nilu inda aka ɓoye Musa sa'ad da yake jariri. Suna da tsayi, da rami ciki suna cinƙoso a cikin kogi.
  • An yi amfani da busasshen iwa a Masar wurin yin takarda, kwando, da kuma kwale-kwalan ruwa.

(Hakanan duba: Masar, Musa, Kogin Nilu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 14:15
  • Luka 07:24
  • Matiyu 11:07
  • Matiyu 12:20
  • Zabura 068:30

iyali

Ma'ana

Wannan kalma "iyali" ana nufin faffaɗar iyali na 'yan'uwan da suka fito daga zuriya ɗaya.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, ana ƙirga Isara'ilawa bisa ga iyalansu, ko ƙungiyar iyalinsu.
  • An saba ba iyali sunan wani sanannen kakansu.
  • Mutum guda ma wani lokaci ana kiransa da sunan iyalinsu. Ga misalin haka, lokacin da surukin Musa Yetro aka kira shi da sunan iyalinsa, Ruwel.
  • Za a iya fassara iyali haka "ƙungiyar iyali" ko "faffaɗar iyali" ko "yan'uwa."

(Hakanan duba: iyali, Yetro, kabila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:33-35
  • Farawa 10:2-5
  • Farawa 36:15-16
  • Farawa 36:29-30
  • Farawa 36:40
  • Yoshuwa 15:20
  • Littafin Lissafi 03:38-39

iyali, iyalai

Ma'ana

Kalmar nan "iyali" tana nufin mutane ne dake da dangantaka ta jini, kuma har kullum sun haɗa da mahaifi, uwa, da 'ya'yansu. Haka nan yakan ƙunshi sauran dangi kamar kakani, jikoki, ƙanen baba da 'yan'uwan mama.

  • Iyalan Ibraniyawa sun kasance al'uma ce ta addini wadda aka gãda ta wurin sujada da gaegaɗi.
  • Har kullum mahaifi shi ne ya fi iko akan iyali.
  • Haka nan iyali zai iya haɗawa da bayi, sa ɗaka, har ma da bãƙi.
  • Waɗansu harsunan na da kalmomi masu faɗi irin su "kabila" ko "gidan wãne" wanda dai ya fi dacewa a wurin a inda akwai fiye da iyaye da 'ya'ya ake magana.
  • Kalmar nan "iyali" ana amfani da ita a ambaci mutane da ke da dangantaka ta ruhaniya, irin mutane da ke ɗaya daga cikin iyalin Allah sabo da sun yi imani da Yesu.

(Hakanan duba: kabila, ubanni, gida)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 08:1-2
  • 1 Sama'ila 18:18
  • Fitowa 01:21
  • Yoshuwa 02:12-13
  • Luka 02:04

iyali, iyalai

Ma'ana

Kalmar nan "iyali"tana nufin dukkan iyalin da ke rayuwa tare a cikin gida,da suka haɗa da dangi da dukkan bayinsu.

  • Sarrafa iyali zai haɗa da biyar da bayi da kuma kula da mallaka.
  • A waɗansu lokuta za'a iya baiyana "iyali"zai iya zama salon magana domin yin magana akan dukkan iyalai na wani, musamman zuriyarsa.

(Hakanan duba: gida)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:10
  • Galatiyawa 06:10
  • Farawa 07:01
  • Farawa 34:19
  • Yahaya 04:53
  • Matiyu 10:25
  • Matiyu 10:36
  • Filibiyawa 04:22

jagoranci, hukuma, hukumomi, gwabna, gwabnoni, gwabnan daula, gwabnonin daula

Ma'ana

"Gwabna" mutum ne da aka ba ikon jan ragamar jiha, yanki, ko gunduma. Yin jagara na nufin a nuna tafarki, a shugabanta, ko a biyar da su.

  • Kalmar nan gabnan daula na nufin wani matsayi ne na musamman da akan ba gwabnan da ke mulkin daular Roma.
  • A kwanakin Littafi Mai Tsarki sarkin daula ne ke zaɓar gwabnoni domin su yi mulkin wani yanki a ƙarƙashin ikonsa.
  • Gwabnati ta ƙunshi dukkan tattaruwar shugabanin da ke mulkin daula ko ƙasa. Waɗanan shugabannin ne ke tsara dokokin da 'yan ƙasa za su bi domin a sami salama, da kariya da kuma ƙaruwar arzaki domin dukkan mutanen ƙasa.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "gwabna" za'a iya fassara ta da "mai mulki" ko "mai lura" shugaban yanki" ko wani dake mulkin wani yanki."
  • Ya danganta ga wurin kalmar nan "jagoranci" ita ma za'a iya fassara ta da "yin shugabanci" ko biyarwa, ko "sarrafawa" ko "lura da."
  • Kalmar nan "gwabna" ita ma za'a iya fassara ta da bam da kalmar "sarki" ko "babban sarki na daula" tun da yake gwabna bai kai ikon su ba kuma yana ƙarƙashin mulkinsu.
  • Kalmar nan "gwabnan daula" ita ma za'a iya fassara ta da "gwabnan Roma" ko "shugaba mai mulkin daular Roma."

(Hakanan duba: hukuma, sarki, iko, lardi, Roma, mai mulki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:9-10
  • Ayyukan Manzanni 23:22
  • Ayyukan Manzanni 26:30
  • Markus 13:9-10
  • Matiyu 10:18
  • Matiyu 27:1-2

jakada, jakadai, wakili, wakilai

Ma'ana

Jakada wani mutum ne da aka zaɓa ya wakilci ƙasarsa a wajen wasu baƙin al'ummai. Ana kuma iya fasara wannan kalma a ce "wakili."

  • Jakada ko wakili yana miƙa saƙonni ga mutane wanda wani mutum ko gwamnati ta aike shi.
  • Yawancin lokaci "wakili" mutum ne da aka bashi iko ya yi wani abu ko ya yi magana a madadin wani mutum da yake wakilta.
  • Manzo Bulus ya koyar cewa Kiristoci "jakadu" ne ko kuma "wakilai" tunda shi ke suna wakiltar Kiristi cikin duniyan nan suna kuma koya wa wasu maganarsa.
  • Ya danganta kuma ga yadda aka yi amfani da shi a cikin rubutu za a iya fasara shi ya zama "wakilin gwamnati" ko "ɗan aike" ko "zaɓaɓɓen wakili" ko "wakili kirayayyen Allah"
  • ‌"Ƙungiyar jakadu" za a iya fassara ta zuwa "wasu manzanni shugabanni." ko " ƙungiyar zaɓaɓɓun wakilai" ko "ƙungiyar mutane 'yan siyasa masu magana domin dukkan mutane."

(Hakanan duba: manzo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Afisawa 06:20
  • Luka 14:31-33
  • Luka 19:13-15

jaki, alfadari

Ma'ana

Jaki dabba ce mai ƙafa huɗu, ta yi kama da doki, amma ba ta kai doki ba tana da dogayen kunnuwa.

  • Alfadari dangin namijin jaki ne da goɗiya.
  • Alfadarai dabbobi ne masu ƙarfi, domin haka suna da daraja wajen aikin.
  • Da jakuna da alfadarai ana moron su domin ɗaoko kaya da kuma zirga-zirga.
  • A kwanakin Littafi Mai Tsarki, sarakuna kan hau jaki ne a memakon doki domin nuna salama, domin dawakai ana moron su ne a kwanakin yaƙi.
  • Yesu ya shiga Urshalima akan ɗan aholakin jaki mako gabanin a giciye shi a can.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 01:32-34
  • 1 Sama'ila 09:04
  • 2 Sarakuna 04:21-22
  • Maimaitawar Shari'a 05:12-14
  • Luka 13:15
  • Matiyu 21:02

jan garura, launi shunayya

Ma'ana

Wannan kalma "jan garura" sunan wani launi ne da aka gauraya shuɗi da jan launi.

  • A zamanin dã, ba safai ake samun jan garura ba kuma launi ne mai tsada da ake amfani da shi a rina tufafin sarakai da manyan hakimai.
  • Saboda yana da tsada yana kuma ɗaukar lokaci kafin a yi wannan launin, tufafi masu jan garura ana ɗaukarsu alamar wadata ne, muƙami, da kuma sarauta.
  • Jan garura kuma yana ɗaya daga cikin launukan da ake amfani da shi domin labulen rumfar sujada da haikali, da kuma falmara da firist yake sawa.
  • Ana samun launin jan garura daga wani dodonkoɗin ruwa ta wurin murkushe shi ko tafasa koɗin ko ta wurin sasu su fitar da ruwan rinin sa'ad da suke da rai. Wannan aiki ne mai tsadar gaske.
  • Sojojin Roma sun sa wa Yesu alkyabbar jan garura ta sarauta kafin a gicciye shi, domin su yi masa ba'a saboda ya ce shi Sarkin Yahudawa ne.
  • Lidiya daga garin Filifai mace ce data sami biyan buƙatun rayuwa ta wurin saida tufafin jan garura.

(Hakanan duba: falmara, Filifai, sarauta, rumfar sujada, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 02:13-14
  • Daniyel 05:7
  • Daniyel 05:29-31
  • Littafin Misalai 31:22-23

jayyaya, rigingimu, faɗa, gardama, rikici, rikice-rikice

Ma'ana

Kalmar "jayyaya" na nufin yin rigma a fili ko a lamiri tsakanin mutane.

  • Mutumin da ya tada jayyaya ya jawo abin da yake kawo babbar rashin fahimta tsakanin mutane da kuma jin haushi.
  • Wani lokacin amfani da kalmar "jayyaya" na nuna jin wani abu mai ƙarfi wanda ya haɗa da kamar fushi ko ɗacin rai.
  • Waɗansu hanyoyin fasarta wannan kalma kan haɗa da, "rashin yarda" ko "rigima" ko "rikici."

(Hakanan duba: haushi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 03:3-5
  • Habakuk 01:03
  • Filibiyawa 01:17
  • Littafin Misalai 17: 01
  • Zabura 055:8-9
  • Romawa 13:13

jin daɗi, nuna jin daɗi, abin da aka ji daɗinsa, abu na jin daɗi

Ma'ana

"Jin daɗi" wani abu ne da ke kawo farinciki sosai ga wani.

  • A ji daɗi" na wani abu na nufin a yi "farin ciki ko murna game da wannan abin."
  • Idan aka yarda kan wani abu sosai, ko aka yi murna da shi wannan shi ake kira "jin daɗi".
  • Idan ya ji daɗin abu wannan na nuna mutum ya yi murna sosai da wannan abin.
  • Wannan kalma jin "daɗina na kan sharei'ar Yahweh" za'a iya fassara ta a matsayin "shari'ar Yahweh na ba ni farin ciki sosai" ko kuma ina ƙaunar yin biyayya ga shari'ar Yahweh" ko kuma "ina murna duk sa'ad da na yi biyayya da ummarnan Yahweh."
  • Wannan kalma "kada ka ji daɗi" da kuma "bana jin daɗinsa" za'a iyafasarta ta da "ban ji daɗi ba" ko "ban yi murna da hakan ba."
  • Kalmar nan "jin daɗinsa" tana nufin "yana jin daɗin yin wani abu" ko kuma yana matuƙar jin daɗin wani abu ko wani mutum.
  • Kalmar nan jin daɗi tana nufincewa mutum na jin daɗin yin wani abu. za'a iya fassara ta a matsayin " "yin murna" da ko kuma "wani abu da ya kawo murna."
  • irin wannan kalma kamar ina jin daɗin bin nufinka "za'a iya fassara ta da "ina jin daɗin yin yin nufinka" kuma zata iya fassarar ta da cewa ina murna da yin nufinka" ko kuma ina matuƙar farin ciki da yin biyayya da kai."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Misalai: 08:30
  • Zabura 001:02
  • Zabura 119:69-70
  • Waƙar Suleman 01:3

juriya, halin juriya, yin juriya, ƙarfin hali

Ma'ana

Kalmar nan "juriya" tana nufin a jure wani abu mai wuya cikin haƙuri.

  • Haka nan tana nufin a tsaya da ƙarfi idan lokacin gwaji ya zo ba tare da karaiya ba.
  • Haka nan kalmar nan juriya tana nufin "haƙuri" kom kuma dauriya a lokacin gwaji ko "tsanani"
  • Ƙarfin halin krista na juriya da su jure har matuƙa" kuma wanan na faɗa musu da su dinga yin biyayya da Yesu koma da bain zai kai su ga shan tsanani.

"jure shan wuya na nufin a shatsanani." Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara kalmar "ƙarfin hali" za su haɗa da "juriya" ko "ci gaba da imani" ko "ci gaba da yin abin da Allah ke so ku yi" ko "tsayuwar daka."
  • A waɗansu wuraren, "yin ƙarfin hali" za'a iya fassara shi da "tunkara."
  • Tare da wannan ma'ana ta "ɗorewa" wanan kalma tana da ƙarin fahimta za'a iya fassarar ta da marar ɗorewa, ko rashin tsira."
  • Hanyoyida za'a fassara ƙarfin hali zai haɗa da "jajircewa" ko "zama da aminci."

(Hakanan duba: ƙarfin hali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 02:11-13
  • Yakubu 01:12
  • Luka 21:19
  • Matiyu 13:21
  • Wahayin Yahaya 01:9
  • Romawa 05:3-5

juyawa baya, juyawa, juyewa, juyewa baya, juyi, juyarwa, juyarwa baya, komowa, komar da, komawa, komawa baya, bidawa

Ma'ana

A "juya" na ma'anar a canza tafarki ko asa wani abu daban ya canza tafarki.

  • Kalmar "juyawa" zata iya nufin "juyaw kewaye" a duba baya ko a fuskanci tafarki daban.
  • "Juyarwa baya" ko "juyewa" na nufin a "koma baya" ko "juyewa" ko "asa a koma."
  • A "juyar daga" zai iya zama da ma'anar "daina" yin wani abu ko ayi watsi da wani.
  • A "juya zuwa ga" wani na nufin a dubi wani kai tsaye.
  • A "juya a tafi" ko "ya juya baya domin ya tafi" na ma'ana "ya yi tafiyarsa."
  • A "juya baya zuwa ga" na ma'anar "a sake fara yin wani abu."
  • A "juye daga" na ma'anar "a daina yin wani abu."

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, "juya" za a iya fassarawa haka "a canza tafarki" ko "a tafi" ko "a matsa."
  • Wasu nassosin, "juya" za a iya fassarawa haka "a haddasa" (wani) ya yi wani abu. A "juya (wani) daga" za a iya fassarawa haka " a haddasa (wani) ya yi tafiyarsa" ko "a haddasa (wani) ya daina."
  • A faɗar "juyawa daga Allah" za a iya fassarawa haka "a daina sujada ga Allah."
  • A faɗar "juyawa baya zuwa ga Allah" za a iya fassarawa haka "a fara sujada ga Allah kuma."
  • Idan maƙiya suka "juya baya," ana nufin sun "ja da baya." A "juyar da maƙiyi baya" zai iya nufin a "haddasa maƙiyi ya ja da baya."
  • Ana amfani da haka a misali, sa'ad da Isra'ila suka "juya ga" allolin ƙarya, sai suka "fara yi masu sujada." Sa'ad da suka "juya daga" gumaka, suka "daina yi masu sujada."
  • Sa'ad da Allah "ya juya daga" mutanensa masu taurin kai, ya "daina kiyaye su" ko ya "daina taimakon su."
  • Faɗar "juya zukatan ubanni zuwa ga 'ya'ya" za a iya fassarawa haka "a sake haddasa ubanni su lura da 'ya'ya."
  • Faɗar "juya darajata zuwa kunya" za a iya fassarawa haka "haddasa darajata ta zama kunya" ko "a wulaƙanta ni har sai da naji kunya" ko "kunyatadda ni (ta wurin aikata mugunta) yadda mutane suka daina darjantani."
  • "Zan juya biranenku su zama kango" za a iya fassarawa haka "zan haddasa hallakar biranenku" ko "zan haddasa maƙiya su hallaka biranenku."
  • Faɗar "juyawa ciki" za a iya fassarawa haka "ya zama." Sa'ad da sandar Musa "ta juya zuwa" maciji, ta "zama" maciji." Za a iya fassarawa haka "canzawa zuwa."

(Hakanan duba: allahn ƙarya, kuturta, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 11:02
  • Ayyuka Manzanni 07:42
  • Ayyuka Manzanni 11:21
  • Irmiya 36:1-2
  • Luka 01:17
  • Malakai 04:06
  • Wahayin Yahaya 11:06

kabari, magina kabari, kaburbura, kushewa, kusheyi, maƙabarta

Ma'ana

Kalmomin "kushewa" da "kabari" ana nufin wurin da mutane ke saka jikin talikin da ya mutu. "Maƙabarta" ita ce kalmar da aka fi amfani da ita wajen ambatar wannan wurin.

  • Wasu lokuta Yahudawa na amfani da kogonni a matsayin kusheyi, wasu lokutan kuma suna gina kogonnin a cikin dutse a gefen tudu.
  • A zamanin Sabon Alƙawari, abin da aka saba yi ne a mirgina babban, dutse mai nauyi a bakin ƙofar kushewar domin a rufe shi.
  • Idan yaren fassarar kalmar kushewa na nufin rami inda akae sanya gawa ƙarƙashi ƙasa ne kawai, wasu hanyoyin fassarawa zau haɗa da "kogo" ko "rami a gefen tudu."
  • Faɗar "kabarin" yawanci ana amfani da shi ko'ina kuma a misali mai manufar yanayin kasancewa matattu ko wurin da rayukan matattun mutane suke.

(Hakanan duba: biznewa, mutuwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:29-31
  • Farawa 23:06
  • Farawa 50:05
  • Yahaya 19:41
  • Luka 23:53
  • Markus 05:1-2
  • Matiyu 27:53
  • Romawa 03:13

kabila, kabilu, na kabila, mutanen kabila

Ma'ana

Kabila wata ƙungiyar mutane ce waɗanda zuriya ne daga kaka ɗaya.

  • Mutane daga kabila ɗaya yawanci kuma suna da yare da al'ada ɗaya.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya raba mutanen Isra'ila cikin kabilu sha biyu. Kowanne kabila zuriya ne daga ɗa ɗaya ko jikan Yakubu.
  • Kabila bada kai ƙasa girma ba, amma tafi dangi girma.

(Hakanan duba: dangi, ƙasa, ƙungiyar mutane, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 10:19
  • 2 Sarakuna 17:16-18
  • Farawa 25:16
  • Farawa 49:17
  • Luka 02: 36-38

kabilu sha biyu na Isra'ila, kabilu sha biyu na 'ya'yan Isra'ila, kabilu sha biyu

Ma'ana

Wannan kalma, "kabilu sha biyu" na nufin 'ya'ya maza sha biyu na Yakubu da zuriyarsu.

  • Yakubu jikan Ibrahim ne. Daga baya Allah ya sauya masa suna daga Yakubu zuwa Isra'ila.
  • Waɗannan sune sunayen kabilun: Ruben, Simiyon, Lebi, Yahuda, Dan, Naftali, Gad, Asha, Issaka, Zebulun, Yosef da Benyamin.
  • Zuriyar Lebi basu gaji wata ƙasa ba a Kan'ana domin su kabilar firitoci ne waɗanda aka keɓe domin bauta wa Allah da mutanensa.
  • Yosef ya sami rabo biyu na ƙasar gãdo, waɗanda aka miƙa wa 'ya'yansa biyu maza, Ifraim da Manasse.
  • Akwai wurare da dama a Littafi Mai Tsarki inda jerin sunayen kabilun sha biyu sun banbanta kaɗan. Wani lokaci Lebi, Yosef, ko Dan ba a sa shi cikin jerin kuma wani lokacin 'ya'yan Yosef biyu maza Ifraim da Manasse ana sa su a jerin.

(Hakanan duba: gãji, Isra'ila, Yakubu, firist, kabila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 26:07
  • Farawa 49:28
  • Luka 22:28-30
  • Matiyu 19:28

kafa, kafaffe, wanda ya kafa, harsashi, harsasan

Ma'ana

Kalmar aikatau "kafaffe" tana nufin halitta, ko kafa tushe dominwani abu. kalmar nan tana nufin madogari. "Harsashi" shi ne tushen gini wato wurin da ake ɗora gini.

  • Harsashin gini ko gini dole ya zama da ƙarfi da kuma abin dogara domin temakawa dukkan ginin.
  • Kalmar "harsashi" za ta iya zama fara wani abu ko kuma can farkon abu ne, ko kuma lokacin da aka fara yin wani abu.
  • A cikin salon magana, masu bi cikin Almasihu an kwatata su da gini da aka kafa harsashinsa kan koyarwar manzanni, da annabawa, da kuma Yesu da kansa wanda ya zama dutsen kan kusurwa na ginin.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "kafin a kafa harsashin duniya" za'a iya fassara ta da "kafin a hallici duniya" ko "kafin lokacin da duniya ta fara kasancewa" ko "kafin a fara hallitar komai."
  • Kalmar nan "kafaffe" za'a iya fassara ta "kafaffen abu sosai," ko "abin da ya kafu sosai."
  • Ya danganta ga wurin, za'a iya fassara harsashi da "ƙaƙƙarfan gini" ko "daɓe mai kauri" ko "farawa" ko "halitta."

(Hakanan duba: dutsen kan kusurwa, halitta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 06:37-38
  • 2 Tarihi 03:1-3
  • Ezekiyel 13:13-14
  • Luka 14:29
  • Matiyu 13:35
  • Matiyu 25:34

kai, kawuna, goshi, goshi fiye da ɗaya, saiƙo, farkon kai, iyakokin kai, kogonnin kai, hallakarwa

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "kai" an more ta sosai cikn salon magana da ma'anoni masu yawa.

  • A mafi yawan lokuta ana moron kalmar domin a nuna kasancewa cikin iko akan mutane, kamar yadda yake a "ka maishe ni kai a kan dukkan al'ummai." Za'a iya fassara wanan da cewa "Ka maishe ni shugaba..." ko "Ka bani iko akan..."
  • An kira Yesu "kan ikkilisiya." Kamar dai yadda mutum ke bi da kuma sarrafa iyalin gidansa, haka Yesu ke biyar da mambobin "jikinsa," wato ikkilisiya.
  • Sabon Alƙawari na koyar da cewa miji shi ne "shugaban" matarsa. An danƙa masa ragamar shugabanci da kuma jagorantar matarsa da kuma iyali.
  • Batun nan "ba wata aska da zata taɓa kansa" na nufin "ba zai taɓa aske gashin kansa ba."
  • Kalmar nan "kai" zata iya zama farko ko kuma tushen wani abu kamar yadda yake "a tushen titi."
  • Kalmar nan "kawunan hatsi" tana nufin zangarkun alkama ne ko sha'ir da ke ɗauke da iraruwa.
  • Wani salon maganar da ake mora a kan "kai" shi ne a lokacin da ake magana akan mutum ɗungun misali, kamar "wanan kai mai furfura," tana magana ne akan dattijo, ko kuma misali "kan Yusufuwanda ke magana akan Yosef.
  • Maganar nan "bari jininsu ya zauna a kansa" na nufin cewamutumin shi ne sanadin mutuwarsu kuma za'a hukunta shi sab da hakan.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin, kalmar nan "kai" za'a iya fassara ta da "mulki" ko kuma "wanda ke jagoranta da kuma biyarwa" ko wanda ke da alhakin."
  • Maganar nan "kan" zata iya zama game da mutum ne ɗungun sabo da haka za'a iya fassara ta da moron sunan mutum kawai. misali, "kan Yosef" cikin sauƙin sauƙi za'a iya cewa "Yosef."
  • Maganar nan "zai kasance a kansance a kansa" za'a iya fassara ta da za'a "hukunta shi sabo da" ko kuma "shi za'a ɗorawa alhakin abin" ko "a ɗauke shi da cewa shi ne mai laifi kan al'amarin."
  • Ya danganta ga wurin, waɗansu hanyoyi na fassara wanan kalma sun haɗa da "farko" ko "tushe" ko "mai mulki" ko "shugaba" ko na can "ƙoli."

(Hakanan duba: hatsi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 1:51-54
  • 1 Sarakuna 08:1-2
  • 1 Sama'ila 09:22
  • Kolosiyawa 02:10
  • Kolosiyawa 02:19
  • Littafin Lissafi 01:4

kala, yin kala, kalatacce, aikin kala

Ma'ana

Kalmar nan "kala" tana nufin a zagaya fili ko gidan gona a tsince duk sauran hatsi ko 'ya'yan hatsi da masu girbi suka rage a baya.

  • Allah ya ce da 'ya'yan Isra'ila su bar gwauraye, da mataulata, da bãƙi su yi kala a ganakinsu da suka yi girbi su kuma dinga rage musu domin su sama wa kansu abinci.
  • A waɗansu lokutan mai gonar yakan bar masu kalar su shiga gonar kai tsaye su yi kala su bin bayan masu girbi suna kala wanan kan sa su sami kala hatsi mai yawa.
  • Misali na zahiri shi ne yadda wanan ya yi aiki a labarin Rut, wadda aka yi mata alheri aka bar ta ta yi kala a cikin masu girbi a fagen danginta Bo'aza.
  • Waɗansu hanyoyi na yin fassarar "kala" sune "tsince" ko "tari" ko "tattarawa."

(Hakanan duba: Bo'aza, hatsi, gibi, Rut)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 24:21-22
  • Ishaya 17:4-5
  • Ayuba 24:6
  • Rut 02:2
  • Rut 02:15

kalma ko magana, kalmomi ko maganganu, jawabi, umarni

Ma'ana

"Kalma" wani abu ne da wani ya faɗa.

  • Misalin wannan kuwa shi ne lokacin da mala'ika ya gaya wa Zakariya, "baka gaskanta da maganganu na ba," ma'ana, "baka gaskanta da bin da na faɗi ba."
  • Wannan kalma na manufar dukkan saƙon, ba wai kalma ɗaya kawai ba.
  • Wani lokaci "kalma" na nufin dukkan jawabi, kamar "iko cikin magana da ayyuka" wato "cike da iko a jawabi da hali."
  • A yawancin wurare cikin Littafi Mai Tsarki "kalma" na nufin dukkan abin da Allah ya faɗi ko ya umarta, kamar "maganar Allah" ko "maganar gaskiya."
  • Wata hanya ta musamman na amfani da wannan kalma ita ce ambatar Yesu "Kalma." Domin waɗannan fassara na guda biyu daga baya, duba "maganar Allah."

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyi daban-daban da ake fassara "magana" ko "maganganu" sun haɗa da "koyarwa" ko "saƙo" ko "labarai" ko "a faɗa" ko "abin da aka ce."

(Hakanan duba: maganar Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:02
  • Ayyukan Manzanni 08:04
  • Kolosiyawa 04:03
  • Yakubu 01:18
  • Irmiya 27:04
  • Yahaya 01:03
  • Yahaya 01:14
  • Luka 08:15
  • Matiyu 02:08
  • Matiyu 07:27

kamammu, bautar talala

Ma'ana

Waɗannan maganganu "kamammu" da "bautar talala" suna faɗi ne akan kama mutane a tilasta masu su zauna inda basu so su zauna, kamar cikin baƙuwar ƙasa.

  • Isra'ilawa daga mulkin Yahuda an riƙe su kamammu a mulkin Babiloniya shekaru 70.
  • Yawancin lokaci akan buƙaci kamammu suyi wa mutanen aiki ko al'ummar da ta kama su.
  • Daniyel da Nehemiya kamammun 'ya'yan Isra'ila ne da suka yiwa sarkin Babila aiki.
  • Wannan furci "a ɗauke kamamme" wata hanya ce ta yin magana akan kama mutum.
  • Wannan furci, "a ɗauke a kora su kamammu" za a iya fassara shi haka, "a tilasta wa mutane suyi zaman kamammmu" ko "a ɗauke ku a kai ku wata ƙasa a matsayin 'yan kurkukui."
  • Manzo Bulus ya fassara wannan da misali cewa Kiristoci "su kama" kowanne tunani su sa ya yi biyayya da Almasihu.
  • Ya kuma yi magana akan yadda mutum zai iya zama "kamamme" ga zunubi wato zunubi ne yake mallaƙarsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, zama "kamamme" za a iya fassarawa da, "ba a bari a sake ba" ko "tsarewa a kurkuku" ko "tilastawa a zauna a baƙuwar ƙasa."
  • Furcin "kaiwa ga bauta" ko "ɗaukewa zuwa bauta" za a iya fassarawa a matsayin, "cafkowa" ko "sanyawa kurkuku" ko "tilastawa a tafi baƙuwar ƙasa."
  • Kalmar "kamammu" za a iya fassarawa a matsayin, "mutanen da aka kamo" ko "mutane bãyi."
  • Ya danganta ga nassin, "bauta" za a iya fassarawa a matsayin, "zaman kurkuku" ko "gudun hijira" ko "tilastawa, a zauna cikin baƙuwar ƙasa."

(Hakanan duba: Babila, hijira, kurkuku, karɓewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 10:05
  • Ishaya 20:04
  • Irmiya 43:03
  • Luka 04:18

kamar, ra'ayi ɗaya, kamalta, kamamni, kama da yawa, haka ma, sun yi kama, ba kamar, sai ka ce

Ma'ana

Wannan furci "kamar" da "kamanni" ana nufin wani abu ya yi dai-dai da, ko ya yi kusan kama, da wani abu.

Kalmar nan "kamar" ana amfani da ita cikin maganar da ake ceda ita "kamaltawa" idan za a gwada wani abu da wani abun da ban, tare da faɗin inda suka yi kama musamman. Misali, "tufafinsa suka yi walƙiya kamar rana" da "muryar ta yi ƙara kamar aradu."

  • A "zama kamar" ko "ƙara kamar" ko "ya yi kama" da wani abu ko wani mutum ma'ana yana da wasu halaiya da suka yi kama wannan abu ko wannan mutumin da ake gwada wa da shi.
  • An hallici mutane a cikin "kamannin" Allah, wato a cikin "surarsa." Ma'ana, suna da wasu ɗabi'arsa ko jamalinsa da suke kamar ko "kusan kamar" yadda Allah yake, kamar iya tunani, yadda yake ji, da yadda yake magana.
  • A zama da "kamannin wani abu" ko wani mutum, ma'ana ana da ɗabi'u da suka yi kama da wannan abu ko mutumin nan.

Shawarwarin Fassara:

  • A cikin wasu wurare, furcin haka "kamannin haka" za a iya fassara shi "abin da ya yi kama" ko "abinda yaso ya yi kama."
  • Wannan furci "a cikin kamannin mutuwarsa" za a iya fassarawa "yin tarayya da shi cikin mutuwarsa."
  • Wannan furci "cikin kamannin jiki mai zunubi" za aiya fassara shi haka "zama kamar mutum mai zunubi ko "ya zama mutum." A tabbatar fassararnan bata yi kamar Yesu mai zunubi ne ba.
  • A cikin nasa kamannin" za a iya fassara shi haka "zama kamarsa" ko "ana da abubuwa da yawa da aka haɗa kamannin da shi.
  • Wannan furci "kamannin surar mutum mai mutuwa, ko tsuntsaye da dabbobi masu ƙafafu hur huɗu da masu rarrafe za a iya fassara shi haka "gumaku da aka yi su da kamannin mutum mai lalacewa ko dabbobi kamar su tsuntsaye, namun jeji, da ƙananan abubuwa masu rarrafe."

(Hakanan duba: dabbobi, nama, surrar Allah, sura, lalacewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 01:05
  • Markus 08:24
  • Matiyu 17:02
  • Matiyu18:03
  • Zabura 073:05
  • Wahayin Yahaya 01:12-13

kamawa, kamowa, kamun

Ma'ana

Kalmar "kama" na nufin karɓa ko kamo wani ko wani abu da karfi. Yana kuma nufin nuna iko da fin karfin wani.

  • Idan aka runtumi gari ta karfin soji, sojojin zasu kwashe waɗansu kayyayaki masu amfani na mutanen da suka yashe.
  • Idan akayi amfani da razanarwa, za a iya cewa mutumin an "kame shi ne da tsoro." Wannan na nufin cewa an "ci nasara da mutumin ne ta wurin tsoro." idan an "kama wani da tsoro" za a iya cewa mutumin" ya cika da matuƙar tsoro."
  • A lokacin nakuda mai zafi dake "kama" mace. ma'anar ita ce zafin ya zama da matukar kuna. za a iya fassara wannan ta wurin cewa zafin ya " mamaye" ko ya zo baki ɗaya" ga matar.
  • Za a kuma iya fassara wannan da cewa "ɗaukar ikon kan wani abu" ko ɗaukewa farat ɗaya" ko "samu."
  • Faɗar "kamowa ka kwana da ita" kan iya fassaruwa da "tilastawa kansa gare ta" ko "ɓata ta" ko "yi mata fyaɗe." a tabbatar wannan fassarar ta sami karɓuwa.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 16:19-21
  • Fitowa 15:14
  • Yahaya 10:37-39
  • Luka 08:29
  • Matiyu 26:48

kambi, sa masa kambi

Ma'ana

Kambi wani abu ne mai ado, da ake sawa akan masu mulki, kamar sarakai da sarauniyoyi. Wannan kalma "sa masa" ma'anarta a aza kambi akan wani; kwatancin an "gimama" shi.

  • Akan yi kambi da zinariya ko azurfa, sa'annan a sa masa duwatsu masu daraja kamar su turkos da lu'ulu'ai.
  • Kambi alamace mai nuna ikon sarki da wadatarsa.
  • Ga bambamci, kambin ƙayayuwan rassan itace wanda sojojin Romawa suka sa akan Yesu saboda suyi masa ba'a ne da cutarwa.
  • A zamanin dã, waɗanda suka yi nasara a wasan tsalle tsalle akan basu kambin da aka yi da rassan zaitun. Manzo Bulus yayi magana akan wannan kambi a wasiƙarsa ta biyu ga Timoti.
  • Idan a misali aka ce, "a sa wa wani mutum kambi" zai zama da ma'ana haka "agirmama wani mutum." Mukan girmama Allah tawurin yi masa biyayya da kuma yabonsa wurin waɗansu. Wannan ya zama kamar sa masa kambi a kansa da amincewa shi Sarki ne.
  • Bulus ya kira 'yan'uwa masu bada gaskiya "murnarsa da kambinsa." An yi amfani da "kambi" a misalta yadda Bulus ya sami babban albarka da girmamawa tawurin yadda waɗannan masu bada gaskiya suka cigaba cikin aminci a bauta wa Allah.
  • Idan a yi amfani da maganan nan "sa wa wani kambi" cikin misali, ma'anarta zai iya zama "lada" ko "girmamawa" ko "sakamako."
  • Idan an yi amfani da "naɗa kambi" a misalce, za a fassara shi haka "a girmama" ko "a darajanta."
  • Idan an "naɗa wa wani mutum kambi" za a iya fasara wannan haka, "an sa masa kambi a kansa."
  • Wannan furci, "an naɗa masa kambi da ɗaukaka da bangirma" za a iya fassara wannan haka, " an ɗibiya masa ɗaukaka da bangirma "ko "an bashi ɗaukaka da bangirma" ko "an yi masa baiwar ɗaukaka da bangirma."

(Hakanan duba: ɗaukaka, sarki, zaitun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 19:03
  • Littafin Makoki 05:16
  • Matiyu 27:29
  • Filibiyawa 04:01
  • Zabura 021:03
  • Wahayin Yahaya 03:11

kamun farauta, farauta akan

Ma'ana

Wannan magana "kamun farauta" na nufin wani abu da aka farauto, misali dabba da ake ci.

  • A misalce, "kamun farauta" zai iya zama mutumin da ake cin zalinsa, cutar sa, ko ƙwarar sa ta wurin mutumin da ya fi shi ƙarfi.
  • Idan ana "farautar" mutane, ma'ana, ana ƙwararsu ta wurin wulaƙanta su ko sace wani abu daga gare su.
  • Wannan kalma "farauta" za a iya kuma fassara ta haka, "'dabbar farauta" ko "wanda ake farautar sa" ko "cafke marar laifi."

(Hakanan duba: wulaƙanci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Irmiya 12:09
  • Zabura 104:21

kamun kai, kãmẽ kai, keɓe kai

Ma'ana

Kamun kai shi ne iya kame halayyar wani domin ya gujewa zunubi.

  • Yana nufin hali mai kyau, wato, gujewa tunane tunanen saɓo, furci, da ayyuka.
  • kamun kai ɗiya ne ko ɗabi'ar da aka bayar ga masu bi.
  • mutumin dake amfani da kamun kai ya yi nasarar tsai da kansa ga aikata abu marar kyau da yake son yi. Allah ne ke sa mutum ya sami kamun kai.

(Hakanan duba: ɗiyan Itace, Ruhu Mai Tsarki )

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 07:8-9
  • 2 Bitrus 01:5-7
  • 2 Timoti 03:1-4
  • Galatiyawa 05:23

karɓa, karɓawa, karɓa, mai karɓa, marabta, ɗaukawa sama, karɓuwa

Ma'ana

Kalmar "karɓa" na manufar a samu ko a yarda da wani abu da aka bayar, miƙa, ko gabatar.

  • A "karɓa" na iya nufin shan wahala ko samun wani yanayi, kamar 'ya samun hukuncin da ya dace da abin da ya yi."
  • Muna iya kuma mu karɓi bãƙo. Ga misali muna iya yin maraba da wani bãƙo ko bãƙi na musamman mu kuma girmama su domin mu ƙulla abokantaka da su.
  • A "karɓa Ruhu Mai Tsarki" na manufar an bamu Ruhu Mai Tsarki mun kuma marabce shi ya yi aiki cikinmu kuma ta rayuwarmu.
  • A "karɓi Yesu" na manufar a yi maraba da ceton Allah ta wurin Yesu Almasihu.
  • A yayin da wani makaho ya "karɓi ganin gari" ya nuna cewa Allah ya warkar da shi ya kuma ba shi ikon ganin gari.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, "karɓi" za a iya fassarawa haka "anshi" ko "maraba" ko "samun sabawa" ko "a bayar."
  • Faɗar "za ku karɓi iko" za a iya fassarawa haka "za a ba ku iko" ko "Allah zai ba ku iko" ko "za a bayar da iko a gare ku (ta wurin Allah)" ko "Allah zaya sa Ruhu Mai Tsarki ya yi aiki da iko a cikin ku."
  • Faɗar "ya karɓi ganinsa" za a iya fassarawa haka "ya samu iya gani" ko "ya sake samun iya ganin gari" ko "Allah ya warkar da shi har ya samu iya ganin gari."

(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, Yesu, ubangiji, ceto)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 05:09
  • 1 Tasalonikawa 01:06
  • 2 Tasalonikawa 04:01
  • Ayyukan Manzanni 08:15
  • Irmiya 32:33
  • Luka 09:05
  • Malakai 03:10-12
  • Zabura 049:14-15

karkata, karkatarwa, karkatattun hanyoyi, ɓaɓɓata wa, dukkan rashin adalci, rashin gaskiya, ruɗi, maguɗi

Ma'ana

Wannan magana "karkatar wa" ana amfani da ita a kan mutumin da al'amuransa karkatattu ne, mai maguɗi. Ma'anar wannan kalma "karkatarwa" shi ne "yin abu a rashin gaskiya." Idan an "karkatar" da wani abu wato an murɗe shi ko janye shi daga inda ya kamata ko daga wari mafi kyau.

  • Wani mutum ko wani abu daya karkace ya kauce daga abin da yake mai kyau da kuma dai-dai.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, Isra'ilawa suka karkace sa'ad da suka yi rashin biyayya ga Allah. Sun yi haka yawancin lokuta ta wurin yin sujada ga gumaku.
  • Duk wani aiki dake gãba da tutar Allah ko halinsa ana ɗaukarsa karkatacce.
  • Wasu hanyoyin fassara "karkata" za a haɗa da "halin maguɗi" ko "ƙazamtacciyar rayuwa" ko "juyawa daga miƙaƙƙiyar hanyar Allah," zai danganta bisa ga nassi.
  • "Karkatattun maganganu" za a fassarasu haka "faɗin miyagun maganganu" ko "maganar ruɗi" ko "ƙazamtattun hanyoyin yin magana."
  • Karkatattun mutane" za a iya fassarawa haka "mutane marasa tsabtar rai" ko "mutane masu rayuwar ƙazamta" ko "mutane waɗanda suke ci gaba dayi wa Allah rashin biyayya."
  • Wannan magana "yin karkatattun ayyuka" za a iya fassara ta haka "yin abu da mugunta" ko "yin abubuwa gãba da umarnan Allah" ko "yin zaman rayuwa a tafarkin da ya ƙi koyarwar Allah."
  • Wannan kalma "karkata" za a kuma iya fassara ta zuwa "sa wani mutum ya lalace" ko "juyawa zuwa ga abin mugunta."

(Hakanan duba: lalatarwa, ruɗi, rashin biyayya, mugunta, juyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 08:47
  • 1 Sama'ila 20:30
  • Ayuba 33:27-28
  • Luka 23:02
  • Zabura 101:4-6

karkiya, karkiyoyi, ansa karkiya, ɗaurewa

Ma'ana

Karkiya ɗan katako ne ko ƙarfe da ake ɗaura wa wata dabba ko dabbobi a haɗa su domin su jã keken noma. Akwai wasu misalai daban-daban daga wannan kalma.

  • Kalmar "karkiya" ana amfani da ita a kwatanta wani abin da ya haɗa mutane tare domin aiki tare, kamar yin hidima ga Yesu.
  • Manzo Bulus ya yi amfani da kalmar "abokin karkiya" ya bayyana wani wanda ke bauta wa Almasihu kamar sa. Ina iya fassara wannan kuma a ce "abokin aiki" ko "abokin bauta" ko "aboki cikin hidima."
  • Kalmar "karkiya" ana amfani da ita a bayyana kaya mai nauyi da wani zai ɗauka dole, kamar wanda aka musguna masa ko yana cikin bauta ko tsananci.
  • A yawancin nassosi, yana da kyau a fassara yadda take, ana yin amfani da kalmar kamar yadda manomi ke iya amfani da ita.
  • Wasu hanyoyin fassara wannan kalmar na iya zama, "nawaya ta zalunci" ko "kayan nauyi" ko "abin ɗaurewa," ya danganta da nassin.

(Hakanan duba: ɗaura, kaya, zalunta, tsanantawa, bawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 15:10
  • Galatiyawa 05:01
  • Farawa 27:40
  • Ishaya 09:04
  • Irmiya 27:04
  • Matiyu 11:30
  • Filibiyawa 04:03

karkuwa, garkuwoyi, kãre

Ma'ana

Garkuwa wani abu ne da soja yake riƙewa a fagen dãga domin kãre kansa daga samun rauni daga makamin abokin gãbã. a samar da "garkuwa" ga wani na nufin a kare wannan mutumin daga cutuwa.

  • Garkuwoyi sunanan kamar fai-fai ko abun da yake a zagaye, akan yi shi da abubuwa kamar su leda, itace, ko ƙarfe da kuma sanda mai kaurin gaske da ake sa takobi ko kibiya daga sashin su.
  • Yin amfani da wannan misalin, Littafi Mai Tsarki ya bayyana Yahweh a matsayin garkuwa domin mutanensa.
  • Bulus ya yi magana akan "kariyar bangaskiya", wanda hanya ce ta cewa samun bangaskiya cikin Yesu da kuma rayuwa a cikinta cikin biyayya da Allah zai kare masu bi daga farmakin Shaiɗan.

(Hakanan duba: bangaskiya, biyayya, Shaiɗan, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 14:26
  • 2 Tarihi 23:8-9
  • 2 Sama'ila 22:36
  • Maimaitawar Shari'a 33:29
  • Zabura 018:35

karusa

Ma'ana

A zamanan dã, karusai wasu akwatunan keke ne marasa nawi, da tayoyi biyu da dawakai ke ja.

  • Mutane sukan zauna ko su tsaya cikin karusai, suna amfani da su domin yaƙi ko tafiya.
  • A lokacin yaƙi, rundunar da take da karusai tana da fifiko wajen gudu da ƙutsawa cikin rundunar da bata da karusai.
  • Masarawa da Romawan dã sanannu ne wajen yin amfani da dawakai da karusai.

(Hakanan duba: Masar, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 09:22
  • 2 Tarihi 18:28-30
  • Ayyukan Manzanni 08:29
  • Ayyukan Manzanni 08:38
  • Daniyel 11:40-41
  • Fitowa 14:25
  • Farawa 41:43

karuwa, karuwanci, karuwai, mazinaciya

Ma'ana

Wannan magana "karuwa" na nufin mutumiyar da take kwana da maza saboda kuɗi ko tsarin addini. Karuwai yawancin lokaci mata ne, amma wasu maza ne.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan magana "karuwa" wani lokaci ana yin amfani da ita domin a kwatanta mutumin dake bauta wa gumaku ko aikata sihiri.
  • Wannan furci "yin karuwanci" ma'anarta yi kamar karuwa ta wurin ƙazantaccen kwana da maza, Wannan magana kuma a cikin Littafi Mai Tsarki na faɗi akan mutumin dake yiwa gumaku sujada.
  • Idan mutum ya "karuwantar da kansa" ga wani abu ana nufin rayuwar zina ko in an kwatanta, wato ana rashin aminci ga Allah ta wurin yin sujada ga gumaku.
  • A zamanin dã, wasu haikalin gumaku sukan yi amfani da karuwai maza da mata a cikin hidimar tsafinsu.
  • Wannan magana za a iya fassarata da kalma ko furci da ake amfani da ita a harshen masu juyi da zai nuna karuwa ake nufi. Mai yiwuwa wasu yare suna da maganar da ta kamanta ta da harshensu.

(Hakanan duba: zina, gunki, shashanci, gunki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 34:31
  • Farawa 38:21
  • Luka 15:30
  • Matiyu 21:31

kashi goma, kasusuwa goma, zakka, zakkoki

Ma'ana

Kalmar "kashi goma" ko "zakka" na nufin "kashi goma cikin ɗari" ko "guda ɗaya cikin kashi goma" na kuɗin wani, amfanin gona, dabbobi, ko wasu mallakokin, wanda ake ba Allah.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya umarci Isra'ilawa da su keɓe daga abin da suke da shi su bayar a matsayin baikon godiya a gare shi.
  • Ana amfani da baikon a taimaki Lebiyawa kabilar Isra'ila waɗanda ke yiwa Isra'ilawa hidima a matsayin firistoci da masu lura da rumfar sujada daga bisani kuma, a haikali.
  • A cikin Sabon Alƙawari, Allah bai buƙaci bayar da zakka ba, amma maimako ya bada umarni ga masubi da su bayar hannu sake da farinciki ga mutane mabuƙata su kuma taimaki aikin hidimar Kiristanci.
  • Ana iya kuma fassara wannan haka "ɗaya cikin goma" ko "ɗaya daga cikin goma."

(Hakanan duba: mai bi, Isra'ila, Balebi, dabbobi, Melkizadek, mai hidima, hadaya, rumfar sujada, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 14:19-20
  • Farawa 28:20-22
  • Ibraniyawa 07:4-6
  • Ishaya 06:13
  • Luka 11:42
  • Luka 18:11-12
  • Matiyu 23:23-24

kashi, kashin dabbobi

Ma'ana

Wanan kalmar tana nufin wani kash maikauri na mutum ko na dabba, ana kiransa najasa, bayi. In aka yi amfani da shi a matsayin taki domin inganta ƙasa sai a kira shi "takin gargajiya."

  • Waɗannan kalmomin ana iya moron su a matsayin salon magana domin a nuna wani abu marar daraja ko muhimmanci.
  • Akan yi amfani da busassun kashin dabbobi a matsayin makamashin man fetur.
  • Wanan furci "Kamar kashi a ƙasa" za'a iya fassara shi da "an warwatsu kamar kashin dabbabi marar amfani a saura."
  • "Ƙofar Kashi" a kudu da garun Yerusalem, zai iya yiwuwa ƙoface a can da inda akan bi a zubar da shara daga cikinn birnin.

(Hakanan duba: ƙofa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 14:10
  • 2 Sarakuna 06:25
  • Ishaya 25:10
  • Irmiya 08:2

keɓewa, yin keɓewa, keɓaɓɓe, tsarkakewa, kafawa, sadaukakke

Ma'ana

A keɓe na ma'anar na nufinware ko kuma miƙa wani abu domin wani dalili na musamman ko kuma wani aiki na musamman.

  • Dauda ya keɓe zinariyarsa da azurfarsa domin Ubangiji.
  • A mafi yawancin lokaci "keɓewa" na nufin yin wani tsararren biki ko abu domin keɓe wani abu domin wani dalili na musamman.
  • Keɓe bagadi ya haɖa da hadaya ko kuma baiko ga Allah.
  • Nehemiya ya jagoranci Isra'ilawa domin keɓe Yerusalem da kuma gyara bangonta tare da sabunta alƙawari domin a bautawa Yahweh da kuma lura da birninsa. Wannan al'a marin ya haɗa da miƙa godiya ga Allah tare da kayan kiɗa da waƙa.
  • Wannan kalmar na nufin keɓewa, ko kuma "miƙa wani abu domin amfani da shi domin wani abu na musammam" ko "wani aike na musamman" ko kuma "asa wani ya yi wani abu na musamman."

(Hakanan duba: miƙawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi15:11-12
  • 1 Korintiyawa 06:9-11
  • 1 Sarakuna 07: 51
  • 1 Timoti 04:5
  • 2 Tarihi 02:4-5
  • Yahaya 17:18-19
  • Luka 02:22-24

kerkeci

Ma'ana

Kerkeci wata babbar dabba ce, mai ƙafafu huɗu mai zafin rai da gashi mai baƙin ƙasa-ƙasa, ko baƙi, da haƙora masu tsini da kofatai. Kerketai suna ko'ina a Isra'ila a lokacin Littafi Mai Tsarki.

  • Waɗannan dabbobi suna zama a kurmi da tsaunuka; suna cin kifi, ƙwari, da shuke-shuke.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, ana amfani da alamar kerkeci a kwatanta ƙarfi.
  • Sa'ad da yake kiwon tumaki, makiyayi Dauda ya yi faɗa da kerkeci ya ci nasara a kansa.
  • Kerkeci guda biyu suka fito daga kurmi suka fafari ƙungiyar matasa waɗanda suka yiwa annabi Elisha ba'a.

(Hakanan duba: Dauda, Elisha)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:


kerub, kerubim, kerubobi

Ma'ana

Wannan kalma "kerub" idan kuma suna da yawa "kerubobi" ana nufin wasu rayayyun sammai ne musamman da Allah ya hallita. Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa kerubobi suna da fukafukai da harshen wuta.

  • Kerubobi suna bayyana ɗaukakar Allah da kuma ikonsa kuma su matsaran keɓaɓɓun abubuwa masu tsarki ne.
  • Bayan su Adamu da Hauwa'u suka yi zunubi, Allah ya aje kerubobi da takkuban wuta a gabashin lambun Aidan saboda kada mutane su isa wurin itacen rai.
  • Allah ya umarci Isra'ilawa su ƙera kerubobi biyu suke fuskantar juna, da fukafukai masu taɓa juna, bisa marufin kafara na akwatin alƙawari.
  • Ya kuma gaya masu su saƙa hotunan kerubobi a cikin labulen haikali.
  • A wasu nassoshin, waɗannan hallitun an ce suna da fuskoki huɗu: dana mutum, da zaki, da bijimi, da kuma gaggafa.
  • Wani lokaci ana tunanin kerubobi mala'iku ne, amma Littafi Mai Tsarki bai faɗi haka a sarari ba.

Shawarwarin Fassara

  • Wannan kalma "kerubibi" za a iya fassara shi ya zama "hallitu masu fukafukai" ko "matsara masu fukafukai" ko "matsara cikin ruhaniya masu fukafukai" ko tsarkakakkun matsara masu fukafukai."
  • "Kerub" guda ɗaya kenan daga cikin kerubobi haka kuma a fassara sai a fassara shi a matsayin ɗaya misali "hallita mai fukafukai" ko "mai tsaro mai fukafukai."
  • A tabbatar fassarar wannan kalma "kerub" ta bambanta dana "mala'ika."
  • Kuma a yi lura yadda aka fassara wannan suna ko aka rubuta shi cikin Littafi Mai Tsarki na wani yare ko yaren ƙasar.

(Hakanan duba: mala'ika)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 13:06
  • 1 Sarakuna 06:23-26
  • Fitowa 25:15-18
  • Ezekiyel 09:03
  • Farawa 03:22-24

kewayewa, mamaye, zagaye, 'yan kwantan ɓauna, zagayewa, ayyukan mamayewa

Ma'ana

"Kewayewa" na aukuwa ne lokacin da sojoji suka kai wa gari hari suka hana shigar da kowanne irin kayan abinci da ruwa. A "mamaye" gari ko a sashi karkashin "kewayewa" na nufin a kai mashi hari ta hanyar kewayewa.

  • Lokacin da Babilawa suka kai wa Isra'ila hari, sunyi amfani da dabarar kewayewa gãbã da Yerusalem domin su raunana mutanen dake cikin garin.
  • mafi yawa lokacin kewayewa, akan matakalai da juji ayi lodinsu domin sojoji su iya haura katangar garin su mamayeshi.
  • A "Mamayewa" gari yana iya zama "yin kwantan ɓauna" a kan shi ko "yin hinge" a kan shi.
  • Kalmar "mamayewa" ma'anarsu ɗaya da cewa "karkashin kewaya". duk waɗannan maganganu suna nuna garin da rundunar abokin gãbã ya kewaye ya kuma mamaye.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 20:1
  • 1 Sarakuna 20:1-3
  • 1 Sama'ila 11:1-2
  • Irmiya 33:04

kisan aure

Ma'ana

Kisan aure wani aiki ne a ƙarƙashin shari'a da ke kawo ƙarshen aure. Kalmar nan kisan aure tana nufin rabuwa ta zaman aure bisa matakin doka wanda ta kawo ƙarshen aure a tsakanin ma'aurata.

  • Ma'anar wanan kalmar mai sauƙi ita ce kora, saki, ko rabuwa da ma'aurata, waɗansu harsunan za su iy amfani da irin waɗannan kalamai wajen baiyana kisan aure.
  • "Takardae shedar kisan aure" aza' iya fassara ta da da ke baiyana cewa aure ya kawo ƙarshe."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 08:8-11
  • Lebitikus 21:7-9
  • Luka 16:18
  • Markus 10:04
  • Matiyu 05:32
  • Matiyu 15:03

kishi, ƙyashi

Ma'ana

Kalmar nan "kishi" tana magana ne akan kishin wani sabo da abin da ya mallaka ko kuma sabo da kyawawan halayensa. Kalmar nan ƙyashi tana hufin wani mummunan marmari ne na son samun wani abu.

  • Kishi yakan zama abu ne da bai kamata ba ta hanyar nuna tunani marar kyau akan nasarar wani, ko sa'ar da ya samu, ko kuma mallaka.
  • Ƙyashi shi ne babbar mummunan marmamari na son abin da wani ya mallaka, ko kuma abokin taraiyar wani ko wata.

(Hakanan duba: kishi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Korintiyawa 13:4-7
  • 1 Bitrus 02: 1
  • Fitowa 20:17
  • Markus 7:20-23
  • Littafin Misalai 03:31-32
  • Romawa 01:29

kishimi, kishima, matan matan kishimai, jairran kishimai, remaye, remayen jeji

Ma'ana

Kishimi babban naman dawa ne da ke da ƙafafu huɗu wanda ke zama a jeji ko kuma kan duwatsu,wannan tamatar dabbar tana da dogayen ƙahonni ko wani abu mai kama da haka kanta.

  • Kalmar nan kishima tana ma'anar tamatar kishimi jariran kuma sune 'ya'yansu ƙanana
  • Kalmar kishimi tana nufin namijin kishimi.
  • Rema kuwa wata irin dabba ce mai zama a kan dutse
  • Kishimi na da ƙarfi sosai, da siraran ƙafafu kuma yakan yi gudu da sauri.
  • Ƙafafunsu na da rababben kofato wanda ke temakonsu su hau samanitace ko dutse cikin sauƙi.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 22:34
  • Farawa 49:21
  • Ayuba 39:02
  • Zabura 018:33
  • Waƙar Suleman 02:7

kofato, kofatai, kofatoci

Ma'ana

Kalmar nan na nufin wani wani abu mai tauri da ke rufe tafin ƙafafu na waɗansu irin dabbobi kamar raƙumi, garke, kishimi, dawakai, jakuna, aladu, takarkari, tumakai, awakai.

  • Kofaton dabba na kare ƙafarta a lokacin tafiya.
  • Waɗansu dabbobin na da rababbun kofatai waɗansu kuma babu.
  • Allah ya faɗawa Israilawa cewa dabbbar da ke da rababben kofato take kuma tuƙa an ɗauke ta mai tsafta kuma ana iya aci. Waɗanan sun haɗa da awaki, tumaki, kishimi, da takarkari.

(Hakanan duba: raƙumi, shanu, alfadari, jaki, akuya, alade, tumaki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 14:06
  • Ezekiyel 26:9-11
  • Lebitikus 11:04
  • Zabura 069:31

komowa, sakamako, an koma, ana komowa

Ma'ana

Kalmar "komowa" na nufin a koma baya ko a maido da wani abu.

  • "Komowa ga" wani abu na nufin a sake yin ayyukan nan kuma. A "komo ga" wani wuri ko ga mutane na nufin a koma ga baya ga wannan wuri ko ga mutanen.
  • Sa'ad da Isra'ila suka komo sujada ga allolinsu, suna sake yin sujada gare su kuma.
  • Da suka dawo ga Yahweh, suka tuba suka kuma soma sujada ga Yahweh kuma.
  • Idan aka maido da ƙasa ko wasu abubuwan da aka ɗauke ko aka karɓe daga wurin wani manufa shi ne a maido da wannan kaya zuwa ga mutumin dake da wannan kaya.

(Hakanan duba: juyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:


koyawa, koyarda, koya, koyarwa, marar koyarwa

Ma'ana

A "koyawa" wani shi ne a gaya masa wani abu da bai riga ya sani ba. Yana kuma iya nufin "a wadatar da labarai" a taƙaice, ba tare da ambaton wanda ke koyon ba. Yawanci ana bada labarai ta hanya dai-daitacciya ko bisa tsari. Mai "koyawa" ko "koyarwar" sa sune abin da yake koyarwa.

  • Shi "malami" wani ne mai koyarwa. "Koyar" da abin da ya wuce shi ne "koya."
  • Sa'ad da Yesu yake koyarwa, yana bayanin abubuwa game da Allah da mulkinsa.
  • Almajiran Yesu na kiransa "Malami" a matsayin nuna bangirma ga wanda yake koyarwa game da Allah.
  • Abin da ake koyarwa za a iya nuna wa ko magana akai.
  • Kalmar "koyarwa" na nufin jerin koyarwa daga Allah game da shi kansa da kuma umarnan Allah game da yadda za a yi rayuwa. Za a iya fassara wannan ma a matsayin "koyarwa daga Allah" ko "abin da Allah yake koyarwa."
  • Faɗar "abin da kuka koya" za a iya fassarawa kuma, "abin da waɗannan mutane suka koyar daku" ko "abin da Allah ya koyar daku," ya danganta da nassin.
  • Wasu hanyoyin fassara "koyawa" sun haɗa da a "faɗi" ko ayi "bayani" ko bada "umarni."
  • Yawanci ana fassara wannan kalma a matsayin "koyawa mutane game da Allah."

(Hakanan duba: umarni, malami, maganar Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 01:03
  • Ayyukan Manzanni 02:40-42
  • Yahaya 07:14
  • Luka 04:31
  • Matiyu 04:23
  • Zabura 032:08

koyi da, mai koyi da, masu koyi da

Ma'ana

Kalmar nan "koyi da" da "mai koyi da" na nufin kwaikwayon wani abu da bam ko wani abin da wani ke yi.

  • An koyawa Krista su yi koyi da Yesu ta wurin yin biyayya da Allah da ƙaunar juna kamar dai yadda Yesu ya yi.
  • Manzo Bulus ya faɗawa masubi na farko su yi koyi da shi kamar yadda ya yi koyi da Kristi.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "koyi da" ana iya fassarar ta da "yin wani abu kamar yadda wani ya yi" ko kuma "bin misalinsa."
  • Maganar nan "ku yi koyi da Allah" za'a iya fassara ta da "ku zama mutane masu yin abu kamar yadda Allah ke yi."
  • "Kun za zama masu koyi da mu" za a iya fassara ta da "kun bi misalinmu" ko "kuna yin irin abin kirki da kuka ga muna yi."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 3 Yahaya 01:11
  • Matiyu 23:1-3

kuɓutarwa, kuɓutarwar, kuɓutacce, yin kuɓutarwa, mai kuɓutarwa, aikin kuɓutarwa, miƙawa, wanda aka miƙa, juyawa, saki, ceta, yin ceto, cetacce, wanda za'a ceta, bada dama domintsira

Ma'ana

A "Kuɓutar da wani" wannan na nufin a kutar da mutum nan. "mai kuɓutarwa" na nufin mutumin da ke aikin kuɓutarwa wanda ke 'yanto mutane daga bauta, ƙunci, ko waɗansu al'amura masu hatsari. Kalmar nan "kuɓutarwa" na nufin abin da ya faru a lokacin da wani ya yi 'yantarwa ko 'yantar da wasu daga ƙangin bauta, ko hatsarori.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya naɗa masu kuɓutarwa domin su kare Isra'ilawa ta wurin jagorancin su a cikin yaƙi gãba da waɗansu ƙungiyoyin mutane da ke kawo musu hari.
  • Waɗannan masu kuɓutarwar ana kiransu "alƙalai" littafin Tsohon Alƙawari na da Littafin Alƙalai a cikin tarihi a lokacin da alƙalai ke jagorancin Isra'ila
  • Hakanan ana ana kiran Allah "mai kuɓutarwa." A cikin dukkan tarihin Isra'ila ya kuɓutar da kuma 'yantar da su daga maƙiyansu.
  • Kalmar nan "miƙawa" yana da bambancin ma'ana da da miƙa wani ko cusa wani ga maƙiyi, kamar dai yadda Yahuza ya bada Yesu ga shugabannin Yahudawa.

Shawarwarin Fassara:

  • A cikin yanayin temakon mutane su tsira daga maƙiyansu, kalmar nan "kuɓuta" za a iya fassara ta da "cetowa"ko "Yantowa" ko "ceta."
  • A lokacin da kalmar nan a miƙa wani ga maƙiya, ko "badawa" ko "miƙawa" za'a iya fassara ta da "bada wani" ko "sallama wani," "sadaukarwa."
  • Kalmar nan "mai kuɓutarwa" za'a fassara ta da mai "'yantarwa" ko "mai cetowa"
  • A lokacin da aka mori mai kuɓutarwa na nufin alƙalai waɗanda suka shugabanci Isra'ila, suma za'a fassara ta da "gwafna" ko "alƙali" ko "shugaba."

(Hakanan duba: alƙali, ceta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 01:10
  • Ayyukan Manzanni 07:35
  • Galatiyawa 01:4
  • Littafin Alƙalai 10:12

kuka, kwala kuka

Ma'ana

Waɗannan maganganu "kuka" ko "kwala kuka" yawancin lokaci faɗin wani abu ne da ƙara da kuma hamzari. Wani zai "kwala kuka" don ciwo ko wahala ko fushi.

  • Wannan furci "kwala kuka" yana da ma'anar ihu, kira da ƙarfi, yawancin lokaci da nufin neman taimako.
  • Wannan magana kuma za a iya fasara ta haka, "yin mamaki da ƙara" ko "a nemi taimako da sauri," ya danganta ga yadda zai shiga cikin rubutu.
  • Magana kamar haka, "na yi kuka gare ka" za a iya fassara shi "na kira ka domin taimako" ko "na kira ka da sauri domin in roƙe ka taimako."

(Hakanan duba: kira, roƙo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayuba 27:09
  • Markus 05:5-6
  • Markus 06:48-50
  • Zabura 022:1-2

kumbura, cika da batsewa

Ma'ana

Wannan magana "kumbura" furci ne da aka misalta mutumin dake da girman kai ko fahariya.

  • Mutum mai kumburi yana da halin ganin yafi waɗansu.
  • Bulus ya koyar cewa sanin abubuwa da yawa ko istiharan addini zai iya sa kumburi ko girman kai.
  • Wasu yarurruka watakila suna da magana irin haka ko wani daban daya bayyana wannan ma'ana, kamar a ce "'yana da ƙaton kai."
  • Za a iya kuma fassarawa haka "mai girman kai ainun" ko "'wanda yake rena mutane" ko "hura hanci" ko "tunanin ya fi wasu."

(Hakanan duba: fahariya, girman kai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 04:6-7
  • 1 Korintiyawa 08:01
  • 2 Korintiyawa 12:6-7
  • Habakuk 02:04

kunya, kunyata, kunyata sosai, rashin kunya, rashin kunya sosai, jin kunya, rashin kunya, hassada yin rashin kunya

Ma'ana

Kalmar "kunya" na nufin jin kunar kunyatarwa da wani zai yi saboda wani abin wulakanci ko na rashin dai-dai da shi ko wani ya aikata.

  • Wani abu da yake na "kunyatarwa" shi ne " rashin dai-dai" ko "wulakantarwa".
  • Kalmar "jin kunya" tana nuna yadda mutum kan ji idan ya aikata wani abin kunya.
  • Kalmar "sa jin kunya" na nufin kãda mutane ko tona zunubansu domin suji kunyar kansu.
  • Annabi Ishaya ya ce duk waɗanda suke bautar gumaka za su kunyata.
  • Yahweh zai kunyata mutumin da bai tuba ba ta wurin fayyace zunubinsa ba, ya kuma sa shi ya wulaƙanta.

(Hakanan duba: allahn ƙarya, ƙasƙantar da kai, wulaƙantawa, Ishaya, zunubi, bauta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 03:15-17
  • 2 Sarakuna 02:17
  • 2 Sama'ila 13:13
  • Luka 20:11
  • Markus 08:38
  • Markus 12:4-5

kurciya, tantabara

Ma'ana

Kurciyoyi da tantabara waɗan ƙananan tsuntsaye ne masu fari-fari da kuma kala a jikkunansuwadda ta yi kama da fari a waɗansu lokutan.

  • A waɗansu harsunan suna da mabambantan suna ga kowacce su.
  • Ana amfani da kurciyoyi da tantabaru domin yin hadaya ga Allah, musamman ga mutanen da basu da ƙarfin sayen manyan dabba.
  • Kurciya ce ta kawo ganye n zaitun ga nuhu a sa'ad da ruwan tsufana ya tsanye.
  • Kurciyoyi a waɗansu lokutan suna alamta tsabta, rashin laifi,ko salama.
  • Idan a harshen da za'a yi fassara basu da sunan tantabara ko kurciya, za'a iya moron kalmar tsuntsuwa mai tsanwa-tsanwa, a ba ta fittaccen suna na tsuntsu.
  • Idan an yi amfani da sunan tantabara daq kurciya a wuri ɗaya to ya fi kyau a mori mabambantan sunaye ga waɗanan tsuntsaye, idan mai yiwuwa ne.

(Hakanan duba: zitun, mara laifi, tsaftatacce)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 08:09
  • Luka 02:22-24
  • Markus 01:10
  • Matiyu 03:16
  • Matiyu 21:12-14

kurkuku, ɗan kurkuku, 'yan kurkuku, ɗan yari

Ma'ana

Wannan magana "kurkuku" wuri ne da ake ajiye masu laifi a matsayin hukunci domin laifofinsu. ‌"Ɗan yari" mutum ne wanda aka sa shi a kurkuku.

  • Za a iya sa mutum a kurkuku domin jiran shari'a da hukunci.
  • Wannan magana "ɗauri a kurkuku" nada wannan ma'ana, wato, "an ajiye mutum a kurkuku" ko "an sa shi a gidan yari."
  • An saka annabawa da wasu bayin Allah a kurkuku koda shi ke basu yi wani laifi ba.

Shawarwarin Fassara:

  • Wani sunan "kurkuku" shi ne "gidan yari."
  • Za a iya fassara wannan haka "wuri mai duhu baƙi ƙirin" idan kurkukun wataƙila yana ƙarƙashin ƙasa ko ƙasa da fada ko wani gini.
  • Wannan magana "'yan yari" za ta iya zama kamammun mutanen da abokan gãba suka riƙe bada son ransu ba. Wata hanyar fassara wannan ma'ana shi ne ace "kamammu."
  • Wasu hanyoyi kuma na fassara "ɗauri a kurkuku" shi ne ace "an aje ɗan yari" ko "an aje shi a tsare" ko "an riƙe shi kamamme."

(Hakanan duba: kamamme)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 25:04
  • Afisawa 04:01
  • Luka 12:58
  • Luka 22:33-34
  • Markus 06:17
  • Matiyu 05:26
  • Matiyu 14:03
  • Matiyu 25:34-36

kursiyi, kursiyoyi, ɗorawa bisa kursiyi

Ma'ana

Kursiyi wata kujera ce da aka sassaƙa musamman inda mai mulki ke zama sa'ad da yake ɗaukar matakai akan muhimman al'amura kuma yake sauraren roƙe-roƙe daga mutanensa.

  • Kursiyi kuma alama ne na hukunci da iko da mai mulki ke da shi.
  • Kalmar "kursiyi" yawanci ana amfani da ita a misali da ma'anar mai mulki, mulkinsa, ko ikonsa.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, ana yawan bayyana Allah a matsayin sarki dake zaune akan kursiyi. Ana bayyana Yesu na zaune a bisa kursiyi a hannun dama na Allah Uba.
  • Yesu yace sama kursiyin Allah ne. Hanya ɗaya ta fassara wannan zata iya zama, "inda Allah yake mulki a matsayin sarki."

(Hakanan duba: hukunci, iko, sarki, mulki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Kolosiyawa 01:15-17
  • Farawa 41:40
  • Luka 01:32
  • Luka 22:30
  • Matiyu 05:34
  • Matiyu 19:28
  • Wahayin Yahaya 01:4-6

kuturu, kutare, kuturta, mai kuturta

Ma'ana

Kalmar "kuturta" anyi amfani da ita a Littafi Mai tsarki da manufar cututtukan fatar jiki masu yawa. "Kuturu" wani taliki ne mai kuturta. Kalmar "mai kuturta" na bayyana wani taliki ko fannin jiki wanda ya kamu da kuturta.

  • Wasu ire-iren kuturta na sanya fatar jiki ta canza kala da dabbare-dabbaren fari, kamar sa'ad da Miriyam da Na'aman suka kamu da kuturta.
  • A wannan zamanin, yawanci kuturta na sanya hannaye, ƙafafu, da wasu fannin jiki su lalace su nakasa.
  • Bisa ga umarnai da Allah ya bayar ga Isra'ilawa, sa'ad da wani taliki ya kamu da kuturta, za a ɗauke shi a matsayin "marar tsarki" kuma dole a keɓe shi daga sauran mutane domin kada su kamu da cutar.
  • A koyaushe "kuturu" zai riƙa kira "marar tsarki" saboda ya dokaci wasu don kada su kusance shi.
  • Yesu ya warƙar da kutare masu yawa, da wasu mutane da keda wasu ire-iren cututtuka.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "kuturta" a cikin Littafi Mai tsarki ana iya fassara ta a matsayin "cutar fãta" ko "mummunar cutar fãta."
  • Hanyoyin fassara "mai kuturta" suna iya haɗawa da "cike da kuturta" ko "wanda ya kamu da cutar fãtar jiki" ko "lulluɓe da ƙurajen fãta."

(Hakanan duba: Miriyam, Na'aman, tsabta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 05:13
  • Luka 17:12
  • Markus 01:40
  • Markus 14: 03
  • Matiyu 08:03
  • Matiyu 10:8-10
  • Matiyu 11:05

kwando, kwanduna, kwando cike

Ma'ana

Wannan kalma "kwando" wani daron zuba kaya ne da aka saƙa shi da wani abu.

  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, watakila ana saƙa kwanduna da tsire-tsire masu ƙarfi, kamar su itatuwan da aka ɓare rassansu ko ƙirare.
  • Za a iya dalaye kwando da katsi domin ya iya iyo.
  • Sa'ad da Musa yake jariri, mahaifiyarsa ta saƙa kwando ta shafe shi da katsi ta saka jaririn a ciki yana fito tsakanin ciyayin iwa a Kogin Nilu.
  • Wannan kalma da aka fassara "kwando" a wancan labari ita ce kalmar da aka fassara ta a matsayin "jirgi" ana nufin kwale-kwalen da Nuhu ya gina. Ma'anar fassararsu ɗaya ce a yadda aka yin amfani da su dukka biyun wato, "abin sa kaya a ciki dake iyo."

(Hakanan duba: akwati, Musa, Gokin Nilu, Nuhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 11:33
  • Ayyukan Manzanni 09:25
  • Amos 08:01
  • Yahaya 06:13-15
  • Littafin Alƙalai 06:19-20
  • Matiyu 14:20

kyarkeci, kyarketai, karnukan daji

Ma'ana

Kyarkeci dabba ce mai bantsoro, mai cin nama dai-dai da karen daji.

  • Kyarketai na kiwo tare kuma suna farautar ganimarsu da hikima da basira.
  • A Littafi Mai Tsarki, kalmar "kyarketai" an yi amfani da su a bayyana malaman ƙarya da annabawan ƙarya waɗanda suke hallakar da masu bãda gaskiya, waɗanda ake kwatantawa da tumaki. Koyarwar ƙarya na sã mutane su gaskanta da abubuwan da basu dãce ba da zai cutar da su.
  • Wannan kwatancin dalilin kuwa shi ne domin tumaki bãsu da wata kãriya ta musamman kyarketai na iya kai masu hãri su cinye su, domin raunannu ne basu kuma iya kãre kansa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma za a iya fassarawa haka "karen daji" ko "dabbar daji."
  • Wasu sunayen na karnukan daji zasu iya zama "diloli" ko "beyar."
  • Sa'ad da aka yi amfani da kalmar a misali da manufar mutane, za a iya fassarawa haka "miyagun mutane da suke yiwa mutane lahani kamar dabbobin dake kai hari ga tumaki."

(Hakanan duba: mugunta, annabawan ƙarya, tumaki, koyarwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 20:29
  • Ishaya 11:07
  • Yahaya 10:11-13
  • Luka 10:03
  • Matiyu 07:15
  • Zafaniya 03:03

ƙaho, ƙahonni, busa

Ma'ana

Ƙahonni zaunannun wani tattauran abu ne mai ƙarfi da ke yin girma akan da yawa daga cikin dabbobi da suka haɗa da raguna, awaki, da kishimi.

  • Ƙahon rago akan mayar da shu abin busar waƙe-waƙe da ake kira ƙahon rago" ko "Shofar," wadda akan busa ta a al'amari na musamman kamar a bikin addini.
  • Allah ya ce da Isra'ilawa su yi ƙaho su sashi ya dubi kusorwoyi huɗu na teburin tagulla na ƙona turare. Ko da yake ana kiran wannan "ƙahonni," amma ainahi ba ƙahonnin dabbobi ba ne.
  • Kalmar nan "ƙaho" ana moronta wani lokacin a ambaci wata roba da aka goge ta zama kamar ƙaho kuma ana moron ta domin riƙe ruwa ko mai. ‌‌Ƙahon mai ana amfani da shi domin ajiye man keɓew sarki kamar yadda Sama'ila ya yi da Dauda.
  • Wannan kalmar za'a fassara ta da ban da kaimar da ke nufin kakaki.
  • Kalmar nan "ƙaho" ana moron ta cikin salon magana domin alamta ƙarfi, da sarauta.

(Hakanan duba: iko, shanu, kishimi, awaki, hukuma, sarauta, tumaki, kakaki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 15:27-28
  • 1 Sarakuna 01:22:03
  • 2 Sama'ila 22:03
  • Irmiya 17:01
  • Zabura 022:21

ƙaho, ƙahonni, mabusa ƙaho, kakaki, kakakai, mabusa kakaki

Ma'ana

Kalmar "ƙaho" na nufin wani abu dake fitar da busa ko domin kiran mutane su tattaru tare domin wata sanarwa ko taro.

  • Shi dai ƙaho ko kakai ana yinsa daga ko dai ƙarfe, koɗin dabbar teku, ko ƙahon dabba.
  • Ƙahonni ko kakakai su dai busa su ake yi a kira mutane su zo su taru domin yaƙi, da kuma tarurrukan Isra'ilawa a fili.
  • Littafi Wahayin Yahaya ya yi bayanin kasancewar a lokutan ƙarshe inda mala'iku suka busa ƙahonni su bada alamar zubowar hasalar Allah bisa duniya.

(Hakanan duba: mala'ika, taro, duniya, ƙaho, Isra'ila, hasala)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 13:7-8
  • 2 Sarakuna 09:13
  • Fitowa 19:12-13
  • Ibraniyawa 12:19
  • Matiyu 06:02
  • Matiyu 24:31

ƙaiƙai

Ma'ana

‌Ƙaiƙai shi ne sheƙan nan busasshe dake rufe kwayar hatsi. ‌Ƙaiƙai bashi da kyau don abinci saboda haka mutane suke fitar da shi daga kwaya su jefar da shi.

  • Yawancin lokaci, akan raba ƙaiƙai da kwayar tsaba tawurin sheƙe shi a iska. Sai iska ta kwashe ƙaiƙan ƙwayar kuwa ta faɗi a ƙasa. Ana kiran wannan "'shiƙa."
  • A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma akan yi amfani da ita a misalta mugayen mutane da mugayen abubuwa marasa amfani.

(Hakanan duba: hatsi, alkama, shiƙa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 02:35
  • Ayuba 21:18
  • Luka 03:17
  • Matiyu 03:12

ƙanƙara, duwatsun ƙanƙara, ruwa da ƙanƙara

Ma'ana

Kalmar nan har kullum abin da take nufi shi ne curin ruwa da ke faɗowa daga sarari sama. Duk da yake ana a'boton kalmar a turance dai-dai da gaisuwa ga wani.

  • Wanan dutsen ƙanƙarar da ke saukowa daga sama yana kama da curin ƙwallo ko curin ƙanƙara.
  • Har kullum waɗanan duwatsun ba su cika girma ba, amma a waɗansu lokutan a kan sami waɗanda kan kaimita ashirin a faɗi sukan fi kuma nauyin kilogiram.
  • Littafin Wahayin Yahaya a cikin Sabon Alƙawari ya baiyana ire-iren duwatsun masu yawa da suka kai kilogiram 50 waɗanda Allah zai sa su faɗo bisa duniya a lokacin da ya hukunta mutane sabo da miyagun ayukansu a ƙarshen kwanaki.
  • Kalmar da ke nuna gaisuwa a harshen Ingilishi, ma'anarta ita ce "yi murna" kuma za'a iya fassara ta da "gaisuwa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Matiyu 27:29
  • Matiyu 28:8-10
  • Zabura 078:48
  • Zabura 148:8
  • Wahayin Yahaya 08:7

ƙara, kai ƙara, mai ƙara

Ma'ana

Wannan kalma "ƙara" da "kai ƙara" na nufin zargin wani domin ya yi abin da ba dai-dai ba. Mutumin da ya yi ƙarar wasu shi ne "mai ƙara."

  • ‌Ƙara marar gaskiya shi ne sa'ad da zargin da ake tuhumar wani da ita ba gaskiya bace, kamar yadda shugabannin Yahudawa suka yi ƙarar Yesu akan abin da bai yi ba.
  • A Sabon Alƙawari cikin littafin Wahayin Yahaya, ana kiran Shaiɗan "mai ƙarar 'yan'uwa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 19:40
  • Hosiya 04:04
  • Irmiya 02:9-11
  • Luka 06:6-8
  • Romawa 08:33

ƙarfi, ƙarfafuwa, ƙara ƙarfafa, ƙarfi

Ma'ana

Kalmar "ƙarfi" na nufin jiki, lamiri, ko ikon ruhaniya. A "ƙarfafa" wani ko wani abu na nufin a mai da wannan mutumin ko abin ya yi ƙarfi.

  • "Ƙarfi" na nufin ikon iya tsayar da wani abu da ƙarfi.
  • Mutum yana da "ƙarfin nufi" idan ya gujewa gwajin zunubi.
  • Ɗaya daga cikin marubucin Zabura ya kira Yahweh "ƙarfinsa" domin Allah ya taimake shi ya zama da ƙarfi.
  • Idan taswirar da ake gani kamar, bango ko gini ne ake, "ƙarfafawa," mutane na sake gina taswirar, da ƙarfafa shi da duwatsu ko tubali domin ya iya tsayawa daram.

Shawarwarin Fassara:

  • Gabaɗaya, kalmar "ƙarfafa" akan fassarta ta da "samar da ƙarfi" ko "yin ƙarfi sosai".
  • A fannin ruhaniya, kalmar "ƙarfafa 'yan'uwan ka." akan fassara shi da"ƙarfafa 'yan'uwanka" ko "taimakon 'yan'uwanka su jure."
  • Waɗannan misalan dake biye sun nuna ma'anar waɗannan kalmomin, da kuma yadda za a fasarta su, idan aka haɗa su da magana mai tsawo.
  • "Ka sa ƙarfi a cikina kamar ɗamara" na nufin sa ni in sami ƙarfi sosai, kamar ɗamarar da ta zagaye ƙugu na."
  • "Cikin natsuwa da yarda zai zama ƙarfinka" na nufin "yin abu cikin natsuwa da yarda da Allah zai sa ka ƙarfafa cikin ruhaniya."
  • "Zan sabunta ƙarfinsu" na nufin " za su kuma zama da ƙarfi kuma."
  • "Ta wurin ƙarfina da himmata nake aiki" na nufin "na iya yin dukkan wannan domin ina da ƙarfi da wayo."
  • "Ƙarfafa bango" na nufin "sake ƙarfafa bango " ko "sake gina bango."
  • "zan ƙarfafa ka" na nufin "zan sa ka zama da ƙarfi."
  • "A cikin Yahweh kaɗai akwai ceto da ƙarfi" na nufin " Yahweh ne kaɗai wanda zai cecemu ya ƙarfafa mu."
  • "Dutsen ƙarfin ka" na nufin "amintattun da suka sa ka sami ƙarfi."
  • "Ta wurin ƙarfin ceton hannunsa na dama" na nufin "ya kuɓutar da kai daga haɗari kamar wanda ya tallafe ka lafiya da hannayensa masu ƙarfi."
  • "Ƙaramin ƙarfi" na nufin "ba ƙarfi sosai" ko "kasala."
  • "Da dukkan ƙarfi na" na nufin "amfani da dukkan ƙarfi na" ko "da ƙarfi sosai da bakiɗaya."

(Hakanan duba: amintacce, jurewa, hannun dama, ceto)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 18:19-21
  • 2 Bitrus 02:11
  • Luka 10:27
  • Zabura 021:01

ƙarfin hali, yin ƙarfin hali

Ma'ana

Wannan kalma "ƙarfin hali" ma'anarta yin wani abu gabagaɗi mai wuya, mai bantsoro, da kuma hatsari.

  • Wannan kalma "ƙarfin hali" yana bayyana mutum wanda yake nuna ƙarfin hali, wanda yake yin abin dake dai dai ko yana jin tsoro ko an matsa masa ya bari.
  • Mutum yakan nuna ƙarfin hali sa'ad da ya fuskanci tashin hankali ko ciwon jiki tare da ƙarfi da naciya.
  • Wannan furci "kayi ƙarfin hali" ma'anar shi ne "kada kaji tsoro" ko " ina tabbatar maka cewa komai zai zama lafiya."
  • Lokacin da Yoshuwa yake shirin shiga cikin ƙasan nan mai hatsari ta Kan'ana, Musa ya karfafa shi ya "dage yayi ƙarfin hali."
  • Wannan kalma "ƙarfin hali" za a iya fasara ta haka, ko "mai ƙarfin hali" ko "marar tsoro" ko "mai gabagaɗi."

Bisa ga yadda za a yi amfani da shi a rubutu, idan an ce "kayi ƙarfin hali" za a iya fassara shi haka, "kayi ƙarfi cikin hankalinka" ko "ka ƙarfafa" ko "ka tsaya daram." A yi magana da ƙarfin hali" za a iya fassara shi haka, "yi magana gabagaɗi" ko "yi magana ba tare da tsoro ba ko "yi magana da ƙarfi."

(Hakanan duba: gabagaɗi, gargaɗi, tsoro, ƙarfi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 01:37-38
  • 2 Sarakuna 18:19-21
  • 1 Tarihi 17:25
  • Matiyu 09:20-22
  • 1 Korintiyawa 14:1-4
  • 2 Korintiyawa 07:13
  • Ayyukan Manzanni 05:12-13
  • Ayyukan Manzanni 16:40
  • Ibraniyawa 03:12-13
  • Ibraniyawa 13:5-6

ƙasƙantar kai, mafi ƙasƙanci, ƙasƙancewa

Ma'ana

Wannan kalma "ƙasƙantar kai" da "ƙasƙancewa" na nufin talauci ko ƙaramin matsayi. Idan mutum mai ƙasƙantar da kai ne ana nufi bashi da girman kai.

  • Yesu ya ƙasƙantar da kansa zuwa matsayin zama mutum har ya bauta wa wasu.
  • Haihuwarsa ta ƙasƙanci ce domin an haife shi a inda ake aje dabbobi, ba a fãda ba
  • Halin tawali'u shi ne akasin girman kai.
  • Ga yadda za a fassara halin "tawal'u" shi ne "ƙasƙancin kai" ko "ƙaramin matsayi" ko "marar mahimmanci."
  • Wannan magana "ƙasƙancin kai" za a fassara ta a ce "tawali'u" ko "ba mahimmanci."

(Hakanan duba: tawali'u, girman kai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 20:19
  • Ezekiyel 17:14
  • Luka 01:48-49
  • Romawa 12:16

ƙasƙantarwa, ƙasƙantacce, halin ƙasƙantarwa

Ma'ana

Kalmar "ƙasƙantarwa"na nufin a sa wani ya kunyata ko ya wulaƙantu. Akan fi yin wannan a cikin mutane. Yin wani abu ne domin kunyatar da wani. yin wannan shi ake kira "kunyatarwa."

  • Lokacin da Allah ke ƙasƙantar da wani wannan na nufin yana sa mutum mai halinfahariya ya gane cewa shi kasashe ne wannan zai sa ya yi nadamar fahariyarsa. wannan ya bambanta da tozartar da wani domin ya ciwatu.
  • A "kunyatar" shima za'a iya fassara shi da "kunyatarwa" ko a sa mutum ya kunyata" ko a "yabunta mutum."
  • Ya danganta ga wurin, hanyoyin yin fassarar halin ƙasƙantarwa sun haɗa da "Kunya" ko "rage daraja" ko "wulaƙantarwa."

(Hakanan duba: wulaƙantarwa, tawali'u, kunya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 21:14
  • Ezra 09:05
  • Littafin Masalai 25:7-8
  • Zabura 006:8-10
  • Zabura 123:3

ƙasƙantarwa, masu ƙasƙanci, ƙasƙantattu, marasa ƙasƙanci

Ma'ana

Kalmar nan "ƙasƙantarwa"tana nufin yin wani abu da ke na rashin girmamawa ga wani. Wanan zai iya jawowa mutumin kunya ko wulaƙanci.

  • Kalmar nan abu na rashin girma" na nuna aiki ne na kunya ga wani domin a ƙasƙantar da shi.
  • A waɗansu lokutan abubuwa na rashin girma na nufin a dubi abu a matsayin marar amfani ko muhimanci.
  • An umarci 'ya'ya da su yi biyayya da iyayensu. Sa'ad da yara suka yi rashin biyayya ga iyayensu, sun ƙasƙantar da su kenan. kuma suna yiwa iyayensu abin daba na girmamawa ba.
  • Isra'ilawa sun ƙasƙantar da Yahweh a lokacin da suka bautawa allolin ƙarya suka kuma yi rayuwa marar kyau.
  • Yahudawa sun ƙasƙantar da Yesu ta wurin cewa yana da aljanu.
  • Za'a iya fassara wanan da kalmar rashin "girmamawa" ko "rasa girma."
  • Kalmar "rashin girmamawa" za'a iya fassara ta da "rashin bada girma."
  • Ya danganta ga wurin, "rashin zama da girmamawa" shima za'a iya fassara shi "rashin girma" ko "abin kunya" ko "abin da bai cancata ba" ko "abu mara daraja."

(Hakanan duba: wulaƙanci, girma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 04 10
  • 1 Sama'ila 20:34
  • 2 Korintiyawa 06:8-10
  • Ezekiyel 22:07
  • Yahaya 08:48
  • Lebitikus 18:08

ƙato, ƙarti

Ma'ana

Kalmar nan "ƙato" har kullum tana nufin mutum wanda da tsayi da kuma ƙarfi.

  • Goliyat, Bafilistiyen soja wanda ya yi faɗa da Dauda an kira shi ƙato domin yana da tsayi da ƙiba da kuma ƙarfi.
  • Isra'ilawan da suka gewayo ƙasar Kan'ana suka ce mutanen da ke zama a can ƙarti ne.

(Hakanan duba: Kan'ana, Goliyat, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 06:4
  • Littafin Lissafi 13:32-33

ƙaya, sarƙaƙiyar ƙaya, ƙayayuwa, furen ƙaya, furannin ƙaya

Ma'ana

Sarƙaƙiyar ƙaya da furannin ƙaya dukka tsire-tsire ne ko 'yan itatuwa da suke da rassa ko furannin ƙaya. Waɗannan itatuwa basu haifar da 'ya'ya ko wani abin amfani.

  • "Ƙaya" wani abu ne mai tsini da ƙarfi dake fitowa a jikin reshe ko jikin itacen. "Sarƙaƙiyar ƙaya" wani irin ƙaramin itace ne ko tsiro wanda keda ƙayayuwa da yawa a rassansa.
  • "Furen ƙaya" itace ne dake da rassa masu ƙai-ƙai da ganyaye. Yawanci kalar furannin shunayya ne.
  • Itatuwan sarƙaƙiyar ƙaya da furen ƙaya suna ruɓanɓanya da sauri su kuma sa sauran itatuwa da shuke-shuke dake kusa da su su kasa yin girma. Wannan hoto ne na yadda zunubi ke hana wani taliki haifar da kyawawan 'ya'yan ruhaniya.
  • Kambin da aka yi da naɗaɗɗun rassan ƙaya aka ɗora bisa kan Yesu kafin a gicciye shi.
  • Idan mai yiwuwa ne, waɗannan kalmomi za a fassara su da sunayen itatuwa biyu daban ko sarƙaƙiyu da aka san su a yaren wurin.

(Hakanan duba: kambi, 'ya'yan itace, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 06:7-8
  • Maityu 13:07
  • Maityu 13:22
  • Littafin Lissafi 33:55

‌ƙazanta, ƙazantacce, ƙazantarwa

Ma'ana

Kalmar nan "ƙazanytata" tana ma'anar, a ɓata ko a ƙazantar da wuri mai tsarki ko wani abu mai tsarki ta hanyar da ba za'a yarda ayi amfani da shi a sujada ba.

  • An fi ayyana abin da ya ƙazantu ta wurin nuna rashin darajantawa a gare shi.
  • Misali sarakunan arna sun ƙazantar da tasa ta musamman daga haikalin Allah ta yadda suka more su domin shagli a wurarensu
  • An yi amfani da ƙasusuwan matattun mutane ta hannun maƙiya aka ƙazantar da bagadin Allah a cikin haikalin Allah.
  • Za'a iya fassnara wanan kalma a matsyin "ƙazantarwa"ko "ƙasƙantarwa" ko kuma "rashin tsarki" ko "marar girmamawa ƙazantacce" ko "mayar da shi "marar tsarki."

(Hakanan: duba: bagadi, ƙazanta, ƙasƙantarwa, abin ƙyama, tsaftatacce, haikali, tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzani 24:4-6
  • Ishaya 30:22
  • Zabura 074:7-8
  • Zabura 089:39

ƙazanta, mai ƙazanta, ƙazantacce, mai ƙazantarwa, zama ƙazantacce, sun ƙazantu, wanda aka ƙazantar, waɗanda aka ƙazantar

Ma'ana

Kalmar nan "ƙazanta" da "zama ƙazantacce" tana ma'anar zama lalatacce ko ƙazantacce. Wani abu zai iya zama ƙazantacce a zahirance, a ɗabi'ance, ko ta fannin addini.

  • Allah ya gargaɗi Isra'ilawa da kada su ƙazantar da kansu ta wurin ƙazantuwa ta wurin ci da kuma taɓa abin da ba shi da "tsarki" ko "haramtacce"
  • Akwai waɗansu abubuwa kamar gawa da cututtuka masu yaɗuwa da Allah ya aiyana su akan mara sa tsarki idan mutum ya taɓa su.
  • Allah ya dokaci Isra'ilawa da su guji zunubin zina. Wannan zai ƙazantar da su ya sa Allah ya ƙi karɓar su.
  • Akwai kuma waɗansu al'amura na jiki da ke ƙazantar da mutum na ɗan lokaci har kuma sai an bi ka'idodin addini kafin ya sake zama da tsarki.
  • A cikin Sabon Alkawari, Yesu ya koyar cewatunane tunane na zunubi da abuwabuwan da mutum ke yi su ke ƙazantar da mutum.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "ƙazanta" har ila yau za a iyan fassara ta akan abubuwan da "ƙazantarwa" ko ya sa mutum ya zama "ƙazantacce mara karɓuwa"
  • "Zama da ƙazantuwa" za'a iya fassara ta da zama da "rashin tsarki" ko ya zama marar karɓuwa ga Allah, ko duk abin da rashin "karɓuwa a addinance."

(Hakanan duba: tsafta, tsaftacewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 23:08
  • Fitowa 20:24-26
  • Farawa 34: 27
  • Farawa 49:04
  • Ishaya 43:27-28
  • Lebitikus 11:43-45
  • Markus 07:14-16
  • Matiyu 15:10

ƙazantar, ƙazantacce, ƙazantarwa

Ma'ana

Idan an ƙazantar da wani abu an gurɓanta shi ko an ɓata shi, ko a tozartar da wani abu mai tsarki.

  • ‌Ƙ‌azamin mutum shi ne wanda yake yin abubuwa marasa tsarki yana ƙasƙantar da Allah.
  • Wannan magana "ƙazantarwa" za a iya fassarawa haka, "a ɗauki abu ba tsarki" ko "a nuna rashin bangirma ga" ko "a yi watsi da."
  • Allah ya cewa Isra'ilawa sun "ƙazantar" da kansu da gumaku, ma'ana, mutanen sun kawo wa kansu "rashin tsarki" ko "ƙasƙanci" ta wurin wannan zunubi. Suna kuma aikata rashin girmama Allah.
  • Ya danganta ga nassi, za a iya fassara "ƙazantarwa" haka "rashin girmamawa" ko "babu tsoron Allah" ko "marar tsarki."

(Hakanan duba: ƙazantu, tsarki, tsabta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 02:16-18
  • Ezekiyel 20:09
  • Malakai 01:10-12
  • Matiyu 12:05
  • Littafin ‌Lissafi 18:30-32

ƙibiritu, mai ƙibiritu

Ma'ana

Ƙibiritu wani abu ne mai launin garin ɗorawa idan aka ƙona shi da wuta yakan zama ruwa.

  • Ƙibiritu na da tsananin wari kamar warin riɓaɓɓen kwai.
  • A Littafi Mai Tsarki ƙunar ƙibiritu alama ce ta hukuncin Allah akan waɗanda ba na Allah bada mutane masu tayarwa.
  • A zamanin Lot, Allah ya sauko da wuta da ƙibiritu akan mugun birnin Sodom da Gomora.
  • A waɗansu Littatafai masu tsarki na Turanci, ƙibiritu an danganta ta da "wutar dutse" wanda yake nufin "dutsan ƙonewa."

Shawarwarin Fassara:

  • Fassara mai yiwuwa ta wannan kalmar ta haɗa da "ruwan ɗorawar dutsen da yake ƙonewa" ko "ƙone ruwan ɗorawar dutse."

(Hakanan duba: Gomora, alƙali, Lot, tawaye, Sodom, nagari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fawara 19:24
  • Ishaya 34:09
  • Luka 17:29
  • Wahayin Yahaya 20:10

ƙidaya

Ma'ana

Wannan kalma "ƙidaya" ana magana ne akan ƙayadadden ƙidaya domin sanin yawan mutane a cikin al'umma ko mulki.

  • Tsohon Alƙawari ya rubuta lokatai da dama sa'ad da Allah ya umarta a ƙidaya mutanen Isra'ila, misali lokacin da Isra'ilawa suka fara barin Masar da kuma kafin su shiga Kan'ana.
  • Yawancin lokaci dalilin ƙirga mutane shi ne don a san mutane nawa ne yakamata su biya haraji.
  • Misali, a wani lokaci a cikin Fitowa aka ƙirga mazajen Isra'ila domin kowanne ɗayansu ya biya rabin shekel saboda lura da haikali.
  • Lokacin da Yesu yake ɗan jariri, gwamnatin Roma tayi ƙidaya domin ƙirga dukkan mutane waɗanda suke mazaunnan yankin mulkinsu, domin a buƙace su su biya haraji.

Shawarwarin Fassara

  • Wasu hanyoyin fassara wannan kalma zai haɗa da waɗannan "ƙidayar sunaye" ko "ɗaukar sunaye" ko "rubutawa."
  • Wannan furci "yin ƙidaya" za a iya fassara shi zuwa "shigar da sunayen mutane" ko "ɗiban mutane" ko "rubuta sunayen mutane."

(Hakanan duba: ƙasa, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 05:37
  • Fitowa 30:12
  • Fitowa 38:26
  • Luka 02:03
  • Littafin Lissafi 04:1-4

ƙofa, ƙofofi, madogaran ƙofa, mai tsaron ƙofa, masu tsaron ƙofa, daɓen ƙofa, hanyar shiga ƙofa, hanyoyin shiga ƙofa

Ma'ana

"Ƙofa" wani ƙyaure ne da ake sawa wanda ke liƙe da garu kohanyoyin shiga gari ko birni ko gidaje. "Madogaran ƙofofi" waɗansu katakai ne ko ƙarafa da akan sa domin kare ƙofa ko kulle ƙofa.

  • A kan buɗe ƙofar shiga birni domin abar mutane da dabbobi da jiragen ruwa su shiga da kuma fita daga birnin.
  • Domin bada kariya ga birni, garun birnin da ƙofofin sukan zama da kauri. Akan kulle da kuma buɗe ƙofofi da ƙarafa ko da katako domin hana sojoji maƙiya shiga birni
  • Ƙofar shiga birni wuri ne na labarai da kuma tattaruwar mutane. Hakanan wuri ni ne da ake gudanar da shari'a da kuma shari'a domin garun birni na da kauri sosai yana da wani abu da samar da inuwa mai sanyi domin samun kariya daga kariya daga zafin rana. Mazuna garin kan ji daɗin Zama domin gudanar da kasuwancin su har ma da zartar da hukunci kan waɗansu al'amura.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin, waɗansu hanyoyi da za'a fassara "ƙofa" ita ce "ƙyaure" wurin "shiga ko buɗe garu" ko "mashigi ko makari" ko "makari" ko "hanyar shiga"
  • Kalmar nan "makaran ƙofa" za'a iya fassara ta da "makullai na ƙofofi" ko kuma "wani makari na katako da ake moro domin rufe ƙofa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzani 09:24
  • Ayyukan Manzanni 10:18
  • Maimaitawar Shari'a 21:18-19
  • Farawa 19:1
  • Farawa 24:60
  • Matiyu 07:13

ƙoƙon kai

Ma'ana

Kalmar "ƙoƙon kai" na nufin ƙashin kan mutum ko dabba.

  • Wasu lokutan kalmar "ƙoƙon kai" na nufin "kai", kamar yadda yake a faɗar "aske kanka."
  • Kalmar "wurin ƙoƙon kai" wani suna ne kuma na Golgota,inda aka gicciye Yesu.
  • Akan iya fassara wannan da "kai" ko "ƙashin kai."

(Hakanan duba: gicciye, Golgota)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 09:35-37
  • Irmiya 02:16
  • Yahaya 19:17
  • Matiyu 27:32-34

ƙunci

Ma'ana

Wannan furci "wahala" yana nuna zafin ciwo da baƙinciki.

  • "Wahala" zata iya zama ta jiki ko ta damuwar lamiri ko baƙinciki.
  • Yawancin lokaci mutanen dake cikin zafin wahala za su nuna ta a fuska da kuma motsin jikinsu.
  • Misali, mutumin dake jin zafin ciwo ko wahala zai dinga cizon haƙoransa ko ya kwala ihu.
  • Kalman nan "wahala" za a iya fassara ta haka, "baƙincikin ruhu" ko "baƙinciki ƙwarai" ko "ciwo mai tsanani."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Irmiya 06:24
  • Irmiya 19:09
  • Ayuba 15:24
  • Luka 16:24
  • Zabura 116:3-4

ƙungiyar mutane, jinsin mutane, mutane

Ma'ana

Wannan magana "mutane" ko "ƙungiyar mutane" na nufin ƙungiyar mutane dake da yare ɗaya da al'adu iri ɗaya. Wannan magana "mutane" yawancin lokaci ana nufin taron mutane a wani wuri masamman ko a wani sha'ani.

  • Lokacin da Allah ya keɓe "wasu mutane" domin kansa, ma'ana ya zaɓi wasu mutane domin su zama nasa su kuma bauta masa.
  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, 'yan ƙungiyar mutane yawancin lokaci suna daga zuriya guda kuma suna zaune masamman wuri guda ko ƙasa guda.
  • Ya danganta bisa ga nassi, furci kamar haka, "mutanen ku" ma'anar zai iya zama "ƙungiyar mutanen ku" ko "iyalinku" ko "'yan'uwan ku."
  • Furcin nan "mutane" yawancin lokaci ana amfani da shi da nufin dukkan jinsin mutane dake cikin duniya. Wasu lokuta ana nufin musamman mutanen daba Isra'ilawa ba, ko waɗanda basa bauta wa Yahweh. A wasu juyin Littafi Mai Tsarki na Turanci akan yi amfani da wannan kalma "al'ummai."

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "ƙungiyar mutane" za a iya fassara ta da kalma ko furci mai ma'ana haka "ƙungiyar iyali mai girma" ko "iyali" ko "ƙungiyar asali."
  • Furci kamar haka "mutanena" za a iya fassara shi zuwa "yan'uwa na" ko "'yan'uwa Isra'ilawa" ko "iyalina" ko "mutanen jinsina," zai danganta dai bisa ga nassi.
  • Wannan furci "zan warwatsa ku cikin mutane" za a iya fassara shi haka "zan sa ku tafi ku zauna da jinsunan mutane daban-daban" ko "in sa ku rabu da junanku ku tafi wurare daban-daban a duniya."
  • Wannan magana "mutane" za a iya fassara ta haka "mutanen dake cikin duniya" ko "ƙungiyar mutane" zai danganta bisa da nassi.
  • Wannan magana "mutanen da" za a iya fassara shi haka, "mutanen dake zaune ciki" ko "zuriyar mutane daga" ko "iyalin wane" ya danganta ga yadda aka bi baya da sunan wuri ko na mutum.
  • "Dukkan mutanen duniya" za a iya fassara shi zuwa, "kowanne mutum mai zama a duniya" ko "kowanne mutum a duniya" ko "dukkan mutane."
  • Wannan magana "wasu mutane" za a iya fassara shi a ce, "ƙungiyar mutane" ko "waɗansu mutane" ko "mutanen gari ko wuri guda" ko "iyali guda na mutane."

(Hakanan duba: zuriya, al'umma, kabila, duniya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 08:51-53
  • 1 Sama'ila 08:07
  • Maimaitawar Shari'a 28:09
  • Farawa 49:16
  • Rut 01:16

ƙuri'a, jefa ƙuri'a

Ma'ana

"Ƙuri'a abu ne da aka yi masa lamba daga cikin sauran abubuwa masu kama da shi domin a yanke zaɓe. "Jefa ƙuri'a" ita ce a jefa wasu abubuwa da aka yi masu lambobi a ƙasa ko wani fili.

  • Yawancin lokaci ƙuri'o 'in ƙananan duwatsu ne ko fasassun kasake.
  • Wasu a al'adunsu sukan "ja" ko su "zare" ƙuri'ar ne idan sun yi amfani da tsinkaye. Wasu sukan riƙe tsinkayen domin kada wasu su ga tsayinsu. Kowanne mutum zai zare tsinke ɗaya wanda ya zari tsinke mafi tsawo (ko gajere) to, shi ne aka zaɓa.
  • Isra'ilawa sun yi amfani da jefa ƙuri'a domin su fayyace abin da Allah yake so su yi.
  • Kamar a zamanin Zakariya da Alisabatu, an yi amfani da ita a zaɓi firist da zai yi hidima ta musamman a haikali a ƙayyadadden lokaci.
  • Sojojin da suka gicciye Yesu suna kãɗa ƙuri'a domin su zaɓi wanda zai ɗauki alkyabbar Yesu.
  • Wannan magana "kãɗa ƙuri'a" za a iya fassara ta ace "jefa ƙuri'a" ko "jan ƙuri'a" ko "mulmula ƙuri'a." A dai tabbata fassarar "jefawa" bai yi ƙara kamar ƙuri'ar ana jefata ne can nesa ba.
  • Ya danganta ga nassi, wannan magana "ƙuri'a" za a kuma iya fassarata haka "dutsen da aka sa masa lamba" ko "kaskon tukunya" ko "tsinke" ko "ɗan haki."
  • Idan an yanke zaɓe ta wurin "ƙuri'a" za a iya fassarawa haka "ta wurin jan (jefa) ƙuri'a."

(Hakanan duba: Elisabet, firist, Zakariya, (Tsohon Al‌ƙawari), Zakariya (Sabon Al‌ƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yona 01;07
  • Luka 0:8-10
  • Luka 23:34
  • Markus 15:22
  • Matiyu 27:35-37
  • Zabura 022:18-19

ƙwarƙwara, ƙwarƙwarai

Ma'ana

‌Ƙwarƙwara mace ce wadda ta auri namijin da ya rigaya ya auri wata mata. Yawancin lokaci ƙwarƙwara ba matar aure bace bisa ga doka.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, yawancin lokaci ƙwarƙwarai bayin mataye ne.
  • Za a iya samun ƙwarƙwara idan ansaye ta, ko tawurin cin mutane a yaƙi, ko tawurin biyan bashi.
  • Ga sarki, yawan ƙwaraƙwarai alamar iko ne yawancin lokaci.
  • Sabon Alƙawari ya koyar cewa ajiye ƙwarƙwara ba nufin Allah bane.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 03:07
  • Farawa 22:24
  • Farawa 25:5-6
  • Farawa 35:21-22
  • Farawa 36:12
  • Littafin Alƙalai 19:1-2

ƙyama, abin da aka ƙyamata, aikin ƙyama

Ma'ana

Kalmar nan "ƙyama" tana nufin wani abu da za'a ƙi so a kuma ƙi shi. A ƙyamaci abu wannan na nufin a ƙi shi sosai.

  • A lokuta da yawa Littafi mai tsarki ya yi magana akan abubuwan banƙyama na mugunta. Wanan na nufin mu ƙi mugunta mu kuma guje ta.
  • Allah ya yi amfani da kalmar "aikinbanƙyama" domin baiyana miyagun ayuka na masu bautar allolin ƙarya.
  • Isra'ilawa an umarce su da su "ƙyamaci" halin zunubi, muguwar ɗabi'a na waɗanda ke kewaye da su ko kuma maƙwaftaka da su ke yi.
  • Allah ya kira dukkan wani nau'i na jima'i ba bisa ka'ida ba akan "aikin banƙyama".
  • Duba .sihiri da miƙa yara hadaya duk ayuka ne na "banƙyama" ga Allah.
  • Kalmar nan ƙyama za'a iya fassara ta da cewa "abu ne da aka ƙi sosai" ko kuma aka ɗauke shi "haramtacce na mugunta"
  • Kalmar nan "aikin banƙyama" za'a iya fassarar ta akan duk wani mummunan aikin mugunta" "wanda kan sa a ƙi mutum"
  • In an alaƙanta shi ga adalin mutum aikin ban ƙyama abin ƙi ne ga adalin mutum, abu ne da ya ke ƙi.
  • Allah ya faɗa wa Isra'ilawa da su "ƙyamaci" waɗansu ire-iren dabbobi waɗanda Allah ya aiyana a matsayin "mara sa tsarki" ba su dace da zama abinci ba, Za'a iya fassara wanan akan babbar "ƙiyayya" ko "abin da ba'a karɓa ba."

(Hakanan duba: tsafta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 43:32
  • Irmiya 07:30
  • Lebitikus 11:10
  • Luka 16:15
  • Wahayin Yahaya 17:3-5

labule

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "labule" wani yadi ne mai kauri, ga kuma nawi ana amfani da shi domin yin rumfar taruwa da kuma haikali.

  • An gina rumfar taruwa da ninki huɗu na labulai domin samansa da gefunansa. Waɗannan labulan da su aka zagaye shirayin rumfar taruwa suka zama katanga. An yi waɗannan labulai da "lilin" wani irin ƙyelle da aka yi daga ciyawar iwa.
  • Cikin dukkan su biyu da rumfar taruwa da haikali, wani yadin labule mai kauri na rataye tsakanin wuri mai tsarki da wuri mafi tsarki. Wannan shi ne labulen daya ya tsage da al'ajibi kashi biyu lokacin da Yesu ya mutu.

Shawarwarin Fassara:

  • Da shike labulanmu na zamani daban suke da labulan da aka yi amfani da su a Littafi Mai Tsarki, zai fi kyau a yi amfani da wata kalma daban ko a ƙara wasu maganganu da za su fassara ta da kyau.
  • Zai danganta ga yadda ake so a yi amfani da ita a cikin rubutu, hanyoyin da za a fassara wannan kalma zai haɗa da waɗannan, "labulen rufewa" ko "abin rufewa" ko "yadi mai kauri" ko "fatar dabba domin rufewa" ko "ƙyellen ratayewa."

(Hakanan duba: wuri mai tsarki, rumfar sujada, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 10:20
  • Lebitikus 04:17
  • Luka 23:45
  • Matiyu 27:51
  • Littafin Lissafi 04:05

lada, sakamako, biyan ladar aiki, cancanta, albashi

Ma'ana

Kalmar "lada" na manufar abin da mutum ya samu sabili da wani aikin da ya yi, ko mai kyau ko mugu. Bada "lada" ga wani na nufin bada abu ga wani abin da shi bai cancanta ba.

  • Lada na iya zama mai kyau ko nagari domin wannan mutum ya yi abu da kyau ko ya yi biyayya da Allah.
  • Wani lokacin lada kan zama bada daɗi ba da ya faru saboda mugun hali, kamar faɗin da ya ce "ladar mugaye." A wannan wuri lada na manufar muguwar lada da aka karɓa sabili da zunubansu.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, kalmar "lada" za a iya fassarawa haka "biya" ko "wani abin da aka cancanta" ko "horo."
  • A bada "lada" wani za a iya fassarawa ta haka "a biya" ko a "horar" ko "a bayar da abin da aka cancanta."
  • A tabbata cewa fassara wannan kalma ba biyan albashi bane. lada ko sakamako ba lallai game da neman kuɗi ba ne a matsayin fannin aiki.

(Hakanan duba: horar)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 32:06
  • Ishaya 40:10
  • Luka 06:35
  • Markus 09:40-41
  • Matiyu 05:11-12
  • Matiyu 06:3-4
  • Zabura 127:3-5
  • Wahayin Yahaya 11:18

lahani, lahanoni, marar lahani, cikas

Ma'ana

Wannan kalma "lahani" na nufin cikas a jiki ko nakasa a jikin dabba ko mutum. Zai kuma iya zama nakasa a cikin ruhaniya da kuma laifofi cikin mutane.

  • Domin wasu hadayu, Allah ya umarci Isra'ilawa su miƙa dabba marar lahani ko aibi.
  • Wannan hoton yadda Yesu Almasihu ya zama cikakken hadaya, marar zunubi.
  • Masu bada gaskiya da Almasihu an wanke su daga zunubansu da jininsa an mai she mu marasa lahani.
  • Hanyoyin fassara wannan kalma za su haɗa da waɗannan, "cikas" ko "nakasasshe" ko "zunubi," ya danganta bisa ga nassi.

(Hakanan duba: gaskatawa, tsabta, hadaya, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:19
  • 2 Bitrus 02:13
  • Maimaitawar Shari'a 15:19-21
  • Littafin Lissafi 06:13-15
  • Waƙar Suleman 04:07

laifi, mai laifi

Ma'ana

Wannan kalma "laifi" ma'anar, zunubi ne da ya haɗa da karya dokar ƙasa ko lardi. Wannan kalma "mai laifi" na nufin mutumin da ya karya doka.

  • Wasu irin laifufuka sune abubuwa kamar su kisan kai ko satan kayan wani.
  • Yawancin lokaci akan kama mai laifi a ajiye shi kamar ɗan kamu cikin kurkuku.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki wasu masu laifi suka gudu suna yawo barkatai domin su guje wa mutanen da suke so su cuce su sakamako laifin da suka yi.

(Hakanan duba: ɓarawo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 02:09
  • Hosiya 06:8-9
  • Ayuba 31:26-28
  • Luka 23:32
  • Matiyu 27:23-24

lalata, halaiya marar kyau, marar halaiya mai kyau, fasiƙanci

Ma'ana

Kalmar nan "lalata" tana nufin yin jima'i ba tare da yin aure ba a tsakanin mace da namiji. Wanan ya saɓawa shirin Allah. Littafi Mai Tsarki ya kira shi "fasiƙanci."

  • Kalmar nan tana nufin kowane irin nau'i na jima'i da ya saɓawa nufin Allah, har ma da luɗu da kallon hoyunan tsiraici.
  • Wani kuma irin nau'i na lalata shi ne zina wanan shi ne yin jima'i tsakanin wanda ya yi aure da kuma wata da matarsa ba ko kuma ba mijin ta ba.
  • Wani kuma irin nau'i na lalata shi ne "karuwanci" wanda ya haɗa da biyan kuɗi domin yin jima'i da wani.
  • Wanan kalmar ana moronta cikin salon magana domin a nuna rashin amincin Isra'ila ga Allah a lokacin da suka bautawa waɗansu alloli.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "lalata" za'a iya fassara ta da halaiya marar kyau kamar yadda aka fahimci kalmar.
  • Waɗansu hanyoyi da za'a iya fassara wanan kalmar sun haɗa da "yin jima'i a hanyar da bata dace ba" ko "yin jima'i da wanda ba miji ba ko kuma ba mata ba."
  • Za'a iya fassara kalmar a matsayin "zina"
  • A yin fassara ta salon magana ana iya barin kalmar yadda take tunda yake akwai kamanci na rashin aminci ga Allah da kuma rashin aminci cikin aure a fanin jima'i.

(Hakanan duba: zina, allolin ƙarya, karuwanci, aminci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 15:20
  • Ayyukan Manzanni 21:25-26
  • Kolosiyawa 3:5-8
  • Afisawa 05:3
  • Farawa 38:24-26
  • Hosiya 04:13-14
  • Matiyu 05:31-32
  • Matiyu 19:7-9

lalatacce, lalatarwa

Ma'ana

Wannan kalma "lalatacce" da l"alatarwa" wani yanayi ne da mutane suke zama ƙazamtattu, marasa tsarki ko mazambata.

  • Wannan kalma "lalatacce" ma'anarta "tanƙwararre" ko "karyayye" game da tsabtar rai.
  • Lalataccen mutum shi ne wanda ya juya daga gaskiya kuma yana yin abubuwan zamba dana lalata.
  • Lalatar da wani mutum shi ne a yaudari mutum nan yayi abubuwan zamba da ƙazamtattun ayuyyuka shashanci.

Shawarwarin Fassara:

  • A "lalatar" za a iya fassarashi zuwa, "iya rinjayar wani mutm yayi mugunta" ko "a iya sa wani mutum yayi lalata."
  • Za a iya fassara lalataccen mutum haka, "shi ne wanda yake rayyuwar lalata" ko " mai yin mugunta."
  • Wannan kalma za a iya fassarata da "marar kyau" ko "mazinaci" ko "mugunta.
  • Wannan kalma lalacewa za a iya fasara ta haka, "saba

yin mugunta" ko "zinace zinace."

(Hakanan duba: mugunta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 20:42-44
  • Galatiyawa 06:12
  • Farawa 06:12
  • Matiyu 12:33-35
  • Zabura 014:1

lanƙwame, lanƙwamammu, lanƙwamamme, yin lanƙwama

Ma'ana

Kalmar nan "lanƙwama" tana nufin a. ci abu ko a cinye abu ta cikin fushi.

  • Ana amfani da sallon magana a amfani da wanan kalma, Bulus ya gargaɗi masubi da kada su ci naman juna, ma'ana kada su hari juna ko kuma su kashe juna da kalmomin bakunansu, ko ayukansu. (Galatiyawa 5:15).
  • Hakanan cikin salon magana kalmar nan :cinye" ana amfani da ita a nuna hallakarwa ta baki ɗaya, kamar yadda ake maganar al'umma ta tassawa al'umma ko wuta ta cinye gine-gine da mutane.
  • Haka nan wanan kalmar za'a iya fassara ta a matsayin "abin da aka cinye baki ɗaya" ko aka "hallakar baki ɗaya."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 5:8
  • Amos 01:10
  • Fitowa 24:17
  • Ezekiyel 16:20
  • Luka 15:30
  • Matiyu 23:13-15
  • Zabura 21:09

lardi, larduna, gunduma

Ma'ana

Lardi wani yanki ne ko sashen wata al'umma ko mulki. Wannan magana "na lardin" ana nufin abin nan dake game da wannan lardin, misali "gwamnan lardi."

  • Ga misali, tsofuwar daular Fasiya an rarraba ta lardi lardi kamar su Mediya, Fasiya Siriya, da Masar.
  • A lokacin Sabon Alƙawari, an rarraba mulkin Roma cikin larduna kamar su Makidoniya, Asiya, Siriya,Yudiya, Samariya, Galili, da Galatiyawa.
  • Kowanne lardi nada mai ikon mulkinsa, wanda ke ƙarƙashin sarki ko mai mulkin sarautar baki ɗaya. Wannan mai mulki wani lokaci ana ce da shi "hakimin lardi" ko "gwamnan lardi."
  • Wannan magana "lardi" da "na lardin" za a iya fassara shi haka "yanki" da "na yankin."

(Hakanan duba: Asiya, Masar, Esta, Galatiya, Galili, Yudiya, Macidoniya, Medes, Roma, Samariya, Siriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 19:30
  • Daniyel 03:02
  • Daniyel 06:02
  • Littafin Mai Wa'azi 02:08

Littafin Rai

Ma'ana

Wannan furci "Littafin Rai" ana ambatar inda Allah ya rubuta sunayen dukkan waɗanda ya fansa ya kuma basu rai madawwami.

  • Wahayin Yahaya ya ambaci wannan littafi ya ce "Littafin ‌Ɗan Rago na Rai." Za a iya fassara shi haka "littafin rai na Yesu, ‌Ɗan Ragon Allah." Hadayar Yesu akan gicciye ya biya hakin zunuban mutane domin mu sami rai madawwami ta wurin bangaskiya a cikinsa.
  • Wannan kalma "littafi" zai iya zama da ma'ana haka "naɗaɗɗen littafi" ko "wasiƙa" ko "rubutu" ko ƙaiyadaddar takarda," Zai iya yiwuwa hakanan ko a misalce.

(Hakanan duba: madawwami, ɗan rago, rai, hadaya, naɗaɗɗen littafi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Filibiyawa 04:03
  • Zabura 069:28-29
  • Wahayin Yahaya 03:5-6
  • Wahayin Yahaya 20:11-12

Liyafa

Ma'ana

Liyafa babban sha'anin abinci ne, abinci ne da aka saba ci amma yawancin lokaci abincin ya kan zama iri-iri.

  • A zamanin dã, sarakuna suke liyafa domin su marabci 'yan siyasa shugabannai da wasu manyan bãƙi.
  • Za a iya fasara shi haka "wadataccen abinci" ko "biki mai muhimmanci ko "abinci iri-iri."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 05:10
  • Ishaya 05:11-12
  • Irmiya 16:08
  • Luka 05:29-32
  • Waƙar Suleman 02:3-4

lokaci tsaro (a cikin Littafi Mai Tsarki)

Ma'ana

A cikin lokaci irin na Littafi Mai Tsarki, "tsaro" wani lokaci ne da dare sa'ad da mutum mai tsaro ko mai tsaron birni zai kasance kan aikinsa yana dubawa ko akwai hari daga maƙiyi.

  • A Tsohon Alƙawari, Isra'ilawa suna da lokutan tsaro uku da ake kira "farawa" (faɗuwar rana zuwa ƙarfe 10 na yamma), "tsakiya" (karfe10 na dare zuwa ƙarfe 2 na safe), da "safe" (ƙarfe 2 na safe zuwa hantsi ).
  • A Sabon Alƙawari, Yahudawa sun bi tsarin Romawa dake da lokacin tsaro huɗu, a sauƙaƙe "na farko" (daga faɗuwar rana zuwa ƙarfe 9 na dare), "na biyu" (ƙarfe 9 na dare zuwa tsakiyar dare ƙarfe 12), "na uku" (tsakiyar dare ƙarfe 12 zuwa ƙarfe 3 na dare), da "na huɗu" (ƙarfe 3 na dare zuwa asubahi).

(Hakanan duba: zaman tsaro)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 12:37-38
  • Markus 06:48-50
  • Matiyu 14:25-27
  • Zabura 090:3-4

lokaci, kan lokaci, lokuta, kafin lokaci, rana

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar "lokaci" anyi yawan amfani da ita a matsayin misali dake nufin wani ainihin zamani ko lokaci sa'ad da wasu al'amura suka faru. Tana da ma'ana kusan ɗaya da "shekara" ko "lokacin tarihi" ko "zamani."

  • A cikin Daniyel duk da Wahayin Yahaya maganar "lokacin" babban ƙalubale ko tsanani wanda zai zo bisa duniya.
  • A cikin faɗar "lokaci, lokuta, da rabin lokaci" kalmar "lokaci" na ma'anar "shekara." Wannan faɗar na nufin lokaci shekaru uku da rabi a lokacin babban tsanani a ƙarshen wannan zamanin.
  • "Lokaci" na iya zama "zarafi ko karo" a faɗar kamar haka "kokaci na uku." Faɗar "lokuta da yawa" zai iya zama "zarafi ko karo."
  • A zama "kan lokaci" na ma'anar a iso lokacin da ake zato, babu latti.
  • Ya danganta da nassin, kalmar "lokaci" za a iya fassarawa haka, "zamani" ko "lokacin sa'a" ko "lokacin" ko "faruwa."
  • Faɗar "lokuta da zamanai" faɗar misali ne wanda ke manufar abu ɗaya aka maimaita sau biyu. Wannan shima za a fassara haka "wasu abubuwa na faruwa a wani lokacin sa'o'i."

(Hakanan duba; shekara, tsanani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 01:07
  • Daniyel 12:1-2
  • Markus 11:11
  • Matiyu 08:29
  • Zabura 068:28-29
  • Wahayin Yahaya 14:15

maɓulɓula, maɓulɓulai, mafita, wuraren fita, ƙorama, ƙoramu

Ma'ana

Kalmar nan "maɓulɓula" da "ƙorama" har kullum tana nufin wurin da ruwa mai yawa ke fitowa ne daga ƙasa wanda kuma ba mutum ne ya haƙa ba.

  • Waɗanan kalmomin kuma ana moron su cikin salon magana a cikin Littafi Mai Tsarki domin ambaton albarkun Allah da ke fitowa zuwa wani abu wanda kan Tsarkake ya kuma tsaftace.
  • A kwanakin yau, maɓulɓula kusan takan zama abin da mutum ya yi ne wanda akan sa wani abu da ruwa zai dinga zubowa daga cikin sa, kamar maɓuiɓular ruwan sha,. A tabbatar cewa fassarar wanan kalma tana nufin maɓulɓula ce da Allah ya yi.
  • Kwatanta fassarar wanan kalma da yadda ake fassarar "ambaliya."

(Hakanan duba: ambaliya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 02:17
  • Farawa 07:11
  • Farawa 08:2
  • Farawa 24:13
  • Farawa 24:42
  • Yakubu 03:11

maciji, macizai, macijin kaikai

Ma'ana

Waɗannan dukka na nufin irin halitta mai tsawo da take rarrafe, tana da ƙaramin jiki da babba suna da haƙoran fiƙa, suna kuma tafiya a kwance suna jan ciki a ƙasa. Kalmar "Maciji" akan ce babban maciji, "gansheƙa" kuma wani irin maciji ne mai dafin gaske idan ya yi tsartuwa.

  • Wannan dabba anyi amfani da shi wajen nuna misalin mutumin da yake mugu, masamman wanda yake cike da mugunta.
  • Yesu ya kira shugabannin addini "'ya'yan gansheƙa" domin suna ɗauke da siffar ibada amma suna saɓa mata, suna kuma yiwa mutane rashin adalci.
  • A gonar Iden, shaiɗan ya ɗauki siffar maciji lokacin da ya yi magana da Hauwa ya jarrabce ta da ta yiwa Yahweh rashin biyyaya.
  • Bayan da macijin ya gama jarrabtar Hauwa ta yi zunubi, kuma Hauwa da mijinta duka suka yi zunubi, Yahweh ya la'anci macijin, ya ce daga yau, dukkan maciji zai ja ciki a ƙasa, wannan na nuna cewa kafin wannan lokacin suna tafiya da kafafu ne.

(Hakanan duba: la'ana, yaudara, rashin biyayya, Iden, mugunta, 'ya'ya, ganima, Shaiɗan, zunubi, gwaji)

Wuraren da ake samunsu a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 03:03
  • Farawa 03:4-6
  • Farawa 03:12-13
  • Markus 16:17-18
  • Matiyu 03:07
  • Matiyu 23:33

madogaran ƙofa

Ma'ana

Madogaran ƙofa wani daɓe ne da ake yi a bangon ƙofa da kuma gefen ƙofa wadda ta ke saman ƙofa tana ba ta kariya.

  • Gabanin Allah ya temaki Isra'ilawa su kuɓuta daga Masar ya bada ummarni gare su da su yanka ɗan rago su kuma sa jininsa a madogaran ƙofofinsu.
  • A cikin Tsohon Alƙawari idan bawa na son zama bawan mai gidansa na muddin ransa zai sa kunnensa a madogaran ƙofar ubangijinsa a kuma sa guduma a kafe kunnensa kowanne madagari na ƙofa.
  • Za'a iya fassara wanan da "madogaran katako da aka yi a kowanne gefe na ƙofa" ko kuma a gefen madogarin ƙofar.

(Hakanan duba: Masar, Ƙetarewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 06:31-32
  • Maimaitawar Shari'a 11:20
  • Fitowa 12 :07
  • Ishaya 57:7-8

mafaka, ɗan gudun hijira, 'yan gudun hijira, mahalli, mahallai,

Ma'ana

Kalmar "mafaka" na manufar wuri ne ko wani yanayi na tsaro da kariya. "Ɗan gudun hijira" wani ne dake neman wuri mai tsaro. "Mahalli" wuri ne da ake iya ɓoye wa daga wani yanayi ko hatsari.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah shi ne mafaka inda mutanensa na iya gudu su ɓuya, a kãresu, a kuma kula da su.
  • "Birnin mafaka" ɗaya daga cikin birane masu yawa ne a Tsohon Alƙawari inda idan wani ya kashe mutum cikin kuskure yana iya gudu can domin ɓuya daga mutanen da ke iya kai masa hari neman ramuwa.
  • "Mahalli" wuri ne kamar gini ko da ake iya tanadin kariya ga mutum ko dabba.
  • Wani lokacin "mahalli" na nufin "kariya," kamar yadda Lot ya ce da cewa baƙinsa na "ƙarƙashin mahalli" na rufinsa. Yana cewa su zauna lafiya gare shi domin nawayarsu na bisansa kuma zai kare su kamar 'yan gidansa.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "mafaka" za a iya fassarawa haka "wurin tsaro" ko "wurin kariya."
  • "'yan gudun hijira" mutane ne waɗanda suka bar gidansu domin su tsere daga yanayin hatsari, ana kuma iya fassarawa haka "bãre," "mutane marasa gida," ko "'yan talala."
  • Ya danganta ga nassin, "mafaka" za a iya fassarawa haka "wani abin dake yin kariya" ko "kariya" ko "wurin kariya."
  • Idan ana nufin gini a zahiri, "mafaka" za a iya kuma fassarawa haka "tsararren gini" ko "gidan tsaro."
  • Faɗar "cikin tsararren mahalli" za a iya fassarawa haka "cikin wurin tsaro" ko "cikin wuri da zai yi kariya."
  • A "samu mahalli" ko "ɗaukar mahalli" ko a "ɗaukar mafaka" za a iya fassarawa haka "samunwurin tsaro" ko a "sa wani wurin kariya."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 22:3-4
  • Maimaitawar Shari'a 32:37-38
  • Ishaya 23:14
  • Irmiya 16:19
  • Littafin Lissafi 35:24-25
  • Zabura 046:01
  • Zabura 028:08

mafarki

Ma'ana

Mafarki wani abu ne mutane ke gani ko ji a cikin ransu a lokacin da suke barci.

  • Mafarki yakan zama kamar abu ne zahiri ke faruwa, amma ba haka ba ne
  • A waɗansu lokuta Allah kan sa mutane su yi mafarki domin su koyi wani ab u game da shi. Haka nan zai iya magana da mutane da mutane kai tsaye a cikin mafarkinsu.
  • A cikin Bebil, Allah ya bada waɗansu mafarkai na musamman ga waɗansu mutane domin ya ba su saƙo, a mafi yawan lokuta akan abin da zai faru anan gaba.
  • Mafarki ya bambanta da wahayi. Mafarki kan faru ne a sa'ad da mutum ke barci, amma wahayi mutum kan ganshi ne a lokacin da mutum ke tsaye.

(Hakanan duba: wahayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:16-17
  • Daniyel 01:17-18
  • Daniyel 02:01
  • Farawa 37:06
  • Farawa 40:4-5
  • Matiyu 02:13
  • Matiyu 02 :19-21

magabci, magabta, maƙiyi, maƙiya

Ma'ana

"Magabci' za a iya cewa mutum ne ko ƙungiya ce dake gãba da wani mutum ko ƙin wani abu. Kalmar nan "maƙiyi" ita ma ma'anarta kusan ɗaya take da ta farko.

  • Magabci zai iya zama mutum wanda yake ƙoƙarin kushe ka ko ya cutar da kai.
  • Wata al'umma za a iya ce da ita "magabta sa'ad da ta yaƙi wata al'umma.

A littafi Mai Tsarki, ana ce da shaiɗan "magabci" da kuma "maƙiyi,"

  • Za a iya juya "magabci" ya zama "mai tsayayya da" ko "maƙiyi," wannan na nuna mummunar gãba.

(Hakanan duba: Shaiɗan)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 05:14
  • Ishaya 09:11
  • Littafin Makoki 04:12
  • Luka 12:59
  • Matiyu 13:25

magãji, magãda

Ma'ana

"Magãji" mutum ne wanda bisa ga doka ya karɓi mallaka ko kuɗi na wani mutum da ya mutu.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, wanda ya fi samun gãdo shi ne ɗan fari, wanda ke karɓar mafi yawa daga cikin mallaka da kuma kuɗin mahaifinsa.
  • Hakanan Littafi Mai Tsarki ya mori "magãji" ta hanyar salon magana ya ambaci mutum wanda a matsayinsa na krista ya karɓi moriya ta ruhaniya daga Allah, mahaifinsa na ruhaniya.
  • A matsayin 'ya'yan Allah, an kira krista su zama abokai gãdo tare da Yesu Kristi. Za'a iya fassara wanan da "abokan gãdo" ko masu taraiya cikn "gãdo" ko masu taraiya cikin gãdo taare da."
  • Hakanan Kalmar nan "mãgaji za'a iya fassara ta da nufin "mutum wanda ya karbi wani kaso" ko dukwani irin batu da aka yi a cikin harshen da aka mora wanda ke nuna ma'anar cewa wani ya karɓi wani kaso na mallaka bayan iyaye ko wani dangi ya mutu.

(Hakanan duba: ɗan fari, gãji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 04:1-2
  • Galatiyawa 04:7
  • Farawa 15 1
  • Farawa 21:10-11
  • Luka 20:14
  • Markus 12:7
  • Matiyu 21:38-39

mahaifa, mahaifai

Ma'ana

Kalmar "mahaifa" wuri ne inda jariri ke girma a cikin cikin mahaifiyarsa.

  • Wannan tsohuwar kalma ce da ake amfani da ita ba kai tsaye ba.
  • Sunan mahaifa na zamani shi ne "wurin zaman jariri a ciki."
  • Wasu harsuna na amfani da kalmar "ciki" da nufin mahaifiyar mace ko wurin zaman jariri.
  • Ayi amfani da kalmar dake ma'anar haka a harshen da ake aikin fassarawar wanda aka fi sani sosai, a zahiri kuma karɓaɓɓe.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 25:23
  • Farawa 25:24-26
  • Farawa 38:27-28
  • Farawa 49:25
  • Luka 02:21
  • Luka 11:27
  • Luka 23:29
  • Matiyu 19:12

maharbi, maharba

Ma'ana

Wannan kalma "maharbi" na nufin ƙwararren mutum mai iya harbi da baka da kibiya kayan yaƙi.

  • A Littafi Mai Tsarki, maharbi yawancin lokaci mai yaƙi ne wanda yake amfani da baka da kibiya ya yi faɗa cikin rundunar mayaƙa.
  • Maharba muhimmiyar ƙungiya ce a cikin rundunar Asiriyawa.
  • Wasu harsuna mai yiwuwa suna da wani suna domin wannan kamar haka, "mutumin baka."

(Hakanan duba: Asiriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 31:1-3
  • 2 Tarihi 35:23-24
  • Farawa 21:20
  • Ishaya 21:16-17
  • Ayuba 16:13
  • Littafin Misalai 26:9-10

mai

Ma'ana

Mai wani abu ne mai kauri, ruwa-ruwa da za a iya samunsa daga wasu tsire-tsire. A lokacin Littafi Mai Tsarki

  • Ana amfani da man zaitun a yi girki, keɓewa, hadaya, fitilu da kuma magani.
  • A zamanin dã, man zaitun yana da tsada, kuma idan kana da man za a ɗauke ka wani mai arziki ne.
  • A tabbatar fassarar wannan kalmar an yi amfani da mai da ake girki da shi, ba na mota ba. Wasu yarurruka suna da kalmomi daban-daban domin irin waɗannan mai.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 01:21
  • Fitowa 29:02
  • Lebitikus 05:11
  • Lebitikus 08:1-3
  • Markus 06:12-13
  • Matiyu 25:7-9

mai ba'a, masu ba'a, ba'a, maganganun ba'a, dariyar ba'a

Ma'ana

Wannan kalma "ba'a," dariyar ba'a, da maganganun wofintarwa duk manufarsu ɗaya a mai da wani mutum abin dariya musamman a cikin mugunta.

  • Yin ba'a ya ƙunshi kwaikwayon yadda mutum ke magana ko motsawa da nufin kunyatarwa ko nuna reni.
  • Sojojin Romawa suka yiwa Yesu ba'a da reni lokacin da suka sa masa al'kyabba suka yi kamar suna girmama shi kamar sarki.
  • Wata ƙungiyar mutane matasa suka yiwa annabi Elisha ba'a da dariya da suka kira shi da wani suna, suka yi dariyar kansa mai saiƙo.
  • Wannan kalma "dariyar ba'a" ƙarin bayaninsa shi ne yin ba'a ga wani abin da aka ga ba ya gaskantuwa ko mahimmanci.
  • Mai ba'a shi ne mutumin da yake ba'a da reni kullayomi.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki.

  • 2 Bitrus 03:04
  • Ayyukan Manzanni 02:12-13
  • Galatiyawa 06:6-8
  • Farawa 39:13-15
  • Luka 22:63-65
  • Markus 10:34
  • Matiyu 09:23-24
  • Matiyu 20:19
  • Matiyu 27:29

mai bada gaskiya

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki "mai bada gaskiya" ana nufin mutum ne da ya bada gaskiya da Yesu yana kuma dogara gareshi a matsayin mai cetonsa.

  • Wannan furci "mai bada gaskiya" ma'anar shi ne "mutumin da ya bada gaskiya."
  • Wannan suna "Krista" daga bisani ya zo ya zama sunan masu bada gaskiya domin ya nuna sun gaskata da Kristi kuma suna biyayya da koyarwarsa.

Shawarwarin Fassara

  • Wasu juyin zasu fi son su ce "mai gaskatawa da Yesu" ko "mai gaskata Kristi."
  • Wannan furci za a iya fassarata da kalma ko furci dake da ma'ana haka, "mutumin da ya dogara ga Yesu" ko "wani wanda ya san Yesu yana kuma rayuwa dominsa."
  • Wasu hanyoyin fassara "mai bada gaskiya" shi ne "mai bin Yesu" ko "mutumin da ya san Yesu yana kuma yi masa biyayya."
  • Furcin nan "mai bada gaskiya" ana amfani da ita kullum domin kowanne mai gaskatawa da Kristi, sa'annan "almajiri" da "manzo" ana amfani dasu domin mutane musamman da suka san Yesu lokacin da yake a raye. ya fi kyau a fassara waɗannan maganganun ta hanyoyi dabam dabam, domin a bambanta su.

mai bin, masu bin, bin, zama ƙasan, na ƙasa, a ƙasan

Ma'ana

Mutum na "bin" wani mutumin idan mutum na biyun yana mulki bisan na faskon. Zama "ƙasan" shi ne "yin biyayya" ko "a miƙa kai ga ikon wani."

  • Kalmar "zama ƙasan" na nufin sa mutane su zama suna ƙarƙashin ikon shugaba ko mai mulki.
  • "Sa wani akan wani abu" na nufin sa wannan mutumin ya ji ba daɗi, kamar hukunci.
  • Waɗansu lokutan kalmar "bin" kan yi amfani da nufin abin mai da hankali akan wani abu, kamar a cikin, "za ka zama abin tsokana."
  • Kalmar "zama ƙasan" na nufin abu ɗaya da " miƙa kai ga" ko "bada kai ga."

(Hakanan duba: bãda)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 02:14-16
  • 1 Sarakuna 04:06
  • 1 Bitrus 02:18-20
  • Ibraniyawa 02:05
  • Littafin Misalai 12:23-24

mai girbi, masu girbi

Ma'ana

Kalmar nan "girbi" tana tara 'ya'yan itacen da suka nuna ko kuma hatsi waɗanda suka yi girma.

  • Lokacin girbi kusan kullum yakan zo ne a ƙarshen yanayi.
  • Isra'ilawa kan yi "Bikin Girbi" ko "Bikin Tattara amfanin" gona zuwa gida. Allah ya umarce su da su miƙa nunar fari amfaninsu a matsayin hadaya a gare shi.
  • A cikin salon, kalmar "girbi" zata iya zama mutanen da ke zuwa domin yin imani da Yesu, ko kuma ta baiyana girman ruhaniya na mutum.
  • Masaniya game da girbi na abinci na ruhaniya ya yi dai-dai da salon maganar da ke nuna kamannin 'ya'ya a matsayin halaye masu iganci.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya fi kyau a fassara wanan kalmar da kalmar da aka fi sani sosai a cikin harshen domin ta nuna girbi na hatsi.
  • Abubuwa na girbar za'a iya fassara su a matsayin "lokaci na tattara kayan girbi" ko "lokacin tattara amfani" ko "roron amfani.
  • Kalmar aikatau ta "girbi" za'a iya fassara ta da, "tara" ko "roro" ko "tattara."

(Hakanan duba: nunar fari, biki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 09:9-11
  • 2 Sama'ila 21:7-9
  • Galatiyawa 06:9-10
  • Ishaya 17:11
  • Yakubu 05:7-8
  • Lebitikus 19:9
  • Matiyu 09:38
  • Rut 01:22

mai martaba ko masani, masu martaba ko masana, mutumin martaba, masanan mutane, muƙaddashin sarauta,

Ma'ana

Wannan kalma "masani" na nufin wani abin da ya yi fice kuma amintacce. "Masanin mutum" shi ne wanda yake cikin ƙungiyar siyasa ko muhimman mutanen gari. Mutum mai "martabar haihuwa" shi ne wanda aka haife shi da "mai martaba."

  • "Masani ko mai martaba" yawancin lokaci shugaba ne a ƙasa, baran sarki ne na kurkusa.
  • Wannan magana *masani ko mai martaba" za a iya fassarawa haka, "muƙaddashin sarki" ko "shugaban hukuma."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 23:20-21
  • Daniyel 04:36
  • Littafin Mai Wa'azi 10:17
  • Luke 19:12
  • Zabura 016:1-3

mai shayarwa

Ma'ana

  • A lokacin Tsohon Alƙawari, "mai shayarwa baran sarki ne wanda shi ke hidimar kawo wa sarki ruwan inabi a moɗarsa, yawancin lokaci sai ya ɗanɗana da fari ya tabbatar ba a sa dafi ba.
  • Ma'anar wannan a sauƙaƙe shi ne "mai kawo moɗar sha" ko "wani mutum wanda yake kawo moɗa."
  • Mai shayarwa an san shi mutum ne da za a iya dogara a gareshi mai aminci ne ga sarki.
  • Saboda matsayinsa na aminci, mai shayarwa yana da hannu cikin yanke shari'ar da mai mulki ke yi.
  • Nehemiya mai shayarwa ne na Sarki Artashate na Fasha a lokacin da wasu Isra'ilawa suke bautar talala a Babila.

(Hakanan duba: Atazazas, Babila, bawa, Fasiya, Fir'auna)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 10:3-5
  • Nehemiya 01:11

mai tawali'u, tawali'u

Ma'ana

Wannan furci "mai tawali'u" yana magana akan mutum mai hankali, mai bada kai, mai jure rashin adalci.Tawali'u iya jimiri ne koda tsawatawa da tilastawa sun zama dai-dai.

  • Yawancin lokaci akan fassara tawali'u da rashin girman kai.
  • wannan furci za a iya fassara shi da "kamun kai" ko "marar garaje" ko "mai sassanyar zuciya"
  • Wannan kalmar "tawali'u" za a iya fassarata a ce "mai hankali" ko "marar girman kai."

(Hakanan duba: marar girman kai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 03:15-17
  • 2 Korantiyawa 10:1-2
  • 2 Timoti 02:25
  • Matiyu 05:05
  • Matiyu 11:29
  • Zabura 37:11

mai yinaikin mugunta, masu yin aikin mugunta, yin aikin mugunta

Ma'ana

Kalmar nan "mai aikin mugunta" tana magana ne kai tsaye akan mutane da ke aikataabu na zunubi da mugayen abubuwa.

  • Zata iya zama kalma ta bai ɗaya ga mutanen da ba su yin biyayya ga Allah.
  • Wanan kuma za'a iya fassara ta kalmar "mugunta" ko "mugu,' da kalmar "yin" "ƙirƙiro" ko "sa" wani abu ya faru.

(Hakanan duba: mugunta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 02:13-17
  • Ishaya 09:16-17
  • Luka 13:25-27
  • Malakai 03:13-15
  • Matiyu 07:21-23

maitayarwa, masu tayarwa, tayas, tayarwa, halin tayarwa, na tayarwa

Ma'ana

kalmar tayarwa na ma'anar ƙin sadaukar da kai ga ikon wani. Mutum mai tayarwa na rashin biyayya da kuma aikata abubuwan mugunta. Irin wannan mutum ana ce da shi "mai tayarwa."

  • Mutum na tayarwa yayin da yake aikata abin da hukumar dake a bisan shi ta hana shi ya yi.
  • Mutum kuma na iya ya tayar sa'ad da ya ƙi aikata abin da hukuma ta dokace shi da ya aikata.
  • Wani lokacin mutane na tayar wa gwamnatinsu ko shugabansu dake bisansu.
  • Ana iya amfani da kalmar "tayarwa" a fassara ta a ce "rashin biyayya" ko a ce "tãda tarzoma," ya danganta da nassin.
  • "Halin tayarwa" na kuma nuna "ci gaba cikin rashin biyayya" ko "ƙin yin biyayya."
  • Kalmar na nuna "rashin biyayya" ko kuma "ƙin yin biyayya" da kuma "karya doka."
  • Kalmar "mai tayarwa" ko "masu tayarwa" dake fitowa a fili su nuna rashin yardarsu da hukumar dake mulkinsu ta hanyar karya doka da kuma kai farmaki ga sauran mutane. Wasu lokutan suna neman wasu mutanen su haɗa hannu wajen tayarwa.

(Hakanan duba: hukuma, gwamna)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 12:18-19
  • 1 Sama'ila 12:14
  • 1 Timoti 01:9-11
  • 2 Tarihi 10:17-19
  • Ayyukan Manzanni 21:38
  • Luka 23:19

majalisa

Ma'ana

Majalisa wata ƙungiyar mutane ce dake taruwa su tattauna, su bada shawara, su kuma ɗauki mataki game da mahimman abubuwa.

  • Yawancin lokaci akan kafa majalisa akan tsararren tafarki da zai zama din din din domin wani dalili, kamar su yanke shari'a game da abubuwan shari'a.
  • "Majalisar Yahudawa" a Urshalima, an sansu da sunan "Sanhedarin," suna da 'yan majalisa 70, da ta haɗa da shugabannin Yahudawa kamar su manyan firistoci, ma rubuta, Farisawa da Sadukiyawa waɗanda suke taruwa akai akai domin su yanke shari'a game da abubuwan da suka shafi shari'ar Yahudawa. Wannan majalisar ce ta shugabannin ad'dini wadanda suka kawo ƙarar Yesu kuma suka yanke shari'ar cewa a kashe shi.
  • Akwai kuma ƙananan majalisu na Yahudawa a waɗansu biranen.
  • An kawo manzo Bulus gaban majalisar Roma lokacin da aka kama shi domin yana shaida da bishara.
  • Ya danganta ga yadda za a yi amfani da shi a cikin rubutu, wannan kalma "majalisa" za a iya fassara ta a ce "taron mahukunta" ko "taron 'yan siyasa."
  • Idan ana cikin 'yan majalisa" to k=ana cikin wani taro ne na musamman domin yanke shari'a akan wani abu.
  • A yi lura wannan kalma dabam take da "shawara" wadda ma'anarta "bada shawara mai hikima."

(Hakanan duba: tattaruwa, shawara, Farisi, shari'a, firist, Sadusi, marubuci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:57-58
  • Ayyukan Manzanni 24:20
  • Yahaya 03:02
  • Luka 22:68
  • Markus 13:09
  • Matiyu 05:22
  • Matiyu 26:59

makamai, ma'ajin makamai

Ma'ana

Wannan kalma "makami" na nufin kayan da soja yake amfani dasu cikin yaƙi ya kare kansa daga harin maƙiyi. Ana kuma amfani da ita a ruhaniyance a matsayin "'makaman ruhaniya."

  • Wasu daga cikin makaman soja sune kwalkwali, garkuwa, sulke, takalmi, da takobi.
  • Bulus ya yi amfani da kwatanci ta wurin auna makaman jiki dana ruhaniya da Allah ya ba masu gaskatawa domin ya taimake su a yaƙoƙin ruhaniya.
  • Makaman ruhaniya da Allah yaba mutanensa domin su yaƙi zunubi da shaiɗan sun ƙunshi, gaskiya, adalci, bisharar salama, bangaskiya, ceto da kuma Ruhu Mai Tsarki.
  • Za a iya fassara wannan da ma'ana haka, "makarin soja" ko "kayayyakin tsare kai a

yaƙi" ko "marufi mai karewa" ko "makamai."

(Hakanan duba: bangaskiya, Ruhu Mai Tsarki, salama, ceto, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila, 31:9-10
  • 2 Sama'ila 20:8
  • Afisawa 06:11
  • Irmiya 51:3-4
  • Luka 11:22
  • Nehemiya 04:15-16

makiyayi, makiyaya, lura da, kula da, babban makiyayi

Ma'ana

Makiyayi shi ne mutumin da yake kula da tumaki. Aikin "makiyayi" na nufin a kare tumaki a samar masu abinci da ruwa. Makiyaya kan lura da tumaki, da jagorantarsu zuwa wuri mai abinci mai kyau da ruwa. Makiyaya na kare tumakin daga ɓata da kuma kare su daga dabbobin daji.

  • Anyi amfani da wannan kalmar sosai a cikin Littafi Mai Tsarki inda a kayi amfani da ita a matsayin kula da mutane cikin buƙatun ruhaniya. Wannan ya haɗa da koyar da su abin da Yahweh ya faɗa masu a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma jagorantarsu hanyar da zasu rayu.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, an kira Allah "makiyayi" na mutanensa domin yana lura da su da dukkan buƙatunsu ya kuma kare su. Ya kuma bida su da jagorantarsu.
  • Musa makiyayin Isra'ila ne ya jagorance su cikin ruhaniya da yadda suka bautawa Yahweh da kuma bida su cikin jiki a lokacin tafiyarsu zuwa ƙasar Kan'ana.
  • A cikin Sabon Alƙawari, Yesu ya kira kansa "makiyayi mai kyau." Manzo Bulus shima ya kira kansa "babban makiyayi" ga ikkilisiya.
  • Kuma a cikin Sabon Alƙawari, kalmar "makiyayi" anyi amfani da ita ga mutum wanda yake shugaba cikin ruhaniya bisan masu bi. An fassara kalmar a matsayin "pasto" ita ce kalmar da aka fassara da "makiyayi". Dattawa da shugabanni suma akan kira su makiyaya.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan kayi amfani da sassaukar ma'ana, aikin "makiyayi" za a iya fassara shi da "lura da tumaki" ko "sa'ido kan tumaki."
  • Mutumin "makiyayi" akan iya fassara shi a "mutumin da yake lura da tumaki" ko "mai bada kai ga tumaki" ko "mai ba da kula ga tumaki."
  • Idan akayi amfani da kamar misali, hanyoyi da yawa na yin fassara na iya haɗawa da "makiyayi na ruhaniya" ko "shugaba na ruhaniya" ko "wanda yake kama da makiyayi" ko " wanda ya damu da mutanensa kamar yadda makiyayi ya damu da tumakinsa" ko " wanda yake jagorantar mutanensa kamar yadda makiyayi ke kula da tumakinsa" ko "wanda yake kula da tumakin Allah."
  • A waɗansu nassosin, "makiyayi" ana iya fassarashi a matsayin "shugaba" ko "jagora" ko "mai bada kula."
  • Faɗar ruhaniyar game da "makiyayi" akan iya fassara ta zuwa " kula da " ko "sabunta ruhaniya" ko " jagoranta da koyarwa" ko " jagora da kula da" (kamar makiyayi mai kula da tumaki)."
  • A cikin amfani da misali, yana da kyau ayi amfani ko a haɗa da sassaukar kalma domin "makiyayi" a wannan fassarar.

(Hakanan duba: gaskatawa, Kan'ana, ikkilisiya, Musa, pasto, tumaki, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 49:24
  • Luka 02:09
  • Markus 06: 34
  • Markus 14:26-27
  • Matiyu 02:06
  • Matiyu 09: 36
  • Matiyu 25:32
  • Matiyu 26:31

makoki, masu makoki, kuka

Ma'ana

Wannan furci "makoki" manufarsa shi ne nuna baƙinciki yawancin lokaci a mutuwar wani mutum.

  • A cikin al'adu da yawa, makoki ya ƙunshi yin wasu abubuwa a sarari da zai nuna baƙinciki da damuwa.
  • Isra'ilawa da sauran mutane a zamanin dã sukan nuna makokinsu ta wurin kwala ihu da kururuwa. Sukan sa kaya mararsa kintsi da aka yi da tsummokara su kuma baɗa toka a kawunansu.
  • Gwanayen makoki, yawancin lokaci mata ne da ake biyan su, za su saka kururuwa suyi kuka mai zafi daga lokacin mutuwar har bayan an bizne gawar a kabari.
  • ‌Ƙayadadden lokacin makoki kwana bakwai ne, amma zai iya zarcewa har kwana talatin (kamar na Musa da Haruna) ko kwana sabba'in (kamar na Yakubu).
  • Littafi Mai Tsarki ya yi magana da misali akan "makoki" domin zunubi. Ya yi magana akan nuna baƙinciki mai zafi domin zunubi yana kawo wa Allah baƙinciki da kuma mutane.

(Hakanan duba: tsummoki, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila15:34-35
  • 2 Sama'ila 01:11
  • Farawa 23:02
  • Luka 07:31-32
  • Matiyu 11:17

maƙwabci, maƙwabta, maƙwabtaka, makusanta,

Ma'ana

Wannan furci "maƙwabci" na nufin wani mutum dake zaune kusa. Zai iya zama kuma wani mutum da ake zaune tare da shi ko ƙungiyar mutane.

  • Maƙwabci wani mutum ne da za a kare ana masa alheri domin shi ɗaya ne daga cikin iyali.
  • A cikin Sabon Alƙawari, a labarin Ba'samariye mai alheri, Yesu ya yi amfani da kalman nan "maƙwabci" ya faɗaɗa ma'anarta har zuwa ga dukkan 'yan adam, har ma da wanda ake ɗauka abokin gãba.
  • Idan ya yiwu zai fi kyau a fassara wannan kalmar a sauƙaƙe da kalma ko furci mai ma'ana haka, "mutumin dake zaune kurkusa.

(Hakanan duba: abokin gãba, misali, ƙungiyar mutane, Samariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:26-28
  • Afisawa 04:25-27
  • Galatiyawa 05:14
  • Yakubu 02:08
  • Yahaya 09:8-9
  • Luka 01:58
  • Matiyu 05-43
  • Matiyu 19:19
  • Matiyu 22:39

malami, malamai, Malami

Ma'ana

Malami wani taliki ne dake bayar da sabobbin labarai ga mutane. Malamai suna taimakawa mutane su sami ilimi da fasaha.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "malami" ana amfani da ita da manufa ta musamman a nuna wani dake koyarwa game da Allah.
  • Mutanen dake koyo daga malami ana kiransu "ɗalibai" ko "almajirai."
  • A wasu fassarorin Littafi Mai Tsarki, ana amfani da babban harafi ("Malami") sa'ad da aka yi amfani da laƙabin ga Yesu.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar da aka saba da ita ta malami za a iya amfani da ita wajen fassara wannan kalma, sai dai idan kalmar domin malamin makaranta ne kawai ake amfani da ita.
  • Wasu al'adun na iya kasancewa da wani laƙabi na musamman domin malaman addini, kamar su "Yallaɓai" ko "Rabbi" ko "Mai Wa'azi."

(Hakanan duba: almajiri, wa'azi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Mai Wa'azi 01:12-15
  • Afisawa 04:11-13
  • Galatiyawa 06:6-8
  • Habakuk 02:18
  • Yakubu 03:02
  • Yahaya 01:37-39
  • Luka 06:40
  • Matiyu 12:38-40

mallaka, mallakewa, mallakowa

Ma'ana

Wannan magana "mallaka" yawancin lokaci ana nufin abin da ke naka. Zai iya zama kuma samun iko bisa wani abu ko a maye wani ɓangaren ƙasa.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, ana amfani da wannan magana da ma'anar "samu" ko "karɓe wani abu" kamar sashen ƙasa."
  • Lokacin da Yahweh ya umarci Isra'ilawa su "mallaki" ƙasar Kan'ana, ana nufin su tafi su zauna a can. Wannan zai haɗa da yaƙar mutanen Kan'ana waɗanda ke zaune a ƙasar.
  • Yahweh ya gaya wa Isra'ilawa ya basu ƙasar Kan'ana ta zama "mallakarsu." Za a iya fassara wannan haka, "madaidaicin wurin mazauninsu na gaske."
  • Ana kiran mutanen Isra'ila "mallakar Yahweh ta musamman." Ma'ana, su nasa ne mutanen daya kira su musamman suyi masa sujada su kuma bauta masa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "mallaka" za a iya fassara ta haka "na ka" ko "samu" ko "mai kula da abu."
  • Wannan furci "karɓar mallaka" za a iya fassarawa haka "a ɗauki jagoranci" ko "yin aiki" ko "a rayu akan," ya danganta akan nassi."
  • Idan ana magana akan abin da mutane suka mallaka, za a fassara "mallaka" haka "kayayyakinsu" ko "dukiya" ko "abubuwansu" ko "abubuwan da suka mallaka."
  • Sa'ad da Yahweh ya kira Isra'ilawa "abin mallakata na musamman" za a iya fassara wannan ma haka "mutanena na musamman" ko "mutanena" ko "mutane da nake ƙauna ina mulkinsu."
  • Wannan magana "zasu zama mallakarsu idan ana nufin ƙasa ne, ma'anar shi ne "zasu gaji ƙasar" ko "ƙasar zata zama tasu."
  • Wannan furci "an samu a kayansa" za a iya fassarawa haka "yana riƙe da shi" ko "yana tare da shi."
  • Wannan magana "kamar mallakarka" za a iya fassarawa haka "kamar wani abin da ke naka" ko "kamar wurin da mutanenka zasu zauna."
  • Wannan magana, "a gunsa" za a iya fassarawa haka "nasa ne" ko "da yake nasa."

(Hakanan duba: Kan'ana, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:70
  • 1 Sarakuna 09:17-19
  • Ayyukan Manzanni 02:45
  • Maimaitawar Shari'a 04:5-6
  • Farawa 31:36-37
  • Matiyu 13:44

mamaki, al'ajibi, rikicewa

Ma'ana

Dukkan waɗannan kalmomi na fassara ban mamaki ne saboda wani abin da ba a saba gani ba ya faru.

  • Waɗansu kalmomin nan fassara ne furcin harshen Girik dake nufin "mamaki ya kama shi" ko "ya tsaya a waje (shi kansa)." Waɗannan furcin sun nuna mafificin mamaki da mutum ya ji. Wasu yare mai yiwuwa suna da tasu irin faɗin idan mamaki ya kama su.
  • Yawancin lokaci abin da ya bada mamaki wani abin al'ajibi ne, wani abu da Allah ne kaɗai zai iya yi.
  • Wata ma'ana ga kalmomin nan zai iya zama jin ruɗewa domin abin da ya faru ya zo ba zato ba tsammani.
  • Wasu hanyoyin fassara waɗannan maganganu sune, "banmamaki" ko "firgicewa ainun."
  • Wasu kalmomi kusa a fassararsu sune: "ƙasaitaccen abu mai ɗaukar hankali" ko "ban mamaki" ko "al'ajibi" ko "al'ajibi mai ban mamaki."
  • Gabaɗaya dai, duk kalmomin nan suna nuna abu mai kyau ne mutane kuma sun nuna gamsuwa game da abin da ya faru.

(Hakanan duba: al'ajibi, alama)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08:9-11
  • Ayyukan Manzanni 09:20-22
  • Galatiyawa 01:06
  • Markus 02:10-12
  • Matiyu 07:28
  • Matiyu 15:29-31
  • Matiyu 19:25

mamaye, mamayewa, iske, cimma wani, tarar da, shan kai

Ma'ana

Wannan magana "mamayewa" ana nufin samun nasara kan wani ko wani abu. Ya haɗa kuma da ma'anar bin wani da gudu har sai an iske shi.

  • Idan rundunar yaƙi ta "mamaye" abokan gabarta, ma'anar shi ne, sun cinye maƙiyansu a yaƙi.
  • Idan mugun dabba ya cimma wani dabba ya kama shi, ana nufin ya bi shi a guje har sai da ya kama shi.
  • Idan la'ana "ta bi" wani mutum, ana nufin dukkan abin da aka faɗa a cikin la'anar ta faru da mutumin nan,
  • Idan albarku sun "mamaye" mutane, wato mutanen nan sun ɗanɗana albarkun nan.
  • Ya danganta ga nassi, "mamayewa" za a iya fassara ta haka, "cin nasara" ko "kama wa" "cin wasu a yaƙi" ko "cin ma matafiyi" ko "shan kai gaba ɗaya."
  • "Idan an tarar da wani" ana nufin koda yake yana gaba amma an "cim masa", ko "ana tafiya tare gefe da gefe" ko "cin nasara" ko "ci a yaƙi" ko "an cutar da wani."
  • Idan an yi amfani da shi domin faɗakarwa cewa, duhu, ko hukunci, ko razana za su mamaye mutane saboda zunubansu, ma'anar shi ne, abubuwan nan zasu faru da mutanen nan idan basu tuba ba.
  • Furcin nan "Maganganuna sun bi sun mamaye ubanninku" ma'anar shi ne, koyarwa da Yahweh ya ba kakanninsu zai sa kakannin su karɓi hukunci domin sun ƙi su yi biyayya da koyarwar.

(Hakanan duba: albaka, la'ana, farauta, horo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi MaiTsarki:

  • 2 Sarakuna 25:4-5
  • Yahaya 12:35

manyan firistoci

Ma'ana

Manyan firistoci wasu mahimman shugabannin addinin Yahudawa ne a lokacin da Yesu yayi rayuwa a duniya.

  • Manyan firistoci sune aka rataya masu kula da dukkan abubuwan da ake buƙata domin sujada a haikali. Sune kuma suke da hakin lura da kuɗin da aka bayar domin haikali.
  • Sune sama a muƙami da iko fiye da ƙananan firistoci. Babban firist ne kaɗai yake da iko fiye da su.
  • Manyan firistoci suna cikin wasu maƙiyan Yesu kuma sun iza shugabannin Roma su kama shi su kashe.

Shawarwarin Fassara

  • Wannan furci "manyan firistoci" za a iya fasara shi haka "firistoci dake bisa firistoci" ko "firistoci masu bishewa" ko "firistoci masu mulki."
  • A tabbatar an fassara wannan kalma ta fita dabam da "babban firist."

manzo, manzanni

Ma'ana

Wannan magana "manzo" ma'anasa wani mutum da aka bashi saƙo ya je ya faɗa wa waɗansu.

  • A zamanin dã, akan aika manzo daga dagar yaƙi ya je ya gaya wa mutane a cikin birni abin da ya faru.
  • Mala'ika wani irin manzo ne musamman wanda Allah ke aika su kai wa mutane saƙonni. Wasu juyi sukan fassara "'mala'ika" "manzo" ne.
  • An ce da Yahaya Mai Baftisma manzo ne da ya zo kafin Yesu domin yayi shela Almasihu yana zuwa a shirya mutane su karɓe shi.
  • Manzannin Yesu sune masu kai saƙonsa ga mutane labari mai daɗi game da mulkin Allah.

(Hakanan duba: mala'ika, manzanni, Yahaya (mai Baftisma))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 19:1-3
  • 1 Sama'ila 06:21
  • 2 Sarakuna 01:1-2
  • Luka 07:27
  • Matiyu 11:10

martaba

Ma'ana

Kalmar "martaba" na nufin matuƙar kyau da gayu da a koda yaushe yake da nasaba da wadata da fita ta alfarma.

  • Koyaushe akan yi amfani da ado mai martaba a nuna wadatar da sarki yake da ita, ko yadda yake a cikin kayan adonsa masu tsada.
  • Kalmar "martaba" kan iya amfani wajen bayyana kyan bishiyoyi, duwatsu, da sauran abubuwa da Allah ya halitta.
  • Garuruwa da dama ana cewa suna da martaba saboda ma'adanan da suke da su suna bunƙasa gine-gine da hanyoyi, da kuma dukiyar jama'arsu,wadda ta haɗa da tufafi mai tsada, gwal zinariya da azurfa.
  • Ya danganta da nassin, za a iya fassara wannan kalmar da "kyau mai kayatarwa" ko "daraja mai ban mamaki" ko "girman sarauta."

(Hakanan duba: ɗaukaka, sarki, daraja)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 16:27
  • Fitowa 28:1-3
  • Ezekiyel 28:07
  • Luka 04:07
  • Zabura 089:44-45
  • Wahayin Yahaya 21:26-27

masarauta, masarautai

Ma'ana

Masarauta wata ƙungiyar mutane ce wadda sarki ke mulki. Tana kuma nufin wasu ƙasashe ko lardunan siyasa in da wani sarki ko wani shugaba ke da ikon mulkawa da hukuntawa.

  • Masarauta na iya zama da girma yankin ƙasa daban-daban. Sarki na iya mulkin al'umma ko ƙasa ko birni ɗaya kawai.
  • Kalmar "masarauta" tana kuma iya zama sarauta ko hukumar ruhaniya, kamar yadda ake amfani da kalmar "masarautar Allah."
  • Allah ne mai mulkin dukkan halitta, amma kalmar "masarautar Allah" musamman na nufin mulkinsa da hukuncinsa bisa mutanen da suka bada gaskiya da Yesu waɗanda kuma suka miƙa kansu ga hukuncinsa.
  • Littafi Mai Tsarki kuma yayi maganar Shaiɗan shima yana da "masarauta" inda yake a matsayin mai riƙon ƙwaryar mulki bisa abubuwa da yawa a duniya. Mulkinsa na mugunta ne kuma yana nufin "duhu."

Shawarwarin Fassarawa:

  • Idan ana zancen lardi na zahiri wanda sarki ke mulki, kamar "masarauta" ana iya fassarawa "ƙasa (inda sarki ke mulki)" ko "gundumar sarki" ko "lardin da sarki ke mulki."
  • A ruhaniya, "masarauta" na iya fassaruwa "mulki" ko "shugabanci."
  • Wata hanyar fassara "masarautar firistoci" shi ne "firistocin ruhaniya waɗanda Allah ke mulki."
  • Furcin "masarautar haske" ko "mulkin haske" za a fassara "mulkin Allah wanda ke da kyau kamar haske" ko "sa'ad da Allah, wanda shi haske ne, yake mulkin mutane" ko "haske da nagartar mulkin Allah." Yafi kyau a riƙe kalmar "haske" a wannan wurin tunda wani darasi ne mai muhimmanci a cikin Littafi Mai Tsarki.
  • Ayi la'akari da cewa kalmar "masarauta" ta sha ban-ban da daula, inda wani basarake ke mulkin ƙasashe da yawa.

(Hakanan duba: hukuma, sarki, masarautar ko mulkin Allah, masarautar Isra'ila, Yahuda, Yahuda, firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 02:12
  • 2 Timothy 04:17-18
  • Kolosiyawa 01:13-14
  • Yahaya 18:36
  • Markus 03:24
  • Matiyu 04:7-9
  • Matiyu 13:19
  • Matiyu 16:28
  • Wahayin Yahaya 01:09

mashi, mashika, mutanen mashi

Ma'ana

Mashi makami ne da yake da dogon mariƙin itace da kuma ƙarfe mai tsini da kaifi a kansa da ake iya jefa shi da nisa.

  • Ana amfani da mashi ne mafi akasari a yaƙi a zamanin littafi mai tsarki. Har yanzu akanyi amfani da su idan rikici ya ɓarke tsakanin kabilu.
  • Wani sojan Roma ya yi amfani da mashi ya soki kwiɓin Yesu lokacin da yake kafe akan gicciye.
  • Sau da yawa mutane kan jefa mashi domin su kama kifi ko wata ganima su ci.
  • Makamanta makaman sun haɗa da "mashin" ko "barandami."
  • A tabbata fassarar "mashi" ta sha banban da fassarar "takobi" wanda makami ne na sara da daddatsawa ba na jifa ba. kuma takobi na da kaifi mai tsawo da mariƙi, inda kuma mashi yake da tsini gajere akansa da kuma da dogon kaifi.

(Hakanan duba: ganima, Roma, takobi, mayaƙi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 13:19-21
  • 2 Sama'ila 21:19
  • Nehemiya 04:12-14
  • Zabura 035:03

masoyi, masoya

Ma'ana

Wannan kalma "masoyi" ma'anarsa "mutum mai ƙauna." Yawancin lokaci ana nufin mutane dake dangantakar jima'i da junansu.

  • Sa'ad da aka yi amfani da wannan kalma "masoyi" a cikin Littafi Mai Tsarki, ana nufin mutum wanda yake sha'anin jima'i da wani ko wata wanda basu yi aure ba.
  • Wannan dangantakar jima'i marar kyau ana amfani da shi a cikin Littafi Mai Tsarki a nuna rashin biyayyar Isra'ila ga Allah yadda sukan juya ga bautar gumaku. Saboda haka wannan kalma "masoya" ana amfani da ita a misalta gumakun da mutanen Isra'ila suka bautawa. A cikin wannan magana, wannan furci za a iya fassarata haka "dangantakar ƙyama" ko "dangantakar zina" ko "gumaku." [Duba misali]
  • Mai "ƙaunar" kuɗi mutum ne da yasa mahimmanci kan neman kuɗi da yin arziki.
  • A cikin Tsohon Alƙawari a littafin Waƙoƙi Suleman, wannan kalma "masoyi" an yi amfani da ita yadda ya kamata.

(Hakanan duba: zina, gunki, ƙauna)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Hosiya 02:05
  • Irmiya 03:02
  • Littafin Makoki 01:02
  • Luka 16:14

masu hikima

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, "masu hikima" na nuna mutanen da suka bauta wa Allah cikin ayyuka masu hikima, ba cikin wawanci ba. Wannan na kuma bayyana mutane masu hikima da ilimi da ƙwarewa na musamman da suka yi bauta cikin fadar sarki.

  • Wasu lokuta kalmar "masu hikima" ana bayanin ta a nassi a matsayin "masu tattali" ko "mutane masu fahimta." Wannan na nufin mutane da suka aikata hikima da adalci saboda sunyi biyayya da Allah.
  • "Masu hikima" waɗanda suka yi wa Fir'auna da wasu sarakuna hidima yawanci masanan taurari ne, musamman domin su fahimci yanayi na yadda taurarin sama ke shimfiɗe a sama.
  • Yawancin lokaci masu hikima ana buƙace su da su fassara ma'anar mafarkai. Ga misali, Sarki Nebukadnezza ya bukaci masu hikimarsa da su bayyana su kuma fassara masa mafarkin da ya yi, amma babu wani daga cikinsu da ya iya yin hakan, sai dai Daniyel wanda ya sami wannan hikimar daga wurin Allah.
  • Wasu lokutan mutane masu hikima na yin dabo kamar duba ko aikin al'ajibai ta yin amfani da ikon miyagun ruhohi.
  • A cikin Sabon Alƙawari, ƙungiyar mutanen da suka zo daga gabas domin su yi wa Yesu sujada ana ce da su "magi," wanda ake fassara shi a ce "masu hikima," wannan ya nuna masu ilimi waɗanda suka yi wa shugabannin ƙasashen gabas bauta.
  • Tabbas waɗannan mutane masu ilimin bokanci ne da suka karanci taurarin sammai. Waɗansu suna tunanin cewar sune zuriyar masana waɗanda Daniyel ya karantar da su sa'ad da yake a Babila.
  • Ya danganta da nassin, kalmar"masu hikima" za a iya fassarawa ta wurin amfani da kalmar "mai hikima" ko da faɗar kamar haka "masu baiwa" ko "masu ilimi" ko wasu kalmomin da suna nufin waɗanda ke yi wa shugabanni bauta ta musamman.
  • Sa'ad da "masu hikima" ya kasance faɗar jimlar suna, kalmar "mai hikima" za a fassara ta a hanyar ko shegen hanyar da aka fassara ta a wasu wuraren cikin Littafi Mai Tsarki.

(Hakanan duba: Babila, Daniyel, sihiri, dabo, Nebukadnezza, mai mulki, mai hikima)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 27:32-34
  • Daniyel 02:1-2
  • Daniyel 02:10-11
  • Daniyel 02:10-11

masunta, masu kamun kifi

Ma'ana

Masunta mutane ne da ke kamun kifi daga ruwa wanda kuma shi ne hanyar samun abin zaman garinsu. A cikin Sabon Alƙawari, masunta na amfani da manyan taruna domin kamun kifi. kalmar nan masunta wani suna na masu kamun kifi.

  • Bitrus da sauran manzanni sun yi aiki a matsayin masunta kafin Yesu ya kira su.
  • Tun da yake ƙasar Isra'ila na kusa da ruwa Littafi Mai Tsarki na da misalai sosai game da masunta da kuma kifi.
  • Wanan kalma za'a iya fassara ta da kalmar kamar "mutanen da ke kamo kifi" ko "mutane masu sana'ar kamun kifi."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 47:9-10
  • Ishaya 19:8
  • Luka 05:1-3
  • Matiyu 04:19
  • Matiyu 13:47

matashin sawaye

Ma'ana

Kalmar nan "matashin sawaye" tana nufin wani abu ne da mutum ya ɗora ƙafafunsa a mafi yawanci lokuta domin hutu a lokacin da mutum ke zaune. Itama wanan kalmar tana da salon ma'ana na miƙa wuya da kuma ƙasƙantar da kai.

  • Mutane a cikin Littafi Mai Tsarki kan ɗauki ƙafafu a matsayin ƙasƙantaccen ɓangare na jiki. To wanan "matashin sawaye" ta fi ƙafafu ƙasƙanci domin a kansa ne ake ɗora ƙafa.
  • Sa'ad da Allah ya ce "zan mayar da maƙiyana matashin sawayena" yana nuna iko ne, sarrafawa, da nasara akan mutane waɗanda suka tayar masa. Za ƙasƙantar da su a yi nasara da su har sai sun miƙa wuya ga Allah.
  • Dauda ya baiyana haikali a matsayin "matashin sawayen Allah," wanan zai iya nufin cikakken ikonsa akan mutanensa. Hakanan wanan zai iya nuna Allah a matsayin sarki akan kursiyinsa, da ƙafafunsasuna hutawa a kan matashin sawayensa, wanda ke nuna kowa na ƙarƙashin ikonsa.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:49
  • Ishaya 66:1
  • Luka 20:43
  • Matiyu 05:35
  • Matiyu 22:44
  • Zabura 110:1

matatsar ruwan inabi

Ma'ana

A kwanakin Littafi Mai Tsarki, "matatsar ruwan inabi" babbar gidauniya ce ko wuri ne mai faɗi inda ake tatsar 'ya'yan itacen inabi domin samun ruwan inabi.

  • A Isra'ila, matatsun ruwan inabi wurare ne masu girma, manyan darurukan da aka sassaƙo daga dutse. Curin 'ya'yan itacen inabi za a zuba su mutane su tattake da kafafunsu ruwan inabin na zubowa.
  • Akwai matakai guda biyu, sama da ƙasa da ake zuba 'ya'yan itacen inabin domin a tattake su daga sama ruwan na zubowa a sashe na ƙasa inda ake tarawa.
  • "Matatsar inabi" ana amfani da ita a nuna bayyanuwar hasala da fushin Allah da ake kwararowa bisa mugayen mutane.

(Hakanan duba: itacen inabi, hasala)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ishaya 63:02
  • Markus 12:01
  • Matiyu 21:33
  • Wahayin Yahaya 14:20

matokari, matokarai, gwafa, ginshiƙi, ginshiƙai

Ma'ana

Wannan magana "ginshiƙi" ana nufin wani babban gini mai tsayi ne da ake amfani da shi a riƙe jinkar ɗaki ko wani shashen gini. Wata kalma mai kama da "ginshiƙi" shi ne "'gwafa."

  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, ginshiƙan da ake riƙe gini da su akan sassaƙo su daga dutse guda ne.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, lokacin da Filistiyawa suka kama Samson, ya rushe haikalin tsafinsu ta wurin ture ginshiƙan dake riƙe da ginin, ta haka yasa haikalin ya faɗi ya ragargaje.
  • Wannan kalma "ginshiƙi" wani lokaci ana nufin wani babban dutse ne da ake kafawa a bisa kabari domin tunawa ko a shaida wurin da wani abu mai mahimmanci ya auku.
  • Zai kuma iya zama wani gunki da aka yi domin a bauta wa maƙaryacin allah. Wani suna ne kuma domin wani "sassaƙaƙƙen sura" za a iya fassara shi "mutum-mutumi."
  • Wannan kalma "ginshiƙi" ana amfani da shi domin wani abu da aka siffanta shi kamar ginshiƙi, kamar a ce "ginshiƙin wuta" daya bida Isra'ilawa da dare cikin jeji ko "ginshiƙin gishiri" da matar Lot ta zama bayan ta waiwaya ta kalli birnin.
  • A matsayin abu mai tokare gini, wannan kalma "ginshiƙi" ko "gwafa" za a iya fassara ta haka "dutse mai tsayi mai riƙewa" ko "dutse mai ɗaukar gini."
  • Wasu hanyoyin amfani da "ginshiƙi" sai dai a fassara ne haka "mutum-mutumi" ko "tari" ko "gini" ko "siffa" ko "tarin abu mai tsayi," zai dai danganta ga yadda za a yi amfani da shi a nassi.

(Hakanan duba: harshashen gini, gunki, sura)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 18:04
  • Fitowa 13:21
  • Fitowa 33:09
  • Farawa 31;45
  • Littafin Misalai 09:1-2

matsafi, matsafa,matsafiya, tsafi, tsafe-tsafe, maita, boka

Ma'ana

"Tsafi" ko "maita" na nufin amfani da sihiri, wanda ya haɗa da yin wasu abubuwa da iko ta wurin taimakon mugun ruhu. "Matsafi" wani mutum ne da yake yin abubuwa masu iko ta wurin sihiri.

  • Amfani da sihiri da tsafi kan haɗa da yin abubuwa masu amfani kamar (warkas da wani) da kuma abubuwan cutarwa (kamar sawa wani la'ana). Amma kowanne irin tsafi bashi da kyau, domin akan yi amfani da mugayen ruhohi.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya ce amfani da tsafi abu ne mai haɗari dai-dai da dukkan sauran zunubai (kamar zina, bautar gumaka, da hadaya da yaro).
  • Kalmar "tsafi" da "maita" akan iya fassara ta da "ikon mugun ruhu" ko "zuba magani."
  • Hanyar fassara "tsafi" kan haɗa da "mai aikin sihiri" ko "mutum mai yin magani" ko "mutumin da yake yin mu'ujizai ta wurin amfani da ikon mugun ruhu."
  • Lura da: "tsafi" na da banbanci ma'ana da "mai duba" wanda yake nufin ƙoƙarin tuntuɓar ruhohin duniya.

(Hakanan duba: zina, aljani, duba, allolin karya, sihiri, hadaya, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08:9-11
  • Fitowa 07: 11-13
  • Galatiyawa 05: 19-21
  • Wahayin Yahaya 09 :20-21

matsakanci

Ma'ana

Matsakanci mutum ne da ya taimaka wa mutum biyu ko mutane da yawa su sasanta jayayya ko rashin jituwarsu da juna.Yakan taimake su su sulhuntu.

  • Domin mutane sun yi zunubi, maƙiyan Allah ne sun cancanci hasalarsa da hukuncinsa. Saboda zunubi, zumuncin tsakanin Allah da mutanensa ya tsinke.
  • Yesu shi ne matsakanci tsakanin Allah Uba da mutanensa, yana maida dangartaka ta wurin mutuwarsa wadda ita ce biyan bashin zunubanmu.

Shawarwarin Fassara:

  • Ga hanyoyin fassara "matsakanci" za a iya cewa haka "mutum mai tsayawa tsakani" ko "mai sulhu" ko "mutumin dake kawo salama."
  • Gwada wannan magana da yadda ake fassara "firist." Zai fi kyau idan an fassara "matsakanci" dabam.

(Hakanan duba: firist, sulhunta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 02:05
  • Galatiyawa 03:20
  • Ibraniyawa 08:06
  • Ibraniyawa 12:24
  • Luka 12:14

matsala, matsaloli, an matsalar, matsalarwa, mai tayar da hankali, rigimamme, damun wasu, motsar da, motsawa, ɓacin rai, girgiza, azaba

Ma'ana

"Matsala" wani yanayi ne na rayuwa dake da wahala sosai da ƙuntatawa. A "matsalar" da wani na ma'anar a "dami" wannan taliki ko a jawo masa ƙuntatawa. A kasance cikin "matsala" na ma'anar aji ɓacin rai ko ƙuntatawa game da wani abu.

  • Matsaloli zasu iya zama a zahiri, a lamiri, ko abubuwan ruhaniya da suka yiwa wani zafi.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, yawanci matsaloli lokutan jarabawa ne da Allah yake amfani dasu ya taimaki masu bada gaskiya su balaga da girma cikin bangaskiyarsu.
  • Tsohon Alƙawari ya yi amfani da "matsala" yana kuma nufin hukunci dake zuwa bisa ƙungiyoyin mutane waɗanda suke lalatattu suka kuma yi watsi da Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "matsala" ko "matsaloli" za a iya fassara su kuma haka "haɗari" ko "abubuwa masu zafi da suka faru" ko "tsanani" ko "mawuyacin yanayi" ko "ƙunci."
  • Kalmar "an matsalar" za a iya fassarawa da kalma ko faɗar dake da ma'anar "kasancewa cikin ƙunci" ko "jin ƙunci mai tsanani" ko "damuwa" ko "ganin nawa" ko "ƙuntatawa" ko "gigicewa" ko "damun rai."
  • "Kada a bata matsala" za a kuma iya fassarawa "kada a dame ta" ko "kada ka yi mata yanke."
  • Faɗar "ranar matsala" ko "lokutan matsala" za a iya fassarawa kuma "sa'ad da kake fuskantar ƙunci" ko "sa'ad da mawuyatan al'amura suka faru da kai" ko "sa'ad da Allah yasa abubuwan ƙuntatawa su faru da kai."
  • Hanyoyin fassara "tayar da hankali" ko "kawo tashin hankali" zasu iya haɗawa da "sanya abubuwan ƙuntatawa su faru" ko "sanya mawuyatan hali" ko "a sanya su fuskanci abubuwa masu wuya sosai."

(Hakanan duba: azaba, tsanani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 18:18-19
  • 2 Tarihi 25:19
  • Luka 24:38
  • Matiyu 24:06
  • Matiyu 26:36-38

mayakin doki, mayaƙan dawakai

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar "mayaƙan doki" ana ganin su akan mayaƙa a fagen dãga.

  • Mayaƙan da ke tuƙa karusai suma ana iya kiran su "mahaya dawakai," duk da yake hakika ana nufin masu tuƙa karusai ne.
  • Isra'ilawa sun yi imanin cewa yin amfani da dawakai a fagen dãga yana da tasiri sosai wanda kan sa mutane su sa dogararsu a kan su a maimakon dogara ga Yahweh, domin haka ba su da mahaya dawakai da yawa.
  • Wannan kalmar za'a iya fassara ta da "mai tuƙa dawakai" ko "mahaya dawakai."

(Hakanan duba: karusa, dawakai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 01:05
  • Daniyel 11:40-41
  • Fitowa 14:23-25
  • Farawa 50:7-9

mãye, mashayi (buguwa)

Ma'ana

Kalmar nan "mãye" ko "buguwa" tana nufin yin tatul ta wurin shan barasa mai yawa.

  • Mashayi mutum ne wanda ke yawan buguwa. Irin wanan mutum ana iya kiran sa da "ɗan giya"
  • Littafi mai tsarki ya ce da masubi da su bugu fda giya amma Ruhun Allah ya bi da su.
  • Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Buguwa wawanci ne yakan kuma kai mutum ga yin zunubi ta wata hanyar.
  • Waɗansu hanyoyi na yin fassarar "buguwa" su ne "mãye" ko "jiri" ko "yin tatul da barasa" ko buguwa da abu mai sa mãye."

(Hakanan duba: ruwan inabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:11-13
  • 1 Sama'ila 25:36
  • Irmiya 13:13
  • Luka 07:34
  • Luka 21:34
  • Littafin Misalai 23:19-21

mazaunin fitila, mazaunin fitili

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "mazaunin fitila" a taƙaice yana nufin wani wuri inda ake ɗora fitila domin ta bada haske ga ɗakin.

  • Mazaunin fitila mai sauki fitila ɗaya yake riƙewa kuma ana yinsa da yumɓu, katako ko ƙarfe (kamar su tagulla, azurfa, ko zinariya.)
  • A cikin haikalin Yerusalem akwai mazaunin fitila na zinariya musamman wanda ke da rassa bakwai domin riƙe fitilu bakwai.

Shawarwarin Fassara:

  • Ana iya fassara wannan kalma a matsayin "ƙafar fitila" ko "abin riƙe fitila" ko "mariƙin fitila."
  • Game da mazaunin fitilar haikali, ana iya fassara wannan a matsayin "mazaunin fitila bakwai" ko "ƙafar zinariya tare da fitilu bakwai."
  • Kuma zai taimaka wurin fassarawa idan aka haɗa da hotunan mazaunin fitila da mazaunin fitila mai rassa bakwai a shafofin Littafi Mai tsarki dake zancen su.

(Hakanan duba: tagulla, zinariya, haske, azurfa, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 05:5-6
  • Fitowa 37:17
  • Markus 04:21-23
  • Matiyu 05:15-16
  • Wahayin Yahaya 01:12-13
  • Wahayin Yahaya 01:20

mikiya, mikiyoyi

Ma'ana

Mikiya wata babbar tsuntsuwa ce mai iko wadda ke firiya tana cin ƙananan dabbobi, kamar kifi, ɓera, maciji da kaji.

  • Littafi Mai Tsarki ya kwatanta sauri da ƙarfi na sojoji da yadda sukan kai bãra kan yadda mikiya ke kawo bãra domin ta kama abin da ta samu.
  • Ishaya ya baiyana cewa waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su yi shawagi kamar yadda mikiya ke yi. Wanan salon magana ne aka mora domin a nuna irin 'yanci da kuma ƙarfi da akan samu a cikin dogara da kuma yin biyayyya da Allah.
  • A cikin Littafin Daniyel, an kwatanta tsawon sumar sarki Nebukadnezza da tsawon fiffiken mikiya wanda ya fi kamu hamsin a tsawo.

(Hakanan duba: Daniyel, 'yanci, Nebudkadnezar, iko)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 01:23
  • Daniyel 07:4
  • Irmiya 04:13-15
  • Lebitikus 11:13-16
  • Wahayin Yahaya 04:7

misali, misalai, karin magana

Ma'ana

Karin magana wata guntuwar magana ce wadda ke faɗin wasu hikima ko gaskiya.

  • Karin Magana na da ƙarfi domin tana da sauƙin tunawa da kuma maimaitawa.
  • Yawancin lokaci karin magana na bada aikatattun misalai ne daga rayuwar yau da kullum.
  • Wasu misalan masu sauƙin fahimta ne miƙaƙƙu, wasu kuwa suna da wuyar ganewa.
  • Sarki Suleman sananne ne wajen hikimarsa kuma ya rubuta karin magana sama da 1,000.
  • Yawancin lokaci Yesu ya yi amfani da karin magana ko misalai sa'ad da yake koyar da mutane.
  • Hanyoyin fassara "karin magana" zai haɗa da "faɗin hikima" ko "maganar gaskiya."

(Hakanan duba: Suleman, gaskiya, hikima)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 04:32-34
  • 1 Sama'ila 24:12-13
  • 2 Bitrus 02:22
  • Luka 04:24
  • Littafin Misalai 01:1-3

mulki, yin mulki

Ma'ana

Kalmar "mulki" na nufin shugabanci bisa mutane na cikin ƙasa ko masarauta. Mulkin sarki shi ne cikin lokacin da yake shugabancinsa.

  • Kalmar "mulki" na nuna yadda Allah ke mulki a matsayin sarki bisa dukkan duniya.
  • Allah ya bar sarakuna mutane da su yi mulki bisa Isra'ila bayan da mutanen suka ƙi shi a matsayin sarkinsu.
  • Idan Yesu ya dawo, za ya yi mulki bisa dukkan duniya a matsayin sarki, kuma kiristoci zasu yi mulki tare da shi.
  • Wannan kalma kuma ana iya fassarata a ce "mulki ɗungum" ko "mulki a matsayin sarki."

(Hakanan duba: masarauta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 02:11-13
  • Farawa 36:34-36
  • Luka 01:30-33
  • Luka 19:26-27
  • Matiyu 02:22-23

murya, muryoyi

Ma'ana

Kalmar "murya" ana amfani da ita ne domin yin bayani ko faɗin wani abu.

  • Allah kansa ana cewa yana amfani da muryarsa, koda yake ba shi da murya kamar yadda mutane ke da ita.
  • Wannan kalmar ana iya amfani da ita a bayyana mutum gabaɗaya, ga misali wannan maganar "An ji murya cikin jeji na cewa, 'ku shirya hanyar Ubangiji."' Wannan ana iya fassarata haka "An ji mutum na kira daga cikin jeji..."
  • A "ji muryar wani" za a iya fassara shi kamar a "ji wani na magana."
  • Wasu lokuta kalmar "murya" ana amfani da su a bayyana abubuwan da basu iya magana, kamar yadda Dauda yace cikin zabura cewa "muryar" sammai suna furta manyan ayyukan Allah. Wannan kuma ana iya fassarawa haka "ƙawatawarsu na bayyanawa a sarari yadda girman Allah yake."

(Hakanan duba: kira, shelar, ƙawatawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 05:36-38
  • Luka 01:42
  • Luka 09:35
  • Matiyu 03:17
  • Matiyu 12:19

mutane masana, masu ilimin sararin sama

Ma'ana

A cikin labarin haihuwar Yesu Almasihu bisa ga Matiyu, "mutane masana" ko "mutane masu ilimi" sune "shehuna" da suka kawo wa Yesu kyautai a Baitalami sa'ad da aka haife shi a nan. Mai yiwuwa su "masu ililmin sararin sama" ne, mutanen dake karanta taurari.

  • Mutanen nan suka yiwo tafiya daga ƙasa mai nisa zuwa gabashin Isra'ila. Ba a san zahiiri daga inda suka fito ba ko kuma su su wanene. Amma hakika masana ne waɗanda iliminta a binciken taurari.
  • Wataƙila zuriyar mutanen nan ne masu ilimi da suka bauta wa sarakunan Babila a lokacin Daniyel waɗanda aka horesu a abubuwa masu yawa,har ma game da ilimin taurari da fasara mafalkai.
  • Bisa ga al'adu an ce masana uku ne ko mutane masu ilimi saboda kyautai uku da suka kawo wa Yesu. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki bai faɗi ko su nawa ne ba.

(Hakanan duba: Babila, Betlehim, Daniyel)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 02:27
  • Daniyel 05:7
  • Matiyu 02:01
  • Matiyu 02:07
  • Matiyu 02:16

mutu, mutuwa, wanda ya mutu, mattace, na mutuwa, mai kawo mutuwa, mutuwar, yin mutuwa

Ma'ana

Wannan ana moron wannan ƙaulin a baiyana mutuwa ta jiki da kuma ta ruhaniya. a jiki ana nufin lokacin da jikin mutum ya dena rayuwa. mutuwar ruhaniya kuma na nufin rabuwar mai zunubi da Allah mai tsarki sabo da zunubansu.

  1. Mutuwa ta jiki
  • A mutu wannan na nufin a tsayar da rayuwa. mutuwa ita ce ƙarshen rayuwar jiki.
  • Ruhun mutun yakan rabu da jikinsa a lokacin da ya mutu.
  • Lokacin da Adamu da Hauwa'u suka yi zunubi mutuwa ta jiki ta shigo duniya.
  • Wannan bayanin a kashe na nufin a kashe wani musamman idan sarki ko wani shugaba ya bada ummarni domin a kashe wani.
  1. Mutuwa ta ruhaniya
  • Mutuwa ta ruhaniya ita ce rabuwar mutun daga Allah.
  • Adamu ya mutu a ruhaniyence a lokacin da ya yi wa Allah rashin biyayya, dangatakarsa da Allah ta katse. yaji kunya ya so ya ɓuya

daga Allah

  • Duk wani zuriyar Adamu mai zunubi ne, kuma a mace yake a Ruhu. Allah ya sake rayar da mu a ruhu a lokacin da muka ba da gaskiya ga Yesu Kristi.

Shawarwarin Fassara:

  • domin fassara wannan kalma, ya fi kyau a mori kalmomi na yau da kullum, a harshen da ake yin fassarar wanda ke da alaƙa da mutuwa.
  • A waɗansu harsunan a "mutu" na nufin kada a "rayu" Wanan kalma mutuwa ana iya fassarar ta a "rashin rayuwa" ko "rashin rai" ko kuma "rashin rai baki ɗaya" ko kuma "rashin rayuwa."
  • Harsuna da yawa na moron salon magana wjen bayyana mutuwa, kamar "rasuwa" da Hausa Duk da haka a cikin littafi Mai Tsarki ana moron kalmar mutuwa kai tsaye kamar yadda sauran harsuna ke baiyana ta.
  • A cikin Littafi mai tsarki mutuwa ta jiki duk akan yi maganar mutuwa ta jiki da ta ruhaniya akan mutuwa. yana da muhimmanci a mori kalmar mutuwa wajen bayaninkan mutuwa ta jiki ko ta ruhu.
  • A waɗansu harsunan akan fi ganewa idan aka ce "mutuwa ta ruhaniya" idan har nassin ya bukaci bayanin hakan. Waɗansu masu fassara kuma kan ga cewa ya fi kyau a yi batun "mutuwa ta jiki" a wurin da aka bambanta mutuwa ta ruhaniya.
  • Batun kalmar nan "mutuwa" wata kalma ce da ke nuna waɗanda suka mutu.
  • Batun nan "kashewa" za a iya fassara ta da kisa ko kashe ko "zartar"

(Hakanan duba: imani, bangaskiya, rai, ruhu)

Wuraren da ake samuna a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 15: 21
  • 1 Tassalonikawa 04:17
  • Ayyukan Manzanni 10:42
  • Ayyukan Manzanni 14:19
  • Kolosiyawa 02:15
  • Kolosiyawa 02:20
  • Farawa 02:15-17
  • Farawa 34:27
  • Matiyu 16:28
  • Romawa 05:10
  • Romawa 05:12
  • Romawa 06:10

na sarauta, sarauta, na sarakuna

Ma'ana

Kalmar "na sarauta" na bayyana mutane da abubuwan dake tattare da sarki ko sarauniya.

  • Abubuwan da ake iya cewa suna kusa da "na sarauta" sune kamar rigar sarki, fada, kursiyi, da kuma kambi.
  • Sarki ko kuma sarauniya na zama cikin fadar sarauta ne.
  • Sarki na sanya kaya na musamman, ana kiran kayan da suna "tufafin sarauta."
  • A Sabon Alƙawari, masu gaskatawa da Yesu ana ce da su "ƙungiyar firistoci." Wata hanyar amfani da ita kuma na iya zama "firist wanda ke yi wa Allah Sarki hidima" ko "kirayayye don aikin firist ga Allah Sarki."
  • kalmar "sarauta" ana iya amfani da ita a ce "na sarakuna" ko "na sarki."

(Hakanan duba: sarki, fãda, firist, sarauniya, riga)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna10:13
  • 2 Tarihi 18:28-30
  • Amos 07:13
  • Farawa 49:19-21

nacewa, naciya,

Ma'ana

Waɗannan maganganu "nacewa" da "naciya" na nufin ci gaba da abu koda shi ke yana da wuya sosai ga kuma ɗaukar tsawon lokaci.

  • Naciya kuma nada ma'ana haka, yin halin Kristi koda ana cikin yanayi mai wuyar gaske ko wahala.
  • Idan mutum yana da "naciya" wato yana ci gaba da abin da ya kamata ya yi, koda shike yana da ciwo da wuya kuma.
  • Ci gaba da bada gaskiya ga abin da Allah ya koyar na buƙatar nacewa, musamman lokacin da mutum ya fuskanci koyarwar ƙarya.
  • Ayi lura kada ayi amfani da kalmar nan "taurin kai" wanda yawancin lokaci yana da mummunar ma'ana.

(Hakanan duba: haƙuri, gwaji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Kolosiyawa 01:11
  • Afisawa 06:18
  • Yakubu 05:9-11
  • Luka 08:14-15

naɗaɗɗen littafi, naɗaɗɗun litattafai

Ma'ana

A zamanin dã, naɗaɗɗen littafi wani irin littafi ne dake da tsayi, naɗaɗɗe ne daga fafirus ko fãta.

  • Bayan an yi rubutu a bisa naɗaɗɗen littafi ko an yi karatu daga cikinsa, mutane suna naɗe shi ta wurin yin amfani da ƙarafunan dake harɗe da iyakarsa.
  • Naɗaɗɗun litattafai ana amfani da su domin ajiye rubutun dokoki da littafi mai tsarki.
  • Wasu lokuta naɗaɗɗun litattafan da ɗan saƙo ke kawo wa ana bugawa da hatimi na kakin zuma ko ƙaro. Idan kakin zuma ƙaron na a ɗanyensa a lokacin da aka kawo saƙon, da haka shi mai karɓar saƙon zai san da cewa ba a buɗe wannan naɗaɗɗen littafi,ba ko a yi rubutu cikinsa ba tunda an riga an hatimce shi.
  • Naɗaɗɗun litattafai ɗauke da Litattafan Yahudawa ana karantasu da ƙarfi a cikin majami'unsu.

(Hakanan duba: hatimi, majami'a, maganar Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Irmiya 29:03
  • Luka 04:17
  • Littafin Lissafi 21:14-15
  • Wahayin Yahaya 05:02

naɗawa, shiryayye tun dã, keɓewa, warewa

Ma'ana

Ma'anar "Naɗi" shi ne a zaɓi wani mutum domin wani aiki masamman. Za a iya cewa kuma kafa doka ko umarni.

  • Wannan magana "keɓewa" ma'anarta yawancin lokaci game ne da zaɓen mutumin da zai zama firist, mai hidima, ko malami.
  • Misali, Allah ya naɗa Haruna da zuriyarsa su zama firistoci.
  • Zai iya kuma zama da wannan ma'ana, tsaida, ko kafa wasu bukukuwan addini da alƙawarai.
  • Ya danganta ga nassi, "naɗawa" za a iya fassarawa haka, "bada aiki ga wani mutum" ko "zaɓe" ko "bada doka" ko "kafa doka" ko "soma wani abu."

(Hakanan duba: doka, alƙawari, shari'a. firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 12:31-32
  • 1 Sama'ila 17:13-14
  • Fitowa 28:40-41
  • Littafin ‌Lissafi 03:03
  • Zabura 111:7-9

nagarta

Ma'ana

Kalmar nan "nagarta" tana nufin zama da aminci, daq kuma ƙaƙƙarfan horon kai da halaiya su ake kira nagarta.

  • Zama da nagarta kuma yana nufin yin zaɓi na yin abin da ke na aminci da kuma daidai koma a lokacin da ba wanda ke gani.
  • Waɗansu fitattun mutane cikin Littafi Mai Tsarki, kamar Yosef da Daniyel, sun nuna nagarta a lokacin da suka ƙi su yi abin da ke mugu suka kuma zaɓi su yi biyayyya ga Allah.
  • Littafin Misalai na cewa ya fi kyau a zama da talauci da kuma nagarta fiye da a zama da wadata ta wurin rashawa da rashin aminci.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "nagarta" za'a iya fassara ta da "aminci" ko "yin rayuwar da ke dai-dai" ko "nuna halaiya ta gaskiya" ko "yin abu na aminci, rayuwa ta aminci."

(Hakanan duba: Daniyel, Yosef (Tsohon Al‌ƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 09:04
  • Ayuba 02:3
  • Ayuba 04:06
  • Littafin Misalai 10:8-9
  • Zabura 026:1-3

narke, ya narke, yana narkewa, zube

Ma'ana

Wannan magana "narke" na nufin wani abu ya komo ruwa-ruwa sa'ad da aka gasa shi. Ana kuma amfani da shi a misali. Abin da aka narkar ana ce da shi "zube."

  • Akan gasa ƙarfuna iri-iri har sai sun narke sa'an nan a zuba su cikin daro domin a yi makamai ko gumaku. wannan furci "zuben "ƙarfe" ana nufin ƙarfen da aka narkar.
  • Idan kandur yana ƙonewa, kitsensa yana narkewa yana ɗiɗɗiga. A zamanin dã, akan liƙe wasiƙu da narkakken danƙo a gefunanta.
  • Idan an yi amfani da misali "narkewa" zai zama da wannan ma'ana
  • Wannan furci "zukatansu zasu narke" ma'anarsa "zasu zama da rauni saboda tsoro.
  • Wata manufar wannan magana "za su narke" shi ne zai zamana dole su tafi ko za a bayyana su raunana za su tafi babu nasara.
  • Wata ma'anar "narkewa" mai sauƙi ita ce "ya zama ruwa" ko "a narkar ko "a sa ya zama ruwa-ruwa."
  • Wasu hanyoyin fassara wannan kalma "narkarwa" kuma su ne"sa abu ya yi laushi" ko "ya yi rauni" ko a ci nasara akansa."

(Duba kuma: zuciya, gunki, sura, hatimi)

Wuraren da ake samunsa a cikin Littafi Mai Tsarki:

  • Zabura 112:10

nawaya, nawayoyi, nauyi, aiki tuƙuru, furce-furce

Ma'ana

Nawaya kaya ne mai nauyi. Yana nufin kaya ne sosai wanda dabba ma'aikaci zai ɗauka. Kalmar nan "nawaya" tana kuma da wasu ma'ana cikin misalai da dama:

  • Nawaya zata iya zama wani aiki mai wuya ko abin da aka umarta mai mahimmanci a yi. Za a iya cewa "ɗaukar" ko "ɗauke" da "kaya mai nauyi."
  • Mugun shugaba zai iya sa nawaya mai wuya akan mutanen da yake mulki, misali ta wurin tilasta masu su biya haraji mai yawa.
  • mutumin da baya so ya zama nawaya ga wani bai so ya sa wannan mutumin cikin wahala.
  • Zunubin mutum yakansa laifinsa ya zama masa nawaya.
  • "Nawayar Ubangiji" misali ne na cewa "saƙo daga Allah" ne wanda dole annabi ya miƙa wa mutanen Allah.
  • Wannan kalma "nawaya" za a iya fassara ta ta zama "shugabanci" ko "aiki" ko "kaya mai nauyi" ko "saƙo," ya danganta ga nassin.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tasalonikawa 03:6-9
  • Galatiyawa 06:1-2
  • Galatiyawa 06:03
  • Farawa 49:15
  • Matiyu 11:30
  • Matiyu 23:04

nema, yin nema, neman, dubi, neman

Ma'ana

Kalmar "nema" na nufin duban wani abu ko wani. idan ya riga ya wuce ana kiransa "nema". yana kuma iya zama "yin kokari sosai" ko "kokartawa" a yi wani abu.

  • Yin "nema" ko "dubawa" damar yin wani abu na iya zama kokarin samin" lokacin" yin abu.
  • "Neman Yahweh" na nufin "morar lokaci da karfi domin sanin Yahweh da kuma koyon yin biyayya da shi"
  • "Neman kariya" na nufin " yin kokarin samun wani ko wurin da zai kare ka daga haɗari."
  • "Neman adalci" na nufin "yin kokarin ganin cewa an yiwa mutane adalci da gaskiya".
  • "Neman gaskiya" na nufin yin kokarin gano yadda gaskiya take."
  • "Neman so" na nufin "kokarin samun so" ko " yin abin da zai sa wani ya taimake ka."

(Hakanan: adalci, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1Tarihi 10:14
  • Ayyukan Manzanni 17:26-27
  • Ibraniyawa 11:06
  • Luka 11:09
  • Zabura 027:08

nish, nishe-nishe, nisawa, yin nishi, yin nishe-nishe

Ma'ana

Kalmar nan "nishi" tana nufin yin wata 'yar ajiyarzuciya mai nauyi wadda kan samu a sakamakon wani al'amari ko dai zahirance ko kuma a cikin tunani ko kuma wata damuwa. Zai iya zama wani huci ne da wani ya fitar ba tare da waɗansu kalmomi ba.

  • Mutum kan iya nisawa a sakamokon alhini da yake ji a jikinsa.
  • Hakanan nisawa kan iya faruwa a sakamakon wani mummunan abin takaici ko wani hali na ƙuntatawa.
  • Waɗansu hanyoyi na fassara "nishi" sun haɗa da, yin ɗan kukan zuci na wahala" ko kuma matuƙar baƙin ciki."
  • A sunance, wanan zai iya zama "wani ɗan kuka ne sakamakon damuwa" ko kuma "wani babban gunaguni na wahala."

(Hakanan duba: kuka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 05:2
  • Ibraniyawa 13:17
  • Ayuba 23:2
  • Zabura 032:3-4
  • Zabura 102:5-6

numfashi, yin numfashi

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki "yin numfashi" da "numfashi" ana kamanta su da bada rai ko yana da rai.

  • Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Allah ya "hura a cikin" Adamu numfashin rai. A wannan lokacin ne Adamu ya zama rayayyen taliki.
  • Lokacin da Yesu ya busawa almajiransa numfashinsa ya ce su "karɓi Ruhu Mai Tsarki," watakila ya busa masu iska ne kawai a bisansu ya kwatanta zuwan Ruhu Mai Tsarki gare su.
  • Wani lokaci "shaƙar numfashi ciki" da "shaƙar numfashi waje" ana nufin yin magana ne.
  • Wannan misalin furci "numfashin Allah" ko "numfashin Yahweh" na nufin zubowar fushin Allah akan kangararru da mugayen al'ummai. Yana nuna ikonsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan furci "ya yi numfashinsa na ƙarshe" na cewa "ya mutu." Za a iya cewa kuma, "ya ja numfashinsa na ƙarshe" ko "ya dena numfashi ya mutu" ko "ya shaƙi iska sau ɗaya tak."
  • Fassara Nassi cewa "Allah ne ya hura" ana nufin Allah ya yi magana ko ya iza maganganun Nassi wanda mutane marubuta suka rubuta. Watakila yafi kyau, in ya yiwu a fassara "Allah ya hura" a sauƙaƙe tun da yana da wuyar a fassara ma'anar dai-dai.
  • Idan fassarar "Allah ya hura" bata karɓu ba, wasu hanyoyin fassarawa zai haɗa har da waɗannan "izawar Allah" "Allah marubuci" ko "Allah ya faɗi." Za a kuma iya cewa "Allah ne ya hura maganganunsa na Nassi."
  • Wannan furci "a sa numfashi a ciki" ko "a hura rai a ciki" ko "a bada numfashi ga" za a iya juya shi zuwa "a sa ya yi numfashi"' ko "a sa ya rayu kuma" ko "ya sa su rayu su yi numfashi" ko "bada rai ga."
  • Idan ya yiwu, zaifi kyau a fassara "numfashin Allah" da kalmar da aka yi amfani don "numfashi" a cikin yaren. Idan ba za a iya cewa Allah nada "numfashi," ba, za a iya fassarashi haka "ikon Allah" ko "furcin Allah."
  • Wannan magana "cafke numfashi na" ko karɓi numfashina" za a iya fassara shi haka "ka natsu domin kayi numfashi a hankali." ko "dena gudu domin ka yi numfashi yadda ya kamata."
  • Wannan furci "ɗan numfashin kaɗan ne" ma'anar shi ne "daɗewa na ɗan lokaci."
  • Haka kuma wannan furcin "mutum numfashinsa ɗaya ne kacal" ma'ana "rayuwar mutane na gajeren lokaci ne" ko "ran mutum na gajeren lokaci ne, kamar numfashi ɗaya ne" ko "idan an auna da Allah, ran mutum gajere ne kamar lokacin da ake ɗauka a shaƙi iska sau ɗaya."

(Hakanan duba: Adamu, Bulus, maganar Allah, rai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 17:17
  • Littafin Mai Wa'azi 08:08
  • Ayuba 04:09
  • Wahayin Yahaya 11:11
  • Wahayin Yahaya 13:15

raƙumi, raƙuma

Ma'ana

Raƙumi wani dabba ne, mai ƙafafu huɗu da tozo ɗaya ko biyu a bayansa.

  • A zamanin Littafi Mai Tsarki, raƙumi shi ne dabba mafi girma da ake samu a Isra'ila da lardunan kewaye.
  • Ana amfani da raƙumi musamman domin ɗaukar mutane da kaya.
  • Wasu ƙungiyoyin mutane suma suna amfani da raƙumi domin abinci amma ba Isra'ilawa ba saboda Allah ya ce raƙuma marasa tsabta ne kuma ba za a ci su ba.
  • Raƙuma masu daraja ne saboda zasu iya matsawa da sauri cikin yashi kuma zasu iya zama babu abinci da ruwa na tsawon makwonni da yawa a lokaci guda.

(Hakanan duba: nauyi, tsabta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 05:21
  • 2 Tarihi 09:1-2
  • Fitowa 09:1-4
  • Markus 10:25
  • Matiyu 03:04
  • Matiyu 19:23-24

Rami marar matuƙa

Ma'ana

Wannan furci "rami marar matuƙa" babban rami mai zurfi ne ko holoƙon rami da bashi da ƙarshe a zurfi .

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, "rami marar matuƙa" wurin hukunci ne.
  • Misali, idan Yesu ya umarci mugayen ruhohi su fita daga mutum, sukan roƙe shi kada ya aika da su rami marar matuƙa.
  • Kalmomin nan "rami marar matuƙa" za a iya juya su zuwa "ramin da babu ƙarshe" ko fili mai zurfi."
  • Wannan furci ya sha banban da "wuta," "lahira," ko "jahannama."

(Hakanan duba: Jahannama, lahira, horo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 08:30-31
  • Romawa 10:07

rami, ramuka, sanadin tuntuɓe, kududdufai

Ma'ana

Rami wuri ne mai zurfi da aka tona a ƙasa.

Mutane sukan haƙa rami saboda su kama dabbobi ko su sami ruwa.

  • Za a iya amfani da rami a riƙe ɗan yari na wani ɗan lokaci.
  • Wani lokaci wannan magana "rami" na nufin kabari ko lahira. Wasu lokuta kuwa zai iya zama "rami marar matuƙa."
  • Rami mai zurfi zai iya zama "ma'ajin ruwa."
  • Wannan kalma "rami" ana amfani da ita a cikin misali a maganganu haka "ramin hallaka" wannan ya fayyace cewa an faɗa cikin yanayi mai hallakarwa ko an shiga cikin zunubi da zurfi na ayyukan cutarwa.

(Hakanan: rami marar matuƙa, lahira, kurkuku)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 37:21-22
  • Ayuba 33:18
  • Luka 06:39
  • Littafin Misalai 01:12

ramuwa, ramawa, ramako

Ma'ana

Idan an yi "ramuwa" ko "ramawa" ko "ramako" dukka horo ne ake wa wani mutum domin a sãka mashi sabili da cutarwar da ya yi. Aikata ramuwa ko yin ramako shi ne "ramawa."

  • Yawancin lokaci "ramawa" ana yi domin a ga an yi adalci ko a gyara abin da ba a yi dai-dai ba.
  • Sa'ad da ake magana game da mutane furcin nan "ɗaukar ramuwa" ko "a ramawa wani" yawancin lokaci ana so a mayar da martani ne ga wanda ya yi cutarwa.
  • Sa'ad da Allah "ya yi ramuwa" ko "zartar da ramako" yana yi ne cikin adalci domin yana hukunta zunubi ne da tawaye.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan furci "a rama" wa wani mutum ana nufin "a gyara abin daba dai-dai ba" ko "a ga an yi adalci."
  • Sa'ad da ake magana game da mutane, "su yi ramuwa" za a fassara shi haka "biya kamar yadda ya yi" ko "ka cutar domin a hukunta" ko "mayar da martani."
  • Ya danganta da nassin, "ramuwa" za iya fassarata a ce "horo" ko "horo don zunubi" ko "biya domin yin abin da ba dai-dai ba." Idan an yi amfani da kalmar nan "ɗaukar fansa" mutane ne kaɗai za a faɗi haka a kansu.
  • Sa'ad da Allah yace "ɗaukar mani ramako," za a iya fassara shi haka, "ka horesu saboda laifin da suka yi gãba dani" ko "ka sa wani mugun abu ya faru domin sun yi zunubi gãba dani."
  • Sa'ad da ana magana akan ramuwar Allah, ku tabbatar cewa Allah yana da gaskiya da hukunta zunubi.

(Hakanan duba: horo, barata, adali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 24:12-13
  • Ezekiyel 25:15
  • Ishaya 47:3-5
  • Lebitikus 19:17-18
  • Zabura 018:47
  • Romawa 12:19

rana, ranaku, kwanaki

Ma'ana

Wannan kalma "rana" ana nufin wani lokaci na tsawon awa 24 idan an fara daga faɗuwar rana. Ana kuma yin amfani da ita wajen kwatanci.

  • Ga Isra'ilawa da Yahudawa "rana" takan soma da faɗuwar ranar, kuma ta ƙare a faɗuwar washegari.
  • Wani lokaci "rana" ana amfani da ita domin a misalta tsawon lokaci mai nisa, kamar "ranar Yahweh" ko "kwanakin ƙarshe."
  • Wasu yare za su yi amfani da wasu furci su fassara waɗannan misalan ko su fassara "rana" ba tare da bada misalai ba.
  • Wasu fassarar kalmar nan "rana" za a haɗa har da "lokaci" ko "yanayi" ko "sha'ani" ko "wani abin dake faruwa" ya danganta ga nassi.

(Hakanan duba: ranar hukunci, ranar ƙarshe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 20:06
  • Daniyel 10:04
  • Ezra 06:15
  • Ezra 06:19
  • Matiyu 09:15

rarrabawa, karkasawa, tarwatsawa, tarwatsatse, tarwatsatsu, rababbe

Ma'ana

Kalmar nan "rarrabawa" da "karkasawa"tana nufin warwatsa mutane ko abubuwa zuwa ɓangarori da bam da ban.

  • A cikin tsohon Alƙawari, Allah ya yi magana akan "warwatsa" mutane wanda ya sa su suka ware suka zauna nesa da juna ware kuma da juna a wurare mabambanta. Ya yi haka ne domin ya hore su sabo da zunubansu. Watakila wanan warwatsawar ta temake su su tuba su kuma juyowa bautar Allah.
  • Kalmar nan "rarrabawa" a cikin Sabon Alƙawari tana magana ne akan kan masubi da suka bar gidajensu suka karkasu zuwa wurare da bam da ban domin su tsira daga tsanani.
  • Ƙaulin nan "tarwatsawa" za'a iya fassara shi da tarwatsuwar masubi zuwa "wurare mabambanta" suka shiga ƙasashe da bamda ban."
  • Kalmar nan "karkasuwa" za'a iya fassara ta da gusawa zuwa wurare mabambanta" ko tura su zuwa manisantan wurare su "zauna a ƙasashe da bam da ban."

(Hakanan duba: caskata, tsanani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:01
  • Ezekiyel 12:15
  • Ezekiyel 30:23
  • Zabura 018:14

rarrabewa, aikin rarrabewa

Ma'ana

Kalmar nan "rarrabewa" tana nufin a iya fahimtar wani abu, musamman ta hanyar sanin abin daidai yake ko kuwa ba daidai ba.

  • Kalmar nan tantancewa na nufin fahimta da kuma ɗaukan madaidaicin mataki kan wani al'amari.
  • Tana nufin a zama da hikima da yanke hukunci da ya dace.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin "rarrabewa" za'a iya fassara ta da "ganewa" ko sanin bambanci tsakanin abu nagari da kuma mugu ko abin da ke dai-dai da wanda ba dai-dai ba"
  • Rarrabewa zai iya zama "ganewa" ko iya rarrabe "abu nagari da kuma mugu."

(Hakanan duba: alƙa, basira)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 03:7-9
  • Farawa 41:33-34
  • Misalai 01:05
  • Zabura 19:12

rashin biyayya, halin rashin biyayya, rashin biyayyar da aka yi, kalmar rashin biyayya, ƙin yin biyayya, tayarwa

Ma'ana

Kalmar nan "rashin biyayya" tana nufin ƙin yin biyayya ga wani da ke kan iko bisa ga abin da ya ummarta. Mutumin da ke da ya yi wanan shi ake kira "marar biyayya."

  • Mutumin da ya yi abin da aka faɗa masa ya yi ba marar biyayya ba ne.

Haka nan kin yin biyayya na nufin ƙin yin wani abu da aka ba mutum ummarni.

  • Kalmar rashin biyyaya ana moron ta a nuna halin wani mutum wanda ya kangare da gangan, wanan na nufin cewa su masu zunubi ne ko miyagu.
  • Kalmar nan "rashin biyayya" ma'anarta ita ce "hali na ƙin yin biyayya" "halaiya ce da ke gãba da abin da Allah ke so."
  • "Mutane marasa biyayya" mutane na fasarta su a matsayin "mutanen da ke yin rashin biyayya" ko "mutanen da ba su yin abin da Allah ya umarta."

(Hakanan duba: mulki, mugunta, zunubi, biyayya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 13:21
  • Ayyukan Manzanni 26:19
  • Kolosiyawa 03:07
  • Luka 01:17
  • Luka 06:49
  • Zabura 089:30-32

rataya, ratayewa, ratayayye, yin rataya ratayayyu, sagalalle

Ma'ana

Kalmar nan "rataya" tana nufin a dakatar da wani abu ko wani a bisa ƙasa.

  • Mutuwa ta wurin rataya akan yi wanan ne ta wurin morar igiya da akan sagala a wuyan mutum akuma sagale shi akan wani abu maitsayi kamar reshen bishiya.Yahuza ya kashe kansa ta wurin ratayewa.
  • Ko da yake Yesu ya mutu a lokacin da aka rataye shi a kan gicciyen gungume ba'a sa masa komai a wuya ba sojoji sun sagale shi ta wurin buga ƙusoshi a hannuwansa da ƙafafunsa akan gicciye.
  • A rataye wani har kullum yana nufin yadda ake kashe wani ta hanyar rataye su da igiya zarge da wuyansu.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 17:23
  • Ayyukan Manzanni 10:39
  • Galatiyawa 03:13
  • Farawa 40:22
  • Matiyu 27:3-5

ratsewa, sakin tafarfi, sa wani ya bar tafarki, rabuwa

Ma'ana

Waɗannan kalmomin "ratsewa" ko "barin hanya" ma'anarsu shi ne rashin biyayya ga Allah. Mutanen da ake "sa su su saki tafarki" suke sa waɗansu mutane ko wani dalili ya rinjaye su suyi rashin biyayya ga Allah.

  • Kalmar nan "ratsewa" yana nuna sakin tafarki mai kyau ko lafiyayyen wuri a tafi mugun wuri mai hatsari.
  • Tumaki dake barin makiyayar makiyayinsu sun "ratse." Allah ya kwatanta mutane masu zunubi da tumaki da suka bar shi suka "bi wata hanya."

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan faɗar "barin hanya" za a iya fassara ta a ce "juyawa daga Allah" ko "bin tafarkin da ba dai-dai ba nesa da nufin Allah" ko "daina biyayya da Allah" ko "rayuwa data nuna ratsewa daga Allah."
  • Idan an"ratsar da wani mutum daga tafarki" za a iya fassara shi haka "sa wani ya yi rashin biyayya ga Allah" ko "sa wani mutum ya bika zuwa tafarki marar dacewa."

(Hakanan duba: rashin biyayya, makiyayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 03:07
  • 2 Timoti 03:13
  • Fitowa 23:4-5
  • Ezekiyel 48:10-12
  • Matiyu 18:13
  • Matiyu 24:05
  • Zabura 058:03
  • Zabura 119:110

rawar jiki, yana rawar jiki, ya yi rawar jiki, tangaɗi

Ma'ana

"Rawar jiki" na ma'anar a girgiza ko a firgice domin tsoro ko zafin tsanantawa.

  • Wannan kalma ana amfani da ita a misali da ma'anar "jintsoro sosai."
  • Wasu lokuta sa'ad da ƙasa ke girgiza za a ce tayi "rawar jiki." Za a yi haka lokacin girgizar ƙasa ko babbar ƙara.
  • Littafi Mai Tsarki ya ce a gaban Ubangiji duniya na rawar jiki. Wannan zai iya nufin cewa mutanen duniya zasu girgiza cikin tsoron Allah ko kuma duniyar da kanta zata girgiza.
  • Wannan kalma za a iya fassara ta haka "aji tsoro" ko "tsoron Allah" ko "girgiza," ya danganta ga nassin.

(Hakanan duba: duniya, fear, Ubangiji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 07:15
  • 2 Sama'ila 22:44-46
  • Ayyukan Manzanni 16:29-31
  • Irmiya 05:22
  • Luka 08:47

reni

Ma'ana

Wannan kalma "reni" na nufin mummunar rashi girmamawa da wulaƙanci da ake nuna wa ga wani abu ko wani mutum. Wani abin da ake nuna masa gawuraccen rashin bangirma ana ce da shi "abin reni."

  • Mutum ko halaiya da ta nuna rashin bangirma ƙiri ƙiri ga Allah ana kiran wannan "reni" za a iya fassara shi haka "rashin kunya" ko "babu girmamawa ko kaɗan" ko "mai rashin hakali."
  • A "maida mutum abin reni" wato a maida wani mutum ba a bakin kome yake ba ko a aibata tawurin nunawa an fishi.
  • Waɗannan furci suna da kusan ma'ana ɗaya: "a yi wa mutum abin reni" ko "a aikata abin reni ga wani" ko "a cika da reni" ko "a yi abin reni." Waɗannan dukka suna nuna "mugun reni ko mummunar rashin ban girma ga wani abu ko ga wani mutum tawurin faɗar wani abu ko yin wani abu.
  • Lokacin da Sarki Dauda yayi zunubi tawurin zina da kisan kai, Allah ya ce Dauda ya "nuna reni ga Allah." Ma'ana, ya nuna mummunar rashin ban girma da rashi ɗaukaka Allah da abin da yayi.

(Hakanan duba: rashin girmamawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 12:1-2
  • Littafin Masalai 15:5-6
  • Zabura 031:18

riga 'yar ciki, shimi, shimaye, singileti, singilatai

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "riga 'yar ciki ko singileti" na nufin wata riga da ake sanyawa bisa fatar jiki, ƙarƙashin wasu suturun.

  • Riga 'yar ciki na kaiwa daga kafaɗu zuwa kwankwaso ko gwiwa kuma yawanci ana sanya ta da ɗamara wato bel. Ruguna 'yanciki da masu dukiya ke sanya wa wasu lokuta suna da hannu kuma har sukan kai idon ƙafa
  • Riguna 'yan ciki ana yin su ne da fata, suturun gashi, ulu, ko linin, kuma maza da mata na sanya wa.
  • Riga 'yar ciki dai ana sanya ta ne a ƙarƙashi doguwar riga, kamar su babbar riga ko alkyabba. A lokacin zafi wasu lokuta ana sanya riga 'yar ciki ba tare da sanya wata suturar ba a samanta.
  • Wannan kalma za a iya fassarata haka "doguwar riga" ko "doguwar shimi" ko "singilet" ko "singilet mai kamar riga." Za a kuma iya fassarata hanyar da aka fi sani "riga," tare da ɗan rubutun da zai yi bayanin irin suturar da ake nufi.

(Hakanan duba: alkyabba)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 03:21-23
  • Ishaya 22:21
  • Lebitikus 08:12-13
  • Luka 03:11
  • Markus 06:7-9
  • Matiyu 10:10

riga sani, sanin abu kafin ya faru

Ma'ana

Kalmar nan "riga sani" da "sanin abu kafin ya faru" sun zo ne daga kalmar aikatau wadda ke nuna saninwani abu kafin ya faru.

  • Allah ba shi da iyakar lokaci. Ya san komai da ke faruwa can baya, da yanzu, da kuma nan gaba.
  • Wanan kalmar akan fi yawan ambatonta game da Allah da ke da riga sanin wanda za'a ceta ta wurin karɓar Yesu a matsayin mai ceto.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "rigasani" za'a iya fassara ta da "sanin wani abu tun can baya" ko kuma "sani wani abu kafin faruwarsa" ko kuma "sanin wani abu kafin lokacinsa" ko kuma "abin da tuni aka sani" ko kuma "sanin abu a gabaninsa."

(Hakanan duba: sani, ƙaddara)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Romawa 08:29
  • Romawa 11:2

riga, riguna, suturcewa da riga

Ma'ana

Riga taguwa ce ta waje dake da dogon hannu namiji ko mace na iya sanyawa. Tana kama da kwat.

  • Riguna ana tsaga su daga gaba a kuma ɗaura su da abin kwalliya da maɗauri.
  • Suna iya zama da tsawo ko kajere.
  • Sarakuna na sanya riguna shunayya alamar sarauta, wadata da kuma daraja.

(Hakanan duba: sarauta, taguwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 28:4-5
  • Farawa 49:11-12
  • Luka 15:22
  • Luka 20:46
  • Matiyu 27:27-29

rimi, rimaye

Ma'ana

Itacen rimi, wani dogon itace ne mai inuwantarwa ga shi da kaurin jiki da rassa bazazzu ko'ina.

  • Itatuwan rimi, suna da tauri, ana amfani da su wajen gina jirage da kayan noma, gumaguman shanu da sandar tafiya.
  • Kwayar iri na rimi ana kiran sa akon.
  • Idan aka gwada kaurin jikin wasu itatuwan rimi za su kai mita 6 zagaye.
  • Ana yin kwatancin tsawon rai da itatuwan rimi, akwai kuma wasu ma'ana. A cikin Littafi mai Tsarki, yawancin lokaci ana gamasu da wurare masu tsarki.

Shawarwarin Fassara:

  • Juyi da yawa zasu fi ganin mahimmancin yin amfani da wannan magana "itacen oak" maimakon "oak" kawai.
  • Idan ba a ma san itatuwan rimi ba a wuraren masu fassara, za a iya fassara rimi a ce "babban itace mai bada inuwa..," sa'an nan a bada sunan wani sanannen itace mai kama da fassarar.

(Hakanan duba: tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 10:3-4
  • Farawa 13:18
  • Farawa 14:13-14
  • Farawa 35:4-5
  • Littafin Alƙalai 06:11-12

roƙo, maroƙi, mabaraci, mabuƙaci

Ma'ana

Wannan kalma "roƙo" ma'anarta shi ne tambayar wani domin ya bada wani abu. Yawancin lokaci domin a sami kuɗi ne, amma kuma ana roƙo don wasu abubuwan.

  • Sau da yawa mutane sunkan yi roƙo lokacin da lallai suke buƙatar wani abu, amma ba su sani ko mutumin nan zai basu abin da suke roƙo ba.
  • "Mabaraci" mutum ne da kullum yakan zauna ko ya tsaya a inda mutane suke domin ya roƙe su kuɗi.
  • Ya danganta da nassin, za a iya fasara wannan kalma haka "nacewa da roƙo" ko "'yin tambaya nan da nan" ko "matsawa a bada kuɗi" ko "roƙon kuɗi akai-akai."

(Hakanan duba: roƙo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 16:20
  • Markus 06:56
  • Matiyu 14:36
  • Zabura 045:12-13

ruɗi, ruɗa, ruɗu ruɗuwa, yaudara, mayaudari, mayaudara, na yaudara, na yaudararwa, halin yaudara, tafarkin yaudara, yaudararre, zamba

Ma'ana

Wannan kalma "Yaudara" tana nufin a sa wani ya yi imani akan abin da ba gaskiya ba. yin ƙoƙarin yaudarar wani shi ake kira "yaudara"

  • Wani bayani kuma shine "ruɗi" shima an ganins akan son sa wani ne ya yi imani da abin da ba gaskiya ba.
  • Wani ya sa waɗansu su yi imani da abin da ƙarya, wannan "mayaudari ne" Misali, sheɗan ana kiransa "mayaudari" hakanan miyagun ruhohi da yake mulkinsu suma ana kiran su "mayaudara"
  • Aikin wani mutum ko kuma saƙonsa da ba na gaskiya ba ana iya baiyana shi a matsayin na "yaudara"
  • Kalmar nan ruɗi da hila duk ma'anarsu ɗaya ce, amma akwai 'yan bambance bambance kaɗan akan yadda ake amfani da su.
  • Halin yaudara shi ne yaudara kuma duk ma'anarsu ɗaya ce kuma ana amfani da su a wuri ɗaya.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyin yin fassara da za a fasarta yaudara za su iya haɗawa da "yaudara" sun kuma haɗa da yin "ƙarya ga wani."
  • Kalmar "yaudara" har yanzu tana nufin a fassara ta da cewa "a sa wani ya yi tunani abin da ke na ƙarya" ko a yiwa wani "ƙarya" ko a bad da wani, ko a "zolayi" wani.
  • Ana iya fassara mayaudari a matsayin "maƙaryaci ko Wani mai "ɓad da mutane" ko "mai yin yaudara."
  • Ya danganta dai ga abin da ke rubuce a wurin da ke nuna halin Yaudara ko kuma ƙarya."
  • Kalmar nan halin yaudara na nufin akin yaudara,ko kuma rashin gaskiya ko "karkatarwa", ko yin "ƙarya" mai halin yaudara mutum ne da ke yin magana ko magana ta hanyar da kan sa waɗansu su gaskata da abn da ba gaskiya ba.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 01:08
  • 1 Timoti 02:14
  • 2 Tasalonikawa 02:3-4
  • Farawa 03:12-13
  • Lebitikus 19:11-12
  • Matiyu 27:64
  • Mika 06:11

rumbu, rumbuna

Ma'ana

"Rumbu" wani babban gini ne da ake amfani da shi don ajiye abinci ko waɗansu abubuwa, a kowanne lokaci na wani tsawon lokaci.

  • A Littafi Mai Tsarki, "rumbu" anyi amfani da shi don ajiye hatsi da sauran abinci don a yi amfani dasu nan gaba idan akwai yunwa.
  • An yi ta amfani da wannan kalma don nuna abubuwa masu kyau da Allah yake so ya ba mutanensa.
  • Rumbunan haikali na ɗauke da abubuwa masu daraja da aka keɓewa Yahweh, kamar su zinariya da azurfa. Waɗansu daga cikin waɗannan abubuwan an yi amfani da su a gyara da kuma killace haikali duk an ajiye su anan.
  • Waɗansu hanyoyin fassara "rumbu" sun haɗa da, "gini domin ajiye hatsi" ko "wurin ajiye abinci" ko "ɗakin ajiye abubuwa masu daraja."

(Hakanan duba: tsarkake, keɓewa, yunwa, zinariya, hatsi, azurfa, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 16:2-3
  • Luka 03:17
  • Matiyu 03:13
  • Zabura 033:07

rumfa, rumfuna, masu yin rumfa

Ma'ana

Rumfa madaidaicin mahalli ne wanda ake yi da tufafi mai ƙarfi wanda ake ɗaurawa jikin turaku a manne da su.

  • Rumfuna zasu iya zama ƙanana, da ɗan sararin da zai ishi mutane kaɗan su kwanta a ciki, ko kuma suna iya zama manya sosai, da sarari da zai ishi iyali bakiɗaya su kwana a ciki, suyi girki, su kuma zauna ciki.
  • Ga mutane da yawa, rumfuna ana amfani dasu a matsayin wuraren zama na din-dindin. A misali, yawancin lokutan da Ibrahim da iyalinsa suka zauna a ƙasar Kan'ana, sun zauna a manyan rumfuna a aka yi da tufafi masu ƙarfi da aka yi da gashin akuya.
  • Isra'ilawa suma sunyi zama a rumfuna a lokacin yawonsu na shekaru arba'in cikin jejin Sinai.
  • Ginin rumfar sujada wani irin babbar rumfa ne, da bangaye masu kauri da aka yi da tufafin labulai.
  • Sa'ad da manzo Bulus ya yi ta tafiya zuwa birane yana watsa bishara, ya yi ta taimaka wa kansa ta wurin sana'ar yin rumfuna.
  • Kalmar "rumfuna" wasu lokuta ana amfani da ita a misali da nufin inda mutane suke zama. Za a iya kuma fassara wannan haka "gidajen iyalai" ko "mahallai" ko "gidaje" ko kuma "rukunai."

(Hakanan duba: Ibrahim, Kan'ana, labule, Bulus, Sinai, rumfar sujada, rumfar taruwa)

  • Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
  • 1 Tarihi 05:10
  • Daniyel 11:45
  • Fitowa 16:18
  • Farawa 12:09

rumfar taruwa

Ma'ana

Kalmar "rumfar taruwa" na nufin wata rumfa ce wadda aka kafa na ɗan lokaci inda Allah ke haɗuwa da Musa kafin a kafa rumfar sujada.

  • An kafa rumfar taruwa waje da sansanin Isra'ilawa.
  • Sa'ad da Musa ya shiga rumfar taruwa domin ya gamu da Allah, ginshikin girgije zai tsaya a bakin kofar shiga rumfar a matsayin alamar kasancewar Allah a wurin.
  • Bayan da Isra'ilawa suka kafa rumfar sujada, waccan rumfar ba a buƙatar ta kuma sai kalmar "rumfar taruwa" wasu lokuta ana amfani da ita da nufin rumfar sujada.

(Hakanan duba: Isra'ila, Musa, ginshiƙi, rumfar sujada, rumfa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 02:28-29
  • Yoshuwa 19:51
  • Lebitikus 01:02
  • Littafin Lissafi 04:31-32

rumman, manta uwa

Ma'ana

Rumman ko manta uwa wani irin 'ya'yan ice ne dake da ɓawo mai kauri, da fata mai tauri cike da 'ya'ya lulluɓe da jar tsoka da ake ci.

  • Ɓ‌awonsa ja-ja ne kuma tsokar data lulluɓe ƙwayoyin na da kyalli kuma ja ne.
  • An fi noman rummam ko manta uwa a ƙashashen da suke da busasshen yanayi mai zafi kamar Masar da Isra'ila.
  • Yahweh ya yi alƙawari ga Isra'ilawa cewa Ka'ana ƙasa ce mai gudana da ruwa da tãki ga kuma abinci da yawa a can, har ma da rumman ko manta uwa.
  • A ginin haikalin Suleman an haɗa da adon tagulla a siffar rumman.

(Hakanan duba: tagulla, Kan'ana, Masar, Suleman, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 25:16-17
  • Maimaitawar Shari'a 08:7-8
  • Irmiya 52:22-23
  • Littafin ‌Lissafi 13:23-24
  • Littafin ‌Lissafi 20:5

rusunawa, sujada, faɗuwa ƙasa rub da ciki

Ma'ana

Wannan magana "rusunawa" na nufin kwanciya da fuska ƙasa, a miƙe a ƙasa.

  • "A faɗi a rusuna" a gaban wani shi ne a sunkuya nan da nan ƙasa sosai a gaban wani mutum.
  • Yawancin lokaci ana rusunawa saboda tsorata ne, mamaki, da bangirma, saboda wani abin al'ajibi ya faru. Yana kuma nuna girmamawa da darajanta mutumin da aka sunkuya wa.
  • Rusunawa wata hanya ce ta yiwa Allah sujada.

Yawancin lokaci mutane suna yiwa Yesu haka domin godiya da sujada lokacin da ya yi abin al'ajibi ko domin su girmama shi a matsayin babban malami.

  • Ya danganta ga nassi, wasu hanyoyin fassara "rusunawa" za a haɗa da waɗannan, "sunkuyawa ƙasa da fuska har ƙasa" ko "yi masa sujada ta wurin kwanciya da fuska ƙasa a gabansa" ko "sunkuyawa ƙasa don mamaki" ko "sujada."
  • Wannan furci "ba zamu rusuna kanmu ba" za a iya fassarawa haka, "ba za muyi sujada ba" ko "ba zamu kwanta da fuskoki ƙasa muyi sujada ba" ko "ba zamu rusuna mu yi sujada ba."
  • "Ya rusuna wa" za a iya fassara wannan haka, "yin sujada" ko 'sunkuyawa a gabansa."

(Hakanan duba: jin tsoro da girmamawa, sunkuyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 17:36-38
  • Farawa 43:28
  • Wahayin Yahaya19:3-4

ruwa, ruwaye, ban ruwa, jiƙawa

Ma'ana

Ƙãri bisa asalin ma'anar, "ruwa" na nufin ruwa mai yawa kamar teku, tafki ko kogi.

  • Kalmar "ruwaye" na nufin tattaruwar ruwa ko maɓulɓulan ruwa masu yawa. Yana kuma iya zama da manufar babban tattaruwar ruwa.
  • A misalce amfani da kalmar "ruwaye" na nufin wuya mai girma, wahaloli, da shan wuya. Ga misali, Allah ya yi alƙawari cewa sa'ad da muka "bi ta cikin ruwa" za shi kasance tare da mu.
  • Faɗar "ruwaye masu yawa" na nuna girmar wahalhalun.
  • Ayi "ban ruwan" garke da sauran dabbobi na nufin "yin tanadin ruwa domin su." A zamanin Littafi Mai Tsarki, akan ɗebi ruwa ne daga rijiya ta yin amfani da guga tare da bokati a kuma zuba ruwan cikin kwami ko matarin ruwa domin dabbobi su sha daga nan.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, ana ce da Allah magudanar "ruwan rai" domin mutanensa. Wannan na nufin da cewa shi ne tushen iko na ruhaniya da wartsakewa.
  • A cikin Sabon Alƙawari, Yesu ya mori kalma "ruwan rai" na manufar aikin Ruhu Mai Tsarki a rayuwar mutum domin canza shi ya kuma kawo sabon rai.

Shawarwarin Fassara:

  • Faɗar "jawo ruwa" za a iya fassarawa haka "jawo ruwa sama daga cikin rijiya da bokiti."
  • "Maɓulɓulan ruwan rai zasu malalo daga gare su" za a iya fassarawa haka "iko da albarku daga Ruhu Mai Tsarki zasu malalo daga gare su kamar maɓulɓulan ruwa." A maimakon "albarku" kalmar "baye-baye" ko "'ya'yan itatuwa" ko "halayen kirki" za a iya amfani da haka.
  • Sa'ad da Yesu yake magana da matar nan ta Samariya a bakin rijiya, faɗar "ruwan rai" za a iya fassarawa haka "ruwan dake bayar da rai." A cikin wannan nassin, dole a riƙe tunanin ruwa a cikin fassarar.
  • Ya danganta da nassin, kalmar "ruwaye" ko "ruwaye da yawa" za a iya fassarawa haka "babbar wahala (da ta kewaye ka kamar ruwa)" ko "wahala mai mamayewa (kamar ambaliyar ruwa)" ko "babban tattaruwar ruwa."

(Hakanan duba: rai, ruhu, Ruhu Mai Tsarki, iko)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08:36-38
  • Fitowa 14:21
  • Yahaya 04:10
  • Yahaya 04:14
  • Yahaya 04:15
  • Matiyu 14:28-30

ruwan inabi, ruwayen inabi, salkar ruwan inabi, salkunan ruwan inabi, sabon ruwan inabi

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "ruwan inabi" abin sha ne da ya yi tsima yayi tsami da kumfa da aka yi daga ruwan 'ya'yan itacen inabi. Ruwan inabi akan adana shi cikin "salkar ruwan inabi," waɗanda aka yin su da fatar dabba.

  • Kalmar "sabon ruwan inabi" abin sha ne da aka matse daɗewa ba daga itacen inabi da ba a ajiye shi ya tsima ya yi tsami da kumfa ba.
  • Idan za a yi ruwan inabi, ruwan 'ya'yan itacen inabi ake matsewa a matatsar inabi domin ruwan ya fito. Ruwan inabin daga baya zai tsima sai kuma ya zama giya mai bugarwa.
  • A zamanin Littafi Mai Tsarki, ruwan inabi kamar ruwan da ake sha ne a yau da abinci. Babu bugarwa cikinsa ba kamar ruwan inabin yau ba.
  • Kamin a raba abinci da ruwan inabi, akan gauraya ruwan inabin da ruwa.
  • Salkar ruwan inabin da ta tsufa ta kuma yi tsatsa zata sami tsaga cikinta, da haka kuma ruwan inabin na iya zubewa. Sabon salkar ruwan inabi na da laushi, wannan ya nuna basu fashewa da sauri zasu kuma riƙe ruwan inabi babu matsala.
  • Idan ba a san ruwan inabi ba a al'adarku, za a iya fassarawa a matsayin "ruwan 'ya'yan itace da ya tsima."
  • Hanyoyin fassara "salkar ruwan inabi" zasu haɗa da "jaka domin ruwan inabi" ko "jakar ruwan inabi ta fatar dabba" ko "gudauniyar fatar dabba domin ruwan inabi."

(Hakanan duba: inabi, itacen inabi, gonar inabi, matatsar inabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 05:23
  • Farawa 09:21
  • Farawa 49:12
  • Yahaya 02:3-5
  • Yahaya 02:10
  • Matiyu 09:17
  • Matiyu 11:18

sa'a, sa'o'i

Ma'ana

Buga da ƙari ana magana ne don a nuna yadda da kuma tsawon lokacin da wani abu ya faru "sa'a" an more ta ta hanyoyin salon magana:

  • A waɗansu lokuta "sa'a" na nufin tsararren lokaci da aka ƙayyade, kamar "sa'ar addu'a."
  • Sa'ad da littafi ya ambaci "lokaci ya yi" da Yesu zai sha tsanani a kuma kash shi, wannan na nufin wannan ne lokacin da aka ƙayyade domin wannan ya faru tun dogon lokaci.
  • Kailmar nan "sa'a" kuma ana moron ta domin nuna "a wancan lokaci" ko "dai-dai wannan sa'ar."
  • Lokacin da aka yi magana game da "sa'a" ta makara, wannan na nufin cewa lokcin ya wuce a wannan ranar lokacin da rana zata gau-gauta faɗuwa.

Shawarwarin Fassara:

  • Lokacin da aka mori salon magana a "sa'a" za'a iya fassara ta da "lokaci" "damar" ko "lokacin da aka ƙayyade."
  • Kalmar nan "a wannan "sa'a" ko "a wannan dai sa'a" ko "nan da nan" ko ana nan."
  • Ƙaulin nan cewa "sa'ar ta ƙure" za'a iya fassara ta "bayan da yamma ta yi" "nan da nan duhu zai yi."

(Hakanan duba: sa'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 15:30
  • Ayyukan Manzanni 10:30
  • Markus 14:35

sa'a, sa'o'i, lokaci, nan da nan, har wani lokaci

Ma'ana

Wannan kalma "sa'a" ana amfani da ita a Littafi Mai Tsarki yawancin lokaci domin a faɗi wane lokaci ne a ranar abin nan ya faru. Ana kuma amfani da ita da ma'anar "lokaci" ko "yanzun nan."

  • Yahudawa suna ƙirga sa'o'in yini daga ɗagawar rana (misalin karfe 6 na safe). Misali, " sa'a ta tara" ma'ana "misalin ƙarfe uku na rana."
  • Sa'o'in dare ana ƙirga su daga faɗuwar rana (misalin ƙarfe 6 na yamma). Misali, "sa'a ta uku na dare" na nufin "kusan tara ne da yamma" a yanayinmu na yau.
  • Tunda lokaci a cikin Litafi Mai Tsarki ba zai yi dai-dai tsab da na duniyarmu yanzu ba, furci kamar "wajen ƙarfe tara" ko "wajen ƙarfe shida" za a iya amfani da su.
  • Wasu juyin za su iya ƙara magana haka "da yamma" ko "da safe" ko "da rana" domin a sani sosai wane lokaci ne da rana ake magana akai.
  • Wannan furci, "a wannan sa'a"' za a fassarata haka "a lokacin nan" ko "a wannan sa'ar."
  • Game da Yesu, wannan furci "sa'arsa ta zo" za a iya fassara shi haka, "lokaci ya zo da zai" ko "ƙayyadadden lokaci dominsa ya zo."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:15
  • Yahaya 04:51-52
  • Luka 23:44
  • Matiyu 20:03

sabon wata, sabobbin watanni

Ma'ana

Wannan magana "sabon wata" ana nufin lokacin da wata ya ke ɗan karami kamar siffar ruwan lauje mai hasken azurfa. Wannan shi ne farkon fuskar wata sa'ad da yake tafiya kan hanyarsa yana zagaye duniya a faɗuwar rana. Ana kuma nufin rana ta fari da ake fara ganin sabon wata bayan wata ya duhunta na 'yan kwanaki.

  • A zamanin dã, sabobbin watanni suna nuna farkon wasu lokatai ne kamar su watanni.
  • Isra'ilawa sun yi idin sabon wata wanda sukan busa ƙahon rago.
  • Littafi Mai Tsarki kuma ya ambaci wannan lokaci haka, "farkon wata."

(Hakanan duba: wata, duniya, idi, ƙaho, tumaki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 23:31
  • 1 Sama'ila 20:05
  • 2 Sarakuna 04:23-24
  • Ezekiyel 45:16-17
  • Ishaya 01:12-13

Sadaka

Ma'ana

Wannan kalma "sadaka" yana magana ne akan kuɗi, abinci, ko abin da ake bayarwa domin a taimaki mutane matalauta.

  • Yawancin lokaci bada sadaka wani abu ne da mutane ke ganin cewa addininsu ya umarta ayi saboda a zama da adalci.
  • Yesu ya ce kada a bada sadaka a fili domin kada wasu mutane su gani.
  • Wannan kalmar za a iya fassara ta haka "kuɗi" ko " kyauta ga mutane matalauta" ko "taimako ga matalauta."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 03:1-3
  • Matiyu 06:01
  • Matiyu 06:03

sadaukar da kai, ana sadaukar da kai, an sadaukar da kai, miƙa kai, cikin sadaukar da kai

Ma'ana

"Sadaukar da kai" da ma tana nufin sa wani ƙarƙashi ikon shugabancin wani.

  • Littafi Mai Tsarki ya gayawa masu bada gaskiya ga Yesu su yi biyayya ga Allah da kuma sauran ikoki a rayuwarsu.
  • Umarnin "sadaukar ga kai da juna" na nufin a iya yarda da gyara cikin nadama a kuma mai da hankali ga buƙatun waɗansu fiye da buƙatar kanmu.
  • A "rayu cikin sadaukar da kai ga wani" na nufin sa wani ƙarƙashin ikon wani abu ko wani.

Shawarwarin Fassara:

  • Umarnin "sadaukar da kai" za a iya fassara shi da "sa kanka ƙarƙashin ikon" ko "bin shugabancin" ko "girmamawa cikin tawali'u da darajantawa."
  • Kalmar "sadaukar da kai" akan iya fassara ta da "biyayya" ko" bin iko."
  • Kalmar "ku zauna cikin sadaukar da kai ga" za'a iya fassara shi da " zama da biyayya ga" ko "sa wani a ƙarƙashin ikon wani."
  • Kalmar "zama da sadaukar da kai" za a iya fassara shi da "yarda da iko."

(Hakanan duba: mai bin)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 14:34-36
  • 1 Bitrus 03:01
  • Ibraniyawa 13:15-17
  • Luka 10:20

salama, masu sulhu

Ma'ana

Wannan kalma "salama" na nufin yanayi ne na jin babu wata matsala, damuwa ko tsoratarwa. Mutum mai "salama" yana da natsuwa kuma yana da tabbacin yana tsare babu abin cutarwa.

  • "Salama" kuma na nufin lokacin da ƙungiyar mutane ko ƙasashe basa cikin yaƙi da junansu. Akan ce waɗannan mutane suna da "zumunci ta salama a tsakaninsu."
  • Idan an "shirya salama" da mutum ko ƙungiyar mutane ana nufin an ɗauki mataki domin a tsaida faɗa a tsakaninsu.
  • A "zauna lafiya" da dukkan mutane, shi ne kasancewa tare babu tashin hankali da wasu mutane.
  • Dangantaka tsakanin Allah da mutane yakan faru sa'ad da Allah ya ceci mutane daga zunubansu. Ana ce da wannan "salama da Allah."
  • Wannan gaisuwa "alheri da salama" manzanni sun yi amfani da ita cikin wasiƙunsu zuwa ga 'yan'uwa cikin bangaskiya sakamakon albarka.
  • Wannan kalma "salama" tana kuma nuna sahihiyar dangantaka da sauran mutane da kuma Allah.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 05:1-3
  • Ayyukan Manzanni 07:26
  • Kolosiyawa 01:18-20
  • Kolosiyawa 03:15
  • Galatiyawa 05:23
  • Luka 07:50
  • Luka 02:51
  • Markus 04:39
  • Matiyu 05:09
  • Matiyu 10:13

sananne, an sanar da shi, yin suna

Ma'ana

Kalmar "sananne" tana nufin girman dake tattare da a san abu da kuma samun halin yabo. Wani abu ko wani "sananne ne" idan kowa ya san da shi.

  • "Sanannen" mutum wani ne wanda aka san shi ana kuma girmama shi.
  • "Sananne" na ma'anar yin suna da ya bazu a ko'ina mai daɗin suna na tsawon lokaci.
  • "Sanannen" birni ya yi fice wurin arziki da wadata.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "sananne" za a iya kuma fassarawa haka "yin suna" ko "darjantawa" ko "girman da ya zama sannanne ga mutane da yawa."
  • Kalmar "sananne" za a iya fassarawa haka "sananne kuma an darjanta" ko "yin kyakkyawan suna."
  • Faɗar "Bari sunan Ubangiji ya zama sananne a Isra'ila" za a iya fassarawa haka "Bari sunan Ubangiji ya zama sananne da daraja ga mutanen Isra'ila."
  • Faɗar "sanannnun mutane" za a iya fassarawa haka "mutanen da aka san su wurin ƙarfin halinsu" ko "sanannun mayaƙa" ko "mutanen da ake girmamawa sosai."
  • Faɗar "sanin ka ya zarce dukkan tsararraki" za a iya fassarawa haka "cikin dukkan shekaru mutane zasu ji yadda girman ka yake" ko "mutanen dukkan tsararraki sunji kuma sunga girmanka."

(Hakanan duba: daraja)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 06:4
  • Zabura 135:12-14

sanda, sanduna

Ma'ana

kalmar "sanda" wani itace ce miƙaƙƙe mai kauri da ake amfani da shii ta hanyoyi daban-daban. Ta kai kamar mita ɗaya a tsayi.

  • Makiyaya na amfani da sandar itace don tsare garke daga wasu dabbobin. Ana kuma jefa ta ga tunkiyar da ta bijire domin a maido cikin garken.
  • A Zabura 23, sarki Dauda ya yi amfani da kalmomin "sanda" da "kere" domin ya nuna bishewar Allah da kuma horarwarsa ga mutanensa.
  • Sandar makiyayi akan yi amfani da ita wajen kirgen tumaki yayin da suke wucewa daga ƙarƙashin ta.
  • Akan ce da ita "sandar ƙarfe," ma'ana, Allah na horar da mutane masu tawaye da shi suna kuma aikata mugunta.
  • A zamanin dã, sandar ma'auni na ƙarfe, itace, ko dutse akan yi amfani da su a gwada tsawon gini ko wani abu.
  • A Littafi Mai Tsarki, sandar itace ana ce da ita kayan aiki na horon yara.

(Hakanan duba: kere, tumaki, makiyayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 04:21
  • 1 Sama'ila 14:43-44
  • Ayyukan Manzanni 16:23
  • Fitowa 27:9-10
  • Wahayin Yahaya 11:01

sanda, sanduna, kere

Ma'ana

Sanda wani dogon itace ne ko kulki da ake amfani da ita domin tafiya.

  • Lokacin da Yakubu ya tsufa, ya yi amfani da sanda domin ta taimake shi yin tafiya.
  • Allah ya maida sandar Musa maciji domin ya nuna ikonsa ga Fir'auna.
  • Makiyaya ma na amfani da sanda domin su iya kula da tumakinsu, ko su kare su idan sun faɗi ko sun watse.
  • Sandar makiyayi tana da lankwasa a kanta, don ta banbanta da kulkin makiyayi, da yake a miƙe kuma ana amfani da shi ne wajen kashe dabbobin daji da suke ƙoƙarin su farmaki tumakin.

(Hakanan duba: Fir'auna, iko, tumaki, makiyayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 04:1-3
  • Fitowa 07:09
  • Luka 09:03
  • Markus 06:7-9
  • Matiyu 10:8-10
  • Matiyu 27:29

sandar sarauta, sandunan sarauta

Ma'ana

"Sandar sarauta" sanda ce wadda shugaba, kamar sarki ke riƙe wa a hannu.

  • Sandar sarauta asali reshen itace ne da ake yiwa sassakar ãdo. Daga baya sandunan sarauta ana yinsu da duwatsu masu daraja kamar zinariya.
  • Sanda alama ce ta sarauta da iko tana kuma nuna girma da darajar dake tattare da sarki.
  • A Tsohon Alƙawari, an kamanta Allah da riƙe da sandar sarauta na adalci domin Allah na mulki bisa mutanensa.
  • Wani annabci daga Tsohon Alƙawari na bayyana Mai Ceto kamar alamar sandar sarautar da zai fito daga Isra'ila ya yi shugabancin al'ummai.
  • Wannan ana iya fassarawa haka "sandar mulki" ko "sandar sarki."

(Hakanan duba: iko, Almasihu, sarki, adalci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Amos 01:5
  • Esta 04:11
  • Farawa 49:10
  • Ibraniyawa 01:08
  • Littafin Lissafi 21:18
  • Zabura 045:06

sani, sanin, Ilimi, sananne, bada sani, sanin gaba, Ilimin gaba

Ma'ana

"A sani" na ma'anar a fahimci wani abu ko ayi la'akari da abu zahiri. Faɗin "bada sani" faɗi ne dake ma'anar faɗar bayyana labari.

  • Kalmar "ilimi" na nufin bayyana labari da mutane suka sani. Yana iya nufin sanin abubuwa a duniyoyin zahiri da na ruhaniya dukka.
  • "sani game da" Allah na ma'ana fahimtar al'amura game da shi saboda abin da ya bayyana mana.
  • "A san" Allah na ma'anar a kasance da zumunci tare da shi. Wannan ma ya haɗa da sanin mutane.
  • A san nufin Allah na ma'anar a san abin da ya dokatar, ko a fahimci abin da Allah yake so wani taliki yayi.
  • "A san shari'a" na ma'anar a faɗaka da abin da Allah ya dokatar ko a fahimci abin da Allah ya umarta a cikin shari'ar da yaba Musa.
  • Wasu lokutta "ilimi" ana amfani da shi a madadin "hikima," wanda ya haɗa da yin rayuwa ta hanyar da ta gamshi Allah.
  • "Sanin Allah" wasu lokutta ana amfani da shi a mamadin "tsoron Yahweh."

Shawarwarin Fassara:

  • Bisa ga nassin. hanyoyin fassara "sani" zasu haɗa da "fahimta" ko "ganewa da" ko "faɗaka da" ko "sabawa da" ko "kasancewa cikin zumunci da."
  • Wasu harsunan suna da kalmomi biyu daban domin "sani," ɗaya domin sanin al'amura ɗaya kuma domin sanin wani taliki da kasancewa cikin zumunta da shi.
  • Kalmar "bada sani" ana iya fassarawa a matsayin "sanya mutane su sani" ko "bayyanawa" ko "faɗi game da" ko "yin bayani."
  • A "sani game da" wani lokaci ana iya fassarawa a matsayin "a faɗaka da" ko "a saba da."
  • Faɗar "a san yadda za'a" na ma'anar a fahimci matakai ko hanyoyin samun aiwatar da wani abu. Ana iya kuma fassarawa a matsayin "iya aiwatar da" ko "samun dabarar yin."
  • Kalmar "ilimi" ana iya fassarawa a matsayin "abin da aka sani" ko "hikima" ko "fahimta," ya danganta da nassin.

(Hakanan duba: shari'a, bayyana, fahimta, wayau)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 02:12-13
  • 1 Sama'ila 17:46
  • 2 Korintiyawa 02:15
  • 2 Bitrus 01:3-4
  • Maimaitawar Shari'a 04:39-40
  • Farawa 19:05
  • Luka 01:77

saniya, ɗan maraƙi, bijimi, shanu

Ma'ana

Wannan kalma, "shanu" sunan wasu irin manyan dabbobi ne, masu ƙafafu hurhuɗu dabbobin gona ne masu cin ciyawa kuma ana kiwonsu musamman domin nama da madararsu.

  • Ta macen irin wannan dabbar ana ce da ita "saniya," na mijin kuma "bijimi," ɗansu kuma "ɗan maraƙi."
  • Wani lokaci wannan kalma "shanu" ana kiran dukkan ire iren dabbobi da shi.
  • A wasu al'adu, ana musayan shanu wajen cinikaiya da kayayyaki. Wani lokaci ana amfani da su wajen yin kyauta da su ga iyayen yarinyar da namiji yake so ya aura.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, mutanen Yahudawa sukan yi amfani da shanu domin yin hadaya, musamman wani iri da ake ce da shi jar karsana.
  • "Jar karsana" wata saniya ce da bata haihu ba tukuna.
  • "Sã" wani irin bijimi ne musamman da ake amfani da shi wajen aikin gona, misali, jan garmar huɗa.

(Hakanan duba: karkiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 15:9-11
  • Fitowa 24:5-6
  • Littafin Lissafi 19:1-2
  • Maimaitawar Shari'a 21:3-4
  • 1 Sama'ila 01:24-25
  • 1 Sama'ila 15:03
  • 1 Sama'ila 16:2-3
  • 1 Sarakuna 01:09
  • 2 Tarihi 11:15
  • 2 Tarihi 15:10-11
  • Matiyu 22:4
  • Luka 13:15
  • Luka 14:05
  • Ibraniyawa 09:13

sarauniya, sarauniyoyi

Ma'ana

Sarauniya ita ce mai mulkin ƙasa ko kuma matar sarki.

  • Esta ta zama sarauniyar mulkin Fasiya da ta auri Sarki Ahasuros.
  • Sarauniya Yezebel muguwar matar Sarki Ahab ce.
  • Sarauniya Sheba wata shahararriyar mai mulki ce wadda ta kawo wa Sarki Suleman ziyara.
  • Furci kamar haka "uwar sarauniya" ana nufin uwa ko kakar sarki mai mulki ko gwauruwar sarki da bai daɗe da rasuwa ba. Uwar sarki tana da iko sosai; Ataliya, misali, ta sa mutane suka yi sujada ga gumaku.

(Hakanan duba: Ahasurus, Ataliya, Esta, sarki, Fasiya, mai mulki, Sheba)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 10:10
  • 1 Sarakuna 11:18-19
  • 2 Sarakuna 10:12-14
  • Ayyukan Manzanni 08:27
  • Esta 01:17
  • Luka 11:31
  • Matiyu 12:42

sarewa, sarewu, kwaekwaro, kwarakwari

Ma'ana

A kwanakin Littafi Mai Tsarki, kwarakwarai su ne kayan waƙe-waƙe waɗanda aka yi da ƙashi ko itace da ramummukan da za su sa ƙara ta fito waje. sarewa wani irin kwarkwaro ne.

  • Kwarakwarai da yawa na da waɗansu 'yan ciyayi masu ƙarfi da ke kyarma a lokacin da iska ta bi ta kansa.
  • Duk wani kwarkwaro mara komai a ciki shi ake kira "sarewa"
  • Makiyayi kan hura kwaekwaro domin tsayar da garken tumakinsa.
  • Ana amfani da kwarkwaro ko sarewa domin yin waƙoƙin farin ciki ko na baƙin ciki.

(Hakanan duba: garke, makiyayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 14:7
  • 1 Sarakuna 01:38-40
  • Daniyel 03:3-5
  • Luka 07:31-32
  • Matiyu 09:23
  • Matiyu 11:17

sarki, sarakuna

Ma'ana

Wannan kalma "sarki" na nufin wannan mafi iko ko muhimmin shugaba a cikin wata ƙungiya.

  • Ga wasu misalan da za a haɗa da su, "sarkin mawaƙa," "babban firist," da "shugaban masu ƙarɓar haraji," da "sarki mai mulki."
  • Kuma za a iya amfani da shi a kira kan gida ko iyali, kamar misali a Farawa 36 inda aka kira wasu mazaje "sarakan" iyalansu. Idan aka sami haka, wannan kalma "sarki" za a iya ba ta fassara haka "shugaba" ko "maigida."
  • Idan kuma za a yi magana akan wani abu ne za a iya amfani da kalman nan "shugabanci" ko "mulki," misali "shugaban mawaƙa" ko "firist mai mulki."

(Hakanan duba: babban firist, firist, mai karɓar haraji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 01:11-13
  • Ezekiyel 26:15-16
  • Luka 19:02
  • Zabura 004:1

sarki, sarakuna, masarauta, masarautai, sarauta, a sarake

Ma'ana

Kalmar "sarki" na nufin wani mutum wanda shi ne babban mai mulkin birni, jiha,ko ƙasa.

  • Yawanci ana zaɓen sarki ya yi mulki saboda dangantakar iyalinsa da sarakunan da suka wuce.
  • Sa'ad da sarki ya mutu, yawanci ɗan fãrinsa ne yake zama sarki na gaba.
  • A zamanan dã, sarki yana da cikakken iko bisa mutanen masarautarsa.
  • Da wuya ayi amfani da kalmar "sarki" ga wanda ba sarki na gaske ba, kamar "sarki hiridus" a cikin sabon alƙawari.
  • A cikin Littafi Mai tsarki, sau da dama ana kiran Allah sarki wanda ke mulki bisa mutanensa.
  • An kira Yesu "sarkin Yahudawa," "sarkin Isra'ila," da "sarkin sarakuna."
  • Sa'ad da Yesu zai dawo, zai yi mulki a matsayin sarki bisa duniya.
  • Wannan kalma kuma ana iya fassarata a matsayin "babban shugaba" ko "shugaba baki ɗaya" ko "mai mulki mafi girma."
  • Furcin "sarkin sarakuna" ana iya fassarawa a matsayin "sarki wanda ke mulki bisa dukkan sauran sarakuna" ko "babban mai mulki wanda ke da iko bisa dukkan masu sauran mulki."

(Hakanan duba : hukuma, Herod Antifas, masarauta, masarautar Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 06:15-16
  • 2 Sarakuna 05:18
  • 2 Sama'ila 05:03
  • Ayyukan Manzanni 07:9-10
  • Ayyukan Manzanni 13:22
  • Yahaya 01:49-51
  • Luka 01:05
  • Luka 22:24-25
  • Matiyu 05:35
  • Matiyu 14:09

sati, mako, makonni

Ma'ana

Wannan kalma "sati ko mako" ana nufin tsawon lokaci da ya kai kwana bakwai.

  • A tsarin ƙirga lokaci na Yahudawa, sati guda yakan fara da maraicen ranar Asabar ya ƙarasa da maraicen ranar Asabar mai zuwa.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "sati ko mako" wani tsawon lokaci ne da ake amfani da shi domin a misalta wasu lokatai haɗaɗɗu bakwai, kamar shekaru bakwai.
  • Bikin Makonni' idi ne na girbi dake ɗaukar sati bakwai bayan idin ‌Ƙetarewa. Shima ana kiransa "Fentikos."

(Hakanan duba: Fentikos)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 20:7-8
  • Maimaitawar Shari'a 16:09
  • Lebitikus 23:15-16

sauka, iya sauka, saukakke, saukowa, zuriya, zuriyoyi

Ma'ana

Ɗan zuriya shi ne wanda yake da dangantaka ta jini kai tsaye da wani dangi na can tarihin baya.

  • Misali, Ibrahim zuriyar Nuhu ne.
  • 'Yan zuriyar mutum sune 'ya'yansa, jikokinsa, tattaɓa kunnensa, da dai sauran su. Zuriyar Yakubu sune ƙabilun Isra'ila goma sha biyu.
  • Kalmar nan "daga zuriya" wata hanya ce ta cewa "ɗan zuriyar wani" kamar yadda "Ibrahim ya zama zuriyar Nuhu." Hakanan za'a iya fassara wannan da cewa "daga iyalin ne."

(Hakanan duba: Ibrahim, uba, Yakubu, Nuhu, ƙabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 09:4-5
  • Ayyukan Manzanni 13:23
  • Maimaitawar Shari'a 2:20-22
  • Farawa 10:1
  • Farawa 28:12-13

sela

Ma'ana

Kalmar "sela" kalmar Ibraniyanci ce da aka fi ganinta a cikin littafin Zabura. Tana da ma'anoni da yawa.

  • Tana iya zama "tsayawa da yabo," wadda kan iya gayyatar masu sauraro su iya tunani da kyau game da abin da aka faɗa.
  • Tunda yake yawanci cikin zabura an rubuta sune a matsayin waƙoƙi, an faɗi

cewa "sela" na iya zama wani salon kiɗa da kan umarci mawaƙi ya tsayar da waƙarsa ya bar kayan kiɗan suyi ta yi su kaɗai ko ya ƙarfafa masu sauraro suyi tunani kan kalmomin da ake yi a waƙar.

(Hakanan duba: zabura)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Zabura 003:3-4
  • Zabura 024:5-6
  • Zabura 046:6-7

sha'awa, zaƙuwa, marmari, muradi

Ma'ana

Sha'awa wani irin son zuciya ne mai ƙarfi, yawancin lokaci na son wani abin zunubi ko lalata. Idan an ji sha'awa shi ne yin sha'awa.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, yawancin lokaci idan an yi magana akan "sha'awa" ana nufin kwana da wani ko wata batare da aure ba.
  • Wasu lokutta kuma wannan kalma a kan yi misali da ita da manufar bautar gumaku.
  • Ya danganta bisa ga nassi, za a iya fassara "sha'awa" haka "marmari marar kyau" ko "marmari mai ƙarfi" ko "marmarin jima'i marar dacewa" ko "muradin jiki mai ƙarfi." ko "marmarin yin zunubi."
  • Wannan furci "zuwa ga sha'awa" za a iya fassara ta haka "marmari marar dacewa" ko "yin tunanin lalata na jiki" ko "kwaɗayin jiki na lalata."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:16
  • 2 Timoti 02:22
  • Galatiyawa 05:16
  • Galatiyawa 05:19-21
  • Farawa 39:7-9
  • Matiyu 05:28

shaida, ɗauka, yadda

Ma'ana

Wanan kalma "shaida" ma'anarta shi ne bada cikakken nuna sani ga wani abu ko wani mutum.

  • Shaida Allah ya ƙunshi yin abin da zai nuna cewa abin da yake faɗi gaskiya ne.
  • Mutanen da suke shaidar Allah suna haka ta wurin yi masa biyayya, wanda yake kawo wa sunansa ɗaukaka.
  • Ma'anar "shaida wani abu" shi ne ka hakikance wannan abin gaskiya ne, ta wurin ayyuka da maganganun da zasu tabbatar da haka.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan ana so a shaidi abu cewa gaskiya ne, za a iya juya kalman nan "shaida" ta zama "faɗi" ko "shela" ko "furta gaskiya" ko "gaskatawa."
  • Idan ana so a shaidi wani mutum ne, za a iya juya kalman nan "shaida" ta zama "karɓa" ko " yadda da darajar abu" ko "a faɗa wa wasu cewa (wani taliki) mai aminci ne."
  • A cikin nassin dake shaida Allah, za a iya fassara wannan haka "gaskatawa da biyayya da Allah" ko "furta wanene Allah" ko "gayawa wasu mutane game da girman Allah" ko "A furta cewa abin da Allah ya ce kuma yake yi gaskiya ne."

(Hakanan duba: biyayya, ɗaukaka, ceto)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 11:38-39
  • Irmiya 09:4-6
  • Ayuba 34:26-28
  • Lebitikus 22:32
  • Zabura 029:1-2

shara, share, yin shara, sharewa

Ma'ana

Yin "shara" na nufin cire ƙazanta ta wurin yin shara, tafiya da sauri da tsintsiya ko burushi. "share" ita ce kalmar da ta wuce ta "shara." waɗannan kalmomin ana amfani da su akai-akai.

  • Kalmar "shara" ana amfani da ita don a nuna yadda soja yake kai hari da gaggawa, hukunci, matsawa a kai da yawa.
  • A misali, Ishaya ya yi anabci cewa Asiriyawa zasu "share" masarautar Yahuda. Wannan na nufin zasu hallaka Yahuda a kuma kame mutanensa.
  • Kalmar "shara" ta kan bayyana yanayin gudun ruwa yakan tura abubuwa da yawa ya tilasta masu barin wurin.
  • Idan abu ya ta'azzara, abubuwa masu wahala na faruwa da mutum, za a iya cewa suna "shara a kansa."

(Hakanan duba: Asiriya, Ishaya, Yahuda, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 16:03
  • Daniyel 11:40-41
  • Farawa 18:24
  • Misalai 21:7-8
  • Zabura 090:05

sharewa, gogewa

Ma'ana

Waɗannan kalmomi "sharewa" da "gogewa" kalmomi ne waɗanda ma'anarsu shi ne cirewa gabaɗaya ko hallaka wani abu ko wani mutum.

  • Waɗannan furci za a iya amfani da su ta hanya mai kyau, kamar idan Allah ya "goge" zunubai ta wurin gafartawa ya kuma zaɓa ya manta da su.
  • Ana kuma yin amfani da su ta hanyoyi marasa kyau, kamar idan Allah ya "gogewa" ko "share" wasu mutane, ya hallaka su saboda zunubansu.
  • Littafi Mai Tsarki ya yi magana akan "gogewa" ko "share" sunan mutum daga littafin rai na Allah, wato wannan mutum ba zai sami rai madawwami ba.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga yadda yake cikin nassi, waɗannan maganganu za a iya fassara su a ce, "a jefar da" ko "a cire" ko "a hallaka gabaɗaya" ko "a cire gabaɗaya."
  • Sa'da da ana magana akan cire sunan wani mutum daga littafin Rai, za a iya fassara wannan haka, "cirewa daga" ko "gogewa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 29:20
  • Fitowa 32:30-32
  • Farawa 07:23
  • Zabura 051:01

shari'a, shari'u, mai bayar da doka, mai karya doka, masu karya doka, ɗakin shari'a, mai shari'a, ka'ida, ka'idance, ka'idoji

Ma'ana

"Shari'a" tsayayyar doka ce wadda ake rubutawa kuma wani dake shi hukuma ne yana sa a kiyaye. "Ka'ida" jagora ne wurin ɗaukar mataki da hali.

  • Dukka "shari'a" da "ka'ida" zasu nufi doka bakiɗaya ko bangaskiya da ke jagorancin halin wani taliki.
  • Wannan ma'anar "shari'a" ta sha bamban da ma'anar kalmar "shari'ar Musa," inda ake nufin dokoki da umarnai waɗanda Allah ya ba Isra'ilawa.
  • Sa'ad da ake zancen shari'a bakiɗaya, "shari'a" za a iya fassara ta a matsayin "ka'ida" ko "doka bakiɗaya."

(Hakanan duba: shari'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 04:02
  • Esta 03:8-9
  • Fitowa 12:12-14
  • Farawa 26:05
  • Yahaya 18:31
  • Romawa 07:1

shawara, mashawarci, shawara domin zaɓi, mai bada shawara

Ma'ana

Waɗannan kalmomi "shawarci" da "mai bada shawara " ma'anar su ɗaya dukka biyu suna nufin taimaka wa wani mutum domin yayi zaɓe mai kyau game da wani abu da ya kamata yayi a ciki yanayin da yake. Mashawarci mai hikima yakan bada shawara mai kyau da zai taimaki mutum yayi zaɓen da ya dace.

  • Yawancin lokaci sarakuna suna da masu basu shawara ko 'yan majalisu dake taimaka masu wajen yanke shari'a akan muhimman abubuwa da ya shafi mutanen da suke mulki.
  • Wasu lokuta shawarar da ake bayarwa bata da kyau. Mugayen mashawarta za su iya iza sarki yayi wani abu ko ya bada doka da zai cuce shi ko mutanensa.
  • Bisa ga yadda yadda yake cikin nassi, "shawara" ko "shawara domin zaɓi" za a iya fassara shi haka, "taimakawa wani yayi zaɓe" ko "faɗakarwa" ko "ƙarfafawa" ko "bishewa."
  • Idan an ce "bada shawara" za a iya fassara wannan zuwa "a shawarci" ko "a bada zaɓi" ko "a karfafa."
  • Ayi lura "bada shawara" dabam take da wannan kalma "mashawarta" wanda ana nufin ƙungiyar mutane ne.

(Hakanan duba: gargaɗi, Ruhu Mai Tsarki, wayau)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:


shekara, shekaru

Ma'ana

Idan an yi amfani da kalmar nan "shekara" kamar yadda aka saba yi, a cikin Littafi Mai Tsarki ana nufin wani tsawon lokaci na kwanaki 354 ne. Bisa ga tsarin kalandar wata wanda ya danganta ga lokacin da wata ke ɗauka ya kewaye duniya.

  • Shekara guda a cikin kalandar wata na zamani ya kai kwanaki 365 a raba su watanni 12, bisa ga tsawon lokaci da duniya ke ɗauka ta kewaye rana.
  • A cikin dukkan tsarin biyu shekara na da watanni 12. Amma da ƙarin wata na 13 wani lokaci a shekara ta kalandar wata domin shekara takan gaza da kwana goma sha ɗaya dana shekara ta rana. Wannan yakan taimaka wajen sa kalandojin su jera tare.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan "shekara" ana amfani da ita a nuna lokacin da wani sha'ani na musamman ya faru. Misali, "shekara ta Yahweh" ko "a shekarar fari" ko "shekara ta alherin Ubangiji" A cikin abubuwa haka, "shekara" za a iya fasarata zuwa "lokaci" ko "lotonsa" ko "sa lokaci."

(Hakanan duba: wata)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 23:31
  • Ayyukan Manzanni 19:8-10
  • Daniyel 08:01
  • Fitowa 12:02

shekara, shekaru, manyanta

Ma'ana

Idan an ce "shekara" ana nufin adadin shekarun da mutum ya yi rayuwa. Ana amfani da shi kuma yawancin lokaci domin a nuna tsawon lokaci.

  • Wasu kalmomi da ake amfani da su a nuna tsawon lokaci sune, "zamani" da "lokaci."
  • Yesu ya yi magana akan "wannan zamani" wato lokacin yanzu da mugunta, zunubi da rashin biyayya sun cika duniya.
  • Za a sami zamani mai zuwa lokacin da adalci zai yi mulki akan sabuwar sama da sabuwar ƙasa.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya dangana ga nassin, kalmar "shekara" a cikin rubutu don za a iya juya wa ya zama, "zamani" ko "lissafin shekaru nawa" ko "lokaci nawa" ko "'lokaci."
  • Faɗar haka, "cikin kyakkyawan tsufa" za a iya juya shi haka, "shekarun tsufa masu yawa" ko "sa'ad da ya tsufa tukuf" ko "bayan ya daɗe sosai a shekaru."
  • Faɗar haka, "wannan mugun zamani" na nufin "a wannan lokaci yanzun nan lokacin da mutane suke mugaye."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 29:28
  • 1 Korintiyawa 02:07
  • Ibraniyawa 06:05
  • Ayuba 05:26

shiƙa, sheƙewa, an sheƙe, ana sheƙewa, bakace, bakacewa

Ma'ana

Kalmar "shiƙa" da "tankaɗe" na manufar raba hatsi daga kayayyakin da ba a so. A Littafi Mai Tsarki, kalmomin biyu ana amfani da su a bayyana rabawa ko wãre mutane.

  • A yi "shiƙa" na nufin a raba hatsi daga sauran sashen hatsin da basu da amfani ta kaɗa hatsin da ƙaiƙayin cikin iska, iskar tana hurar da ƙaiƙayin.
  • Kalmar "bakace" na bayyana kakkaɓe hatsin da aka yi shiƙarsa cikin abin bakacecewa domin a cire sauran abubuwan da ba a buƙata, kamar datti ko duwatsu.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, "shiƙa" da "bakace" ana amfani da su ne a bayyana shan wuyar dake banbanta tsakanin adalai da marasa adalci.
  • Yesu ya yi amfani da kalmar "sheƙewa" yayin da yake faɗi wa Siman Bitrus yadda za a gwada bangaskiyarsa da na sauran almajiran.
  • A fassarar waɗannan kalmomin, ayi amfani da kalmomi ko faɗar a cikin yare da ake aiki a kai dake ma'anar waɗannan ayyuka; wasu fassarorin masu yiwuwa su ne "girgiza" ko "tankaɗe." Idan ba a san shiƙa ko bakace ba, daga nan waɗannan kalmomi za a iya fassara su ta wurin kalmar dake ma'anar hanya daban-daban ta rarrabe hatsi daga ƙaiƙayi ko datti, ko ta wurin bayyana wannan aikin.

(Hakanan duba: ƙaiƙayi, hatsi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ishaya 21:10
  • Luka 22:31
  • Matiyu 03:12
  • Littafin Misalai 20:08
  • Rut 03:02

shinge mai ƙarfi, shingaye masu ƙarfi, garuka, garu, sansani, sansanoni

Ma'ana

Kalmar "shinge mai ƙarfi" da "sansani" dukka na nufin wuraren da aka kare da kyau daga harin sojoji abokan gãba . kalmar "garu" na nuna gari ko wani wuri da akayi domin kariya daga hari.

  • Sau da yawa, shingaye masu ƙarfi da sansanoni mutane ne suke yinsu da kangun kariya. Akan sa su a wurare masu abubuwan kariya sosai kamar su, ƙasa mai duwatsu, ko dutse mai tudu.
  • Mutane sukan yi sansanin shingaye masu ƙarfi ta wurin gina bango mai kauri ko waɗansu gine-ginen da kan zama da wuya ga abokin gãba ya iya haurawa.
  • "Shinge mai ƙarfi" ko "sansani" akan iya fassara su da "wurin da aka yi matuƙar karewa" ko "wurin da aka yi matuƙar tsarewa."
  • Kalmar "gari mai sansani" za a iya fasarta ta da "gari mai cike da tsaro" ko "garin da aka gina shi da ƙarfi."
  • Wannan kalmar anyi ta amfani da ita ana magana kan Allah a matsayin shinge mai ƙarfi ko sansani ga waɗanda suka dogara gare shi.
  • Wata ma'anar kuma ta kalmar "shinge mai ƙarfi" na magana kan wani abu da wani ya yi kuskure dogara ga tsaronsa, kamar su allolin ƙarya ko wani abun da ake bautawa a madadin Yahweh. Za a iya fassara wannan da "shingaye masu ƙarfi na ƙarya."
  • Wannan kalmar za'a fassara ta daban da "kariya" wadda take jaddada kwanciyar hankali fiye da jan dãga.

(Hakanan duba : allahn ƙarya, allahn ƙarya, kariya, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 10:04
  • 2 Sarakuna 08:10-12
  • 2 Sama'ila 05:8-10
  • Ayyukan Manzanni 21:35
  • Habakuk 01:10-11

shirayin kotu, kotu

Ma'ana

Wannan wuri "shirayin kotu" da "kotu" ana magana ne akan filin da ake iya duban sararin sama kuma an yi masa katanga. Wannan kalma "kotu" yana kuma fasara inda al'ƙalai suke yanke shari'a akan abubuwan laifi.

  • Rumfar taruwa an zagayeta da shirayi wanda an yi masa katanga da labulan zanuwa masu kauri.
  • Haikalin nan mai girma yana da shirayun ciki guda uku: ɗaya domin firistoci, ɗaya domin Yahudawa maza, ɗaya domin matan Yahudawa.
  • Waɗannan shirayun ciki an zagaye su da katanga marar tsayi da aka yi ta da duwatsu wadda ta raba su da shirayin waje inda aka yardar wa al'ummai suyi sujada.
  • Shirayin gida ana nufin wani buɗaɗɗen fili ne a tsakiyar cikin gida.
  • Wanna kalma "shirayin sarki" ana magana ne akan fadar sarki ko wani wuri a fadarsa inda yake yanke shari'a.
  • Wannan furci, "shirayin Yahweh" magana ce ta kwatanta mazaunin Yahweh ko inda mutane suke zuwa suyi wa Yahweh sujada.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "shirayi" za iya fasara shi haka "filin da aka zagaye" ko "ƙasar da aka yi mata katanga" ko "filayen haikali" ko "wuraren haikali da aka zagaye."
  • Wani lokaci wannan kalma "haikali" za a buƙata a fassara shi ya zama, "shirayun haikali" ko "ɗakunan haikali" domin a gane sosai ana nufin shirayun ne ba ginin haikalin ba.
  • Wannan furci, "shirayin Yahweh" za a iya fassara shi haka, "inda Yahweh yake zaune" ko "wurin da ake yiwa Yahweh sujada.
  • Maganar da ake amfani da ita domin shirayin sarki za a iya amfani da ita domin shirayin Yahweh.

(Hakanan duba: Ba'al'umme, alƙali, sarki, rumfar sujada, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 20:4-5
  • Fitowa 27:09
  • Irmiya 19:14-15
  • Luka 22:55
  • Matiyu 26:69-70
  • Littafin Lissafi 03:26
  • Zabura 065:4

shugaba, mai shugabantarwa, mai lura, masu lura

Ma'ana

Wannan magana "shugaba" ana nufin wanda ke lura da aiki, da kuma lafiyar da wasu mutane.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, aikin shugaba shi ne ya tabbata ma'aikatan dake ƙarƙashinsa sun yi aikinsu da kyau.
  • A cikin Sabon Alƙawari, wannan kalma ana amfani da ita a gaya mana akan shugabannin Ikilisiya ta farko. Aikinsu suyi tattalin buƙatun ruhaniya ta ikilisiya, su tabbata masu bada gaskiya sun sami cikakken koyarwa na Littafi Mai Tsarki.
  • Bulus ya ce shugaba kamar makiyayi ne da yake lura da masu bada gaskiya a cikin ikilisiya, waɗanda sune "tumakinsa."
  • Shugaba, kamar makiyayi, yana duba tumakinsa. Yana tsaron masu bada gaskiya yana kare su daga koyarwar ƙarya da mugayen hare-hare.
  • A cikin Sabon Alƙawari, waɗannan kalmomi "shugaba," da "dattawa da "makiyaya/pastoci" dukkansu hanyoyi ni na fassara abu guda wato shugabannin ruhaniya.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fassara wannan magana sune, "mai bishewa" ko "mai kula" ko "wakili."
  • idan ana magana akan shugaban wata ƙungiya ta mutanen Allah, yakamata a fassara wannan kalma da wata magana kamar haka "mai bishewa cikin ruhaniya" ko "wani mutum dake lura da buƙatun ruhaniya na ƙungiyar masu bada gaskiya" ko "mutumin dake lura da buƙatun ruhaniyar Ikkilisiya."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 26:31-32
  • 1 Timoti 03:02
  • Ayyukan Manzanni 20:28
  • Farawa 41:33-34
  • Filibiyawa 01:01

shugaban rundunar mayaƙa, umarta

Ma'ana

Wannan furci "shugaban rundunar mayaƙa" ana nufin shugaban sojoji wanda shi ke da nawayar bishewa da umartar ƙungiyar sojoji.

  • "Umartar" sojoji shi ne a bi da su ana kuma kulawa da su.
  • Shugaban rundunar mayaƙa zai iya zama mai kula da ƙaramar ƙungiya ko babba, kamar a ce mutum dubu.
  • Wannan kalma ana amfani da ita a kira Yahweh a ce da shi shugaban rundunar mala'iku mayaƙa.
  • Wasu hanyoyin fasara wannan kalma "shugaban rundunar mayaƙa" zai haɗa da waɗannan, "shugaba" ko "hafsa" ko "ofisa."
  • Wannan furci "a umarci" sojoji za a iya fassarashi haka, "bida" ko "zama mai lura da abu."

(Hakanan duba: umarni, mai mulki, hafsan soja)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 11:4-6
  • 2 Tarihi 11:11-12
  • Daniyel 02:21-22
  • Markus 06:21-22
  • Littafin Misalai 06:07

shugabanci, shugaba, shugabanni

Ma'ana

Wannan kalma "shugabanci" da "shugaba" yana magana ne akan sarrafa ko mulkin mutanen ƙasa domin a taimake ta ta yi tafiya cikin ƙoshin lafiya.

  • An zaɓi Daniyel da wasu samarin Yahudawa an zaɓe su da su zama shugabannai, ko jakadun gwamnati, bisa wasu lardunan Babila.
  • A Sabon Alƙawari wannan kalman "shugabanci" ɗaya ce daga cikin baye-baye na Ruhu Mai Tsarki.
  • Mutumin dake da baiwar ruhaniya ta shugabanci yana iya bida mutane da mulkinsu da kuma lura da kiyaye lafiyar gine-gine da wasu kayayyaki.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, wasu hanyoyin fasarar kalman nan "shugaba" zai iya zama, "gwamna" ko "mai shiryawa" ko "manaja" ko mai mulki" ko "jakadan gwamnati."
  • Kalman nan "shugabantarwa" za a iya fasara ta haka, "mai mulki" ko "bida wa" ko "jagora" ko "shiryawa."
  • Furci kamar su "mai dubawa da" ko "mai lura da" ko "mai tsaron lafiya" zasu iya zama juyin wannan kalma.

(Hakanan duba: Babilon, Daniyel, kyauta, gwamna, Hananiya, Mishayel, Azariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 18:14
  • Daniyel 06:1-3
  • Esta 09:3-5

shugabanci, yin shugabanci, ana shugabanci, shugaba, shugabanni, yin shugabanci

Ma'ana

Kalmar "shugaba" na nuna duk wani ne dake da iko bisa mutane, ga misali shugaban ƙasa, na masarauta, ko na addini. Shugaba wani ne dake "shugabanci," kuma ikonsa shi ne "mulkinsa."

  • A cikin Tsohon Alƙawari, sarki ana yawan ce da shi "shugaba," kamar yadda ake cewa "an sanya shi shugaba bisa Isra'ila."
  • Ana ce da Allah Shugaba mafi girma, mai mulkin dukkan masu mulki.
  • A cikin Sabon Alƙawari, jagorar wurin masujada ana ce da shi "shugaba."
  • Wani shugaba kuma cikin Sabon Alƙawari "gwamna" ne.
  • Bisa ga yadda za a yi amfani da shi a cikin karatun, "shugaba" ana iya ce da shi "mai mulki" ko "mutum dake da iko bisa."
  • Yin "shugabanci" na nufin "jagoranci" ko "samun iko bisa." Dai-dai ne da a ce "mulki" idan ana nufin shugabancin sarki.

(Hakanan duba: izini, gwamna, sarki, masujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 03:17-18
  • Ayyukan Manzanni 07:35-37
  • Luka 12:11
  • Luka 23:35
  • Markus 10:42
  • Matiyu 09:32-34
  • Matiyu 20:25
  • Titus 03:01

shuka, shukoki, shukawa, sake shukawa, dashe, shukoki, shukawa, yin shuka

Ma'ana

"Shuka" baki ɗaya abu ne mai girma da aka haɗa shi da ƙasa. A "shuka" na nufin a sa iri a ƙasa domin ya girma ya zama shuka. Mai "shuka" na nufin mutumin da ya yi shuka ko shuka iri.

  • Hikimar yin shuka ko dashe sun banbanta, amma ɗaya daga ciki itace a ɗauki iri a watsa su a ƙasa.
  • Wata hikimar shukar kuma ita ce a yi ramuka a ƙasa a saka irin a kowanne rami.
  • Kalmar "shuka" akan yi amfani da ita a koyaushe, kamar a "mutum ya kan girbi abin da ya shuka." Wannan na nufin idan mutum ya yi wani abin mugunta, zai sami sakamako marar kyau, amma idan mutum ya yi abin da yake mai kyau, zai karɓi sakamako mai kyau.

Shawarwarin fassara:

  • Kalmar "shuka" za a iya fassara ta da "dasawa." A tabbata kalmar da aka mora wajen fassara wannan kalmar ta haɗa da shuka iri.
  • Waɗansu hanyoyi na fassara "mai shuka" sun haɗa da, "mashuki" ko "manomi" ko "mutumin da yake shuka iri."
  • A Turanci, "shuka" tana amfani ne kawai a shukar iri, amma kalmar Turanci ta "shuki" takanyi amfani a shuka iri da kuma waɗansu manyan abubuwan, kamar su bishiyoyi. Waɗansu yarurrukan kan yi amfani da kalmar akan wani abu daban, ya danganta da abin da aka shuka.
  • Maganar "mutum zai girbi abin da ya shuka" za a iya fassara ta da "kamar irin wani irin da aka samar a irin wata shuka, haka yake mutum ta wurin kyakkyawan aikinsa zai sami sakamako mai kyau, kuma ,mutum ta wurin mugun aikinsa zai sami sakamakon muguntarsa."

(Hakanan duba: mugu, mai kyau, girbi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 06:08
  • Luka 08:05
  • Matiyu 06:25-26
  • Matiyu 13:04
  • Matiyu 13:19
  • Matiyu 25:24

siffofi na ƙarfe, alamomi, shafaffu, ƙarafa na zubi, siffofi

Ma'ana

Waɗannan kalmomin an mori dukkansu domin a ambaci gumaka domin yin sujada ga allolin ƙarya. Bisa ga tsarin bautar gumaka, kalmar "siffa" an taƙaita kalmar "gumaka ne sassaƙaƙƙu."

  • "Sassaƙaƙƙiyar siffa" ko "sassaƙaƙƙiyar gumaka" kayan itace ne da aka mayar su zama kamar dabba, mutum, ko abu.
  • Wannan "siffa ta zubi ta ƙarfe" siffa ce da aka narka ƙarfe aka zuba shi cikin wata kama ta dabba, ko mutum.
  • Waɗannan siffofi na ƙarfe da na katako akan more su a cikin sujada ga allolin ƙarya.
  • Kalmar nan "siffa" in ana magana game da gunki ko dai na katako ka na ƙarfe.

Shawarwarin Fassara:

  • Lokacin da ake ambaton gunki, kalmar "siffa" za'a iya fassara ta da "gunki" ko "sassaƙaƙƙun siffofi" domin wata "hidima ta addini."
  • Za'a iya gane shi a fili a waɗansu harsunan har kullum suna amfani da nuni game da wannan wajen ambaton wannan siffa a wuraren sujada.
  • A tabbatar an bayyana shi a fili don aga cewa ya bambanta da mutum da aka halitta cikin kamanni Allah.

(Hakanan duba: allahn ƙarya, Allah, kamannin Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 14:9-10
  • Ayyukan Manzanni 07:43
  • Ishaya 21:8-9
  • Matiyu 22:21
  • Romawa 01:23

soja, sojoji, jarumi, jarumawa

Ma'ana

Kalmomin "jarumi" da "soja" dukkansu biyu na bayyana wani ne wanda ke faɗa cikin rundunar soja. Amma akwai wasu 'yan banbanci.

  • Yawanci kalmar "jarumi" janar ne, wannan na nuna mutum mai baiwa da ƙarfin hali cikin yaƙi.
  • Ana kwatatan Yahweh a matsayin "jarumi."
  • Kalmar "soja" na bayyana musamman wani wanda ke yaƙi tare da rundunar sojoji cikin dãgar yaƙi.
  • Sojojin Romawa dake zama ciki Yerusalem aikinsu shi ne su tabbatar da zaman lafiya da kuma hukunta 'yan kurkuku. Sun yi gadin Yesu kamin suka gicciye shi wasu kuma aka sanya su gadin kabarinsa.

(Hakanan duba: ƙarfin hali, gicciye, Roma, kabari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 21:05
  • Ayyukan Manzanni 21:33
  • Luka 03:14
  • Luka 23:11
  • Matiyu 08:8-10

sokewa, suka, soki, hudawa

Ma'ana

Wannan magana "sokewa" ma'anarta shi ne a tsire wani abu da wani abu mai tsini. Akan yi amfani da ita a misalta yadda ake sa wani mutum ya ji ciwo a ransa.

  • Wani soja ya soki kwiɓin Yesu lokacin da aka rataye shi akan gicciye.
  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, bawan da aka baratar akan huda kunnensa, alamar ya zaɓa ya ci gaba da aiki da maigidansa.
  • Simiyon ya yi magana da misali sa'ad da yace wa Maryamu takobi zai soki zuciyarki, ma'ana, zata sami baƙinciki ainun domin abin da zai faru da ɗanta Yesu.

(Hakanan duba: gicciye, Yesu, bawa, Simiyon)

Wuraren da ake samunsa a ittafi Mai Tsarki:

  • Ayuba 16:13
  • Ayuba 20:23-25
  • Yahaya 19:37
  • Zabura 022:16

sulke, sulkaye, ƙyallen ƙirji

Ma'ana

Wannan kalma "sulke" na nufin wani kayan yaƙi ne da yake rufe gaban ƙirji ya tsare soja a lokacin yaƙi. Kalmar nan "ƙyallen ƙirji " yana nufin wani ƙyalle ne musamman da babban firist na Isra'ila yake sakawa akan fuskar ƙirjinsa.

  • "Sulke" da soja ke amfani da shi ana yinsa da itace, ƙarfe, ko fatar dabba. An yi shi domin a kare kibau, mãsu, ko takkuba daga sukar ƙirjin soja.
  • "‌Ƙyallen ƙirji" da babban firist na Isra'ila ke sawa anyi shi da ƙyalle yana kuma da wasu duwatsu masu daraja da aka manna a kansa. Firist yakan sa wannan sa'ad da yake hidimarsa ga Allah a haikali.
  • Wasu hanyoyi na fassara "sulke" za a haɗa da waɗannan "makari na ƙarfe mai rufe ƙirji" ko "makamin yaƙi mai kare ƙirji."
  • Wannan abin da ake ce da shi "ƙyallen kirji" za a iya fassara shi da kalmomin nan haka, "suturar firist mai rufe kirji" ko "rigar firist" ko "ƙyallen gaba na suturar firist."

(Hakanan duba: makami, babban firist, sokewa, firist, haikali, mayaƙi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 05:08
  • Fitowa 39:14-16
  • Ishaya 59:17
  • Wahayin Yahaya 09:7-9

sumba, sumbace-sumbace, yin sumba

Ma'ana

Sumba wata aiwatarwa ce da wani taliki zai sanya leɓunansa ga leɓunan wani talikin ko fuska. Ana iya amfani da wannan kalma cikin misali.

  • Wasu al'adun suna sumbar juna a kumatu a matsayin gaisuwa ko ban kwana.
  • Sumba zai iya zartar da zancen ƙauna mai zurfi tsakanin mutane biyu, kamar a matsayin miji da mata.
  • Nuna "sumbar ban kwana ga wani" na ma'ana ace sai wata rana da sumba.
  • Wasu lokutta kalmar "sumba" ana amfani da ita a ma'anar "ace sai wata rana ga." Sa'ad da Elisha ya cewa Iliya, "bari in fãra tafiya in sumbaci mahaifina da mahaifiyata," yana so ne yace sai wata rana ga iyayensa kafin ya bar su ya bi Iliya.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 05:25-28
  • Farawa 27:26-27
  • Farawa 29:11
  • Farawa 31:28
  • Farawa 45:15
  • Farawa 48:10
  • Luka 22:48
  • Markus 14:45
  • Matiyu 26:48

sunkuya, sunkuyawa ƙasa, rusunawa, durƙusawa, rusunar da gwiwa

Ma'ana

Sunkuyawa shi ne a sunkuya ƙasa domin nuna bangirma da girmamawa ga wani mutum. "Sunkuyawa ƙasa" shi ne a tafi ƙasa sosai ko a durƙusa kan gwiwa ko rusunawa ƙasa yawancin lokaci da fuska da hannu suna nufa ƙasa.

  • Wasu furcin sun haɗa da "rusuna gwiwa" (wato a durƙusa) da "sunkuyar da kai" ( ma'ana a sunkuyar da kai ƙasa cikin tawali'u da bangirma ko cikin baƙinciki).
  • Sunkuyawa ƙasa zai iya zama alamar damuwa da makoki. Mutumin da yake a "sunkuye" an ƙasƙantar da shi zuwa matsayin tawali'u.
  • Yawancin lokaci mutum zai sunkuya a gaban wani da ya fi shi girma a matsayi ko muhimmanci, kamar sarakai da wasu masu mulki.
  • Sunkuyawa a gaban Allah yin sujada ne a gare shi.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, mutane sun durƙusa wa Yesu da suka gane ta wurin al'ajibansa da koyarwarsa ya zo daga Allah.
  • Littafi Mai Tsarki ya ce lokacin da Yesu zai sake dawowa wata rana, kowa da kowa zai durƙusa gwiwarsa ya yi masa sujada.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, wannan kalma za a iya fasarata da kalma ko faɗa da wannan ma'ana, "a sunkuya gaba" ko "a sunkuyar da kai" ko "a durƙusa."
  • Wannan kalmar "sunkuyawa ƙasa" za a iya fasara ta haka "durƙusawa ƙasa" ko "kwantar da jiki dukka a ƙasa."
  • Wasu yarurruka suna da hanyoyi fiye da ɗaya da za su fassara wannan kalma, ya danganta ga yadda yake cikin rubutu.

(Hakanan duba: tawali'u, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 05:18
  • Fitowa 20:05
  • Farawa 24:26
  • Farawa 44:14
  • Ishaya 44:19
  • Luka 24:05
  • Matiyu 02:11
  • Wahayin Yahaya 03:09

ta'aziya, mai ta'aziya

Ma'ana

Waɗannan kalmomi "ta'aziya" da "mai ta'aziya" ana nufin taimakon wani mutum ne wanda yake shan wahala a jiki ko a ruhu.

  • Mutumin da yake ta'azantar da wani mutum ana kiran sa "mai ta'azantarwa."
  • A cikin Littafin Tsohon Alƙawari, kalman nan "ta'aziya" ana amfani da shi a faɗi yadda Allah yake nuna alheri da ƙauna ga mutanensa yana kuma taimakon su lokacin wahalarsu.
  • A cikin Sabon Alƙawari, an ce Allah zai ta'azantar da mutanensa tawurin Ruhu Mai Tsarki. Waɗanda suka karɓi ta'aziyar sukan iya sadar da wannan ta'aziya ga wasu kuma masu shan wuya.
  • Wannan furci "mai ta'azantar da Isra'ila" ana nufin Almasihu ne wanda zai zo ya kuɓutar da mutanensa.
  • Yesu ya ce da Ruhu Mai Tsarki "Mai Ta'aziya" wanda yake taimakon masu bada gaskiya ga Yesu.

Shawarwarin Fassara

  • Ya danganta ga yadda yake a nassi, " za a iya fassara "ta'aziya" haka, "sanyaya ciwo" ko "taimako."

(Hakanan duba: ƙarfafa, Ruhu Mai Tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tassalonikawa 05:8-11
  • 2 Korintiyawa 01:04
  • 2 Sama'ila 10:1-3
  • Ayyukan Manzanni 20:11-12

tabbata, tabbatarwa

Ma'ana

Waɗannan kalmomi "tabbata" ko "tabbatarwa" ana nufin faɗi ko "haƙƙaƙe wani abu gaskiya ne" ko amincewa" ko "dogara."

  • A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya gaya wa mutanensa zai "tabbatar" da alƙawarisa da su. Ma'ana, yana cewa zai cika alƙawaran da yayi cikin yarjejeniyar.
  • Idan aka "tabbatar" da sarki ana cewa zaɓen da aka yi ya zama sarki an yarda da shi kuma mutane sun goyi baya.
  • Idan za a tabbatar da abinda wani ya rubuta ma'anar shi ne abin da an rubuta gaskiya ne.
  • Tabbatar da bishara, ma'anar shi ne koyawa mutane game da labari mai daɗi na Yesu ta hanya mai ban sha'awa da zai nuna gaskiya ne.
  • Idan an yi rantsuwa mai kwari domin "tabbatarwa" ma'anar shi ne a furta abu gaba gaɗi ko "a rantse cewa wani abu gaskiya ne ko za a iya dogara gareshi.
  • Waɗansu hanyoyin fasara "tabbatarwa" sune, "faɗin abu yadda yake gaskiya" ko "gwada amincinsa" ko "tabbatarwa" ko "alƙawari," ya danganta ga nassi.

(Hakanan duba: alƙawari, rantsuwa, dogara)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 16:15-18
  • 2 Korintiyawa 01:21
  • 2 Sarakuna 23:3
  • Ibraniyawa 06:16-18

tada, kiwata, tada, tashi, tashi, taso, tashi, zuga sama

Ma'ana

tashi, tashi tsaye

A taƙaice kalmar "tada" na manufar " ɗaga sama" ko "a sa a yi sama."

  • Kalmar jimlar "tada sama" na ma'anar a ingiza wani abu ya bayyana ko kasance. Yana iya zama kuma a sanya wani a matsayin yin wani abu.
  • Wani lokacin "tada sama" na iya nufin "maidowa" ko "sãke ginawa."
  • "Tadawa" na da ma'ana ta musamman "tayarwa daga matattu." Ma'ana a tada mataccen mutum domin ya rayu.
  • Wani lokacin "tada sama" na manufar " a girmama" wani ko wani abu.

tashi, a tashi

"Tashi" ko "a tashi" na ma'anar "a yi sama" ko "a haura sama." Kalmomin "an tashi," "an taso" da "tasowa" suna bayyana abin da aka riga aka yi.

  • Idan wani taliki ya tashi za shi wani wuri, wannan wani lokaci ana bayyana shi a "ya taso ya tafi" ko "ya tashi ya tafi."
  • Idan wani abu ya "taso" ana nufin "kasance" ko "ya fara kasance wa."
  • Yesu ya faɗi cewa zai "tashi daga matattu." Kwanaki uku bayan Yesu ya tashi, mala'ikan ya ce, "Ya tashi!"

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "tashi" ko "tasowa sama" ana iya fassarawa "ɗagawa sama" ko "a sa ya yi bisa."
  • "Tasowa sama" ana kuma iya fassarawa "a sa ya bayyana" ko "a ƙayyada" ko "a kawo zuwa wanzuwa."
  • "Tasowar da ikon maƙiyanka" za a iya fassarawa haka, "sanya maƙiyanka su zama da ƙarfi sosai."
  • Faɗar "tada wani daga matattu" ana iya fassarawa haka "a sanya wani ya dawo daga mutuwa zuwa rai" ko "sanya wani ya dawo zuwa rai."
  • Ya danganta ga nassin, "tasowa sama" za a iya fassarawa haka "a wadata" ko "a ƙayyada" ko "a sa a samu" ko "a gina" ko "a sake ginawa" ko "a yi gyara."
  • faɗar "ya taso ya tafi" za a iya fassarawa haka "ya tashi ya tafi" ko "ya tafi."
  • Ya danganta ga nassin, kalmar "ya taso" za a iya kuma fassarawa haka "farawa" ko "a fara yin" ko "a tashi tsaye" ko " a tsaya tsaye."

(Hakanan duba: tashi daga matattu, ɗaukaka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 06:41
  • 2 Sama'ila 07:12
  • Ayyukan Manzanni 10:40
  • Kolosiyawa 03:01
  • Maimaitawar Shari'a 13: 1-3
  • Irmiya 06:01
  • Littafin Alƙalai 02:18
  • Luka 07:22
  • Matiyu 20:19

tafiya, yi tafiya

Ma'ana

Kalmar "tafiya" ana amfani da ita a misali da nuna ma'anar "rayuwa."

  • "Enok ya yi tafiya da Allah" na nufin cewa Enok ya yi zaman zumunci kurkusa da Allah.
  • Ayi "tafiya ta wurin Ruhu Mai Tsarki" na nufin bishewar Ruhu Mai Tsarki domin mu yi abin da zai faranta wa Allah rai ya kuma girmama shi.
  • "Yin tafiya cikin" dokoki ko tafarkun Allah na nufin "zama cikin biyayya ga" umarmansa, wato, "yin biyayya da dokokinsa" ko "yin nufinsa."
  • Idan Allah ya ce "zai yi tafiya tsakanin" mutanensa, wannan ya nuna yana zama tare da su ne ko yana hurɗa da su kurkusa.
  • "Yin tafiya saɓani da" na nufin zama ko aikata ba dai-dai ba gãba da wani abu ko wani.
  • "Yin tafiya bayan" na nufin a neme ko bin wani ko wani abu. Haka yana nufin a aikata dai-dai kamar wani.

Shawarwarin Fassara:

  • Zaifi kyau a fassara "tafiya" kai tsaye, muddan ainihin ma'anar za a fahimce ta.
  • Ko kuwa, a cikin misali amfani da "tafiya" za a iya fassarawa haka "rayuwa" ko "aikata" ko "halayya."
  • Faɗar "tafiya ta wurin Ruhu" za a iya fassarawa ta haka, "zama cikin biyayya da Ruhu Mai Tsarki" ko "rayuwa ta hanyar da ta gamshi Ruhu Mai Tsarki" ko "yin abubuwam dake gamsar Allah kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya bishe ka."
  • A "yi tafiya cikin umarnin Allah" za a iya fassarawa ta haka "ayi rayuwa ta wuri dokokin Allah" ko "ayi biyayya da dokokin Allah."
  • Faɗar "tafiya da Allah" za a iya fassarawa haka, "zama cikin zumuncin kurkusa da Allah ta wurin biyayya da girmama shi."

(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, girmamawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 01:07
  • 1 Sarakuna 02:04
  • Kolosiyawa 02:07
  • Galatiyawa 05:25
  • Farawa 17:01
  • Ishaya 02:05
  • Irmiya 13:10
  • Mika 04:02

tafki, tafkuna, rijiya, rijiyoyi

Ma'ana

Kalmar "rijiya" da "tafki" na bayyana ire-iren maɓulɓulan ruwa cikin zamanin Littafi Mai Tsarki.

  • Rijiya rami ne mai zurfi da aka haƙa cikin ƙasa domin ruwan dake ƙarƙashin ƙasa shi gangara ciki.
  • Tafki rami ne mai zurfi da aka haƙa daga cikin dutse da ake amfani da shi a tare ruwan sama.
  • Tafkuna akan haƙa su daga cikin dutse a kuma yi masu marfin filasta da ake rufe ruwan da shi. "Fasasshen tafki" na faruwa ne sa'ad da marfin filastar ya tsage yadda ruwan zai malale waje.
  • Tafkuna yawanci ana haƙa sune a harabar gidajen mutane domin a tattara ruwan sama dake zubowa daga saman rufin gidaje.
  • Akan haƙa rijiyoyi a inda iyali da yawa ko dukkan jama'ar gari zai masu saukin zuwa ɗebowa.
  • Domin ruwa na da muhimmanci ga mutane da dabbobi, 'yancin amfani da rijiya yana zama sanadiyyar husuma da rigima.
  • Da rijiyoyi da tafkuna dukkansu biyu ana rufe su da babban dutse domin kada wani abu shi faɗa ciki. Yawancin lokatai ana ajiye guga domin a ɗebo ruwa daga ciki.
  • Wani lokacin ana amfani da busasshen tafki a saka mutum ɗan kurkuku, kamar yadda ya faru da Yosef da Irmiya.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "rijiya" zasu haɗa da "ramin ruwa mai zurfi" ko "rami mai zurfi domin maɓuɓɓugar ruwa" ko "rami mai zurfi na jawo ruwa."
  • Kalmar "tafki" za a iya fassarawa haka "ramin ruwa na dutse" ko "rami mai zurfi matsastse domin ruwa" ko "tankin ƙarƙashin ƙasa na riƙe ruwa."
  • Waɗannan kalmomi suna da ma'ana shigen iri ɗaya. Ainihin banbancin shi ne rijiya a koyaushe tana karɓar ruwa daga maɓuɓɓugan ƙarƙashin ƙasa, yayin da tafki tankin riƙewa ne domin ruwan dake zuwa daga ruwan sama.

(Hakanan duba: Irmiya, kurkuku, husuma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 11:17
  • 2 Sama'ila 17:17-18
  • Farawa 16:14
  • Luka 14:4-6
  • Littafin Lissafi 20:17

tagulla

Ma'ana

Wannan kalma "tagulla" wani irin ƙarfe ne da ake yinsa ta wurin narkar da waɗannan ƙarafe tare, tagulla da kuza. Launinsa baƙi ne ƙasa-ƙasa amma da ɗan ja-ja kaɗan.

  • Ruwa baya iya sa tagulla ta yi tsatsa, tana kuma da saurin ɗaukar zafi.
  • A zamanin dã, ana amfani da tagulla a ƙera, kayan yaƙi, kayan aikin hannu, bagadai, tukwanen girki, makaman sojoji, da wasu abubuwa kuma.
  • Yawancin kayan ginin rumfar sujada da haikali, da tagulla aka yi su.
  • Gumakan alloli yawancin lokaci da ƙarfen tagulla ake yinsu.
  • ‌Ƙerarrun abubuwa daga tagulla ake yinsu da farko ta wurin narkar da tagullar kamar kunu sa'annan a zuba ta cikin siffar da ake so ta ɗauka. Ana kiran wannan aiki "zube."

(Hakanan duba: makami, rumfar sujada, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 07:16
  • 1 Sama'ila 17:37-38
  • Daniyel 02:44-45
  • Fitowa 25:3-7
  • Wahayin Yahaya 01:15

takalmi, takalma

Ma'ana

Takalmi abin sawa ne a kafa ɗaure da igiya har zuwa ƙwaurinsa. Maza da mata na iya sanya takalmi.

  • Akan yi amfani da takalmi a tabbatas da yarjejeniya, kamar sayar da kaya: mutum ɗaya zai tuɓe takalminsa ya bayar ga ɗayan.
  • Ta wurin kwaɓe takalmi alama ce ta bangirma, musamman a gaban Allah.
  • Yahaya yace bai cancanta ya kwance takalman Yesu ba, wanda shi ne aikin bara marar daraja ko bawa.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:33
  • Maimaitawar Shari'a 25:10
  • Yahaya 01:27
  • Yoshuwa 05:15
  • Markus 06:7-9

takewa, tattakewa, tattake, tattakawa

Ma'ana

"Takewa" shi ne a taka abu har sai an murje shi da tafin ƙafa. Ana kuma amfani da wannan kalma a misali cikin Littafi Mai Tsarki da manufar "hallakarwa" ko "kayarwa" ko "wulaƙantawa."

  • Misalin "tattakawa" zai iya zama mittsike da tafin ƙafafun mutane idan suna gudu a saura..
  • A zamanin dã, ina ruwan inabi wasu lokutan ta wurin mittsike 'ya'yan inabin domin a mãtso ruwan daga cikin su.
  • Wasu lokuta kalmar "takewa" ana amfani da ita a misali a bayyana yadda Yahweh zai horar mutanensa Isra'ila domin girman kansu da taurin kansu.
  • Sauran hanyoyin da za a iya fassara "takewa" sun haɗa da "gurjewa da tafin ƙafafu" ko "murjewa ƙasa da tafin ƙafafu" ko "takewa da gurjewa" ko "mittsikewa cikin ƙasa."
  • Ya danganta da nassin, wannan kalmar za a kuma iya fassarawa haka nan.

(Hakanan duba: 'ya'yan inabi, wulaƙanta, horar, tawaye, sheƙewa, ruwan inabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 10:29
  • Zabura 007:5

takobi, takkuba, tutanen takobi

Ma'ana

Takobi wani makamin ƙarfe ne mai faɗi da ake amfani da shi wajen yanka ko sara. ta na da mariƙa da kaifi mai tsawo da tsini a kanta.

  • A zamanin dã tsawon takobi yakan kai kusan santi mita 60-91.
  • Waɗansu takkuban suna da kaifi biyu ana kiransu"mai kaifi biyu" ko "takobi mai kaifi biyu" takkuba.
  • Almajiran Yesu suna da takkuba na kare kai. Da takobinsa, Bitrus ya sãre kunnen bawan babban firist.
  • Yahaya mai baftisma da manzo Yakubu an sare masu kai da takkuba.

Shawarwarin Fassara:

  • Takobi an yi amfani da ita a matsayin Maganar Allah. koyarwar Allah a cikin Littafi Mai Tsarki ta kai zuwa tunanin mutane su gane zunubansu. A irin wannan hanya, saran da takobi ta yi mai zurfi, yakan haifar da zafi.
  • Tanya ɗaya ta fassara wannan na iya zama, "Maganar Allah kamar takobi ce, wadda takan yanka da zurfi ta fayyace zunubi."
  • Wani amfani da wannan kalmar kuma ya faru a littafin Zabura, inda harshe ko maganar mutum aka danganta ta da takobi, wadda takan yiwa mutane lahani. za a iya fassara wannan da "harshe takobi ne da kan yiwa wani lahani."
  • Idan ba'a san takobi ba a al'adarku, wannan takobin za a fassarata da sunan wani dogon makami da ake amfani dashi a yi sara ko yanka.
  • Akan kuma bayyana takobi da "makami mai kaifi" ko "doguwar wuƙa." Wata fassarar kan haɗa da hoton takobin.

(Hakanan duba: Yakubu (ɗan'uwan Yesu), Yahaya (mai Baftisma), harshe, maganar Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 12:02
  • Farawa 27:40
  • Farawa 34:25
  • Luka 02:33-35
  • Luka 21:24
  • Matiyu 10:34
  • Matiyu 26:55
  • Wahayin Yahaya 01:16

tanderu

Ma'ana

Tanderu wani babban wuri ne da ake hura wuta domin gasa abubuwa har su gasu.

  • A lokacin dã, ana amfani da tanderu domin narka ƙarafa domin yin abubuwa, kamar tukwanen girki, abin wuya, makamai, da gumaka.
  • Akan mori tanderu domin yin tukwanen ƙasa.
  • A waɗansu lokutan akan mori salon magana domin nuna cewa abin na da zafi.

(Hakanan duba: allolin ƙarya, siffofi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 08:51
  • Farawa 19:28
  • Littafin Misalai 17:3
  • Zabura 021:9
  • Wahayin Yahaya 09:2

tãra, nuna bambanci, wariya

Ma'ana

Wannan magana "tãra" da "nuna bambanci" na nufin son zuciyar wani ya bambanta mutane da nufin wasu sun fi wasu mutane mahimmanci.

  • Wannan kusan ɗaya yake a ma'ana da nuna wariya, wato a fi son wasu mutane kan wasu.
  • Yawancin lokaci ana yin tãra da bambanta mutane domin sun fi wasu arziki ko domin su sanannune fiye da wasu mutanen.
  • Littafi Mai Tsarki ya koya mana kada mu nuna tãra ko bambanci ga mutanen dake da arziki ko matsayi.
  • A cikin wasiƙarsa zuwa ga Romawa, Bulus ya koyar cewa Allah yana shar'anta mutane da adalci ba ya nuna tãra.
  • Littafin Yakubu ya koyar da cewa ba dai-dai bane a ba wani mutum kujera mafi girma ko a fi kulawa da shi domin shi mai arziki ne.

(Hakanan duba: tagomashi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 01:17
  • Malakai 02:09
  • Markus 12:13-15
  • Matiyu 22:16
  • Romawa 02:10-12

Tarihi

Ma'ana

Wannan kalma "tarihi" manufarta shi ne rubutattun labarbaru game da abubuwan da suka faru na dogon lokaci.

  • Litattafai guda biyu na Tsohon Alƙawari ana kiransu "Littafin Tarihi na ‌Farko" da Littafin Tarihi na Biyu."
  • Littattafan da ake kira "Tarihi" an rubuta tarihin mutanen Isra'ila ne, ya fara da jerin sunayen mutane a kowanne tsara tun daga Adamu.
  • "Littafin Farko na Tarihi" ya bada labarin ƙarshen rayuwar Sarki Saul da ayyukan sarautar Sarki Dauda.
  • "Littafin Tarihi na Biyu" ya rubuta akan sarautar Sarki Suleman da wasu sarakuna da dama, akwai kuma ginin haikali da rabuwar mulkin Isra'ila ta arewa daga mulkin Yahuda ta kudu.
  • Karshen Littafin Tarihi na Biyu ya bada labarin farawar kwashewa zuwa Babila.

(Hakanan duba: Babila, Dauda, hijira, masarautar Isra'ila, Yahuda, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 27:24
  • 2 Tarihi 33:19
  • Esta 10:1-2

tarko, tarkuna, ɗana tarko, tankiya, tankiyoyi, faɗawa rami

Ma'ana

Kalmar "tarko" da "tankiya" na nufin abubuwan da ake amfani da su wajen kama dabbobi da kuma hana su kuɓucewa. "Tarko" ko "ɗana tarko" shi ne a kama da tarko da kuma "tarko" ko "tanke" na nufin kamawa da tarko. A littafi Mai Tsarki, waɗannan anyi amfani da su wajen magana kan zunubi da gwaji suna kama da ɓoyayyun taraku da suke kama mutane su cutar da su.

  • "Tarko" tarin igiya ne ko waya da ake ɗaurawa idan dabba ta taka ciki, sai ya kanannaɗe ƙafar.
  • "Tarko" ana yin sa ne da ƙarfe ko itace yana da sassa biyu da suke kusa da juna, su kama dabba ta yadda baza su sami ƙofa ba. wasu lokutan tarko na zama wani rami ne da ake haƙawa domin wani ya faɗa a ciki.
  • Mafi akasari kananaɗewa ko tarko ana ɓoye shi ne domin ya dinga mamayar abin da ake so ya faɗa.
  • Faɗar "haɗa tarko" na nufin a shirya tarko don kama wani abu.
  • "Faɗawa cikin tarko" na nufin faɗawa cikin wani zuzzurfan rami da aka haƙa aka ɓoye don a kama dabba.
  • Mutumin da ya fara yin zunubi ya kasa daina wa akan nunashi a matsayin "ya kanannaɗe da zunubi" a misalin hanyar da dabba za ta iya kanananɗewa yadda ba hali ta kuɓuta.
  • Dabbar da take cikin haɗari da cutuwar tarko, haka mutum yake a cikin tarkon zunubi da yake cutuwa ta wannan zunubin da yake buƙatar kuɓuta.

(Hakanan duba: kuɓuta, ganima, Shaiɗan, gwaji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Mai Wa'azi 07: 26
  • Luka 21:34
  • Markus 12:13
  • Zabura 018:05

taro, tarurruka, tattarawa, taruwa

Ma'ana

"Taro" shi ne idan ƙungiyar mutane sun haɗu domin su tattauna akan matsaloli ko bada shawarwari da ɗaukar matakai.

  • Taro zai iya zama shiryayyen ƙungiya da aka haɗa ta akan tsarin dake din-dindin, ko kuma zai iya zama ƙungiyar mutane da suka haɗe tare na gajeren lokaci domin wani dalili na musamman ko wani sha'ani.
  • A cikin Tsohon Alƙawari akwai wani irin taro na musamman da ake kira "keɓaɓɓen taro, inda mutanen Isra'ila za su taru su yiwa Yahweh sujada.
  • Wani lokaci wannan kalmar "taro" na nufin Isra'ilawa ɗungum a ƙungiyar su.
  • Babbar taruwar sojoji maƙiya wani lokaci ana ce da shi "taro." Wannan za a iya fassara shi a ce "rundunar sojoji."
  • A cikin Sabon Alƙawari, taron shugabannin Yahudawa 70 a manyan birane kamar Yerusalem sukan hallaru domin su zartar da shari'a da sasanta jayayya tsakanin mutane. Sanannen sunan taron nan shi ne "Sanhedirin" ko kuma "majalisa."

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, "taro" za a iya fassara shi ya zama "taruwar musamman" ko "taron jama'a" ko "majalisa" ko "sojoji" ko "babbar ƙungiya."
  • Sa'ad da aka yi amfani da kalmar nan "taro" domin Isra'ilawa gabaɗaya, za a iya fassara shi zuwa "mutanen dake tare" ko "mutanen Isra'ila."
  • Wannan faɗar, "dukkan taro" za a iya fassara shi haka "dukkan mutane" ko "dukkan ƙungiyar Isra'ilawa" ko "kowa da kowa."

(Hakanan duba: majalisa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 08:14
  • Ayyukan Manzanni 07:38
  • Ezra 10:12-13
  • Ibraniyawa 12:22-24
  • Lebitikus 04:20-21
  • Nehemiya 08:1-3

tauri, mai tauri, mafi tauri, tauriƙiƙi, yin tauri, taurararre, taurarewa, halin taurarewa

Ma'ana

Kalmar nan "tauri" tana da ma'ana da yawa, ya danganta ga wurin. Har kullum abin da take nufi shi ne wani abu da ke da wuya, mai tauri, ko mararsauƙi.

  • Batun nan "taurin zuciya" ko "taurin kai" na nufin mutane waɗanda ke tayarwa, marasa tuba. wanan kalmar na baiyana mutane ne da ke da rashin biyayya ga Allah.
  • Salon maganar "taurin zuciya" da "taurin zuciyarsu" shima yana nufin tayarwa ne da rashin biyayya.
  • Idan wani yana da "taurin zuciya" wanan na nufin cewa wanan mutumin ya ƙi yin biyayya, kuma ya ƙi tuba.
  • Idan aka mori kalmar aikatau, misali "aiki tuƙƙuru" ko "yi ƙoƙari sosai" wanan na nufin ayi wani abu da matuƙar ƙarfi da kuma ƙwazo, da kuma yin ƙokarin yin wani abu sosai.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "tauri" za'a iya fassara ta da "wuya" ko "taurin kai" ko "ƙalubale" ya danganta ga wurin.
  • Batun nan "taurarewa" ko "taurare zuciya" ko "taurin zuciya" za'a iya fassara shi "halin taurin kai" ko ci gaba da tayarwa" ko "zama da halin tayarwa" ko "zama cikin halin rashin biyayya" "taurin kai da rashin tuba."
  • Kalmar nan "taurararre" za'a iya fassara ta da "halintaurin kai da ƙin tuba" ko ƙin yin biyayya."
  • "Kada ku taurare zuciyarku" za'a iya fassara shi da "kada ku ƙi tuba" ko kuma "kada ku ci gaba da taurin kai na yin rashin biyayya."
  • Waɗansu hanyoyi na "fassara taurin hali" ko "taurin zuciya" sun haɗa da "rashin ji da ƙin yin biyayya" ko "ci gaba da rashin biyayya" ko "ƙin tuba" ko "tayarwa akullum."
  • A cikin furci kamar "aiki tuƙuru" ko "yi ƙoƙari sosai," za'a fassara kalmar da "matuƙar naciya" ko kuma da "ƙarfin hali."
  • Furcin nan "dagewa sosai gãba da" za'a iya fassara shi da "yin watsi da" ko kuma a "watsar."
  • A "ƙuntatawa mutane da aiki mai wahala" za'a iya fassara shi da a "tilasta mutane su yi aiki sosai har su wahala" ko a sa mutane su sha wahala ta wurin matsa musu su yi aiki mai wuya."
  • Wani irin "aiki mai wuya" akan ji shi a lokacin da mace zata haifi jariri.

(Hakanan duba: rashin biyayya, mugunta, aikin mai wahala, taurin kai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 11:23
  • Maimaitawar Shari'a 15:7
  • Fitowa 14:4
  • Ibraniyawa 04:7
  • Yahaya 12:40
  • Matiyu 19:8

taurin wuya, marar ji, rashin ji

Ma'ana

"Taurin wuya" wata karin magana ce da aka mora a Littafi Mai tsarki a nuna mutanen da suka yiwa Allah rashin biyayya suka kuma ƙi tuba. irin waɗannan mutanen masu girman kai ne kuma ba za su yi biyayya da ikon Allah ba.

  • Haka ma kalmar "marar ji" ta na nuna mutumin da ya ƙi ya canza tunaninsa ko ayyukansa ko da an umarce shi da ya yi. mutane marasa ji ba su kasa kunne ga shawara ta gari ko jan kunne da waɗansu mutane ke yi masu.
  • Tsohon Alƙawari ya bayyana Isra'ilawa da "taurin wuya" saboda basu kasa kunne ga saƙon da ya fito daga bakin annabawan Allah ba waɗanda suka umarce su su tuba su koma ga Yahweh.
  • Idan wuya ya "taurare" baya lanƙwashewa ta daɗi. Yaren aikinnan na iya samun wata karin maganar daban da zata iya gamsar da cewa mutumin "bazai tankwaruba" wannan ya nuna cewa mutumin yaƙi canza hanyarsa.
  • Waɗansu hanyoyi na fassara wannan kalmar sun haɗa da "girman kai na rashin ji" ko "tsageranci da marar amfani" ko "kin canzawa."

(Hakanan duba: tsageranci, girman kai, tuba)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:51
  • Maimaitawar Shari'a 09:13-14
  • Fitowa 13:14-16
  • Irmiya 03:17

toka, ƙura

Ma'ana

Kalmar nan "toka" fassararta shi ne fari-farin ƙurar nan da in wuta ta ci itace sai ta bar wannan garin. Wani lokaci ana amfani da shi a kamalta wani abin wofi ko marar amfani.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki wani lokaci kalman nan "ƙura" ana amfani da ita idan ana magana akan toka. Zai iya kuma zama wannan garin ƙasa laulausa, mai dauɗa dake kan busasshiyar ƙasa.
  • "tarin toka" shi ne tsibin toka.
  • A zamanin dã, zaunawa cikin toka alama ce ta makoki da baƙinciki.
  • Lokacin baƙinciki, al'ada ce a sa kaya marasa guga, yagaggun tsumokara a kuma zauna cikin toka ko kuma a baɗa tokar a kai.
  • Baɗa toka a kai alama ce ta ƙasƙantar da kai da jin kunya.
  • Sa'ad da wani yana ƙoƙarin samun wani abu marar amfani, za a ce "yana cin toka."
  • Sa'ad da ana fassara "toka" ayi amfani da kalmar yaren masu fassara da zai nuna toka abu ne da ya rage bayan itace ya ƙone kakaf.
  • Sai ayi lura "itacen toka" wani abu ne daban.

(Hakanan duba: wuta, suturar makoki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 20;10
  • Irmiya 06:26
  • Zabura 102:09
  • Zabura 113:07

tsanani, ƙunci, matsala

Ma'ana

Kalmar "tsanani" na nufin lokacin shan wuya, wahala, da ƙunci.

  • Anyi bayanin ta a Sabon Alƙawari cewa Kiristoci zas jure lokutan wahalhalu da sauran tsanani daban-daban saboda mutane da yawa a wannan duniya suna tsayayya da koyarwar Yesu.
  • "Babban Tsanani" kalma ce da ake amfani da ita a Littafi Mai Tsarki ayi bayanin wani zamani gab da zuwan Yesu karo na biyu sa'ad da fushin Allah zai zubo bisa duniya na shekaru da yawa.
  • Kalmar "tsanani" za a kuma iya fassarawa haka "lokacin babbar wahala" ko "ƙunci mai zurfi" ko "wahalhalu masu tsanani."

(Hakanan duba: duniya, koyarwa, hasala)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Markus 04:17
  • Markus 13:19
  • Matiyu 13:20-21
  • Matiyu 24:09
  • Matiyu 24:29
  • Romawa 02:09

tsanani, tsanantawa, shan tsanani, mai shan tsanani, mai tsanantawa, masu tsanantawa

Ma'ana

Wannan magana "tsanani" da "shan tsanani" manufar shi ne takura wa mutane da hasala. Mai tsanantawa shi ne mutumin da yake musguna wa mutane da azaba.

  • Wannan kalma "mai tsanantawa" masamman ana magana ne akan yadda mutane da suka fi wasu ƙarfi suna bautar da mutanen dake ƙarƙashin ikonsu da mulkinsu.
  • Wannan kalma "masu shan tsanani" sune mutanen da ake azabtarwa cikin fushi.
  • Yawancin lokaci maƙiyan al'umma da sarakunansu su ne masu wahalar da mutanen Isra'ila.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga yadda za a sa shi cikin rubutu, "wahalshewa" za a iya fassarawa haka, "azabtarwa" ko "sa mutum cikin matsananciyar damuwa" ko "sa mutum cikin mummunar bauta" ko "yin mulkin danniya."
  • Wasu hanyoyin fassara "tsanantawa" zai haɗa da "wahala mai azaba da bautarwa" ko "bishewar ƙarfi da yaji."
  • Wannan magana "mai shan tsanani" za a iya fassarawa haka, "wahalallun mutane" ko "mutanen da suke mummunar bauta" ko "waɗanda ake takura masu."
  • Wannan kalma "mai tsanantawa" za a iya fassarawa haka, "mutumin da yake tilastawa" ko "al'ummar da take tilastawa da hasala da danniya a mulki. ko "mai tuhuma."

(Hakanan duba: ɗauri, bautarwa, tuhuma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 10:17-19
  • Maiamaitawar Shari'a 26:07
  • Littafin Mai Wa'azi 04:1
  • Ayuba 10:03
  • Littafin Alƙalai 02:18-19
  • Nehemiya 05:14-15
  • Zabura 119:134

tsananin yunwa, yunwa

Ma'ana

Kalmar nan tsananin yunwa tana nufin matsanancin yanayi na ƙarancin abinci a cikin dukkan ƙasa ko wani yanki kuma yakan faru ne a sakamakon ƙarancin ruwan sama wato fãri.

  • Haka nan abinci kan kasa samuwa a sakamakon ƙarancin ruwa, ko wani ciwo na amfanin gona.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki Allah kan saukar da yunwa domin ya hukunta al'uma a lokacin da suka yi zunubi.
  • A cikin Amos 8:11 kalmar nan "yunwa" an yi amfani da ita ta "salon magana domin a nuna lokacin da Allah zai hukunta mutanensa ta wurin rashin yi musu magana. Za'a iya fassara wanan kalma da "yunwa" a cikin harshenku, ko kuma a irin kalmominku kamar "matsanancin ƙaranci" ko "matsanancin zalunci."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 21:11-12
  • Ayyukan Manzanni 07:11
  • Farawa 12:10
  • Farawa 45:6
  • Irmiya 11:21-23
  • Luka 04:25
  • Matiyu 24:08

tsanantarwa, tsanantawa, tsanani

Ma'ana

Ma'anar "tsanantawa" shi ne a sa wani cikin azaba ko cutarwa. "tsanani" ita ce cuta, ɓacin rai, ko wani bala'i da ya faru domin sa.

  • Allah ya tsanantawa mutanensa da cuta ko wasu abubuwa masu wuya saboda su tuba daga zunubansu su juyo gare shi.
  • Allah ya sa tsanani ko annobai su abko akan mutanen Masar domin sarkinsu ya ƙi yiwa Allah biyayya.
  • "tsanantarwa daga" na nufin shan wuya daga wani abin rashin jin daɗi, kamar ciwo, tsanani, ko ɓacin rai mai sa nishi.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan ana tsanantawa mutum za a iya cewa "sa mutum ne ya shiga cikin matsaloli" ko "a sa shi ya wahala" ko "a sa wahala ta zo kansa."
  • A cikin wasu rubutu "tsanantawa" a iya juyata ta zama da ma'anar "faruwa ga" ko "zuwa ga" ko "kawo wahala"
  • Faɗa kamar "tsanantawa wani da kuturta" za a iya juyata ta zama "sa wani ya kamu da ciwon kuturta."
  • Bisa ga yadda nassi ya yi amfani da kalman nan "tsanantawa' cikin rubutu za a iya ba ta ma'anar "masifa" ko "ciwo" ko "wahala" ko "babban ƙunci' irin na jiki.

(Hakanan duba: kuturta, annoba, wahala)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tasalonikawa 01:06
  • Amos 05:12
  • Kolosiyawa 01:24
  • Fitowa 22:22-24
  • Farawa 12:17-20
  • Farawa 15:12-13
  • Farawa 29:32

tsanantawa, tsanani, tsanance-tsanance, mai shan tsanani, masu tsanantawa, runtuma, masu bin sawu

Ma'ana

Wannan magana "tsanani" ko "tsanantawa" na nufin takurawa wani mutum ko wasu mutane domin azabta su da kuma cutarwa.

  • Za a iya tsanantawa mutum ɗaya ko mutane da yawa kuma yawancin lokaci za a yi ta maimaitawa ne, ana kai hari ba fasawa.
  • Kabilu daban-daban sun tsanantawa Isra'ilawa, suka kai masu hari, suka cafke su, suka sace abubuwa daga gare su.
  • Shugabannin addinin Yahudawa sun tsananta wa Yesu domin basa son abin da yake koyarwa.
  • Bayanda Yesu ya tafi sama, Shugabannin Yahudawa da gwamnatin Roma suka tsananta wa mabiyansa.
  • Wannan magana "tsanantawa" za a iya fassarawa haka, "'ci gaba da musgunawa" ko "tsawatawa cikin haushi" ko "tsanantawa koyaushe."
  • Hanyoyin fassara "tsanani" zai haɗa da waɗannan, "'takurawa da haushi" ko "danniya" ko "cutarwa kullum."

(Hakanan duba: Krista, ikkilisiya, danniya, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:52
  • Ayyukan Manzanni 13:50
  • Galatiyawa 01:13-14
  • Yahaya 05:16-18
  • Markus 10:30
  • Matiyu 05:10
  • Matiyu 05:43-45
  • Matiyu 10:22
  • Matiyu13:20-21
  • Filibiyawa 03:06

tsara

Ma'ana

Kalmar nan "tsara" tana nufin wataƙungiya ce ta mutane waɗanda aka haifi dukkan su kusan a lokaci ɗaya.

  • Za'a iya baiyana "tsara" a kan cewa wani dogon lokaci ne. A kwanakin Littafi Mai Tsarki akan ɗauki tsara akan a ƙalla shekaru arba'in.
  • Iyaye da 'ya'yansu sun taso ne a mabambantan tsararraki guda biyu.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "tsara" akan more ta a cikin salon magana domin ambaton mutanen da ke da halaiya iri ɗaya.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan wanan "tsara" ko "mutanen wanan tsara" za'a iya fassara ta da "mutanen dake rayuwa a zamanin nan" ko "ku mutane."
  • "Wanan muguwar Tsara" za'a iya fassara ta da "waɗanan mugayen mutanen" ko "waɗanan mugayen mutanen da ke rayuwa yanzu."
  • Batun nan "daga tsara zuwa tsara" ko "daga wanan tsara zuwa tsara mai zuwa" za'a iya fassa shi da "mutanen da ke rayuwa yanzu da kuma 'ya'yansu da jikokinsu" ko "mutane na kowanne lokaci" ko "mutanen wanan zamani da kuma zamani mai zuwa" ko dukkan mutane da zuriyoyinsu."
  • "Tsara mai zuwa za ta bauta masa; za su faɗa wa tsara mai zuwa labarin Yahweh" za'a iya fassara ta da "Mutane da yawa a nan gaba za su bautawa Yahweh kuma za su faɗawa 'ya'yansu daq jikokinsu labarinsa."

(Hakanan duba: zuriya, muguwa, uba)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 15:19-21
  • Fitowa 03:13-15
  • Farawa 15:16
  • Farawa 17:7
  • Markus 08:12
  • Matiyu 11:16
  • Matiyu 23:34-36
  • Matiyu 24:34

tsarkakke, tsarkaka

Ma'ana

Kalmar "tsarkaka" na nufin "masu tsarki" yana bayyana masu bangaskiya ga Yesu.

  • Daga baya a tarihin Ikilisiya, mutumin da aka san shi da ayyuka na gari akan ce da shi "tsarkakke," amma ba haka ake amfani da ita ba a zamanin Sabon Alkawari.
  • Masu bi cikin Yesu tsarkaka ne ko kuma masu tsarki, ba domin abin da suka aikata ba, amma domin bangaskiyarsu cikin aikin ceton Yesu. Shi ne wanda ya maishe su tsarkaka.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassarawa "tsarkaka" sun haɗa da "masu tsarki" ko "mutane masu tsarki" ko "mabiya Yesu masu tsarki" ko "waɗanda aka keɓe."
  • Ayi hankali kada ayi amfani da kalmar da nufin mutane kiristoci 'yan ƙungiya ɗaya.

(Hakanan: tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 05:10
  • 2 Korintiyawa 09:12-15
  • Wahayin Yahaya 16:06
  • Wahayin Yahaya 20:9-10

tsaro, tsarewa, mai tsaro, masu tsaro, mai gadi, masu gadi, yi lura,yi zaman tsaro, zauna a faɗake

Ma'ana

Kalmar "tsaro" na manufar a duba wani abu kurkusa cikin hankali. Tana kuma da wasu ma'ana. "Mai tsaro" wani ne wanda aikinsa shi ne ya yi gadin birnin ta wurin kulawa da kowanne sashe da kyau game da wani haɗari ko abin dake na cutarwa ga mutane dake cikin birnin.

  • Umarnin "ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau" na nufin ka yi rayuwar hikima kada kuma ka amince da koyarwar ƙarya.
  • A "kula da" gargaɗi ne na ayi lura domin a kauce daga dukkan haɗari ko abu mai cutarwa.
  • A "kula da" ko "yi tsaro" na iya manufar kodayaushe a zama a faɗake a kuma kiyaye gãba da zunubi da mugunta. Yana iya kuma ma'ana a "zama a shirye."
  • Wasu hanyoyin fassara "tsaro" zasu haɗa da "ayi lura da kyau" ko "ayi ƙwazo" ko "ayi lura sosai" ko "a zama a faɗake."
  • A "kula da" ko "kula da kyau" na iya zama gadi, kiyaye ko kula da wani ko wani abu.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 05:06
  • Ibraniyawa 13:17
  • Irmiya 31:4-6
  • Markus 08:15
  • Markus 13:33-34
  • Matiyu 25:10-13

tsautawa,

Ma'ana

A tsauta na nufin a yi wa wani kasheɗi mai ƙarfi da murya, yawancin lokuta domin a juyo da shi daga zunubi. Wannan kasheɗin tsautawa ne.

  • Sabon Alƙawari na umartar Kiristoci su tsautawa wasu masu bin sa'ad da suke tafiya a zahiri cikin rashin biyayya ga Allah.
  • Littafin Misalai ya umarce iyaye da su tsautawa 'ya'yansu lokacin da suke rashin biyayya.
  • Tsautawa ana yin ta ne don a kiyaye waɗanda suka aikata laifi kada su ƙara dulmaya kansu cikin zunubi.
  • Ana iya fassara ta da nufin "kasheɗi mai ƙarfi" ko "faɗakarwa."
  • Ana iya faɗin kalmar "ɗan tsautawa" a ce "kasheɗi mai ƙarfi" ko "gyara mai ƙarfi."
  • "Rashin tsautawa" ana iya fassara shi "rashin shawara" ko "rashin gyara."

(Hakanan duba: shawara, rashin biyayya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Markus 01:23-26
  • Markus 16:14
  • Matiyu 08:26-27
  • Matiyu 17:17-18

tsokana, cakuna, ban haushi

Ma'ana

Wannan magana "tsokana" ma'anarta shi ne a sa wani mutum ya yi wani abu marar kyau ko ya ji rashin daɗi.

  • Tsokanar mutum zuwa fushi shi ne ayi wani abin da zai sa mutumin nan ya yi fushi. Za a iya fassarawa haka kuma "sa wani ya yi fushi" ko ya ji haushi."
  • Idan an yi amfani da shi a furci kamar haka, "kada ka tsokane shi," za a iya fassara wannan haka "kada ka husata shi" ko "kada ka sa shi ya yi fushi" ko "kada ka sa ya yi fushi da kai."

(Hakanan duba: fushi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

Ezekiyel 20:27-29


tsumma

Ma'ana

Tsumma tufafi ne marar kyaun gani da ake yinsa daga gashin akuya ko da gashin raƙumi.

  • Duk wanda ya sanya tufafin tsummokara ba zai ji daɗi ba. Akan sanya tsumma domin makoki, damuwa, ko tuba cikin tawali'u.
  • Kalmomin nan "tsumma da toka" daɗaɗɗun kalmomi ne ga al'ada dake nuna damuwa da tuba.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma kuma za a iya fassarawa haka "tufafi marar laushi daga gashin dabba" ko "tufafin da aka yi daga gashin akuya" ko "tufafi marar laushi, mai ƙai-ƙai."
  • Wata hanyar fassara wannan kalma zata haɗa da "tufafin makoki marasa laushi, masu ƙai-ƙai."
  • Faɗar "zama cikin tsummokara da toka" za a iya fassarawa haka "a nuna makoki da tawali'u ta wurin sanya tufafi marasa laushi, masu ƙai-ƙai a kuma zauna cikin toka."

(Hakanan duba: toka, raƙumi, akuya, makoki, tuba, alama)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 03:31
  • Farawa 37:34
  • Yowel 01: 8-10
  • Yona 03:05
  • Luka 10:13
  • Matiyu 11:21

tubalin sa tuntuɓe, tubalan sa tuntuɓe, dutsen sa tuntuɓe

Ma'ana

Kalmar "tubalin sa tuntuɓe" ko "dutsen sa tuntuɓe" na nufin abubuwan da ake iya gani da kan sa mutum ya faɗi.

  • Misalin tubalin sa tuntuɓe shi ne kowanne abu da kansa mutum ya faɗi a jiki ko a ruhaniya.
  • A misali kuma, "tubalin sa tuntuɓe" ko "dutsen sa tuntuɓe" na iya zama abin da zai hana wani samun bangaskiya cikin Yesu ko yasa wani ya kasa girma cikin ruhaniya.
  • Kodayaushe zunubi ne ke kama da tubalin sa tuntuɓe ga wani ko waɗansu.
  • Waɗansu lokuta Allah yana sa tubalin sa tuntuɓe a kan hanyar mutanen da suke yi masa tawaye.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan yaren yana da wata kalma kowani abu dake harziƙo tarko, wannan kalmar za a mora wajen fassara wannan kalmar.
  • Wannan kalmar za'a fassara ta da, "dutsen da ke haddasa tuntuɓe" ko "wani abu da yake haddasa wani ya kasa gaskatawa" ko "matsalar da kan haddasa shakka" ko "matsala ga bangaskiya" ko "wani abu da yake sa wani ya yi zunubi."

(Hakanan duba: tuntuɓe, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 01:23
  • Galatiyawa 05:11
  • Matiyu 05:29-30
  • Matiyu 16:23
  • Romawa 09:33

tufata, tufatar

Ma'ana

Sa'ad da aka yi misali da kalmar nan "tufatar da" a cikin Littafi Mai Tsarki ma'anar shi ne a yiwa wani baiwa ko a bayar da wani abu. "Tufatar" da kai da wani abu shi ne mutum ya nemi samun wasu halaye nagari.

  • Kamar yadda ake saye da tufafi a waje a jiki kuma kowa na gani, haka ma sa'ad da ake saye da "tufa" na wasu halaye nagari, nan da nan wasu za su gan shi. "Tufatar da kai da alheri" yana da ma'ana haka, mutum ya cika ayyukansa da alheri har kowa da kowa zai iya gani a fili.
  • Ma'anar "tufatarwa da iko daga sama" shi ne a baka iko.
  • Wannan kalma kuma ana amfani da ita a faɗi abu marar daɗi, misali, "tufatarwa da kunya" ko "tufatarwa da razana."

Shawarwarin Fassara

  • Idan ya yiwu, zai fi kyau a bar kalmar yadda aka saba amfani da ita, "tufatar da kanka da." Wata hanyar fassara wannan shi ne ace "saka" kamar yadda za a sa riga.
  • Idan bai bada cikakken ma'ana ba, wasu hanyoyin fassara "tufatar da" shi ne "nunawa" ko "bayyana" ko "cike da" ko "yana da irin."
  • Wannan kalma "tufatar da kanka da" za a iya fassara shi haka "rufe kanka da" ko "ka yi yadda zai nuna."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 24:49

tunawa, baikon tunawa

Ma'ana

Wannan magana "tunawa" ana nufin wani aiki ko wani abu da zai zama masu abin tuni, kamar "baikon tunawa," da "kashi na tunawa" na hadaya ko "duwatsun tunawa."

  • A cikin Tsohon Alƙawari ana baye-baye na tunawa domin Isra'ilawa su tuna da abin da Allah ya yi masu.
  • Allah ya cewa firitocin Isra'ila su sa tufafi na musamman dake da duwatsun tunawa. Waɗannan duwatsu suna da sunayen kabilu goma sha biyu na Isra'ila rubuce a kansu. An sa waɗannan watakila domin a tunasshe su game da amincin Allah a gare su."
  • A cikin Sabon Alƙawari, Allah ya girmama wani mutum da ake ce da shi Korniliyus saboda ayyukansa na alheri ga matalauta. Aka ce waɗannan ayyukan suka zama abin "tunawa" a gaban Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Za a iya fassara wannan haka, "abin tunawa mai daɗewa."
  • "Dutsen tunawa" za a iya fassara shi a ce "dutse domin ya tuna masu (wani abu)."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 10:04
  • Fitowa 12:12-14
  • Ishaya 66:3
  • Yoshuwa 04:6-7
  • Lebitikus 23:23-25

tunkiya, tunkiyoyi, rãgõ, tumaki garken tumaki, sausayar tumaki,fatun tumaki

Ma'ana

"Tumaki" matsakaitan dabbobi ne dake da ƙafafu huɗu suna kuma da gashi mai laushi a jikinsu. Tumaki na miji ana kiransa "rãgõ" macen tumaki kuma ana kiranta "tunkiya". Jam'in "tumaki" shi ne "tumaki."

  • Yaron tumaki ana kiranta "ɗan rago".
  • Isra'ilawa sunyi amfani da tumaki sun miƙa hadayu, masamman tumaki maza da ƙanana.
  • mutane kan ci naman tumaki su kuma yi amfani da gashinsu suyi sutura da waɗansu abubuwan.
  • tumakai suna da yarda, rauni da rashin magana. Suna da saukin rinjaya zuwa wani wurin daban. Suna buƙatar makiyayi da kan jagorance su, ya kare su, ya kuma samar masu abinci, ruwa, da mahalli.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki an kwatanta mutane da tumaki waɗanda suke da Yahweh a tsayin makiyayinsu.

(Hakanan duba: Isra'ila, ɗan rãgõ, hadaya, makiyayi)

Wuraren da ake samunsu a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08: 32
  • Farawa 30:32
  • Yahaya 02:14
  • Luka 15:05
  • Markus 06:34
  • Matiyu 09:36
  • Matiyu 10:06
  • Matiyu 12:12
  • Matiyu 25:33

tuntuɓa, yin tuntuɓa, tuntuɓaɓɓe, tuntuɓawa

Ma'ana

Kalmar "tutunɓa" tana nufin a tambayi wani wata sadarwa. Batun nan "tuntuɓa" har kusan kullum ana moron ta a yi nufin roƙon Allah domin hikima ko taimako.

  • Tsohon Alƙawari na da ƙididdigar al'amura da yawa inda mutane suka tuntuɓi Allah.
  • Kalmar za'a iya moronta ga batun sarki ko hukuma masu kula da al'amarin naɗi a cikin kundin tarihi.
  • Ya danganta ga wurin, "tuntuɓa" za'a iya fassara ta da "tambaya" ko "neman wata sadarwa."
  • Batun nan "tuntuɓa daga Yahweh" za'a iya fassara ta da "tambayar Yahweh domin jagora" ko "roƙon Yahweh kan abinda za'a yi."
  • A "yi tuntuɓa game da" wani abu za'a fassara ta da "tambaya game da wani abu."
  • Lokacin Yahweh ya ce "ba zaku tuntuɓe ni ba," za'a iya fassara ta da cewa "ba zan bar ku ku tuntuɓe ni kan wata sadarwa ba" ko "ko ba zan barm ku ku nemi taimako daga wurina ba."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 19:18
  • Ezekiyel 20:1
  • Ezekiyel 20:30-32
  • Ezra 07:14
  • Ayuba 10:07

tuntuɓe, yin tuntuɓe, anyi tuntuɓe, ana tuntuɓe, jujjuyawa

Ma'ana

Kalmar "tuntuɓe" na nufin "kusan faɗuwa" lokacin da ake gudu ko tafiya, sau da yawa yakan ƙunshi yin tuntube da wani abu.

  • A taƙaice, " tuntuɓe" na nufin a yi "zunubi" ko a yi "rauni" a gaskatawa.
  • Wannan kalmar tana iya nufin rauni ko nuna gajiyawa lokacin faɗa a yaƙi ko lokacin tsanantawa ko hukunci.

Shawarwarin Fassara:

  • A wannan nassin inda kalmar "tuntuɓe" ke nufin ɗana tarko ga wani abu, za a iya fassara shi da kalmar da take nufin "kusan faɗuwa" ko tsallakewa."
  • Wannan sassauƙar ma'anar kan iya amfani a wannan nassin, idan ta faɗi ma'anar mai kyau a wancan nassin.
  • Domin amfani na kodayaushe sassauƙar ma'anar ba za ta bada ma'ana a yaren aiki ba, "tuntuɓe" ana iya fassara shi da, "zunubi" ko "rauni" ko "daina gaskatawa" ko "raunana," ya danganta da nassin da kalmar ta fito.
  • Wata hanyar fassara wannan kalmar kuma za ta iya zama, " tuntuɓe ta wurin zunubi" ko "tuntuɓe domin rashin gaskatawa."
  • Kalmar "sã tuntuɓe" akan fassara ta da "sa wa a raunana" ko "sa wa a ji rauni."

(Hakanan duba: gaskatawa, tsanantawa, zunubi, dutsen sa tuntuɓe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 02: 08
  • Hosiya 04:05
  • Ishaya 31:3
  • Matiyu 11:4-6
  • Matiyu 18:08

turaren ƙamshi na ƙonawa, turaren ƙamshi iri-iri

Ma'ana

Kalmar nan turare tana nufin gaurayayyun sinadarai masu ƙamshi da ake ƙonawa domin su bada ƙamshi mai daɗi.

  • Allah yi faɗawa Isra'ilawa cewa su ƙona turare a matsayin baiko a gare shi.
  • Turaren za a auna shi ne da ma'auni dai-dai bisa ga irinsa kamar dai yadda Allah ya umarta. Wanan turare ne ayyananne, don haka ba a yarda su yi aiki da shi ba barkatai.
  • A ƙona turare a ƙalla sau huɗu a rana, a kowacce sa'ar addu'a. Hakanan ana ƙona shi a lokacin baiko na ƙonawa
  • Ƙona turare na zama a matsayin addu'a da sujada da ake miƙawa Allah daga mutanensa.
  • Sauran hanyoyi na fassara turaren wuta su ne "turaren hayaƙi" turaren ganyayyaki" ko "tsirai masu daɗin ƙamshi."

(Hakanan duba: bagadin ƙona turare, baiko na ƙonawa, turaren ƙamshi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 03:1-3
  • 2 Tarihi 13:10-11
  • 2 Sarakuna 14:04
  • Fitowa 25:3-7
  • Luka 01:10

turaren wuta

Ma'ana

Turaren wuta turare ne da ake samu daga wani itace mai ƙamshi, ana kuma amfani da shi a yi man shafawa da kayan ƙamshi.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki ana amfani da turare domin adana gawa domin jana'iza.
  • Wanan turaren na da daraja domin warkarwarsa da kuma abubuwan ƙayatarwarsa.
  • Sa'ad da masanan mutane suka ka zo daga gabashin ƙasa su ziyarci jariri Yesu a baitalami, turare na ɗaya daga cikin ɗaya daga kyautansu da suka kawo masa.

(Hakanan duba: Betlehem, masana mutane)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 09:28-29
  • Fitowa 30:34-36
  • Matiyu 02:11-12
  • Littafin Lissafi 05:15

turawa, turewa, turi,

Ma'ana

Wannan magana "turawa" na da ma'ana haka wato a gusar da abu ƙarfi da yaji. Akwai kuma misalan ma'anar wannan magana yawa.

  • Wannan furci "a tura shi can" ma'anar shi ne "ƙi" ko "ƙin yin taimako."
  • "Turawa ƙasa" zai zama da ma'ana haka "wahalshewa" ko "tsanantawa" ko "kayarwa." Zai iya zama da ma'anar ture wani mutum lallai har ƙasa.
  • "Ture wani mutum waje" yana da ma'ana haka "a fitar da" ko "a kori" wannan mutumin.
  • Wannan furci "a tura gaba" ma'anar shi ne a tsare ko a ci gaba da yin wani abu ba tare da an tabbatar ko lallai mai kyau ne ko lafiya.

(Hakanan duba: wahalshewa, tsanantawa, ƙi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:


tushen ubanni, ubanni, uba, ubanni, waɗanda suka zama ubanni, masu zama ubanni, ubannin ubanni, kakanin-kakanin, kakani

Ma'ana

A duk lokacin da aka ambaci kalmar nan "uba" tana nufin mahaifi namiji. Haka nan akwai salon magana da ake amfani da shi wajen amfani da wanan.

  • Kalmar nan "uba" da "tushen ubanni" akan more ta ne idan ana maganar iyaye fanin maza, na wani mutum ko waɗansu mutane. Za'a iya fassara wanan da "ubanni" ko "tushen ubanni."
  • Ƙaulin nan "uba na" cikin salon magana ana moron sa domin ambaton mutumin da ke shugabantar wata ƙungiya, ko kuma wanda ya zama tushen samuwar wani abu. A misali, a cikin Farawa 4 "uban dukkan mazauna runfuna" za'a iya fassara "shi da shugaban kabila ta farko ta mutanen da suka fara zama a runfuna."
  • Manzo Bulus ya yi amfani da salon magana ya kira kansa "uba" ga waɗanda ya temaka su zama krista ta wurin yi musu wa'azin bishara.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan ana magana game da uba da ɗansa, wanan kalmar za'a fassara ta a yi amfani da kalmar uba a cikin harshen.
  • "Allahn Uba" za'a fassara ta a baiyana ma'anar "uba"
  • Idan ana maganar tushen ubanni, wannan za'a fassara shi da "ubannin farko" ko "tsarar ubanni ta fari."
  • Da da Bulus ya yi amfani da salon magana ya ambaci kansa uba ga masu bi, za'a fassara wanan da wanan da "uba na ruhaniya" ko "uba a cikin Kristi."
  • A waɗansu lokutan kalmar nan "uba" za'a fassara ta da "shugaban kabila."
  • Kalmar "uban maƙaryata" za'a fassara ta da "tushen dukkan maƙaryata" ko kuma "wanda ƙarya ta fito."

(Hakanan duba: Allah Uba, ɗa, Ɗan Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:02
  • Ayyukan Manzanni 07:32
  • Ayyukan Manzanni 07:45
  • Ayyukan Manzanni 22:3
  • Farawa 31:30
  • Farawa 31:42
  • Farawa 31:53
  • Ibraniyawa 07:4-6
  • Yahaya 04:12
  • Yoshuwa 24:3-4
  • Littafin Malakai 03:07
  • Markus 10:7-9
  • Matiyu 01:07
  • Matiyu 03:09
  • Matiyu 10:21
  • Matiyu 18:14
  • Romawa 04:12

tushen zuriya ko kabila, kakan kakanni

Ma'ana

Wannan magana "tushen zuriya" a cikin Littafi Mai Tsarki na nufin wani mutum wanda shi ne kakan kakanin mutanen Yahudawa, masamman Ibrahim, Ishaku, da Yakubu.

  • Ana kuma nufin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu waɗanda suka zama kakani 12 na kabilu 12 na Isra'ila.
  • Wannan magana "kakan kakanni" yana da ma'ana iri ɗaya da "ubannin dã" amma ana nufin masamman wani sanannen na miji wanda shi ne shugaba tun farawar kungiyar mutanen.

(Hakanan duba: kakanni, mahaifi, ubanni a dã)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:29-31
  • Ayyukan Manzanni 07:6-8
  • Ayyukan Manzanni 07:09
  • Ezra 03:12-13

umarni, umarta, umartacce, wanda aka umarta, aikin umarni, umarnai, masu bada umarni

Ma'ana

Kalmomin nan "umarni" da "aikin bada umarni" suna nufin bada wani byani na musamman game da abin da za'a yi.

  • "A bada umarni" na nufin a ba wani ko a faɗa wa wani abu na musamman da ya kamata ya yi.
  • Da Yesu ya ba almajiransa gurasa da kifi domin su rarrabawa mutane, ya basu wani umarni na musamman kan yadda za su rarraba.
  • Ya danganta ga wurin, kalmar nan "umarta" za'a iya fassara ta da a faɗa ko "a biyar" ko "a koyar" ko "a bada umarni."
  • Za'a iya fassara da "nuni" ko "bayani" ko "abin da ya faɗa maku ku yi"
  • Da Allah ya bada umarnai, waɗansu lokutan wannan na nufin "dokoki" ko "doka."

(Hakanan duba: umarta, zartarwa, koyi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 14:4
  • Farawa 26:05
  • Ibraniyawa 11:22
  • Matiyu 10:05
  • Matiyu 11:01
  • Littafin Misalai 01:30

umarta, yin umarni, umartacce

Ma'ana

Umurta wani furci ne ko umarni wanda aka shelanta shi a fili ga dukkan mutane.

  • Shari'ar Allah ana kiran ta umarni ko sharuɗoɗi, ko dokoki.
  • Kamar dokoki da umarnai, dole ne a kiyaye umarni.
  • Misalin umarta shi ne wani umarni na shugaban mutane da Sisa Agustus ya yi cewa dukkan mutanen da ke a daular Roma dole ne su koma garuruwansu domin a ƙidaya su.
  • A umarta wani abu na ma'anar cewa a bada umarni da tilas ayi biyayya da shi. Wannan za;a iya yin fassarar sa akan yin "umarni" ko "doka" ko kuma a furta "wani abu na musamman da ake bukata" "umarni domin mutane"
  • Abin da aka "umarta" da zai faru wannan na nufin hakika abin zai faru" ko kuma "an zartar da shi ba kuma za'a canja ba" ko kuma aka aiyana a fili cewa wannan zai faru."

(Hakanan duba: doka, umarni, shari'a, shela)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 15:13-15
  • 1 Sarakuna 08:57-58
  • Ayyukan Manzanni 17:5-7
  • Daniyel 02:13
  • Esta 01:22
  • Luka 02:01

wa'adi, jingina, wa'adodi

Ma'ana

Wannan kalma "wa'adi" na nufin yin alƙawari tare da faɗakarwa za a yi wani abu ko bada wani abu.

  • A cikin Tsohon Alƙawari hakiman Isra'ila sun yi wa'adi zasu yi aminci da Dauda.
  • Kayan da aka bayar jingina za a mayar wa mai shi sa'ad da aka cika alƙawarin.
  • Idan aka yi "wa'adi" za a iya fassara wannan haka, "miƙa kai" ko "ƙwaƙƙwaran alƙawari."
  • Wannan kalma "wa'adi" zai iya zama wani kaya ne da aka bayar da ya zama tabbaci ko alƙawari cewa za a biya wannan bashi.
  • Wasu hanyoyin fassara "wa'adi" zai haɗa da waɗannan, "alƙawari da faɗakarwa" ko "sa hannu a gaban shaidu" ko "jingina" ko "tabbatarwa da shaida," ya dai danganta ga nassi.

(Hakanan duba: alƙawari, rantsuwa, wa'adi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 05:4-5
  • Fitowa 22:26
  • Farawa 38:17-18
  • Nehemiya 10:28-29

wadata, bunƙasa, wadatacce, samu, lafiya

Ma'ana

Wannan mgana "azurta" yawancin ma'anar shi ne zaman wadata zai iya kuma zama bunƙasa cikin ruhaniya da cikin jiki. Idan mutane ko ƙasa tana "azurta" ma'anar shi ne suna da wadata suna kuma da dukkan abin da suke buƙata suyi nasara. Wato suna da ingantaccen "samu."

  • Wannan magana "wadatacce" yawancin lokaci na nufin nasara wajen samun kuɗi da dukiya ko yin abubuwan da mutane suke buƙata domin su yi rayuwa mai lafiya.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan magana "wadata" yana haɗe da kyakkyawar lafiya da kuma albarkar 'ya'ya.
  • ‌"Birni ko ƙasa "mai wadata" shi ne wanda yake da mutane da yawa, yana bada abinci da kyau, da kuma cinikayya mai kawo kuɗi da yawa.
  • Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa mutum zai wadata a ruhu idan ya yi biyayya da koyarwar Allah. Zai kuma sami murna da kwanciyar rai. Ba kullum Allah ke ba mutane kayan dukiya ba, amma zai azurta su koyaushe a ruhaniya sa'ad da suke bin hanyoyinsa.
  • Ya danganta bisa ga nassi, wannan kalma "wadata" za a iya fassarawa haka, "nasara cikin ruhaniya" ko "Allah ya albarkata" ko "a sami abubuwa masu kyau" ko "rayuwa cikin wadata."
  • Wannan magana "bunƙasa" za a iya fassarata haka "samun nasara" ko "wadata" ko "'ya'ya a ruhaniya."
  • Za a iya fassara "Arziki" haka, "rayuwa mai armashi" ko "wadata" ko "nasara" ko "albarka mai ɗunbin yawa."

(Hakanan duba: albarka, 'ya'ya, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 29:22-23
  • Maimaitawar Shari'a 23:06
  • Ayuba 36:11
  • Lebitikus 25:26-28
  • Zabura 001:3

wahayi, wahayoyi, hangen nesa

Ma'ana

Kalmar "wahayi" na nufin wani abin da mutum ya gani. Wani abu ne wanda yake na musamman da ba a saba gani ba ko na ruhaniya da Allah ke bayyana wa mutane domin ya basu sãƙo.

  • Yawancin lokaci, ana ganin wahayi ne sa'ad da ba barci mutum yake yi ba. Duk da haka, wani lokacin wahayi abu ne wanda mutum ke iya gani a mafarki sa'ad da yake barci.
  • Allah na aiko da wahayi ga mutane domin ya gaya masu abin dake da muhimmanci. Ga misali, an bayyana wa Bitrus wani wahayi domin a gaya masa cewa Allah yana son ya yi maraba da al'ummai.

Shawarwarin Fassara:

  • Faɗar "na ga wahayi" za a iya fassarawa haka "na ga wani abu na daban daga Allah" ko "Allah ya nuna mani wani abu na musamman."
  • Wasu yarurrukan na iya kasancewa basu da kalmomi domin "wahayi" da "mafarki." To jimla kamar haka "Daniyel ya sami mafarkai da wahayoyi a cikin ransa" za a iya fassarawa kamar haka "Daniyel na mafarki yayin da yake barci kuma Allah ya sanya shi ya ga wasu abubuwa daban."

(Hakanan duba: mafalki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 09:10-12
  • Ayyukan Manzanni 10:3-6
  • Ayyukan Manzanni 10:11
  • Ayyukan Manzanni 12:9-10
  • Luka 01:22
  • Luka 24:23
  • Matiyu 17:9-10

wakili wakilai, ma'aikaci, ma'aikata, wakilci

Ma'ana

Wannan magana "wakili" ko "ma'aikaci" a cikin Littafi Mai Tsarki na magana game da bawa da aka bashi amanar lura da dukiyar mai gidansa ko sha'anin kasuwancinsa.

  • A kan ba wakili ayyuka da yawa, da ya haɗa har da duba ayyukan wasu barorin.
  • Wannan furci "ma'aikaci" fassarar zamani ce da ta maye gurbin wakili. Dukkansu biyu dai suna magana ne a kan wani mutum ne da yake lura da sha'anin wani mutum.

Shawarwarin Fassara:

  • Za a iya fassara shi haka, "mai dubawa ko "mai bida gida" ko "bawa mai kulawa" ko "mutum mai bishewa."

(Hakanan duba: bawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 03:4-5
  • Farawa 39:04
  • Farawa 43:16
  • Ishaya 55:10-11
  • Luka 08:03
  • Luka 16:02
  • Matiyu 20:8-10
  • Titus 01:07

warkar, warkarke, warkarwa, warkarke yin warkarwa, mai warkarwa, lafiya, mai lafiya, mara lafiya

Ma'ana

Kalmar nan "warkar" da "watsakar" duk abin da suke nufi shi ne a sa mara lafiya ko mai rauni ya warke.

  • Mutumin da aka "warkar" ko "watsakar" an "maido shi lafiyayye kenan."
  • Warkarwa na iya faruwa haka nan kawai tun da yake Allah ya ba jikkunanmu damar farfaɗowa daga cututtuka da raunuka masu yawa. Har kullum irin wanan warkarwar na faruwa ne sannu kan hankali.
  • Duk da haka, waɗansu al'amura kamar zama makaho, shanyayye, da dai waɗansu cututtuka masu muni kamar kuturta, su basu warkewa haka nan kawai. Lokacin da aka warkar da mutane daga irin wanan cutar abin yakan zama abin mamakiwanda ke faruwa ba zato.
  • Misali, Yesu ya warkar da mutane da yawa da ke da makanta ko gurguntaka ko ciwata, kuma nan take suka warke.
  • Manzanni ma sun warkar da mutane ta hanyar mu'juza, kamar a lokacin da Bitrus ya warkar da gurgu da ya yi wuf ya fara tafiya.

(Hakanan duba: mu'ujuza)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 05:16
  • Ayyukan Manzanni 08:6
  • Luka 05:13
  • Luka 06:19
  • Luka 08:43
  • Matiyu 04:23-25
  • Matiyu 09:35
  • Matiyu 13:15

wasiƙa ta musamman, wasiƙa, wasiƙu

Ma'ana

Wasiƙa saƙo ne a rubuce wanda ake aika wa wani taliki ko wasu ƙungiyar talikai waɗanda yawanci suna nesa da marubucin. Wasiƙa ta musamman wata irin wasiƙa ce da ake rubutawa da wani salo daban, domin wani dalili na musamman, kamar koyarwa.

  • A zamanin Sabon Alƙawari, wasiƙa ta musamman da sauran wasiƙu ana rubuta su a kan fãtar dabbobi ko takardar da aka yi daga dusar katako.
  • Wasiƙu na musamman na Sabon Alƙawari daga Bulus, Yakubu, Yahuda, da Bitrus wasiƙu ne na umarni suka rubuta domin su ƙarfafa, faɗakar, su kuma koyar da Kiristocin farko a birane daban-daban cikin dukkan daular Romawa.
  • Hanyoyin da za a iya fassara wannan kalma sun haɗa da "rubutaccen saƙo" ko "rubutattun maganganu" ko "rubutu."

(Hakanan duba: ƙarfafawa, faɗakarwa, koyarwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 05:27
  • 2 Tasalonikawa 02:15
  • Ayyukan Manzanni 09:1-2
  • Ayyukan Manzanni 28:21-22

wata, watanni, wata-wata

Ma'ana

Wannan kalma "wata" ana nufin wani tsawon lokaci ne da ya kai sati huɗu. Adadin ranaku cikn kowanne wata sun banbanta domin ya danganta ga kalandar da aka yi amfani da ita ko ta wata ce ko kuma ta rana ce.

  • A cikin kalandar wata, tsawon kowanne wata an ƙayyada shi akan tsawon lokacin da wata yake ɗauka ya zagaya duniya, kimamin kwana 29. A cikin wanna tsari akwai watanni 12 ko 13 cikin shekara. Koda shike shekarar tana da watanni 12 ko13, watan fari koyaushe ana kiransa da sunansa ba sauyi koda shike lokaci ya banbanta.
  • "Sabon wata" ko farkon fuskar wata mai ƙyallin azurfa, shi ne ya zama farkon kowanne wata a kalandar da ake kira kalandar wata.
  • Duk sunayen watanni da aka ambata cikin Litafi Mai Tsarki na kalandar wata ne tunda shike wannan tsarin ne Isra'ilawa suka yi amfani da shi. Yahudawan wannan zamani har wa yau suna amfani da wannan kalandar a sha'anin addini.
  • Kalandar rana ta zamani an tsara ta akan tsawon lokacin da duniya ke ɗauka ta zagaya rana (kimamin kwana 365). A wannan tsari koyaushe ana raba shekara cikin watanni goma sha biyu, kowanne wata nada tsawon kwanaki tsakanin 28 zuwa 31.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 20:34
  • Ayyukan Manzanni 18:9-11
  • Ibraniyawa 11:23
  • Littafin Lissafi 10:10

watsi, watsarwa, ƙi, ƙin karɓuwa

Ma'ana

A yi "watsi" da wani ko wani abu na nufin rashin amincewa da wannan mutum ko wani abun.

  • Kalmar "watsi" kuma na iya zama "rashin yarda da" wani abu.
  • A yi watsi da Allah na nufin a ƙi amincewa da shi.
  • Lokacin da Isra'ilawa suka ƙi shugabancin Musa, ya nuna da cewa suna tawaye ne ga ikonsa. Basu so ne su yi biyayya da shi.
  • Isra'ilawa sun nuna cewa sun yi watsi da Allah a sa'ad da suka yi sujada ga allolin ƙarya.
  • Kalmar "tũrewa" shi ne ainihin ma'anar wannan kalma. Wasu yarurruka za su iya samun irin wannan da ke ma'anar watsi ko ƙin a gaskata da wani ko wani abu.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, kalmar "watsi" za a iya fassarawa haka "a ƙi karɓa" ko a "daina taimako" ko "a ƙi yin biyayya" ko "a daina yin biyayya."
  • A faɗar "dutsen da magina suka watsar," kalmar "watsi" za a iya fassarawa "a ƙi amfani da" ko "a ƙi karɓa" ko "a yar" ko "a kawar a matsayin marar amfani."
  • A nassin da mutane suka yi watsi da dokokin Allah, za a iya fassara watsi haka "ƙin yin biyayya" da dokokinsa ko "an zaɓi a taurare daga karɓar" shari'ar Allah.

(Hakanan duba: doka, rashin biyayya, biyayya, taurin wuya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 04:12-14
  • Hosiya 04:6-7
  • Ishaya 41:09
  • Yahaya 12:48-50
  • Markus 07:09

wulaƙanci, wulaƙantarwa, wulaƙantacce, na wulaƙantarwa

Ma'ana

Kalmar nan "wulaƙanci"tana nufin rasa girma da darajantawa.

  • Lokacin da mutum ya yi wani na zunubi, zai iya sa shi ya kasance a cikin halin wulaƙanci da rasa daraja.
  • Kalmar nan "wulaƙantarwa" ana amfani da ita domin nuna aikin zunubi ko kuma ga mutumin da ya yi zunubin.
  • A waɗansu lokutan mutumin da ke yin abin da nagari akan yi ƙoƙarin wulaƙantar da shi ko a kunyatar da shi.
  • Misali a lokacin da aka kashe Yesu akan giciye, wanan tafarki ne na wulaƙantarwa mutuwance, Yesu bai yi wani abu da ba dai-dai ba da har zai sa a yi masa wanan wulaƙancin.
  • Hanyoyin fassara wulaƙantarwa sun haɗa da "kunyatarwa" ko "ƙasƙantarwa."
  • Hanyoyin fassara abin "kunyatarwa" sun haɗa da "ƙasƙantarwa" ko "kunyatarwa."

(Hakanan duba: ƙasƙantarwa, girmamawa, kunyatarwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 03:07
  • Farawa 34:07
  • Ibraniyawa 11:26
  • Littafin Makoki 02:1-2
  • Zabura 022:06

wuri mafi bisa, wurare mafi bisa

Ma'ana

Kalmar nan "wurare mafi bisa" na nufin bagadai na masujujadai da ake bautar gumaka. Akan fi giggina su ne a wurare masu bisa, kamar kan tsaunuka da duwatsu.

  • Sarakunan Isra'ila sun yiwa Allah zunubi ta wurin kafa bagadai na allolin ƙarya a wurare masu tudu. wannan ya cusa mutane su shiga bautar gumaka sosai.
  • Yakan fi faruwa ne a lokacin da sarakuna masu tsoron Allah suka fara mulkin Isra'ila ko Yahuda, sau da yawa sukan kawar da waɗannan wurare masu bisa domin dakatar da bautar waɗannan allohli.
  • Bugu da ƙari, waɗansu daga waɗannan sarakuna na gari sun zama da rashin kula basu kuma kawar da waɗannan wurare masu bisa ba, wanda sakamakon hakan ya kai dukkan al'ummar Isra'ila su ci gaba da bautar gumaka.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyin da za'a fassara wannan kalma "ƙayatattun wurare domin bautar gumaka" ko "dogayen gumaka na dogayen tsaunuka" ko "gunki na zubi."
  • A tabbatar ta fita cewa wannan kalmar tana nufin bagadan gumaka, ba wai kawai wurare masu tudu ba da wurin da aka kakkafa waɗannan bagadai.

(Hakanan duba: bagadi, allahn ƙarya, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 09:12-13
  • 2 Sarakuna 16:4
  • Amos 04:13
  • Maimaitawar Shari'a 33:29
  • Ezekiyel 06:1-3
  • Habakuk 03:19

wuta, wuta da yawa, mafitar wuta, wuraren wuta, tukunyar wuta, tukwanen wuta

Ma'ana

Wuta zafi ne,haske ne da ke samuwa sakamakon ƙona wani abu.

  • Itatuwan da aka aka ƙona kan zama toka.
  • Kalmar nan "wuta" ana iya moron salon magana a ce da ita hukunci ko tsarkakewa.
  • Shari'ar ƙarshe ta marasa bi ita ce wutar jahannama.
  • Ana amfani da wuta domin tsarkake zinariya da sauran ƙarafa. A cikin Littafi mai Tsarki ana amfani da wanan matakin a baiyana yadda Allah ke tace mutane ta wurin abubuwa masu wuya da kan faru a cikin rayuwarsu.
  • Kalmar nan "baftisima da wuta" za'a iya fassara "ta da a sa mutum ya sha wuya domin ya tsarkaka."

(Hakanan duba: tsafta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 16:18-20
  • 2 Sarakuna 01:10
  • 2 Tassalonikawa 01:8
  • 2 Tassalonikawa 01:8
  • Ayyukan Manzanni 07:29-30
  • Yahaya 15:6
  • Luka 03:16
  • Matiyu 03:12
  • Nehemiya 01:3

wuya, barni, wahaloli, shan wuya, sha wuya, shan wahala

Ma'ana

Kalmar "wuya" da "wahala" na nufin fuskantar wani abu marar daɗi, kamar rashin lafiya, tsanani, ko wata damuwa.

  • Idan ana tsanantawa mutane ko idan basu da lafiya, suna shan wuya.
  • Wasu lokutan mutane na shan wuya saboda abubuwa marasa kyau da suka yi; a wasu lokutan sukan sha wuya saboda zunubi da cuta a duniya.
  • Wahala na iya zama a jiki, kamar jin zafi ko rashin lafiya. Yakan iya zama a cikin tunani, kamar jin tsoro, ɓacin rai, ko kaɗaici.
  • Kalmar "barni" na nufin "yi hakuri dani" ko "ka saurare ni" ko "yi hakurin sauraro."

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "wuya" akan fassarata da "jin zafi" ko "jurewa wahala" ko "jin damuwoyi" ko "shiga cikin tsanani da jin zafi."
  • Ya danganta da nassin, "wahala" akan fassara ta da "yanayi mai tsananin wahala" ko "damuwa ta gaske" ko "ɗanɗana matsala" ko "lokacin ɗanɗana tsanani."
  • Kalmar "wuyar ƙishi" akan fassara ta da "ɗanɗana ƙishi" ko "shan wahalar ƙishi."
  • "Wahalar rikici" akan iya fassara shi da "fuskantar rikici" ko "cutuwa ta dalilin rikici."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 02:14-16
  • 2 Tasalonikawa 01:3-5
  • 2 Timoti 01:08
  • Ayyukan Manzanni 07 :11-13
  • Ishaya 53:11
  • Irmiya 06:6-8
  • Matiyu 16:21
  • Zabura 022:24
  • Wahayin Yahaya 01:09
  • Romawa 05:3-5

yabo, yabbai, yabawa, yin yabo, isa yabo

Ma'ana

Idan an yabi mutum ana furta sha'awa da girmamawa ga mutumin nan.

  • Mutane sukan yabi Allah domin yawan girmansa kuma domin dukkan abubuwan al'ajibi da ya yi a matsayin Mahallici da mai ceton duniya.
  • Yabon Allah yawancin lokaci yakan haɗa da godiya domin abin da ya yi.
  • Ana amfani da waƙoƙi yawancin lokaci a yabi Allah.
  • Yabon Allah ma na ɗaya daga cikin hanyoyin yiwa Allah sujada.
  • Wannan magana "yabo" za a iya fassarawa haka "a faɗi abu mai kyau akan wani" ko "a girmama wani da kalamu" ko "a faɗi kyawawan abubuwa game da."
  • Wannan magana "yabo" za a iya fassarawa haka "girmamawa da baka" ko "maganar karamtawa" ko "faɗar abubuwa nagari game da."

(Hakanan duba: sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korantiyawa 01:03
  • Ayyukan Manzanni 02:47
  • Ayyukan Manzanni 13:48
  • Daniyel 03:28
  • Afisawa 01:03
  • Farawa 49:8
  • Yakubu 03:9-10
  • Yahaya 05:41-42
  • Luka 01:46
  • Luka 01:64-66
  • Luka 19:37-38
  • Matiyu 11:25-27
  • Matiyu 15:29-31

Yahudanci, addinin Yahudanci

Ma'ana

Kalmar "Yahudanci" na nufin addinin da Yahudawa suke yi. Kuma ana nufin "addinin Yahudanci."

  • A Tsohon Alƙawari, kalmar "addinin Yahudanci" aka mora, yayin da a Sabon Alƙawari, kalmar "Yahudanci" ake mora.
  • Yahudanci a Tsohon Alƙawari ya haɗa da dukkan shari'u da umarnai waɗanda Allah yaba mutanen Isra'ila suyi biyayya da su. Ya sake kuma haɗawa da ɗabi'u da al'adu da aka haɗa da su a addinin Yahudanci cikin zamanai.
  • Sa'ad da ake fassara kalmar "addinin Yahudanci" ko "addinin Yahudawa" ana iya morar su a Tsohon Alƙawari duk da Sabon Alƙawari.
  • Kalmar "Yahudanci," kuwa za a more ta kawai a Sabon Alƙawari, tunda kalmar bata wanzu ba kafin wannan lokacin.

(Hakanan duba: Bayahude, shari'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 01:13-14

yanka, yankewa, yankawa

Ma'ana

Kalmar " yanka" na nufin kashe dabbobi da yawa ko mutane, ko kashewa ta hanyar tashin hankali. Yana kuma iya zama kashe dabbobi domin ci. Yin aikin yanka shi ake nufi da "yankawa."

  • Lokacin da Ibrahim ya karɓi baƙuncin bãƙi guda uku gidansa a daji, ya umarci baransa ya yanka ya kuma girka bijimi domin bãƙinsa.
  • Annabi Ezekiyel ya yi anabci cewa Yahweh zai aiko da mala'ikansa ya yayyanka duk wanda ya ƙi bin maganarsa.
  • 1 Sama'ila ya rubuta wani gagarimin yanka da akayi inda aka kashe Isra'ilawa guda 30,000 ta hannun maƙiyansu saboda rashin biyayya ga Yahweh.
  • "Makamin yanka" za a iya fassara shi da " makamin kisa."
  • Faɗar "yankan yana da girma" akan iya fassara shi da " dayawa aka yanka" ko yawan waɗanda suka mutu na da yawa" ko " mutanen da suka mutu na da matuƙar yawa."
  • Waɗansu hanyoyin da akan iya fassara "yanka" sun haɗa da "kisa" ko "hallakawa" ko " kashewa."

(Hakanan duba: mala'ika, saniya, rashin biyayya, Ezekiyel, bara, yankawa)

Wuraren da akan samesa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 21:10-11
  • Ibraniyawa 07:01
  • Ishaya 34:02
  • Irmiya 25:34

yarima, yarimai, gimbiya, gimbiyoyi, gwamnoni, gwamnonin larduna, hakimai, dattawa, bafade

Ma'ana

"Yarima" ɗan sarki ne. "Gimbiya" ɗiyar sarki ce.

  • Wannan magana "yarima" yawancin lokaci ana nufin shugaba ne, mai mulki, ko wani mai iko.
  • Saboda arziƙin Ibrahim da girmansa, Hittiyawa da yake zama a tsakiyarsu suka kira shi "yarima."
  • A cikin littafin Daniyel, wannan suna "yarima" an yi amfani da ita a wannan furci "yariman Fasiya" da "yariman Giris," wanda a cikin rubutun ana nufin watakila wasu ruhohi ne masu karfi waɗanda suke da iko akan waɗannan yankunan.
  • Babban Mala'ika Makel shima ana kiransa "yarima" a littafin Daniyel.
  • Wani lokaci a Littafi Mai Tsarki ana ambatar Shaiɗan haka "yariman wannan duniya."
  • Ana kiran Yesu "Yariman Salama" da kuma "Yariman Rai."
  • A cikin Ayyukan Manzanni 2:36, an kira Yesu "Ubangiji da Almasihu" kuma a cikin Ayyukan Manzanni 5:31 an kira shi "Yarima da Mai Ceto," ana nuna ma'ana biyu "Ubangiji" da "Yarima ko sarki."

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "yarima" zai haɗa da waɗannan, "ɗan sarki" ko "mai mulki" ko "shugaba" ko "babba dukka" ko "hafsa."
  • Idan ana magana akan mala'iku, za a iya fassarawa haka, "ruhu mai mulki" ko "mala'ika shugaba."
  • Idan ana magana akan Shaiɗan ne ko wasu mugayen ruhohi, wannan magana za a iya fassarawa haka "mugun ruhu mai mulki" ko "ruhu mai ƙarfi shugaba."ruhu mai mulki," zai danganta bisa ga nassi.

(Hakanan duba: mala'ika, iko, Almasihu, mugun ruhu, ubangiji, ƙarfi, mai mulki, Shaiɗan, Mai Ceto, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 05:29-32
  • Farawa 12:15
  • Farawa 49:26
  • Luka 01:52

yassashe, yasarwa, yasassu, kaɗaici, rabuwa da kowa da zama a kaɗaice, yashewa

Ma'ana

Kalmar nan "yasasshe" da kuma yasarwa tana magana ne akan wani yanki da aka rushe domin ya zama yasasshe ko ba kowa.

  • In kuma ana maganar mutum, kalmar na nufin yanayi na zaman kaɗaici cikin damuwa.
  • Kalmar nan yasarwa" wani yanayi ne na yashewa.
  • In wurin da amfani ke tsirowa ya zama yasashe wannan na nufin wani abu ya ɓata amfanin gonar kamar ƙwari ko tawagar soja mahara.
  • Yasasshen yanki na nufin wuri ko ƙasa inda sai mutane kima ne kawai ke zama sabo da ƙarancin amfanin gona a can.
  • In wani birni ya zama "yasasshe" wannan na nufin an rushe gine-ginen birnin abubuwan da ke cikin birnin kuma an sace ko kuma an hallaka su, kuma an kwashe mutanen birnin ko kuma an kashe su. Birnin ya zama "kango" "kufai kuma" wanan ma ya yi kama da sharewa ko wurin da akayiwa kaca-kaca," amma yana jaddada rashin komai ne.
  • Ya danganta ga abin da wurin ke faɗi, wanan kalmar za'a iya fassara ta a matsayin "kufai" ko "rusasshe" ko wanda aka "ɓata" ko "wanda aka yi watsi da shi" ko wanda aka "yasar."

(Hakanan duba: hamada, rusasshe, kufai, batacce)

Wuraren da ake samuna a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 22:19
  • Ayyukan Manzanni 01:20
  • Daniyel 09:17-19
  • Makoki 3:11
  • Luka 11:17
  • Matiyu 12:25

yin ciki, ɗaukar ciki

Ma'ana

Waɗannan kalmomi "yin ciki" da "ɗaukar ciki" yawancin lokaci ana nufin ɗaukar cikin yaro. Za a iya amfani da kalmar ga dabbobin da suka ɗauki ciki.

  • Wannan furci "yin cikin yaro" za a iya fassara shi haka "yin ciki" ko wasu kalamu karɓaɓɓu.
  • Wannan kalma ta kusa da ita "tayi ciki" za a iya fassara ta haka, "farkon yin ciki" ko "lokacin yin ciki."
  • Waɗannan kalamu suna magana akan yin wani abu ko tunanin wani abu, kamar wani tunani, shiri, ko aiki. Wasu hanyoyin fassara za su haɗa da, "yi tunani a kai" ko "shiri" ko "sifanta," bisa ga yadda ya kamata a cikin rubutu.
  • Wani lokaci wannan kalma za a iya yin misali da ita kamar haka "lokacin da zunubi yayi ciki" ma'ana "lokacin da aka fara tunanin yin zunubi" ko "daga farkon zunubi na fari" ko "lokacin da zunubi yake fara shiga."

(Hakanan duba: halicci, mahaifa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 21:1-4
  • Hosiya 02:4-5
  • Ayuba 15:35
  • Luka 01:24-25
  • Luka 02:21

yin wa'azi, mai wa'azi, wa'azi, shela

Ma'ana

Yin "wa'azi" shi ne yin magana wa wasu taron mutane, ana koya masu game da Allah ana masu gargaɗi suyi masa biyayya. Yin "shela" na nufin faɗar magana da ƙara kowa na ji da kuma gabagaɗi.

  • Yawancin lokaci mutum ɗaya ke wa'azi ga dumbun mutane. Yawancin lokaci ana faɗi ne, ba a rubuce ba.
  • "Wa'azi" da "koyarwa" kusan ɗaya suke, amma ba ɗaya suke ba sosai.
  • "Wa'azi" ana shela ne a fili ga mutane game da ruhaniya da rayuwar gaskiya, ana tuntuɓar masu sauraro su yi wani abu. "Koyarwa" kuwa masamman tana bada shawarwari, wato, ba mutane sani game da abubuwa ko kuma koya masu yadda zasu yi wani abu.
  • Wannan magana "wa'azi" yawancin lokaci ana amfani da ita tare da kalmar nan "bishara."
  • Abin da wani mutum ya yiwa wasu wa'azi akai za a iya kiransa "koyarwarsa."
  • Yawancin lokaci a cikin Littafi Mai Tsarki, ma'anar "shela" shi ne a faɗi abu a fili ga jama'a wani abin da Allah ya umarta ko a faɗa wa wasu game da Allah da yadda yake da girma.
  • A cikin Sabon Alƙawari, manzanni sun yi shelar labari mai daɗi game da Yesu ga mutane da yawa a birane daban-daban da larduna.
  • Wannan magana "shela" za a iya amfani da ita a wajen dokoki da sarakai suke bayarwa ko domin gargaɗi akan mugunta wurin taron mutane.
  • Wasu hanyoyin fassara "shela" zasu haɗa da waɗannan "a faɗi abu da ƙarfi" ko "yin wa'azi a sarari" ko "Faɗin abu a fili."
  • Wannan magana "shela" za a iya fassara ta haka "sanarwa" ko "yin wa'azi ga mutane a fili."

(Hakanan duba: labari mai daɗi, Yesu, mulkin Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:1-2
  • Ayyukan Manzanni 08:4-5
  • Ayyukan Manzanni 10:42-43
  • Ayyukan Manzanni 14:21-22
  • Ayyukan Manzanni 20:25
  • Luka 04:42
  • Matiyu 03:1-3
  • Matiyu 04:17
  • Matiyu 12:41
  • Matiyu 24:14
  • Ayyukan Manzanni 09:20-22
  • Ayyukan Manzanni 13:38-39
  • Yona 03:1-3
  • Luka 04:18-19
  • Markus 01:14-15
  • Matiyu 10:26

zaitun, zaituna

Ma'ana

Zaitun wani ƙaramin ɗiyan itaciya ne da ake samunsa daga itacen zaitun, wanda yake girma a yankin Tekun Baharmaliya.

  • Itacen zaitun wani babba ne cikin ƙananan itatuwa, kullum kore shar yake, yana kuma da wasu ƙananan furanni farare. Sun fi girma a yanayi mai zafi suna da juriyar ƙarancin ruwa.
  • 'Ya'yan itacen zaitun sukan fara fita kore amma idan suka fara nuna sai su sauya su zama baƙaƙe. Ana amfani da zaituna domin abinci da kuma mai da ake matsowa daga cikinsu.
  • Ana amfani da man zaitun domin girki a cikin fitilu da kuma ayyukan addini.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki wani lokaci ana kwatanta mutane da itatuwan zaitun da rassansa.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 27:28-29
  • Maimaitawar Shari'a 06:10-12
  • Fitowa 23:10-11
  • Farawa 08:11
  • Yakubu 03:12
  • Luka 16:06
  • Zabura 052:08

zakoki, zaki, zakanya,

Ma'ana

Zaki wani babban dabba mai kama da kyanwa, yana da hakora masu karfi da kofato domin kisa da yayyage dabbar daya kamo.

  • Zakoki suna da jiki mai karfi ga iya gudu domin kama dabbar farauta. Gashinsu ba tsawo kuma kalar zinariya kasa kasa.
  • Namijin zakoki suna da gashi da ya zagaye kawunansu.
  • Zakoki sukan kashe wasu dabbobi su cinye su suna kuma da hatsari ga mutane.
  • Da Sarki Dauda da yake ɗan yaro, ya kashe zakoki da suka yi kokarin su hari tumakin da yake lura da su.
  • Samson shima ya kashe zaki, da hannuwansa.

(Hakanan duba: Dauda, damisa, Samson, tunkiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 11:22-23
  • 1 Sarakuna 07:29
  • Littafin Misalai 19:12
  • Zabura 017:12
  • Wahayin Yahaya 05:05

zargi, zarge-zarge, yin zargi, da zargi

Ma'ana

Yi wa wani zargi na manufa da a yi masa sukã ko a ƙi yin na'am da hali ko yanayinsa. Zargi mugun furci ne game da mutumin.

  • Kalmar magana da ta ce wani ya "wuce gaban zargi" ko "babu zargi" na nufin cewa wannan mutum yana tafiyarsa cikin tsoron Allah ta hanyar bangirma har ma babu wani sauran abin da za a iya a zarge shi da shi.
  • Kalmar "zargi" za a iya kuma fassarawa haka "bada laifi" ko "kunya" ko "kunyatarwa."
  • A "zargi" za a iya fassarawa haka "tsautawa" ko a "bada laifi" ko ayi "yanke," ya danganta ga nassin.

(Hakanan duba: zargi, tsautawa, kunya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 05:7-8
  • 1 Timoti 06:13-14
  • Irmiya 15:15-16
  • Ayuba 16:9-10
  • Littafin Misalai 18:03

zinariya, na zinariya

Ma'ana

Zinariya wani ƙarfe ne mai inganci da ake mora domin yin abn wuya da kayayyakin addini. A kwanakin da ita ce ƙarfe mafi daraja.

  • A kwanakin Littafi Mai Tsarki, akan yi abubuwa iri-iri da zinariya mai kauri ko kuma a dalaye su da zinariya mai kauri.
  • Waɗanan abubuwan sun haɗa da 'yan kunne da sauran kayayyakin ado, da gumaka, da bagadai, da sauran kayayyakin da ake mora a cikin masujada ko haikali, kamar kuma sunduƙin alƙawari.
  • A Tsohon Alƙawari, ana moron zinariya domin yin ciniki ta fuskar saye da sayarwa. Akan ɗora a ma'auni domin auna darajarta.
  • Daga bisani, azurfa da sauran ƙarafa ana moron su domin yin kuɗi domin gudanar da cinikin saye da sayarwa
  • In ana batun wani abu da ba zinariya mai kauri ba, amma aka dalaye su da zinariya, kalmar nan "na zinariya" ko "wanda aka dalaye da zinariya" ko "abin da aka rufe da azurfa" suma duk za'a iya moron su.
  • Wani lokaci akan baiyana abu da abin da aka yi wa kwalliya da zinariya wanda ke nuna yana da "kalar zinariya' amma ba zai zama cewa tsantsar zinariya ba ce.

(Hakanan duba: bagadi, sanduƙin alƙawari, allahn ƙarya, azurfa, rumfar taruwa, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:7
  • 1 Timoti 02: 8-10
  • 2 Tarihi 01:15
  • Ayyukan Manzanni 03:6
  • Daniyel 02:32

zubar da jini

Ma'ana

Wannan kalma "zubar da jini" na nufin mutuwar mutum ta wajen kisan kai, yaƙi, ko dai ta wurin ta'addancin aiki.

  • Wannan furci ma'anarsa "zubar da jini," wato in jini ya fito daga jikin wani mutum daga ɓuɗaɗɗen rauni.
  • Wannan furci "zubar da jini" ana amfani da shi yawancin lokaci a nuna bazuwar kisan mutane da yawa.
  • Ana kuma amfani da shi a nuna zunubin kisa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "zubar da jini" za a iya fassara ta zuwa "kisan mutane" ko "mutane da yawa da aka kashe."
  • Ta wurin zubar da jini" za a iya fassara shi "ta wurin kisan mutane,"
  • "zubar da jinin marar laifi" za a iya fassara shi, "kisan mutane marasa laifi."
  • "zubar da jini kan zubar da jini" za a iya fasara shi, "suna ta karkashe mutane" ko "karkashe mutane na ta ci gaba-gaba" ko "sun kashe mutane da yawa suna kuma ci gaba da yin haka" ko "mutane suna ta ci gaba da kashe wasu mutane."
  • Wasu kwatanci da ake amfani da su kuma sune, "zubar da jini zai bi ka" za a iya fassara wannan haka, "mutanenka za su ci gaba da samun zubar da jini" ko "mutanenka za su dinga samun kisa" ko "mutanen ku za su dinga yaƙi da wasu al'ummai kuma mutane za su yita mutuwa."

(Hakanan duba: yankan jini)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 22:6-8
  • Farawa 09:5-7
  • Ibraniyawa 09:21-22
  • Ishaya 26:21
  • Matiyu 23:29-31

zuma, saƙar zuma

Ma'ana

"Zuma" wani danƙo ne mai zaƙi, da kauri,abu ne ingantacce,ƙudan zuma yakan samo furanni. Saƙar zuma wani faifai ne inda ƙudan zuma ke adana saƙarsa.

  • Ya danganta ga iri, zuma zai iya zama ruwan madara ja-ja ja-ja.
  • Akan sami zuma a daji, kamar a kogon itace ko duk wurin da zuma zai iya yin gida. Mutane na kiwon zuma domin samun ruwan zuma domin sha ko sayarwa, amma mai yiwuwa zuman da aka ambato cikin littafi mai tsarki zuman jeji ne.
  • Mutane uku na musamman da Littafi mai Tsarki ya baiyana sun sha zuma su ne Yonatan, Samsin, Yahaya mai Baftisima.
  • Wannan kalmar akan fi moron ta cikin salon magana domin baiyana abu mai zaƙi ko mai gamsarwa. Misali, Maganar Allah da farillai ana cewa "suna da zaƙi fiye da zuma."
  • Waɗansu lokutan maganar mutum akan nuna kamar tana da zaƙi kamar zuma, amma a maimakon haka yaudara ce dacutarwa ga waɗansu.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 14:1-3
  • Maimaitawar Shari'a 06:3
  • Fitowa 13:3-5
  • Yoshuwa 05:06
  • Litaffin Misalai 05:03

zuriya

Ma'ana

Wannan kalma "zuriya" ma'anarta waɗanda suka fito daga tsatso guda na mutane ko dabbobi.

  • Yawancin lokaci a cikin Littafi Mai Tsarki "zuriya" na da ma'anar "yara" ko "'ya'ya."
  • Wannan kalma "iri" wani lokaci ana yin misali da shi a maimakon zuriya.

(Hakanan duba: zuriya, iri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 17:29
  • Fitowa 13:11-13
  • Farawa 24:07
  • Ishaya 41: 8-9
  • Ayuba 05:25
  • Luka 03:7
  • Matiyu 12:34