1
Saratu ta rayu tsawon shekaru ɗari da ashirin da bakwai. Waɗannan sune shekarun Saratu.
2
Saratu ta mutu a Kiriyat Arba wato Hebron, a ƙasar Kan'ana. Ibrahim ya yi makoki da kuka domin Saratu.
3
Sai Ibrahim ya tashi ya bar wurin da matarsa ta mutu, ya yi magana da 'ya'yan Het, cewa.
4
"Ni bãƙo ne a cikin ku Ina roƙo ku bani mallakar wurin maƙabarta a cikinku domin in bizne matattuna."
5
Sai 'ya'yan Het suka amsa wa Ibrahim cewa,
6
"Ka saurare mu shugabana. Kai yariman Allah ne a cikin mu. Bizne matattunka a duk inda ka zaɓa a maƙabartunmu, ba wanda zai hana maka maƙabartarsa domin ka bizne matattunka."
7
Sai Ibrahim ya tashi ya rusuna wa mutanen ƙasar, ga "ya'yan Het.
8
Ya yi musu magana cewa, "In kun yarda cewa in bizne matacciyata, sai ku saurare ni ku roƙi Ifron ɗan Zohar domi na.
9
Ku tambaye shi ya sayar mini da kogon Makfela, wadda ya mallaka, wadda yake a ƙarshen filinsa. Domin cikakken farashi ya kuma sayar mini da shi a gaban mutane domin ya zama mallakata, da maƙabarta."
10
Ifron kuma na zaune a cikin 'ya'yan Het, sai Ifron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan 'ya'yan Het maza da kuma duk waɗanda suka zo ƙofar birninsa, cewa,
11
"A'a shugabana, ka saurare ni. Na baka filin da kuma kogon dake cikinsa. Na baka shi a gaban 'ya'yan mutanena maza. Na baka shi domin bizne matacciyarka."
12
Sai Ibrahim ya sunkuyar da kansa ƙasa a gaban mutanen ƙasar.
13
Ya yi magana da Ifron a kunnen mutanen ƙasar cewa. "Amma in ka amince, inka yarda ka saurareni. Zan biya kuɗin filin. Ka karɓi kuɗi daga wuri na, ni kuma zan bizne mattaciyata a can."
14
Ifron ya amsa wa Ibrahim, da cewa,
15
"Ina roƙo, ya shugabana, ka saurare ni. Ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu na azurfa, mene ne wannan a tsakanina da kai? Ka bizne mamaciyarka."
16
Ibrahim ya saurari Ifron, ya auna shekel ɗari huɗu kamar yadda Ifron ya ambata a kunnuwan dukkan 'ya'yan Het maza, mudu ɗari huɗu na zinariya, bisa ga mizanin ma'aunin fatake.