1
Sai Dinah, ɗiyar Liya wadda ta haifawa Yakubu, ta fita ta tafi wurin 'yanmatan ƙasar.
2
Shekem ɗan Hamo Bahibiye, yariman ƙasar, ya ganta ya kuma cafke ta, ya ɓata ta, ya kuma kwana da ita.
3
Ya shaƙu da Dinah, ɗiyar Yakubu. Ya ƙaunaci yarinyar, ya kuma yi mata magana mai taushi.
4
Shekem ya yi magana da mahaifinsa, cewa, "Ka samo mani wannan yarinyar a matsayin mata."
5
Yanzu Yakubu ya ji cewa ya lalata ɗiyarsa Dina. 'Ya'yansa kuma na tare da dabbobinsa a saura, sai Yakubu ya kame bakinsa har sai da su ka zo.
6
Hamo mahaifin Shekem ya tafi wurin Yakubu domin ya yi magana da shi.
7
'Ya'yan Yakubu suka dawo daga saura sa'ad da suka ji batun al'amarin. Mutanen ransu ya ɓaci. Suka fusata sosai saboda ya kunyatar da Isra'ila ta wurin tilasta kansa bisa ɗiyar Yakubu, domin bai kamata a aiwatar da irin haka ba.
8
Hamo ya yi magana da shi, cewa, "Ɗana Shekem na ƙaunar ɗiyarka. Ina roƙon ka. ka bayar da ita a gare shi a matsayin mata.
9
Ku yi auratayya da mu, ku bayar da 'ya'yanku mata a gare mu, ku kuma ɗauki 'ya'yanmu mata domin kanku.
10
Zaku zauna tare da mu, za a buɗe ƙasar kuma a gare ku domin ku zauna ku kuma yi sana'a a ciki, ku kuma mallaki kaddarori."
11
Shekem yace wa mahaifinta da 'yan'uwanta maza, "Bari in sami tagomashi a idanunku, duk kuma abin da kuka ce mani zan bayar.
12
Ku tambaye ni komai yawan sadakin da kyautar da kuke so, kuma zan bayar da duk abin da kuka ce, amma dai ku bani yarinyar a matsayin mata."
13
'Ya'yan Yakubu suka amsa wa Shekem da Hamo mahaifinsa tare da zamba, saboda Shekem ya ɓata Dina 'yar'uwarsu.
14
Suka ce masu, "Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu bayar da 'yar'uwarmu ga duk wani wanda ba shi da kaciya; domin zai zama abin kunya a gare mu.
15
Sai dai a kan wannan matakin kaɗai za mu yarda da ku: Idan zaku zama masu kaciya kamar mu, idan kowanne namiji a cikin ku an yi masa kaciya.
16
Daga nan ne za mu bayar da 'ya'yanmu mata a gare ku, mu kuma zamu ɗauki 'ya'yanku mata a gare mu, mu kuma zauna daku mu zama mutane ɗaya.
17
Amma idan baku saurare mu ba kuka zama masu kaciya, daga nan zamu ɗauki 'yar'uwarmu kuma za mu tashi."