1
To Sarai, matar Ibram, ba ta haifa masa 'ya'ya ba tukuna, amma tana da baiwa, mutumiyar Masar, sunanta Hajara.
2
To sai Sarai ta ce da Ibram, "Duba Yahweh ya hana mani 'ya'ya, ka je ka kwana da baiwata. Watakila na sami 'ya'ya ta wurinta." Ibram ya saurari muryar Sarai.
3
Bayan Ibram ya yi shekaru goma a Kan'ana ne Sarai ta miƙa baiwarta Hajara ga Ibram a matsayin mata.
4
Sai ya yi tarayya da Hajara ta kuwa yi juna biyu. Da taga ta yi juna biyu sai ta fara duban uwargijiyarta da reni.
5
Daga nan Sarai ta ce da Ibram, "Wannan kuskuren a kaina saboda kai ne. Na bada baiwata gare ka, kuma bayan ta ga ta yi juna biyu, sai aka sayar da ni a idonta. Bari Ubangiji ya shari'anta tsakanina da kai."
6
Amma Ibram yace da Sarai, "Duba ita baiwarki ce, tana ƙarƙashin ikonki, ki yi mata abin da kike tunanin ya fi kyau," Sai Sarai ta takura mata sosai, sai ta gudu daga gare ta
15 Hajara ta haifa wa Ibram ɗa namiji ta ba shi suna Isma'ila. 16 Ibram na da shekaru tamanin da shida a lokacin da Hajara ta haifi Isma'ila.