1 Sai Yahweh yace da Ibram "Ka tashi ka bar ƙasarka da danginka, da kuma ƙasar mahaifinka, zuwa ƙasar da zan nuna maka,
10 A kwai yunwa a cikin ƙasar, don haka Ibram ya gangara zuwa Masar ya zauna domin yunwar ta tsananta sosai a cikin ƙasar. 11 Da ya kusa shiga Masar sai ya ce da matarsa Sarai, "Duba na san ke mace ce kyakkyawa. 12 In Masarawa suka gan ki za su ce, 'Wannan matarsa ce; za su kuma kashe ni, amma za su bar ki da rai. 13 Ki ce ke 'yar'uwata ce, domin komai ya yi mani dai-dai saboda ke, don a bar ni in rayu saboda ke." 14 Sai ya zamana bayan Ibram ya shiga cikin Masar, Masarawa suka ga cewa Sarai kyakkyawa ce. 15 'Ya'yan sarki suka gan ta, suka kuma yaba mata a gaban Fir'auna, sai aka ɗauki matar zuwa gidan sarki. 16 FIr'auna ya kyautatawa Ibram saboda ita, ya ba shi tumaki, takarkarai, da jakai maza da mata da bayi maza da mata da kuma raƙuma. 17 Sai Yahweh ya bugi gidan Fir'auna da annoba mai zafi saboda Sarai matar Ibram. 18 Fir'auna ya kira Ibram ya ce da shi me kenan ka yi mini? Meyasa ba ka faɗa mini cewa ita matarka ba ce? 19 Meyasa ka ce ita 'yar'uwarka ce; don in ɗauke ta ta zama matata? To yanzu ga matarka nan. Ka ɗauke ta ku tafi." 20 Sai Fir'auna ya bada umarni game da shi daga nan suka sallame shi ya tafi, tare da matarsa da duk abin da yake da shi.